RA'AYIN ZUCI..!

Chapter: 5

by @zmchubado

RA'AYIN ZUCI...

#The unexpected response#

Ina kwance ban motsa ba har ya gama bude qofar dakin ya shigo, jikina a mace na dauke ganina daga barin kallonsa,ya jima a tsaye sannan ya tako a hankali ya fara qoqarin rage kayan dake jikinsa.
Ganin haka yasa na miqe a hankali na nufi qofar fita daga dakin cikin.
"Bilkisu!" Ya kirani cikin sanyi da taushin harshe.
Tsayawa nayi chak na kasa motsi jin yanda ya ambaci sunana kai tsaye. ban juyo ba sai da na tabbatar da na kori mamakin da ya wanzu akan fuskata sannan, Murmushin takaici nayi sannan na ce,"na'am!"
Tsareni ya yi da idanu kimanin gushewar wasu mintuna sannan ya ce,"wannan sabuwar dabi'a da kika tsiro da ita bana jin zata kawo maslaha a tsakanin mu, idan kina da matsala dani zefi kyau ki fuskanceni a madadin ki tsaya kina boye bacin ranki ta hanyar gujemin."

Wani abune ya tasomin daga cikina zuwa wuyana, nan take naji wani tuquqin baqin ciki da bacin rai suna mamayar zuciya da gangar jikina. Murmushin takaici na qara wadata fuskata dashi a lokacin dana tuna haurawar da mukai dashi a daran jiya. don haka na danne bacin raina cikin qarfin hali dana zuciya na nitsa kwayar idanuna cikin tasa na ce,"hadin Aurenku da Aisha da fari na karbeshi a matsayin umarnin da Hajiya ta baka. amma daga baya sena fahimci akwai kyakkyawar alaqa a tsakaninku, yanayin dana ganku a ciki ya gama fallasa min gaskiyar abinda ke boye a bayan zukatanku." nayi maganar idanuna suna cikowa da ruwan hawaye.

Numfasawa nayi tareda kai hannu na share qwallar data fara zubowa ta tsakanin fatar idanuna, sannan naci gba da cewa,"abinda na gani kwance a tsakiyar idanunka lokacin da ka fito daga mota yasa na fahimci wasa kake da intelligence dina, sannan kayi min qaryar cewa ba zaka hada son da kake min da wata diya mace a duniya ba. Hmmm amma sai gashi tun bamuje ko ina a zamantakewa ba naga irin tausayawar da kake min kwance cikin idanunka a lokacin da kake kallon tsakiyar idanun Aisha Sulaiman!

Yusuf, tell me how can I share the same shade with you?" nayi maganar ina sakin kuka dana jima ina dannewa a qasan ruhina.

Jikinsa ne ya yi sanyi lokaci guda ya ji nadamar abinda ya aikata tana mamayarsa, cikin rashin guzari ya tako gabana ya tsaya akan sawayensa. Cikin wani irin sanyin jiki wanda ban taba ganinsa a ciki ba ya kai hannunsa ya riqe kafaduna. in a weak voice ya ce,"kada ki Dora zuciyarki akan Zargi Bilkisu, wllh abinda nakeji gameda ke a zuciyata babu wata diya mace data isa ta ruski matsayinki a raina har gaban abadah." ya yi maganar yan qoqarin kamo hannuna ya Dora a saitin zuciyarsa, wadda ke bugawa daki bayan daki.

Janye hannuna nayi da sauri har lokacin ban dena zubar da hawaye ba na ce,"wllh idan na rantse ba zanyi kaffara ba cewa irin son da kakemin irinsa na gani kwance a tsakiyar idanunka lokacin da kake kallonta. don Allah Yusuf kada kayi amfani da raunina ka cutar da yarda ta akanka. Na san kana da dalilin qara aure tunda ban baka abinda kafi buqata a rayuwarka ba, idan har zan maka adalci to bai kamata in hanaka qarin aure saboda son zuciyata ba."

Bai ce min komai ba ya janyoni jikinsa ya rungumeni qam yana shafa fatar bayana alamar rarrashi, a wannan lokacin kuka nake sosai ina jin zafin kishinsa yana qara huda min zuciya.

Ranqwafawa ya yi tareda Dora bakinsa a saitin kunnena ya ce,"kin min abubuwa da yawa Bilkisu, you are a darling not only for me, ke abar so ce ga kowa saboda tarin alkhairanki." Ya fadi hakan yana qara Matsoni cikin jikinsa. A haka wannan ranar ta gushe yusuf yana kasheni da dadin bakinsa irin nasu na maza.

