Chapter : 8
by @zmchubado
RA'AYIN ZUCI ❤
Bayan mun gama waya da ya Naimah, ya Zainab na kira ita ma na sanar da ita maganar Auren Yusuf, lokacin da na gaya mata hankalinta ba ƙaramin tashi ya yi ba. Jikinta ne ya yi sanyi tamkar kazar da aka tsoma a ruwan gishi ya Zainab ta ce,"wllahi da ace wani ne ya gaya min wannan maganar ba zan taɓa yarda cewar Yusuf Zai iya miki kishiya ba Pafah! Amma ba komai Allah ya sa hakan ya zama silar buɗewar ƙofofin alkhairanki Bilqis!"
Hawayen da suka zubo min nasa hannu na share sannan na ce,"Ya Zainab ƙijina zafi ya ke min tamkar zai tsage a duk lokacin dana tuna cewa Yusuf kishiya zai min, wallahi sai in ji a raina dama ban aureshi ba tun farko....."
Tausayina ne ya cika zuciyar Ya zainab har bata san lokacin da hawaye ya zubo daga idanunta ba, ba komai ne ya haddasa mata haka ba sai tunawa da ta yi da babbar damar dana samu a shekarun baya amma na ɓarar da ita saboda soyayyar Yusuf wadda bata ƙareni da komai ba sai baƙin ciki da ɓacin rai tunda akai aure. Ajiyar Zuciya ta sauke mai nauyi sannan ta kada baki ta ce,"Kinyi kuskure Bilqis! Wllahi kinyi kuskuren yin jayayya da mutanan da sukafi kowa ƙarfin iko akanki, ina da yaƙinin cewa auren Yusuf da zama tareda familynsa da kikeyi Funishment ne daga Allah duk da cewa Baffa ya jima da yafe miki. Amma sai wani lokaci zaki fara tunkarar mama da matsalarki a matsayinta na mahaifiyar mu?"
Ƙirjina ne ya toshe yayinda zuciyata ta ƙara dunƙulewa a guri guda, sai kawai na fashe da kuka mai ɗaga hankali na ce,"na san nayi kuskure yaya Zainab! amma wllh bani da ƙarfin gwiwar da zan iya tunkarar mama in gaya mata halin da nake ciki. Don Allah ya Zainab ki taimaka min ki ƙara bata haƙuri idan kinzo, a halin da nake ciki bani da wani zaɓi wanda ya wuce nayi haƙuri da duk halin da zan shiga a gidan Yusuf middin ina so in zauna lafiya da Baffa bai kamta na karya sharaɗin da ya shimfiɗa min ba....."
Shiru ne ya ratsa kunnuwan mu ba'a jin sautin komai sai na shashsheƙar kukana, Sai da ta yi da gaske sannan ta iya ƙarfafa kanta ta ce,"Ƙaddarar ki kenan Bilqis! Duk yanda kika so ki tsallake faruwar wasu abubuwan ba ki isa ki kaucema abinda Allah ya tsara miki ba. Sai dai, zan roƙa miki Ubangiji ya taƙaita miki ƙuncin da kike ciki ƙanwata....."
haka ta dinga rarrashina da kalamai masu daɗi da sanyaya Zuciya har sai da ta tabbatar da cewa na ɗan samu salama, mun jima muna magana da ita sannan mukai Sallama bayan ta shaida min cewa za ta shigo Kaduna jibi idan Allah ya kaimu. Miƙewa nayi na koma ɗaki na kwanta saboda ciwon da kaina ke min, ban ji motsin shigowan Yusuf ba har Bacci ya ɗauke ni.
*** *** *** ***
A can ɓangaren Hajar kuwa tun da ta koma gida Inno ta lura da yanayinta, don haka ta Ɗaga kai ta kalleta ta ce "Hajara ina fatan ba wata fitinar kika sake kunnowa ba. Ke tukunna ma daga ina kike jiya bayan kun dawo daga Lere?"
"ni ba inda naje wanda ya wuce gidan Baffah!" Hajar ta faɗi hakan tana juya Abincin data zuba a flet. Ƙura mata idanu Inno ta yi sannan ta kada baki ta ce" Hajara kenan. Ga dukkan alamu kin manta cewa nina haifeki kuma ba zakimin wayo ba, ko ma ina kikaje Allah yana kallonki ina kikaje da mota bayan nace karki ƙara hawa?"
Tura baki ta yi sannan ta janye flet ɗin daga gabanta ta ce,"Gidan Fafah naje."
"innanillahiwa'inna'ilaihirraji'un! Hajara mai ya kai ki gidan Bilkisu a wannan ƙadamin da ake ciki?" Inno ta jefa mata wannan tambayar idanunta a waje don sarai ta san Halin Hajar in dai ta je gidan Bilkisu sai anyi tsiya da ita, wannan dalilin ya sa ta hanata zuwa gabaɗaya.
