Chapter : 6
by @zmchubado
#The contradiction#
Kafin nayi wani yunquri tuni Faridah tabar gurin idanunta na zubar da hawaye, A wannan lokaci ina tsayene kawai amma daga ciki bani da maraba da mutum-mutumi, da ƙyar na iya tattaro suran ƙwarin gwiwar da ya rage min, nabi bayanta da gudu ina kiran sunanta. Sai dai ko waiwaye batayi ba ta ratsa ta ƙofar falon da zai mayar da ita part ɗinsu ta ɓacewa ganina gabaɗaya.
"innanillahiwainnailaihirraji'un!" na sake furtawa ina ƙoƙrin ɗora hannuna bisa kaina, Cikin azama da hanzari Hajar tayi saurin janyoni tana watsa min harara ta ce,"uwar me kike jawa salati dan na mari waccen mara kunyar?" Tayi maganar tana tsareni da idanu cikin jin haushin ɗabi'ata.
Rasa amsar da zan bata nayi sai kawai na raɓa ta gefanta na koma dakin na tattaro mata jakarta da mukullin motar da tazo dashi naja hannunta muka fita harabar gidan, cikin alamun roqo na hada hannayena biyu na ce,"Don girman Allah Hajar ki tafi gida wllh bana so hajiya ta fito ta sameki, idan ta fito gurin nan Allah ne kaɗai ya san irin abinda zai faru. Iya wanda ya faru tsakaninki da da Faridah Attahiru ka ɗai ya isa haka please Twiny." Nayi maganar cikin sanyin murya.
"Ai dole ki turata ta gudu tunda baki taki abin arzuqi ba munafukar Allah ta'allah wadda bakya tsoron Allah." na tsinkayi muryar Hajiya cikin hargagi a tsakiyar kaina, zuciyata ce tai wani irin amsawa kafin inyi wani yunƙuri tuni jikina ya ɗauki rawa. bansan lokacin dana ɗaga kai ina kallonsu ba.
Hajiya ce a gaba Faridah na take mata baya se Aisha Sulaiman wadda ta kafeni da idanu tana aika min da sinqi-sinqin harara wadda tasa naji na qara karaya.
Ganin yanda suka nufo gurin babu annuri a saman fuskokinsu ne yasa nayi hanzarin tura murfin motar na rufe zuciyata na tsananta bugu tamkar zata tsaga tsakanin qirjina ta fito, a zahiri so nake in shiga tsakanin Hajiya da Hajar yasa nayi wannan yunƙurin da sauran guzarin da ya rage min.Sai dai ban kai ga ida nufina ba Hajiya tasa hannu ta hankaɗeni gefe, sannan tasa hannu ta buɗe murfin motar ta cakumo wuyan rigar Hajar ta fito da ita daga cikin motar. Banda haki babu abinda Hajiya keyi amma sabida fitina da rigima irin nata bata fasa ida mnufarta ba.
Kafin nayi wani yunƙuri tuni ta haɗa Hajar da jikin motar ji kake bum. Sannan ta ɗaga hannu da nufin ta zabga mata mari Hajar tayi saurin riqe hannunta ta ce," ke Babba ce Hajiya. So don't do things that make you lose your dignity in my eyes." ta faɗi hakan tana ƙoƙarin cire hannu hajiya dake wuyan rigarta.
Cikin shammata Aisha Sulaiman ta saukewa Hajar wani lafiyayyen mari me shiga a gefan fuskarta na dama, saboda yanda marin ya shigeta seda ɗankunnenta Na ɓangaren dama ya fita. Shirune ya ratsa tsakanin kunnuwan mu babu wanda ya iya cewa ƙale, sai hajar wadda ke riƙe da gefan fuskarta. Kallo ɗaya zakai mata ka fahimci ranta a mugun ɓace yake to the extent, sauke hannunta tayi daga riƙon da taiwa kumatunta. Lokaci guda ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya wadda ta fallasa haƙiƙanin ɓacin ran dake shimfiɗe a ƙirjinta, al'amarin daya ƙara firgita sauran nutsuwata kenan, na yunƙura da nufin in dakatar da ita saboda nafi kowa sanin halinta idan ranta ya ɓaci, sam bata jin bari idanunta rufewa sukeyi.
