RA'AYIN ZUCI..!

Chapter : 4

by @zmchubado

RA'YIN ZUCI.... 

#the rivalry#

Duk abinda ya keyi ina lura dashi ta gefan idanuna don ban nuna alamar da zata sanar dashi nasan da wanzuwarsa a dakin ba, juyar da kaina gefe nayi ina wasa da shimfiɗaɗɗen zanin gadon dana shimfiida tun bayan fitarsa.
Sai da ya gama rage kayan jikinsa tsaf sannan ya daga kai ya sauke idanunsa a kaina, still ban motsa ba ina jin tasirin qwayar idannunsa a gabadaya ilahirin jikina. Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya tako gabana da nufin ya ranqwafa kamar yanda ya saba, cikin azama na miqe na fara qoqarin lalubar wayata wadda ke ajiye Saman bedside drower dina.
Kafin ya yi wani yunquri nayi saurin miqewa nabar masa dakin zuciyata a cike fal da haushinsa. A can qasan zuciyata na ce,"ko uwar me ze gaya min oho" na qare maganar ina jan gajeran tsaki wanda nake da tabbaci akan bejini ba.
Ina fita kai tsaye daya dakin na shiga na kulle qofa don bana buqatar ya biyo bayana, na dade a tsaye ina kai komo sannan nayiwa kaina masauki a kan qaramin gadon da aka qawata dakin dashi. Shiru nayi ina tunanin wanda ya kamata in kira akan matsalar dake cimin tuwo a kwarya, lumshe idanu nayi a lokacin da naji kaina Yana qoqarin sarawa. Nan take sai naji ina tausayawa duk wata mace da mijinta ke qoqarin qarowa abokiyar zama, banyi aune ba naji ruwan hawaye yana kwaranya a saman zagayayyiyar fuskata.
Komawa da baya nayi na kwanta sosai nayi balance. har lokacin ban ajiye wayar dake hannuna ba, na dade idanuna a lumshe suna zubar da hawaye sannan na budesu tar akan wayar, cikin nutsuwa na Fara qoqarin neman number din Ya Zainab. cikin yaqinin cewar zata Bani shawarar da zan samu mafita akan matsalar dake damuna.
Banyi qasa a gwiwaba na doka Mata kira Amma har ta katse ba tai picking call din ba, share hawayen nayi se kawai na lalubo number din Hajar nai dailing don ta Debe min kewar kadaicin dake tareda ni a wannan lokacin. Bugu daya nayi mata ta daga cikin nishadi ta ce,"Matar sir Yusuf. duk yanda akai kinje gidan mu ne ko?" Tayi maganar tana juya qwayar idanunta, cikin salon da ya zame Mata tamkar dabi'a
"Malama ni bazan kulaki ba. tunda kikai tafiya Baki min sallama ba" nayi maganar ina daure fuska tamkar tana Gabana ba alamun wasa a tareda ni.
"Hmmm bazaki gane ba Bilkisu. nima tafiyan yazo min ba shiri ne wllh shiyasa na tafi banyi miki sallama ba,But be patient Hajjajo, In sha Allah i will buy you something sweet idan Zan dawo Kaduna kinji?" 
"Uhmm Allah yasa karki Saba alqawari na San halinki sarai." na firta hakan cikin yanayi me dauke da kasala 
"Ke tsaya don Allah. ya naji muryanki haka What's wrong?"
"Ba abinda ke damuna yanayi ne kawai Hajar!" Na Fadi hakan ina lumshe idanu
"Fafah Are you okay ?"
Gabana ne ya yi wata irin faduwa Jin sunan da Hajar ta kirani dashi, Amma sai na dake ban nuna mata alamar komai ba na ce,"me kike zaton zai dameni Hajar?"