Washe garin ranar ban samu damar Dora komai ba sabida ciwon kan dana tashi dashi, ko iya bude idanuna banayi sabida yanda kan ya matsamin da ciwo. Ganin haka yasa Yusuf ya shiga kitchen ya sama mana abinda da zamuci me dan sauqi, ruwan lipton ya dafa mana wanda yaji kanufari da chitta, banda qamshi babu abinda ke tashi, sannan yay mana tosting bread ya kai mana raining. Da taimakonsa na yunqura na shiga toilet nayi wanka tareda wanke bakina, sannan na fito ina dafe goshina wanda nakeji kamar ze rabe gida biyu.

Yana ganin na fito ya nufoni with care yana min magana qasa-qasa, wanda gabaɗaya maganar tambayace yake min akan yanda nakeji.

Sam ban bashi damar samun amsar da yake fatan ji daga gareni ba, na janye jikina ba tareda na bashi damar shigemin kamar yanda naga take-takensa ba na ce,"thank u but baran iya zuwa falo yanzu ba, infact ma bana jin zan iya cin wani abu." Na firta hakan a wahalce ina qoqarin hayewa gado.

Tsareni yayi da ido ganin irin kallon da yake min ne yasa naja bargo na rufe jikina gabadaya. Ya jima a tsaye sannan ya shiga toilet yayi wanka ya fito, a gaggauce ya gama shiryawa don ya makara sosai. Agogon fatarsa dake ajiye saman dressing mirror ya dauka ya daura tareda daukar jakar laptop dinshi ya matso jikin gadon.

Zame bargon yayi sannan ya kai hannu goshina ya taba, ajiyar zuciya ya sauke sannan ya juya ya fita. Kai tsaye daining aria ya nufa ya cika cikinsa sannan ya nufi bangaren hajiya don ya suka gaisheta, yana shiga falon ya tsaya yana bin ko ina da kallo. abin takaici ko ina datti hatta kwanukan da sukaci abinci jiya suna zube a gurin Faridah bata kwashe ba, hakanan se yaji ransa ya Baci musamman da ya dag kai ya kallesu yaga suna zaune akan kujera suna danna waya.

Daure fuska yayi ya dubi Faridah ya ce,"Binkisu bata da lafiya malama ki ajiye wannan wayar ki tashi ki samar muku abinda zakuci, tunda ke ba abinda kika iya se danna waya" Yayi maganar ransa a ɓace 

"Munafuka ba wani rashin lafiya da takeyi, tsabaragen munafusci ne da son jiki yasa ta kwanta a daki da sunan ciwo. Kai kuma ba kunya ba tsoron Allah ka kwaso uban tsayi kana gaya mana bata da lfy, to idan ma bata da lafiyar ni ina ruwana? Abinci ne wllh seta fito ta dora mana ko zata mutu" Hajiya ta fadi hakan tana galla masa harara

Bece mata komai ba se qura mata idanu da yayi yana mamakin maganganun da take firtawa, sauke idanunsa yayi a hankali sannan yasa kai ya fice don be shiryawa fitinar hajiya ba. Jikinsa ba qwari ya fita harabar gidan zuciyarsa ba dadi, cikin Dan guzarin da yay masa saura ya kai hannu ya bude murfin motar ya shiga ya zauna. Abin mamaki se ya samu kansa da kasa tsinana komai, tausyin irin rayuwar da Bilkisu keyi a tsakanin mahaifiyarsa da qanwarsa yay masa bake-bake a zuciya.
"Anya nayiwa Bilkisu Adalci dana bari aka maida ita tamkar baiwa a qarqashin inuwar Aurena kuwa?" Yusuf yayma kansa wannan tambayar cikin tsananin jin kunyar kansa.
Lumshe idanunsa yay a hankali yanajin yanda zuciyarsa ke takurewa a tsakanin qirjinsa. "Ya Allah ka dedaita tsakanin Hajiya da matata Bilkisu." Ya firta hakan cikin sanyi jiki sannan ya kunna motar ya nufi get. Tun kafin ya qarasa bakin get din Malam Ayuba ya bude masa qofar ya fice,



Tun bayan fitarsa ban qara jin motsin komai ba bacci mai nauyi ya daukeni. Ban farka ba se wajan qarfe daya na rana (1:00pm) Alhamdulillahi lokacin ciwon kan ya dan lafamin don haka na sake yin wanka na dauro Alwala na fito na kabbara sallar Azahar.
B

ayan na idar na dade ina addu'ar samun mafita a dukkan al'amurana sannan na miqe na fara qoqarin gyara dakin, mintuna goma na dauka sannan na kammala na kunna electric burner nasa tularen wuta.



Riga mara nauyi na janyo a drower na saka sannan na fita falo nan ma na fara qoqarin gyarawa, ina tsaka da kakkabe kujerun falon naji jiri ya fara qoqarin daukata. Durqushewa nayi saurin yi a qasan carpet ina maida numfashi, a cikin wannan yanayin naji almar an bude get.

