RA'AYIN ZUCI..!

Chapter : 7

by @zmchubado


      #heartbreak#
Murmushin takaici na saki wanda iyakarsa lips ɗina, sannan na ɗaga kai na ƙara kallon fuskarsa a karo na biyu na ce,"bai kamata ka girgiza da jin haka ba Yusuf. Rayuwa ilimi ce mai zaman kanta ga duk wani mai hankali, ko da ban karbi darasin da ta bani yanzu ba dole ne a nan gaba na karɓeshi, gobe ina so naje gida amma idan hakan ba zai ɗaɗaka da ƙasa ba kamar yanda ka shaidawa Doctor Umar a maganarka ta ƙarshe!" ina kaiwa nan a maganata na fice daga ɗakin ba tareda na san inda zan nufa ba. A wannan lokacin  abinda nafi buƙata  kaɗaici ne don haka na fita harabar gida na yima kaina masauki bisa fararen kujerun da suke nesa da ƙofar shiga falona.
Lumshe ido nayi hawaye suka fara kwaranya tamkar ba zasu tsaya ba, cikin ƙanƙanin lokaci maganar Baffa ta fara dawo min tiryan'tiryan a tsakiyar kaina tamkar a lokacin ya ke firtamin su. Share hawayen nayi da sauri don na ƙudurtama kaina da ga yau na daina zubda hawaye akan baƙin cikin mijina ko na danginsa, abinda yafi min mahimmanci shine yanda zanyi na shawo kan Hajar wadda ke ƙaunata saboda Allah da kuma zumuncin dake tsakanina da ita. Ajiyar Zuciya na sauke mai nauyin gaske sannan na gyara zama sosai akan kujerar ina saƙawa da kwancewa, hannuna na ɗora bisa ɗamammen cikina cikin rauni da ƙasƙantar da kai na ce,"ya Allah! idan haihuwa a gareni Alheri ce ya Ubangiji ka azurtani da samunta! Idan kuma bani da rabon samunta a Duniyata ya Ubangiji ka wadata zuciyata da haƙuri" nayi addu'ar Zuciyata na harbawa. Ban tashi da ga inda nake zaune ba sai da na shafe awa guda sannan na miƙe, a lokacin Zuciyata ta fara sauka daga dokin fishi da ta hau.
Ina shiga falo kujeru na fara kaɗewa cikin gajeran lokaci na gyara gurin ya yi fes sannan na kunna tularen wuta na koma ɗaki, mintuna goma ne suka ɗaukeni na kammala gyaran ɗakin sannan na shiga toilet nayi wanka. Ina sako ƙafata daga banɗakin a dai'dai lokacin ya shigo, Sai dai, yanayin da na ganshi a ciki yanayi ne mai ban tsoro amma sai na dake na ƙarasa fitowa na zauna a gaban mirror na fara shafa mai a jikina. Sai da na kammala tsaf sannan na miƙe na isa jikin drower da nufin ɗaukar kayan da zan saka still yana tsaye bai zauna ba, doguwar rigar atamfa na zaro na saka.
Sai da na saka rigar sannan na zauna nesa da shi na ce,"meye matsalar?"
Shanyayyun idanunsa ya zubawa fuskata, cikin wani irin yanayi wanda ban taɓa ganinsa a ciki ba ya ce,"Aurena da Aisha kwanaki Uku ne suka rage Bilqis."

"Allah ya sa haka shine mafi alkhairi." na faɗi haka zuciyata na harbawa sannan  lokaci guda jikina ya fara rawa tamkar mazari. A zahiri so nake na ƙarfafi kaina don gudun kar gazawata ta baiyana a fili, amma ƙiri'ƙiri haka gangar jikina ta kunyata ni, Raunina ya baiyana muraran sai kawai na fashe da kuka na durƙushe a gurin ina rerawa tamkar marainiyar da ta rasa gatan Uwa da Uba da kuma dangi.

Ganin yanda nake kukane yasa jikinsa ya ƙara yin sanyi sai kawai ya janyoni jikinsa ya rungume yana sauraran  sautin kukana wanda ke huda Zuciyarsa kai tsaye. So ya ke ya yi magana amma ya gaza  jarumtar furta ko kalma guda daga bakinsa.

Wani irin kuka nake mai kassara zuciya da duk wani ƙarfin gwiwar da ɗiya mace ta mallaka, cikin rauni na jefama zuciyata tambayar kai da kai wadda ni kaɗai naje iya jin sautin tambayar na ce  "Ashe dama haka mata Suke ji a duk lokacin da aka labarta musu za'a ɗakko musu abokiyar zama?" na yima kaina wannan tambayar wadda ta haddasa min tasowar wani tuƙuƙin baƙin cikin mai tsananin ɗaci a maƙogaro. 