"Haba Inno don Allah! yanzu laifine don naje gidan ƴar uwata?"
"laifine muddin zaki dinga zuwa kina ɗaga mata hankali, kuma wllhi ki saka a ranki cewa sai na gayama yayanki abinda kika aikata, tunda ni kin raina ni ban isa na gaya miki magana kiji ba."
idanun Hajar ne suka ciko da ƙwalla. cikin sanyin murya da roƙo ta ce,"Don Allah Inno kiyi haƙuri pls Allah ba zan ƙara ba."
Shareta Inno ta yi sannan taci gaba da aikin gabanta don ba zata iya da rikicin Hajar ba, "Ace a rayuwar mutum bai san haƙuri ba sai jan magana da niman masifa? Na tabbata wannan halin naki shine ya hanaki fidda miji kiyi aure kamar yanda Bilkisu ta yi"
"hmmm In dai aure irin na Fafah ne wallahi gwara na mutu a gabanki banyi aure ba, ita ma don ba ki san abinda take fuskanta a gidan Yusuf ɗin bane shiyasa rayuwar auranta take birgeki. Jiyama fa da naje sai da muka kwashi na ƴan kallo da wannan shegiyar ƙanwar mijin nata Faridah, ban bar gidan ba sai da na tabbata na sheƙa mata mari mai lafiya a fuskarta!"
"Innanillahiwa'inna'ilaihirraji'un! Dama abinda kika aikata kenan Hajarah?"
Cikin Azama Hajar ta ɗora hannu akan lips ɗinta lokacin data farga da cewa ta yi ɓarin zance. Shikenan ta tonama kanta asiri, miƙewa ta yi da sauri ta shige ɗaki don gudun kar Inno ta kai mata duka.
Da ido Inno ta raka bayanta har ta ɓace mata da gani, Hakanan sai taji jikinta ya yi sanyi tausayina ya cika mata zuciya. A baya ta yi zaton matsalar Haihuwa ce ta sanya Familyn Yuduf suke addaban rayuwata, amma da taji abinda hajar ta faɗa yanzu sai yasa zuciyarta tsinkewa da lamarin. "Shin wace irin matsala Bilkisu take ciki a gidan Yusuf?" inno ta yima kanta wannan tambayar.
Jin ta kasa bama kanta amsa ne ya sa cikin sanyi jiki ta ce,"Allah ya kawo miki ƙarshen damuwoyinki Bilkisu."
Haka wunin ranar ya kasance Hankalin Inno yana gareni ba tareda ni nasan hakan ba.
A daran da na sanar da su yaya Naimah maganar Auren Yusuf a ranar na kira Inno itama na gaya mata. Sai dai, tashin hankalin da naji a muryarta ya zarta irin wanda naji a muryoyin su yaya Zainab, itama nasiha ta yi min akan haƙuri da juriya sannan a ƙarshe ta yi min fatan alkhairi bayan ta tabbatar da na saki raina.
Wasa farin girki. tun ina jin maganar auren Yusuf a nesa har kwanakin biki suka ƙara matsowa kusa, tun ana saura kwana ɗaya ɗaurin aure mutane suka fara cika gidan, ganin haka ya sa na kulle ɓangarena ta yanda ba wanda zai iya shigowa. Ƙarfe huɗu dedai Dj ɗin da suka ɗakko ya fara aikinsa, ni dai ina cikin gida ban leƙo ba har suka gama kaɗe'kaɗensu suka tashi, sai wurin ƙarfe biyar da rabi sannan motar su Yaya Zainab ta shigo harabar gidan. Jin tsaiwar mota ya sa na yunƙura na isa jikin labulen window na maƙale ina leƙen ganin su waye, Cikin nutsuwa Yaya Zainab ta nemi guri ta yi parking sannan ta kalli ya Naimah ta ce,"waƴan nan dandaxon jama'ar fa sai kace yau ne ɗaurin auren?"
Juya kai Ya Naimah ta yi sannan ta sauke ajiyar Zuciya ta ce,"bikin dangi fa sukeyi dama mai kike expecting?" cewar yaya Naimah.
"hakane kam tunda sun samu dalilin zuwa birni ai dole ne suyi amfani da damar su, amma wllh yaya Naimah Hajiyar Yusuf bata da imani balle kara. Yanzu duk Amintar dake tsakaninta da mama irin sakaiƴar da za ta yi ma ƴar cikinta kenan? wallahi sai yanzu nake realizing dalilin da yasa mama taƙi amincewa da alaƙar Bilqis da Yusuf, it maybe ma saboda baƙin halin uwarsa ne mtswww."