Ba jimawa naji qarar mota ta shigo harabar gidan, ni dai har lokacin ban motsa ba ina zaune a inda nake. A hankali nake jin qarar takun takalmi alamar gab ake da shigowa falon, a nitse tasa hannu ta mirza handle din dake jikin qofar bakinta dauke da sallama.

Jin muryar Hajar kamar a mafarki yasa na daga kaina da sauri ina kallon Direction din qofar fuskata ɗauke da murmushi, sanye take cikin doguwar rigar shadda light purple wadda ta zauna a kyakkyawan jikinta tai mata dass.



Da sauri ta qaraso inda nake tasa hannu ta dagoni tana mai tsareni da fararen idanunta ma'abota kwarjini, murmushin dake fuskarta ne ya dauke a lokacin dataji jikina yayi zafi rau.

Zama mukayi akan three seter din dake gefena still tana kallon fuskata bata dena ba ta ce," Fafah meke damunki naji jikinki da zafi haka?" Ta jera min tambayar tana kai hannunta gefan fuskata.

Zame hannunta nayi daga fuskata ina murmushi na ce," kaina ne ke ciwo wllh, amma dana ganki sai naji har ciwon ya tafi."

Juya idanunta tayi sannan ta ce,"good ya taimaki kansa daya qyalemin ke ki huta." Cewar Hajar 

Dariya mukayi gabadayan mu, sannan na miqe na ce,"let me bring water for u twiny."

"No bari kawai! abinci nafi buqata yanzu hope kina da kifi a freezer." 
"No it has finished sai dai kaza." Na bata amsa ina kallon fuskarta

"OK barin tashi na shiga kitchen din muga abinda zan iya girkawa. Don wllh ba zan wahalar da jikina ba dedai cikina zan dafa." Tayi maganar tana galla min harara.

Sarai na gane me take nufi amm ban tanka mata ba, mayafin jikinta ta cire tareda jefa jakanta kan kujera. Seda ta qarasa min sharan falon tayi mopping sannan ta shiga kitchen, ina jinta tana haɗa abinci ni kuma na koma daki.

Awa daya da rabi ne ya dauketa ta kammala girkin, sannan ta fito da abincin data kwashe a qaramin flacks ta kai mana daining. Sannan ta qara komawa ta juyo pepe chicken din data hada a flet ta kai, seda ta zauna ta cika cikinta sannan ta miqe tabar ragowar a gurin bayan ta rufe komai.

Kai tsaye bedroom dina ta nufa ta sameni a kwance, "twiny ya kamata ki tashi muje Asbiti." Ta yi maganar tana tsareni da idanu

"No twiny ba Se naje Asbiti ba ina shan magani zai dena ciwon."

"Ok" ta firta a gajarce don ta san taurin kaina ba lallai na ji duk abinda zata gayamin ba tunda na kafe.
Ganin tayi shiru ne ya sa na fahimci taji haushin amsar dana bata, don haka nai murmushi na ce,"am sorry twiny wllh ciwon kan yayi sauqi."



"It's ok naji. Amma dai ki tashi muje kici abinci, idan kuma ba kya son abincin seki sha tea ko?" Ta fadi hakan tana kallona with care.



Ganin naqi motsi ya sa tafita daga dakin taje ta jero abincin data kai daining a babban tray, sannan ta hado da falacks din ruwan shayin da Yusuf ya hada kafin ya fita ta kawo min dakin. Ba yanda na iya haka na miqe na sauka daga gadon na zauna a qasa ina kallonta da lumsassun idanuna na ce,"to ki hada min tea din mana."

Wara idanunta tayi sannan tai dariya ta ce,"this is serious a taqaice dai ni zanma sir Yusuf jinyar."

Tabe baki nayi bance komai ba don na lura niman magana take dani, ganin naqi magana yasa ta sauka ta zuba min lipton din a cup ta miqa min. A nitse na karba na ce,"thank you twiny."

Shiru ne ya biyo baya harna gama shan tea din, sannan ta zuba min abinci kadan a flet ta miqa min, abin mamaki ina fara ci sai naji abincin yamin dadi fiye da zatona, don haka na bude ciki na cinye tas sannan na miqa mata flet din na ce,"Twiny a qara min."

Dariya tayi sannan ta juye min ragowar abincin dika a flet da sauran naman, duk abinda nake idanunta na kaina, kamar an fisgo maganar dake maqale a bakina na ce,"twiny Yusuf Aure zai qara. Uhmmm ina nufin wai kishiya zemin."