Haka nan sai na samu kaina da jin haushinsa tamkar in shaƙeshi ya bar Numfashi haka zuciyata ke aiyana min, amma haka na daure na danni kaina don bana son in kasance cikin jerin mata masu kishi irin na jahilci. Da ɗan sauran ƙarfin da ya ragemin na janye jikina da ga ruƙon da ya yi min sannan na yunƙura na miƙe har lokacin ina zubar da ƙwalla na ce," ina so ka kai ni Hayin Ɗanmani! Ina so naje naga Inno zuciyata zafi take Yusuf.."

Cikin sanyin jiki dana gaɓɓai ya sauke wata nannauyar Ajiyar Zuciya ya ce,"don Allah ki nutsu Bilqis karki ɗagama kanki hankali akan wannan maganar. Duk abinda zan gaya miki ba lallai ki yarda ba amma wallahi zuciyar Yusuf da ke kaɗai ta amince"

"kada ka dakatar dani akan  yunƙurina saboda nima ban hanaka yin aurenka ba. don karka tauyeni da wannan daɗin bakin naka ta hanyar hanani yin abida nake so." na firta hakan ina share hawaye da bayan hannuna.

Ƙura min idanu ya yi yana karantar yanayina, sosai yake jin tausayina don sarai ya fahimci halin da zuciyata ke ciki. Kasa motsin kirki ya yi balle ya samu ƙarfin gwiwar rarrashina, cikin rashin guzari ya zame jikinsa zuwa ƙasan ƙafafuna sannan ya ɗora hannunsa bisa ciyoyina ya ce,"Da ma ace ina da ikon kaucewa maganar auren nan, wallahi da na jima da yin haka ko don gudin zubar hawayenki Bilqis. Na so ace murmushi nayi sanadin ɗorawa a fuskarki ba kuka ba!."

Janye jikina nayi hakan yasa shima ya janye hannunsa daga kan ƙafata sai kawai na saka kaina a tsakanin cinyoyina na ƙara fashewa da sabon kuka mai sauti..
Wani irin zafi zuciyata keyi wanda kai tsaye na gaza fassara ma'anarsa, cikin duhun rashin sanin yanda zan kwatanta ɗacin zuciyata nake fidda sautin kukan. Al'amarin da ya ƙara rikita shi kenan duk ya susuce min tamkar wanda ke shirin tayani kukan, ganin da ya yi banida niyar tsagaita kukan ne ya sa ya janyoni jikinsa ya rugumeni ƙam yana sumbatar gashin kaina cikin yanayi irin na wanda ya rasa makama, cikin wani irin sauti mai baiyana raunin zuciya ya ce,"don girman Allah ki daina kuka Bilqis wallahi a zuciyata nake jin kukanki, ni kaina ba'a son raina zan auri Aisha Sulaiman ba kawai don anfi ƙarfina ne babu yanda na iya da umarnin Hajiya."

Miƙewa nayi tsam tamkar wadda aka tsikara ba tareda na ƙara bashi wata damar da zai ƙarasa firta maganar dake maƙale a harshensa ba na faɗa toilet na wanke fuskata sannan na ƙara fitowa. Kai tsaye drower na buɗe na zaro dogon hijabina maroon na saka a jikina sannan na ɗaga rinannun idanuna waƴanda suka fara kumbura saboda kuka na kalleshi na ce,"hmmm wai ba'a son ranka ba. Hala ka manta cewa na san tarihin alaƙarku kai da ita, any way koma dai mene ka dinga auna magana kafin ka firtota waje don ba zan ƙara baka wata damar da zaka raina min wayo ba." 
Ƙuri ya min da idanu zuciyarsa na harbawa, dukda cewa a fuskarsa bata nuna halin da yake ciki ba na fahimci maganar da na yaɓa masa ta dake shi.

"zaka kaini Hayin ɗan'manin ne kokuma naje na hau keke napep?" ya firta hakan ina tsareshi da idanu.