Hannu tayi saurin ɗaga min fuskarta a ɗaure babu salama ko kaɗan ta isa gaban Faridah Attahiru ta tsaya tana mai ƙare mata kallo from head to toe. Sannan tayi murmushi mai sauti ta ce,"lallai mamanki tana matiƙar sonki Faridah, tunda ta kasa haƙuri a lokacin da kikaje mata da shedar yatsuna a saman kumatunki." Hajar ta faɗi hakan tana jinjina girman lamarin a ranta, sedai kafin muyi aune tuni ta ƙara ɗaga hannu ta zabgawa Faridah wani sabon marin wanda yaci uban wanda tai mata a farƙo. A fisace Aisha dake tsaye tayo kan Hajar gadan-gadan da nufin ta cakumeta hajar tai mata wani kalan ihu wanda yasa taja da baya ba tareda ta shirya ba, a haukace ta juya ta kalli Hajiya ta ce," irin abinda kikaji a lokacin dana mari ƴarki irinsa Mama takeji kullum idan kuka addabawa ɗiyarta, tana jin fiye da haka a duk lokacin da kika ƙuntatama Bilkisu. Ko da yake barin dena wahalar da bakina wajan tuna miki matsayinki, kona faɗa ma bazaki gane ba tunda son zuciya yayi maki yawa." ta faɗi hakan tana ɗauke idanunta daga kanta sannan ta juya ga Aisha da Faidah ta ce"idan tashen rashin kunya kukeji wllh ni uwarku ce a wannan fanin." ta qare maganar tana watsa musu mugun kallo.
Gabaɗayansu rasa wanda zaice ƙala akayi saboda sun haɗu da gamonsu, ita kuwa Aisha kasa motsin kirki tayi don bata taɓa zaton a dangin su Bilkisu akwai ƴar bala'i Kamar Hajar ba. Wannan karon ita kanta Hajiya abin ya girgizata ba kaɗan ba, hakanan sai taji zuciyarta ta sosu ranta yai mata baki.
Babban takaicinta shine yanda Hajar ta rufe ido take tsuga mata rashin kunya son ranta, amma kuma ina tsaye na kasa dakatar da ita. Kallo ɗaya zakaiwa Hajiya ka karanci mugun nufin da take ƙullawa a zuciyarta, duba da irin kallon tsanar da take watsa min.
Murmushi Hajar tayi bayan ta karanci yanayin Fuskar Hajiya sannan ta ce,"Hajjaju naga kamar akwai abinda kike son furtawa amma zuciyarki taƙi baki haɗin kai..... Na san duk abinda zaki ƙulla ba zai wuce kisa Yusuf ya saki Bilkisu ba. Bayan haka babu wani abu da zaki iya mata ya cutar da ita, amma kafin nan barin haska maki wani abu. Nifa wannan gyaran da naiwa yaranki banyi musu don komai ba sai don na koya musu hankali saboda na lura basu da shi at all. Sannan Dan munayi muku shiru kuna aikata abinda kukaga dama akanta it does not mean that mu ƴan uwanta does not love her, kawai muna yi miki kawaicine saboda ke kaɗaice Aminiyar da Mama take da ita ne!"
Bata jira jin abinda Hajiya zatace ba ta juya tana kallon Su Aisha dake tsaye.
Sai da tayi taku kaɗan sannan ta isa gaban Faridah ta nunata da yatsa ta ce,"ke marakunyar ƙanwar miji. dama zuwa kikai kika tsaida mijin aure da yafi miki wannan zaman cin arzuqin da kikeyi a gidan wata kina takura mata."
Da sauri na matso gurin na kama hannun Hajar na jata baya, a wannan lokacin fuskata ta gama jiƙewa da ruwan hawaye na ce,"don Allah twiny kije gida pls. Kada ki ɓata sauran abubuwan da basu gama lalacewa ba." na firta hakan a dedai lokacin da muka isa jikin motar da tazo da ita, da kaina na buɗe mata har lokacin idanuna basu dena tsiyayar da hawaye ba.