"Ah haba! wllh wasa yake miki, wani irin aure kuma twiny shekararku nawa da aure da zeyi wannan tunanin?" Hajar ta fadi hakan tana tsareni da idanunta wayanda ke cike da tashin hankali.

"Haka hajiya tace twiny. Amma jiya na lura da wani al'amari a tareda yusuf wanda ke barazanar tarwatsa min zuciya, Twiny Yusuf qarya ya min cewar auren umarni zeyi. Amma wllh jiya ra'ayil'aini naga soyayyar Aisha kwance a tsakiyar idanunsa, ba wani banbanci tsakanina da ita a zuciyarsa adadin irin so da tausayin da yake min wllhi irinsa itama ya ke mata, Twiny na shiga uku ji nake kamar abinda mama ke guje min ne ke shirin faruwa dani!" Nayi maganar ina fashewa da kuka. 

Jikin Hajar ne ya yi masifar sanyi gabadaya ta rasa me zatace. Numfasawa tayi da wani irin cool voice ta ce,"Kiyi Haƙuri twiny karki zama daya daga cikin masu bitilcewa qaddara sabida ba'asin data zo miki da ita. Aure ibadah ne don yusuf ya qara aure ba aibu bane middin baze wulaqanta mana ke ba!" 

"Twiny bana baqin ciki da auren Yusuf saboda bana cikin matan da suke adawa da umarnin Allah. Amma ina matiqar jin tsoron qalubalan da zan fuskanta a lokacin da ya aurota ya kawota cikin gidan nan, na san kinfi kowa sanina don haka ko ban bude baki na gaya miki matsalata ba na san zaki iya fassara shiruna ta hanyar motsina." Nayi maganar ina kuka sosai tamkar zan hadiyi zuciya na mutu.

Shirune ya ratsa gurin ba'ajin sautin komai se na kukana, Hajar ta bude baki kenan zatai magana aka fara buga qofar dakin. Bam tsagaita da kukan da nake ba Hajar ta miqe a hankali ta isa jikin qofar ta bude, kallon kallo suka shiga bin juna dashi sannan farida ta dauke kai ta ce,"ina me dakin?"

Banza Hajar tayi mata don bata isheta kallo ba balle ta samu arziqin samun amsa daga gareta. Cikin nutsuwa ta maida qofar ta rufe sannan ta dawo cikin dakin ta zauna, hakanan sai taji ranta ya masifar Baci, don haka ta dora qafa daya kan daya ta fara kadawa a hankali alamar ƙiris take jira ta hau bala'i.

Ganin yanayinta yasa naji zuciyata ta buqa da qarfi don sa rai nasan wacece ita, ɓoyayyiyar ajiyar zuciya na sauke tareda sirranta tsorona bayan na share hawayena na ce,"Twiny waye?"

Tabe baki ta yi cikin nuna halin ko in kula ta ce,"waccan rasa kunya began tankan ce."

Abin mamaki sai mukaji an sake buga qofar kamar za'a karya.

A nitse na miqe na isa jikin qofar na bude idanuna akanta bance komai ba, se dai a wannan karon fuskata a daure take babu alamun wasa. Faridah wadda ke tsaye tana taunar cingum ta juya idanunta cikin alamun raini da wulaqancin data saba min ta ce,"Hajiya ta ce ki fito ki sama mana abinda zamuci." tayi maganar with confidence 



Abin mamaki sai kawai naji murmushi ya subuce min, al'amarin daya jefa kokwanto a zuciyarta kenan. ba tareda na ankara ba naga Hajar a gabana tamkar wadda aka jefo, kafin nayi wani yunquri tuni har ta isa gaban Faridah ta tsaya. hannu tasa ta turata baya cikin dakakkiyar murya irinta me baiyana kashedi ta ce,"It seems that her patience is what gives you the opportunity to despise my sister right? To ki koma ki gaya mata bilkisu tafi qarfin ta Dorawa qartin yan mata zauna gari banza irinku abincin da zakuci." tayi maganar tana watsa mata harara wadda tasa hanjin cikinta kadawa.

Amma sabida tsabar qarfin hali irin na farida bata fasa maidawa Hajar martani ba, al'amarin daya baqanta zuciyar Hajara Aliyu Lere ta wanke fuskar Faridah Attahiru da lafiyayyen mari kenan! Cikin fishi da qumar rai ta nunata da yatsa ta ce,"idan kina tashen balagar rashin kunyarki to ki gaggauta sanin inda zaki sauketa"

Tunda naji saukar marin jikina ya fara rawa tamkar mazari, babu abinda nake hangowa a gaba se tashin hankalin da abinda ta aikata ze janyo min.

"Innanillahiwa'inna'ilaihirraji'un!" Na firta cikin wata marainiyar murya wadda ke baiyana raunina a fili