Shima ƙura mini idanu ya yi still yana zaune inda na barshi ya kasa koda motsin kirki, a zahiri so ya ke ya nuna ƙin amincewarsa da tafiyata amma ganin yanda na ƙura masa idanu yasa don dole ya canza ma'anar abinda ke ransa ya miƙe yana gyara zaman rigar dake jikinsa. Hanyar fita ya nufa ganin niyarsa yasa na juya na janyo ƙaramar akwatina na buɗe drower na ɗebi kaya kala biyar na zuba a ciki, sannan na koma toilet na ɗauki brush da shower gel ɗina na zuba a ciki. Mintuna goma ne suka ɗaukeni na kammala haɗa komai sannan na rufe akwatin na janyota zuwa harabar gidan, a mota na sameshi zaune yana ganina da kaya ya fito ya amshi akwatin yasa a bayan mota sannan ya kalleni ganin naƙi haɗa ido da shi yasa ya ce,"Kina ganin wannan hukuncin da kika yanke shine dai'dai?"
Ba tareda na kalleshi ba na ce," ƙwarai! saboda zai sama min kwanciyar hankalin da na gaza samu a gidanka na ɗan wani lokaci." na firta hakan ina jin zafin auren da zai yi a maganata.

"It's okay, tunda you chose this, but I want you to know that whatever happens after this decision you made, don't blame me iya abinda zan iya gaya miki kenan"ya firta hakan yana kama hannuna ya jani zuwa inda motar ke ajiye ya buɗe min ya turani ciki sannan ya rufe, a ruɗe nake kallon yanda yake acting ga dukka alamu ranshi a ɓace yake. Haka nan sai naji jikina ya yi sanyi da tafiyar, a hankali na kai hanu na buɗe murfin motar na fita sannan na mayar da murfin motar na rufe. A hankali na na juya na fara tafiya na koma cikin gida na, Wayata na ciro daga cikin jakata na zauna akan kujera ina dannawa, number ɗin ya Naimah na lalubo na danna mata kira.
Bugu ɗaya akai sa'a ta ɗauka cikin cool voice ɗinta ta ce,"Matar Yusuf da kanta."

Ɗan gajeran murmushi na saki wanda iyakarsa laɓɓana na ce,"Three days left until the wedding of Yusuf and Aisha Suleiman!"

"I don't understand what you mean Bilkqis wani Yusuf ɗin kike nufi tukunna?" ya Naimah ta faɗi hakan tana ajiye flacks ɗin dake hannunta akan daining table ɗin dake gabanta.

"Yusuf Attahiru shi nake nufi." na firta hakan ruwan hawaye yana sakkowa daga idanuna

"ya Allah! Bilqis waya faɗa miki wannan maganar? A ina kikaji?"
"shine ya faɗa mini da bakinsa."

"Hmmmmm ke tsaya banson damuwa kina jina ko! Tukunna ma wacece Aisha Sulaiman ɗin?" ya Naima ta wurgo min wannan tambayar

Cikin muryar kuka nace,"his uncle's daughter."

"ya Ilahi!" cewar ya Naimah
Ajiyar zuciya ta sauke mai gajeran sauti sannan taja ɗaya da ga cikin kujerun daining ta zauna jikinta duk a mace  ta ce,"Calm down, Bilqis. Ki kwantar da hankalinki sannan ki cire duk wata damuwa a ranki, na san abin akwai zafi amma idan kika daure abu biyu zakiyi maintening a gidan aurenki. Darajarki da kuma ta iyayenki a idanun mijinki, ƙarin auren Yusuf ba laifi bane ko'a addini, Ubangiji ne ya bashi wannan damar muddin  zai iya yin adalci a tsakanin ku."

"Ni wallahi matsalata ba ta yin auren bane ya Naimah. Dama na san komai daran daɗewa dole zai ƙara aure tunda ban haifa masa ɗa ba, kawai wadda zai aura ɗin ce zuciyata bata sonta ko kaɗan, gani nake kamar bata dace da samun gurbi a tsakanin iyalaina ba!" na faɗi hakan ina kuka.

"karki bari idonki ya rufe Bilqis, Haihuwa ta Allah ce ina da yaƙinin ba don wannan dalilin Yusuf zai ƙara Aure ba. Kawai ki sa a ranki ƙaddarar zama da kishiya ne ya faɗo kanki"

"Ai dama Fitila ɗaya ce a cikin samaniya, kuma wannan fitilar dai ita ce ke nuna mana hanya Yaya Naimah. Zanyi haƙuri kamar yanda kika Umarce ni in sha Allah!" ban bari ta yi magana ba nayi saurin katse kiran hawaye na zuba da ga idanuna.