Gyara zamanta Hajar tayi tamkar tana zaune a gabana ta ce,"wllh idan nai rantsuwa bazanyi kaffara ba cewar akwai abinda ke damunki a qasan zuciyarki Bilqis, Amma tunda bazaki gayamin ba shikenan gobe ina dawowa gidanki Zan fara sauka,ko gida ba zanje ba sai kin sanar dani abinda kike boye min..." tana gama Fadin haka ta katse Kiran tana tunanin akan sauyin da tai katari dashi a cikin muryata. 
A dedai wannan lokacin Amna Khabir lere yar qanin babansu Hajar ta shiga dakin ta sameta, Zama tayi a gefan gadon da Hajar ke zaune. cikin nuna kulawa ta ce,"Hajar keda wa kikai magana a waya na ganki wani iri?"
Tsaki Hajar taja sannan tai wurgi da wayar a Saman gado ta ce,"wa kika sani in ba waccen damo Sarkin haqurin ba, wllh Amna I hate wannan sanyin halin na Bilqis with all my heart." Tayi maganar tana juya qwayar idanunta cikin Jin haushin Bilqis
"Shi haquri da kike ganinsa alkhairi ne Babba a rayuwar dan-adam Wanda ba kowa Allah kema baiwar samunsa ba. Shin Bakya tunanin wannan baiwar haqurin da ubangiji ya bawa Bilkisu a rayuwarta shine dalilin da yasa mutane suke qaunarta?" Amna ta Fadi hakan tana tsare Hajar da fararen idanunta.
"Mtswww to sai akai yaya don mutane na Sonta? Duk son da suke Mata ai bai Hana wayanda suke tareda Ita su cusguna Mata akan abinda ba ita zata bawa kanta ba. Ke!, na rantse da girman Allah gobe a gidanta zanyi branch sai naci uwar wannan qanwar mijin nata, shegiyan yarinya mummuna, don na dade da fahimtar  ita ce matsalar yar uwata" tayi maganar cikin tsantsar fitina.
"No Hajar! ni'a nawa ganin zuwanki gidanta  ba shine maslaha ba, kina daga gidama zaki iya bata shawaran da zai  zama mafita ga matsalolinta, ba se kinje kin tayar mata da fitina a gidanta ba. Nasan halinki sosai wannan yasa nake Jin tsoron zuwanki gidan mutane ba lallaine a ƙare ta lalama ba." Cewar Amna
"Ai sekita jin tsoron Amma wllh sai naje in yaso duk wacce za'ayi ayi. Ke nifa yanda nake jin Bilkisu a raina zan iyayin komai ga duk wanda ya bata mata, saboda nasanta fiye da kowa a familyn mamana, bayan haka she is my best friend na san kin sani."
"kije sai kin dawo amma ina jiye mikin tsoron kar masifanki ta zama sanadin da zata kashe Auren soyayyar da kaf danginku babu kamarsa, abin kunya ma wai fada kike akan wadda taqi dan uwanki na jini ta zabi wani akansa." Amna ta firta hakan cikin jin zafin yanda Hajar ke fifita qaunar da takewa BILKISU akan ta.
Shiru Hajar tayi tana kallon Amna cikin madaukakin mamakin jin maganarta ta qarshe, ada tayi tunanin shawarar Arzuqi take bata, Amma wannan maganar da tayi tasa ta fahimci magana take qoqarin gasa mata. Idan kuwa ya tabbata maganar take son gasa mata wllh ba zata saka ido ta kalleta kawai ba, sai ta tabbatar da cewa ita ma ta gasa mata maganar da tafi wadda ta gaya Mata zafi da ciwo. Don haka ta dubi Amna duba irin na tsanaki ta kasa cewa komai.
Irin kallon da Amna taga Hajar na watsa mata ne yasa tayi far da idanunta ta ce"Malama ya naga kina min kallon qarqanci sai kace nice Faridah Attahirun?"
Ɗaga mata Hannu Haajar tayi cikin jin haushi ta ce"Dalla malama karki gayamin maganr banza. wai jimami kike taya yar uwata kokuma abinda ya jima da wucewa kike qoqarin dawo dashi?"