Tunda na fara magana Hajar ke kallona cikin tsananin tsoro da al'ajabi, runtse idanu tayi da qarfi lokaci guda ta shiga motar ta zauna, har lokacin bata ɗago ta kalleni ba. Al'amrin da ya qara daga min hankali kenan. Ina ji ina gani ta kai hannu zata ja murfin motar ta rufe, cikin azama nakai hannu na ɗora bisa nata hannun na ce,"kiyi haquri twiny. Nayi zaton zakifi kowa fahimta na ne yasa nace ki tafi, amma wllh banyi zaton zaki ɗauki lamarin da zafi haka ba!"
Ɗauke idanunta tayi a hankali cikin alamu na sanyin jiki, bata iya cemin ƙala ba taja murfin motar ta rufe. Sannan ta kunna motar tayi baya kaɗan ta juya motar ta fice daga gidan. Tana fita na juya da sauri na koma cikin gida zuciyata babu daɗi akan abinda nayiwa Twiny. Musamman dana tuna cewa duk abinda tayi don ni tayi shi, kai tsaye ɗaki na nufa na murza mukulli a jikin ƙofar tareda jingina bayana a jikin ƙofar ina juya girman abinda na aikata. Tsorona ɗaƴa shine kada twiny ta fassarani a murɗe don nafi kowa sanin halinta!
Gabadaya a kidime nake sam babu nutsuwa a tareda ni, sai kawai na nufi inda wayata ke ajiye da nufin in kirata na bata haƙuri. Sai dai duk kiran da nai mata bata ɗauka ba don dole na haƙura na ƙyaleta, haka na wuni duk babu daɗi sai yamma liƙis sannan Yusuf ya dawo. Duk abinda nasan zai buƙata sai da na samar masa dashi, sannan na koma ɗaki nayi wanka na kwanta ko mai ban shafawa jikina ba, shi kansa ya san bana cikin yanayi mai daɗi don haka be dameni ba ya ƙyaleni, wanda hakan ba ƙaramin daɗi yamin ba. Washe gari tun 7:00am na tashi na ɗauka zemin faɗa akan abinda ya faru , amma kuma beyi hakan ba wannan ya bani tabbacin be shiga ɓangaren Hajiya ba da ya dawo. A nitse na miƙe na isa inda yake zaune na zauna a gefanshi, a ƙalla mun ɗauki mintuna uku babu wanda yai magana wannan yasa ya ɗaga kai muka haɗa ido cikin na juna. Ɗan motsa lips ɗina nayi da nufin nayi magana amma kuma sai na kasa cewa komai, ajiye wayar dake hannunsa ya yi tareda juyowa ya fuskanceni sosai ya ce,"kamar akwai magana a bakin ƴar mutan saminaka." ya firta hakan yana kai hannunsa gefan fuskata.
Ƙasa nayi da kaina don ban shirya karɓar fitinar yusuf ba, cikin sanyi jiki da ƙosawa da abubuwan dake faruwa a gidan for the first time na ce,"nan da wani lokaci zaka Auri Aisha Sulaiman?"
Zame hannunsa ya yi daga gefan fuskata bayan ya sauke ajiyan zuciya ya ce,"wani kalan fitina kika tashi dashi yau Bilqis?"
"lets be serious about it pls" na katse shi ta hanyar faɗar haka
Wayarsa ya fara ƙokarin ɗauka nayi saurin riƙe hannunsa na ce," kawai ka faɗa min lokacin aurenka da ita. ta yanda zan baka sarari tun yanzu ba tareda na takura maka ba."
"akwai wani abu a cikin kanki Bilqis." ya faɗi hakan yana miƙewa ya shige toilet ya barni a gurin.
Ina zaune a gurin har ya fito daga toilet ɗin ban miƙe ba, ganin ya fara goge jikinsa da towel yasa na miƙe na isa gabansa a karo na biyu na ce,"ba zaka fita a gidannan ba har sai ka sanar dani abinda nake son sani tukunna Yusuf."