"Zainab mai yasa kike magana irin wannan a gaban yaro ƙarami, kalli yanda yake kallon ki sai kace ya samu Tv"
Yatsina fuska ya zainab ta yi sannan ta kashe motar ta fita, sanye take cikin wani tattausan swiss less maroon wanda ya fito da hasken fatar jikinta sosai. Kallo ɗaya za kai mata ka fahimci hutu da jin daɗi sun zauna a jikinta, ba ta damu da irin kallon da mutanan dake harabar gidan suke mata ba ta buɗe bayan mota ta ɗakko Ahmad ta kama hannunsa suna jiran ya Naimah ta fito da ga cikin motar.
A nitse ya Naimah ta fito daga motar hannunta riƙe da ƙaramar jaka mai launin gold, itama less ne a jikinta brown mai kyau an mata ɗinkin doguwan riga, kana kallonta zaka gayama kanka macece mai Capacity na bala'i. A sanyaye ta kalli Ya zainab ta ce,"mu fara shiga gurin Hajiyar Yusuf sannan muje gurin Bilqis ɗin."
Ba don ranta yaso ba ta mara mata baya zuwa ɓangaren Hajiya, a falo suka samu Faridah Attahiru ta caɓa ado suna shirin tafiya kamu, ganin su Ya Naimah ne ya sa ta fara bama yarinyar dake zaune a gefan ta labarin Dinner ɗin da zasu yi gobe. Taɓe Baki ya Zainab ta yi sannan ta kalli ya Naimah ta ce "mu jira Hajiyan a nan ba sai mun shiga ɗaki ba saboda zafi." ta faɗi hakan tana maida kallonta ga Faridah ta ce,"yi mana magana da hajiya sauri mukeyi."
Hakanan sai Faridah ta kasa yi mata musu saboda kwarjininta, haka ta miƙe ta shiga ɗakin ta isar da saƙon ta dawo. Ba jimawa Hajiya ta fito ganin su yaya Naimah ya sa ta ɗan saki fuska ta ce,"maraba."
"Hajiya ya taro?" cewar ya Zainab
"taro alhamdulillah gamu a cikinsa."
"masha Allah. Ubangiji ya sanya alheri ya sa kuma abokiyar arzuƙinsa ce."cewar yaya Naimah.
"Amin ya Allah haka muke fata kuma in sha Allahu nan ba da jimawa ba zata cika mana gida da arzuƙin ƴaƴa ba na kashi ba." cewar wata mata wadda ke ƙoƙarin fitowa daga ɗakin Hajiya.
Da ido suka bita gabaɗaya sun kasa cewa komai don ba su taɓa expecting irin wannan cin fuskar daga babbar mace irin wannan ba. Murmushi yaya Naimah ta yi sannan ta miƙe ta kalli Zainab ta ce,"muje." ta faɗi hakan tana ƙoƙarin ɗaukar Ahmad wanda ke zaune saman ƙafar ya Zainab.
Ran ya Zainab a mugun ɓace ta miƙe still idanunta yana kan matar data faɗi maganar bata janye su ba, ganin yaya Naimah tana ƙoƙarin jan hannunta ne ya sa tayi saurin zamewa ta ce,"Haihuwa dai nufin Allah ce ba siyar da ita ake a kasuwa ba, in da ace siyarwa ake wallahi muna da arzuƙin da zamu iya siyo Bilkisu dozin so dozin." tana kaiwa nan a maganarta ta fice daga falon kamar zata tashi sama. Yaya Naimah ta mara mata baya don bata da abin da zata iya cewa a wannan gabar Zainab ta jiƙa musu aiki.
Rasa wanda zai tanka maganar akayi ciki kuwa har da Hajiya wadda tayi ƙwam a kan kujera tana kallon Hajiya Habiba bakinta a sake. Sai da aka samu gushewar mintuna uku ƙwarara sannan Hajiya Habibah wadda take ƙanwa ga Hajiyar Yusuf ta ce,"amma dai wllh Halima baki kyauta ba abinda kikayi, yanzu gashi nan kin janyoma kanki abin kunya yarinya ƙarama ta gaya miki magana ina amfanin haka saboda Allah?"
"Habibah ki rufe min baki a falon nan tun kafin na ɓata miki rai. Meye laifin Halima don ta faɗi gaskiya ? Ƙarya ta faɗa a maganarta?" Hajiyar Yusuf ta faɗi hakan tana tsare Habiba da idanu.
"hmmm Hajiya kenan, dama tunda halinku yazo ɗaya ai ba zaki ga laifin Halima akan abinda ta yi ba, wallahi Hajiya kiji tsoron Allah ki daina ƙuntatawa yarinyar da babu komai a zuciyarta sai alkhairi, kada ki bari son zuciya ya sa ki janyoma kanki kara da kiyashi." cewar Hajiya Habibah.