Hajari tayi maganar cikin qufula.
Juya zagayayyun idanunta Amna tayi sannan tayi murmushi ta ce,"ikon Allah shikenan daga magana Se cibi ya zama qari kamar dama Jira kike nayi magana?"
"Ai kece naji kina qoqarin wuce Gona da iri a maganganunki, sai kace Bilkisu ce ta hana yaya khadir ya aureki." Cewar Hajar tayi maganar cikin san ta cusawa Amna haushi
Hade rai Amna tayi tareda miqewa tsaye tana kallon Hajar ta ce,"daɗin abin ban tilasta masa akan dole sai ya soni ko ya aureni ba, balle ki Bude bakinki na rashin kunya ki zageni."
"Hhhhhhh. ai ko baki bude Baki kin roqa ba, idanunki da baqin nacinki a kansa sun dade da tona Miki Asiri, ta hanyar baiyana gaskiyar abinda kika ɓoye a ranki practically. Don haka zefi miki alkhairi ki gaggauta dakatar da wannan borin kunyar taki, idan ba haka ba Kuma wllh mu saka qafar wando daya dake...." Cewar Hajar
"To uban wa yake tsoron saka qafar wando daya dake din Hajar?" Amna tayi wannan furucin cikin daga murya
"Hmmm da alama Amna Khabir lere kina qoqarin gaiyatoma kanki rikicin da ze janyo miki dana sani a rayuwarki. wllh idan ki kai gangancin zagin ubana Zan ajiye zumuncin dake tsakanina dake a gefe nai miki rashin mutunci." Hajar ta fadi haka tana kallon tsakiyar idanun Amna cikeda rikici.
Sosai ran Amna ya yi bala'in Baci. cikin fisata ta yunquro ta ce, "Zanso ki ajiye alaqar jinin dake tsakanin mu a gefe kiga idan nima Zan raga miki. kamar yanda kike Jin tashen rashin kunya da fitsara to Nima haka nake Jin kaina."
"Kai! Kai!! Kai!!! Bana son shashanci kunji na gaya muku. Hayaniyar uban me kuke haka?" Gwaggo ta dakatar dasu ta hanyar Fadin haka.
Shiru su kai aka rasa wanda zeyi magana, Zama gwaggo tayi tana binsu da kallo daya bayan daya, sannan ta numfasa ta ce,"amma da hankalinku da tunannin ku lukema junanku irin wannan dibar albarkan?" 
Har lokacin babu wadda tayi magana wannan yasa gwaggo ta kwantar da murya ta ce, "babu alkhairi a cikin tayar da zaune tsaye komai qaqantarta, balle ace kuna iqirarin cin mutuncin juna a tsakanin ku. Ubangiji shi yace muyi zumunci a don haka ko waccen ku tana da haqqi akan yar uwarta, kar in qara ji kuna ambata kalmar cin mutunci a tsakaninku." Gwaggo ta fadi hakan tana tsaresu da idanu tareda yi musu nuni da su zauna a gabanta.
Ba musu suka zauna ko wacce ta maida abinda yar uwarta tayi Mata, nan take gwaggo ta hau su da fada Jin dalilin da ya haifar da saɓanin ba wani abin Azo a gani bane, shiru tayi na tsahon lokaci sannan ta daga Kai ta dubesu ta ce,"Gabadayan Ku dangin juna ne to Akan wani dalili zaku gaiyato abinda ze kawo tangarda a zumuncin Ku?" Gwaggo ta jefa musu wannan tambayar
Rasa Wanda zece qala a tsakaninsu akayi, don haka ta kwantar da harshe ta shiga yi musu nasiha akan fa'idar haquri da kuma amfaninsa. a qarshe ta ce," duk ku tashi ku bani waje."