       ***   ***   ***
Jikinta ne ya yi sanyi hakanan sai taji tausayin Bilqis ya cika mata zuciya, haƙiƙa ta fi kowa sanin cewar yarinya ce mai haƙuri da juriya akan komai. Bilqis irin yaran nan ne masu ɓoye damuwarsu a bayan hawayen su, ya na da matiƙar wahala ta buɗe baki tayi ƙorafi akan abu koda ace tana cutuwa akansa. Tunda ta buɗe baki ta sanar da ita maganar auren Yusuf tabbas akwai wani abu a ƙasa game da yarinyar da Yusuf ɗin zai kwaso.

Ya Naimah ta jima a zaune bayan sun gama waya da Bilqis sannan ta miƙe jiki babu ƙwari ta fara ƙoƙarin haɗa musu abin da za suyi Dinner da shi. A haka mijinta  Dr. Mamoud ya dawo  da ga office ya sameta, kallo ɗaya ya yi mata ya fahimci akwai abinda ke damunta.
Bai ce mata komai ba ta miƙe ta karbi lapcord ɗin da ke hannunsa suka wuce ɓangarensa, suna shiga ya janyota jikinsa ya yi hugging ɗinta ya ce,"madam lfy kuwa?"
Ajiyar zuciya ta sauke tareda gyara zaman kanta a ƙirjinsa ta ce,"Doctor maganan Bilkisu ne da Yusuf."
Wara idanunsa ya yi sannan ya janye jikinsa da ga nata ya ce,"Amma ai na gaya matsa bata da wata matsala kawai lokacin haihuwan ne baiyi ba."
"matsalan is not about that Doctor. Wai kishiya zai yi mata."
"matsalar dai guda ɗaya ce madam maganar Haihuwan ne dai, in ba dan haka ba wani fitinan ne zai kaishi ga ƙara aure bayan yana da mace mai haƙuri da karamci irin Bilkisu?" ya firta hakan yana ƙoƙarin sassauta ɗaurin necktie ɗin dake wuyan  sa.

Cikin rashin fahimtar inda maganarsa ta dosa Ya Naimah ta ce,"Karamci kuma Doctor.?"

"yes haka nace but You will never understand sai nan gaba kaɗan." ya firta hakan yana shafa gefan fuskarta da tafin hannunsa na dama. Da taimakonta ya rage kayan jikinsa yana ƙoƙarin shiga wanka ya juya ya kalleta ya ce,"Where did the children go? I didn't hear their voices."

"Sun fita tareda yaran Halima Abdulra'uf, yau bakina ya huta da fitanan Imran shi dama Farouq yau bai wuni a gidannan ba." 
"Amma kin basu kuɗin da zasu ƙara suyi siyayya ko Madam?"  ya firta hakan yana tsareta da idanu.

"Uhmm kaima neman magana kake amma kafi kowa sanin Halima ba zata karɓi ko sisi a gurina ba."

Murmushi ya yi sannan ya shiga toilet ita kuma ta nufi drower ta fito masa da kaya marasa nauyi sannan ta fita daga ɗakin zuwa nata ɓangaren.........

Shiryawa tayi cikin doguwan riga mara nauyi sannan tayi sallar magrib, a falo ya sameta dedai lokcin Halima Abdulra'uf ta yi sallama tareda yaran gabaɗaya, Imran, Farouq, Aman tare da Amani. Cikin sakin Fuska Doctor da Ya Naimah suka ce,"maraba da maman yara." 
Dariya tayi sannan ta ijiye ledan hannunta ta ce,"Farouq ga kayan ku nan ni barin wuce na bar Daddyn Amani waje yana jirana." ta firta hakan tana ƙoƙarin kama Hannun Aman.

Zame hannunsa yaron ya yi yana tura baki ya ce,"Momy I will stay here and play with Farouq."
"to shikena. amani Muje gida Daddy na jiran mu" Halima ta faɗi hakan tana murmushi ta ce,"to Aunty Naimah kinyi ɗa."

Dariya sukayi gabaɗaya sannan ta fita su kuma suka wuce daining, sai da tayi sarving Doctor sannan ta zuba ma yaran nasu ya kasance ba ka jin sautin komai sai na spoons. Suna kammalawa ta taimakawa  yaran sukayi brush sannan ta musu wanka ta shirya su suka kwanta, sai da ta tabbatar da cewa sunyi bacci sannan ta fita daga ɗakin zuwa ɓangaren Doctor. A lokacin har ya kwanta yana jiran shigowarta, da wannan damar tayi amfani wajan sanar da shi cewar tana so taje kano saboda Auren Yusuf.
Bai mata musu ba ya amince akan jibi zata kama hanya a haka  daran ranar ya gushe zuciyar Yaya Naimah a cike taf da tausayina.