Cikin maɗaukakin mamaki ya dakatar da abinda yake yi ya tsareni da idanunsa yana kallona, banji ko ɗar a zuciyata ba naci gaba da cewa,"wannan pretending ɗin naka ya isheni haka wallahi, idan aurenta shine maslaha kawai ka aureta ni banda matsala da hakan ko kaɗan. Amma ka dena ɓuya a bayan kawaicin da nake maka kana raina min hankali." na firta hakan cikin kakkausan sauti.
Still kallona yake zuciyarsa na harbawa saboda tsananin mamakin dana jefashi a ciki, tunani yake "anya wannan Bilkisu Ibrahim Saminakan da ya sanice tsaye a gabansa take masa raddi?"
"ko dai canza masa ita akai da wata Binkisun Saɓanin Tasa?"
Kamar nasan abinda yake saƙawa a cikin ransa yasa nayi murmushin takaici naci gaba da cewa,"na jima da sanin ɓoyayyiyar alaƙar dake tsakaninka da Aisha Sulaiman, Babu buƙatar sai ka ɓoyemin yallaɓoi.
I think It is better for u both to get married Yusuf, in my opinion it is more respectable for the kind of relationship you have with her. Madadin ku dinga yin komai a ɓoye gwara kuyi a sarari, it maybe she is the one who will give birth to you kamar yanda Ahalinka suke fata!" na firta hakan ina janye idanuna daga cikin nasa gudin kar ya smu ƙwarin gwiwar da zai yi wasa da hankalina again.
Abin mamaki sai naga ya fara zufa still idanunsa ƙurr a kaina be janye su ba.
Ganin ya gaza cewa komai ne yasa na ce,"abinda rai keso ai bai kamata a hanashi mallakarsa ba. Aurena da kai Muƙaddari ne wanda dani da kai bamu isa mu hana faruwar hakan ba, kasancewata da kai ba yana nufin ka horar da kanka wajan hana kanka abinda zuciyarka keso bane Yusuf! Na riga naji komai a Asibiti, babu buƙatar sai ka aikata abinda kake shirin aikatawa, in dai nice to wllh na amince kaje ka Auri Aisha muddin hakan zaisa ku sakarmin mara nayi fitsari. Ni gaskiyarka kawai nake buƙata a zamantakewar mu, sam bana jin daɗin ɓuyan da kake a bayan raunina kana min Ƙary......!" na firta haka cikin karyewar murya. Sai kawai na durƙushe a gurin ina kuka tamkar zan ƙarar da hawayen da ubangiji ya halicceni dashi.
A ɓangaren Yusuf tunda na fara magana ya ƙame ƙam a tsaye yana kallona tamkar gunki, cikin maɗaukakin mamakin jin yanda na ɓaro jirginsa a ɗan ƙanƙanin lokaci, kunya ce ta kamashi wadda tunda yake bai taɓa jin kamarta ba. Babban tashin hankalinsa bai wuce jin da yayi nace naji duk magaɓar da sukayi da Doctor Umar a Asbiti ba!
Share zufar data karyo masa ya yi a ransa yana addu'ar "Allah yasa banji abinda ya gama zaiyanawa ga Doctor Umar ba kamar yanda nake iƙirari.!"
Da ƙyar ya iya haɗiye abinda ya maƙale mishi a maƙoshinsa, sannan ya yi ta maza ya durƙusa har gwiwarsa tana gogar tawa sannan ya ɗora hannunsa bisa hannayena ya ce,"kada ki hukunta ni da abinda baki da tabbacin manufata a kai! Bilkisu ni ɗan'adam ne wanda keda tawaya irinta ajizanci. Kada umarnin da Hajiya ta bani yasa kiyima ƙudirina mummunar Fahimta! Idan da hali don Allah ki bani damar da zan nunawa Duniya ma'anarki a cikin Rayuwata please."