Miqewa Hajar tayi a fusace tana gunguni ta ce,"wllh muddin tana san zama lfy dani karta qara zagin Bilkisu ta hanyar azancin maganar da ta Saba yima mutane." Tayi maganar tana ficewa daga dakin sai hura hanci take kamar zata kai duka don haushi.
Kasa motsawa Amna tayi daga inda take tsaye saboda yanda maganar Hajar ta girgizata, gabadaya bata tsoron uban kowa muddin aka taba dangin mahaifiyarta. Musammam data  fahimci  da biyu Mahaifiyar Amna da Hajia maryam sukeyin wasu abubuwan don kawai suci zarafin familyn mamanta...
Bayanta gwaggo tabi da kallo harta bace Mata da gani, sannan ta sauke ajiyar zuciya ta ce,"like father like daughter. gabadaya halinta irin na ubanta Aliyu ne, rashin tsoron da zafin ran ma duk nasa ne ta debo." Ta qare maganar tana murmushi.
da kyar Amna ta iya hadiye yawun bakinta sannan ta koma ta Zauna dabas a gefan gadon, da Hajar ta tashi. bata San lokacin da wasu zafafan hawaye suka Fara kwaranya a Saman kumatunta ba. Tabbas yanzu ta yarda ba zata iya fada da Hajar Aliyu lere ba, ta ko wani fanni tafi qarfinta balle Kuma Bilkisu, yarinyar da take jinta a zuciya har yau ta kasa manta yankan qaunar da tayi Mata a shekarun baya.
****
A nawa bangaren kuwa.
bayan mun gama waya da Hajar, shiru nayi ina nazari akan rayuwata ta baya. Lumshe idanu nayi wanda ya zama daya daga cikin dabi'u na, a duk lokacin dana kasance ni kadai Bani da wani aiki Wanda ya wuce hakan. Cikin mintunan da bazasu gaza biyar ba na afka cikin duniyar tunanin abubuwan da suka Jima da shudewa. 
Na jima a cikin wannan hali sannan na miqe jiki ba qwari na shiga toilet nayi wanka, sannan na fito na Zauna gaban mirror na caba ado na ban mamaki, kafin na miqe na feshe jikina da turaruka na musamman wayanda na Saba amfani dasu tun ina budurwa, sannan na kawo lafiyayyiyar humrata wadda na siya a gurin Asmyzee na shafa. Babu abinda ke tashi a jikina sai qamshi tamkar nayi barin tulare, wata simple doguwan riga na zaro a cikin kayana,wadda na siyoma kaina lokacin da mukaje aikin haji dasu ya Na'imah na saka, sosai rigan ya amshi kyakkyawan jikina tamkar dama can dan ni aka samar da ita.
Cikin nutsuwa nake taje cikakken gashin kaina Wanda bashi da laushi ko kadan, ina yi ina hutawa a haka na Gama tsaf na daureshi da bands, sannan na Dora hula akai na fita falo na hakimce akan kujera na kunna kallo. Tsaki naja lokacin da naga film din da ake haskawa a tashar beyi dedai da ra'ayina ba, sai kawai nai connecting TV din da wayana nasa wani kdrama Mai suna Our blooming wood na fara kalla.
Duk da bana cikin yanayi Mai dadi hakan bai hanani Jin daɗin film din ba, ina tsaka da kallo naji cikina ya Fara qara cikin sauri na mike nayi kicin. Kai tsaye firinji na bude na fito da kankana da Apple na yankasu a cikin karamin bowl, na zuba musu madaran gari me yawa akai, sannan nasa cokali na koma falo na Zauna. Ina sha ina kallo har na shanye tass sannan naji alamun Bude get.
Har lokacin ban motsa daga inda nake zaune ba naji tsayuwar motarsa, ajiyar zuciya na sauke ina jiran ya shigo falon Amma naji shiru be shigo ba, kamar wadda aka mintsina haka na miqe da sauri na isa jikin window din dake falon na daga labile ina leqensa.