Dariya ce ta kufce min wadda ni kaina ban san inayi ba, sannan na kalleshi ido cikin ido na ce,"na jima da sanin matsayina a wannan zuciyar yusuf" na faɗi haka ina nuna saitin ƙirjinsa ta ɓangaren hagu sannan naci gaba da cewa,"ba sai ka baiyanama duniya ba, irin rayuwar da nakeyi tareda familynka kaɗai ta isa amsa ga duk mai neman ƙarin bayani akan haka. rayuwata da kai zaɓina ce I must be patient with everything I see from you, if I fail to do so, my previous efforts zai tafi a banza ba tareda na riƙi abin tunawa na tsahon har abadah ba!"
Kansa ne ya mishi nauyi ƙirjinsa na ɗagawa ya ƙara matsawa dab dani tamkar zamu haɗe mu zama guda ya ce"mai kike nufi da wannan maganar?" ya firta hakan yana nutsa ƙwayar idanunsa cikin idona.
Ban janye idona daga fuskarsa ba nayi murmushi mai zurfi na ce,"abinda nake nufi manufar iri ɗayace da taka Yusuf Attahiru!" ina gama faɗin haka na tsame jikina na miƙe tsaye na bar masa ɗakin ya raka bayana da idanu cikin tsananin mamaki da al'ajabin yanda nake mayar masa da martanin magana dai'dai da abinda ya gaya min. Ina jin tasirin idanunsa a ilahirin jikina amma naƙi juyawa haka na fice na barshi yana saƙawa da kwancewa, ganin bani da niyar dawowa ne yasa ya miƙe jiki ba ƙwari ya nufi ɓangaren Hajiya.
A nitse ya tura ƙofar falon bakinsa ɗauke da sallama, hajiya wadda ke zaune ƙasan kafet ta ɗaga kai ta kalleshi fuska ba yabo ba fallasa ta ce,"nayi zaton bani da darajar da zaka shigo ka gaisheni har sai ƴar gwal tayi maka izini tukunna."
Murmushi ya yi mai sauti wanda ya ƙarama fuskarsa kwarjini ya ce," idan akwai wanda zai yima Yusuf Izini akan wani abu to bai wuce ki ba hajjaju." ya firta hakan yana ƙoƙarin yima kansa mazauni a saman kujerar dake facing ɗinta. Bai jima da zama ba Aysha ta fito ta zauna a ɗan nesa dashi ta ce,"good morning"
A hankali ya amsa da "mun tashi lafiya where is Faridah ko bata tashi bane?"
"tana ɗaki kanta na ciwo ne." Aisha Ta faɗi hakan a taƙaice.
Risinawa ya yi bayan ya maida hankalinsa ga Hajiya ya ce,"ina kwana?"
"lafiya" ta fita hakan a gajar ce
Cikin alamun neman ƙarin bayani akan sauyin da ya gani tareda ita ya ce,"lafiya dai hajiya naga kamar ranki a ɓace?"
Kafin Hajiya tayi magana Aisha Sulaiman tayi caraf ta ce,"Your wife and her sister Hajar sune suka haɗu suka zagi Hajiya. Saboda Faridah tayi ƙoƙarin taka musu birki shine Hajar ta mareta har abin ya kaisu ga faɗa." tayi maganar tana kallon reaction ɗinsa.
Ɗan jim ya yi yana juya girman abinda ta gama faɗa a cikin zuciyarsa, cikin rashin gamsuwa da maganar ya ce,"I know who Bilkisu is. I swear to God she wouldn't do that bana son ƙarya, the way she respects Hajiya ko Farida doesn't respect Hajiya like that. ko kunya bakiji ba kin zauna kina ƙarya akan matar da ke nufinki da alkhairi, wllahi idan ki kai wasa sai dai ki nima wani mijin amma ba Yusuf ba." ya faɗi hakan ranshi a ɓace ba tareda ya ƙara kallon inda take ba ya miƙe da nufin barin falon. Har ya kusa kaiwa ƙofan fita Hajiya ta ce," nan da kwana Uku Sulaiman zai ɗaura auren Aisha da kai! wannan shine hukuncina" ta firta hakan ba tareda ta ɗaga kai ta kalleshi ba.
Zuciyarsa ce ta buga da ƙarfi don dole ya tsaya cak ya kasa gaba kuma ya kasa baya.......