Gabana ne ya yi wata irin dokawa tamkar zuciyata zata dako tsalle ta fito, cikin hanzari na saki labulan na koma da baya ina maida numfashi. Zama nayi dabas akan kujera na qurawa TV idanu cikin tsananin son na boye raunin kishin dake ƙoƙarin halakani, a haka zuciyata taci gaba da harbawa daki bayan daki.
A wannan lokacin babu kalar abubuwan sharrin da zuciyata bata aiyana min akan Yusuf da Aisha ba. wani kakkauran yawu da daci ne ya Taru a bakina, a haka suka shigo falon suna hira cikeda fara'a a tsakaninsu.
Ko kallonsu ban iya daga kai nayi ba na maida hankalina gabadaya ga TV, tsayawa ya yi turus yana kallona don beyi tsammanin ganina a wannan lokacin ba, daga idanu nayi cikin wata irin dakiya da nuna halin ko in kula da abinda ya aikata na kalleshi nayi murmushi na ce,"Ango da Kanka har ka dawo Kenan ?" Nayi maganar ina janye idanuna daga Kansa, gudin kar ya hango raunin dake boye cikin zuciyata a idanuna.
"Eh wllh. yanzu na dawo muka haɗu da Aisha a bakin layin nan zata gangaro shine na dakko ta." Yayi maganar cikin son yaji irin amsar da zata fito daga bakina.
Miqewa nayi tareda daukar bowl din dana Gama Shan fruits, sannan na dau remote nayi switching TV din tareda daukar wayata na ce," sai naga kamar ban tambayeka wannan ba, why kake son dole seka bani labarin abinda be shafeni ba?" na fadi hakan ba tareda na kalli inda yake tsaye ba.
Jin ya gaza bani amsa ne yasa na fara tafiya cikin nutsuwa nabar masu falon mamaki kwance a Saman fuskarsa. Juyawa ya yi da sauri zebi bayana Aisha Sulaiman tayi saurin Shan gabansa cikin Jin haushi Mai tsanani ta ce,"akan wani dalilin zaka bita alhalin Kai da Kanka kaje gida ka dakkoni?" 
But you know that I won't come to your house don zuciyata tana son hakan, so why are you starting a fight since we're not married? Wannan idan na aureki Allah ne kadai ya san irin fitinar da zaki dinga hadamin a gida.
Tunda ya fara magana take binsa da kallon rainin hankali, sannan ta gyara tsaiwa ta ce,'ya yusuf na tabbata kafi kowa sanin halina da kuma irin abinda zan iya aikatawa idan kazo min da rainin hankali. Don haka ka tsayar da wannan drama din naka haka saboda ba auren alfarma zaka daura dani ba." tayi maganar tana jifansa da wata uwar harara.
Kasa ce mata komai ya yi ganin haka yasa ta raba ta gefansa ta wuce. Ya jima tsaye a gurin a haka na fito kitchen na samesa, ko kallonsa banyiba na wuce daki tareda mirza key nabi lafiyar gado.
Hannu nasa na dauki wayata na fara qoqarin kiran number din Ya zainab, abin takaici har wayar ta gama ringing ba tai picking ba.
Mirginawa nayi sannan na qara danna Mata wani sabon kiran cikin ikon Allah ta dauka, cikin cool voice dinta wadda ke cike da nutsuwa ta ce,"Assalamu'alaikum"
Ajiyar zuciya na sauke tareda gyara kwanciya a tsakiyar gadon na ce,"ya Zainab ina yini?"
"Lafiya lau matar Yusuf ya kike and ya su Hajiya?"
"The are all fine Alhamdulillah." na firta hakan muryata na shirin sarqewa
"Bilqis, are you okay? what is wrong with you Eh?" Ya Zainab ta jero tambayar cikin damuwa, tana qoqarin sauke Ahmad daga Saman cinyanta.
Yawun bakina na hadiye da kyar zuciyata babu dadi na bude Baki kamar me koyan magana na ce," wai dama uhmm wai Yusuf ne zai qara aure!" nayi maganar hawaye na zubowa daga idanuna.
Shiru ya Zainab tayi tana juya girman lamarin a cikin Tata zuciyar, ta dauki lokaci Mai tsayi sannan ta gaiyato jarumtar da take qoqarin rasawa tayi breaking shirun ta ce," ke da shi ya sameki ya gaya miki cewar ze qara aure, kokuwa wani ya turo ya sanar dake?" tayi maganar in a calm voice.
Lumshe idanu nayi tamkar marainiyar da ta rasa uwa da uba na ce "Hajiya said that he remarried because I could not give birth to him" nayi maganar ina rushewa da wani irin kuka wanda ya yi nasarar birkita lissafin ya Zainab gabadaya. Kuka nakeyi sosai cikin yanayi irin na nema agaji daga gareta, a qalla sai da nai mai isata ba tareda ta dakatar dani ba. 
Mintuna biyar ne suka gifta a tsakani sannan ya Zainab ta Fara magana cikin sanyin murya, cikin alamar rarrashi da ban Baki ta ce,"koda wasa Kada ki bari maganar Hajiya ta daga miki hankali Bilqis, because ba dake take fada ba, tanayi ne da ubangijin da ya halicce mu gabadaya. dalilin da yasa nace haka shine ubangiji shike bada Haihuwa ga wanda yaso, sannan ke baki isa ki bama kanki Haihuwa ba. ina so ki sama ranki cewar indai kinada rabon Haihuwa a duniya wllh zaki Haifa, don haka karki qara kuka akan zanan qaddararki, Allan daya halicceki ya fiki sanin dalilin da yasa ya yi miki wannan jarrabawar Fafah!" 
Sosai jikina ya yi sanyi da irin nasihar da take min akan rayuwa, jin hakan yasa ya zainab taci gaba da rarrashina ta sigar nasiha da Jan hankali akan yarda da qaddara.
Shawarwari tai ta Bani wayanda suka sanyaya wutar kishin dake cina a Rai sannan ta tsagaita. Har zan kashe wayar ya Zainab ta kira sunana a sanyaye ta ce,"Bilqis!"
Kasa amsawa nayi don sosai zuciyata tayi rauni, gajeran murmushi ya zainab ta saki har ina iya jin sautinsa  sannan ta ce,"kada ki karaya akan duk abinda rayuwa zatazo miki dashi Fafah, saboda Ubangiji fa'alullimaturid ne shi kadai ke bada duk wani arzuqin duniya da lahira ga wanda yaso. So Idan kina da rabon Haihuwa a duniya wallahil'azim se kin haihu"
Nimfasawa nayi tareda share hawayen dake kwaranya a idanuna. Babu abinda nake saukewa sai ajiyar zuciya, shiru ya zainab tayi tana sauraren yanda nake sauke numfashi, sannan tayi murmushi ta ce," stop crying, you will give birth to Yusuf Attahiru in sha Allahu kinji Bilqis."
Rufe fuskata nayi da sauri ina murmushi sannan ya Zainab tayi min sallama, bayan ta tabbatar da cewa na samu kwanciyar hankali. haqiqa Allah ya yima ya Zainab baiwa me tarin yawa,wannan yasa nake qaunarta har cikin Raina, Sam bata da hayaniya ko kadan, irin mutanan nance waƴanda ubangiji ya yi musu baiwar iya magana da sarrafa harshe. Idan har zaka saurareta to wllh seka samu kalmar da zata amfaneka a cikin maganarta.
Ajiye wayar nayi a gefe still ina kwance ban tashi ba, kamar daga sama naji ana qoqarin bude qofar dakin. Nan take naji zuciyata ta buga da qarfin gaske, ba shiri na miqe na zauna ina zare idanu.

#zainab 
#muhmmd
#chubado
#vote
#comments 
#share pls
@***