"dama na san ba don Allah kika zo taron bikin nan ba Habibah, saboda na jima ina zargin ba kya ƙaunar cigabana dana ƴaƴana ai dama dole kiyi murna tunda Yusuf ya auri juya. to wallahi in dai nice da baƙin cikina zaki mutum ki zuba ido ki gani, sai na goya ɗan Yusuf da Aisha ko zaki mutu."
Murmushi Hajiya Habiba ta yi bata ƙara magana ba haka ta bar hajiya ta na ta kumfar baki ita da su Hajiya Halima.
*** *** *** *** *** ***
Murɗa handile ɗin ƙofar shiga falon ya Zainab ta yi amma ta jita a rufe, jin an taɓa ƙofar ne ya sa na isa jikin ƙofar cikin zumuɗi na buɗe musu.
Sai kawai na faɗa jikinta na rungumeta, a haka ya Naimah ta ƙaraso gurin ta samemu, dariya ta yi mai sauti sannan ta ce,"to uwar gidan Yusuf nima azo a bani nawa hugg ɗin."
Cikin dariya na zame jikina daga na ya Zainab na faɗa jikin ya naimah na ƙanƙameta har sai da Ahmad ya yi ƙara sannan na sake su. Sosai suka ji daɗin ganina saboda nayi ado cikin wata brown ɗin Sufa wadda ta zauna a jikina ɗas.
Hannunsu na kama muka shiga faƙon bayan na garƙame ƙofar da key, nan fa muka fara hirat yaushe gamo. Ganinsu a tareda ni sai ya rage min raɗaɗin wutar kishin da take ƙona min zuciya, ganin haka yasa suka yanke shawarar kwana a gidana dukda cewa basu zo da shirin hakan ba.
Washe gari tun 7am na tashi na shiga kitchen na haɗa mana all abubuwan da zamuyi breakfast dashi, Yusuf bai shigo ba sai wurin 8am saboda jiya bai kwana a gidan ba. Ina fitowa daga kitchen na ganshi zaune a falo, ɗauke idona nayi daga kansa still ina tsaye a inda nake ban motsa ba na ce,"goodmorning"
A nitse ya mike cikin nutsuwa ya tako inda nake tsaye ya jani jikinsa ya rugumeni yana shafa bayana ya ce,"Zuwan su yaya Naimah yasa matata ta manta dani."
Zame jikina nayi ina ƙoƙarin juyawa ya yi saurin ruƙo hannuna ya ce,"Yayanki ya kirani." sai naji gabana ya faɗi lokaci guda na juya ina kallon Yusuf cikin alamu irin na mai nema ƙarin bayani.
Murmushi ya sakar min sannan ya ce,"ki fara shiri tafiyarku keda Inno jibi zai kasance." ya firta hakan ya na kallon agogon fatar dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa.
"wani tafiya kuma?" na firta a sanyaye
"idan lokaci ya yi zakiji oya kira min su mu gaisa pls." ya faɗi hakan a dedai lokacin da ya ke ƙokarin zama a kan kujera.
A hankali na janye idona daga kansa zuciyata na harbawa ganin yanda ya yi kyau cikin farin yadin dake jikinsa, hakanan sai naji hawaye suna ƙoƙarin zubowa daga idanuna.
Sai da na share hawayen sannan na shiga ɗakin na gaya musu yana jiransu a falo, ba su daɗe ba suka fito suka gaisa sannan sukai masa fatan alkhairi, yana ƙoƙarin fita yaya Naimah ta ce,"Malam Yusuf idan babu damuwa don Allah zamu kai Uwar gida ai mata lallen biki."
Cikin sakin fuska ya ce,"ba komai Aunty dama ina da niyar hakan a raina, amma tunda kin rigani ga kuɗin lallen Uwar gida" ya zaro 50k ya ijiye akan kujerar dake kusa dashi.
Har cikin ran sisters ɗina sunji daɗin abinda ya yi, don haka ya Zainab ta kalli ya Naimah ta ce,"bawan Allah ɗin nan yana matiƙar son matarshi amma waccen matar ta hanasu farin ciki muguwar tsohuwa kawai."
Banza ya Naimah ta yi mata don a rayuwanta ta tsani abu na rashin girmamawa. Sai da mukayi breakfast sannan mukayi wanka muka fice daga gidan a motar yaya Zainab, wani haɗaɗɗen spa ya Zainab ta kaimu da nufin ayi min gyaran jiki, 100k ta biya aka min dilka sannan ya Zainab ta biya kuɗin lalle dana special Dukkan ɗin da mai shop ɗin ta bata labari. Cikin gajeran lokaci aka goge min fatan jikina ya yi fess sai ƙyalli da ɗaukan idanu yake yi. Nan aka fara turarani da tularuka masu matiƙar ƙamshi ciki da waje kamin akazo aka shimfiɗa min zanen lalle mai kyau da jan hankali, bamu bar gurin ba sai ƙarfe huɗu na yamma already an riga da an fara shirin tafiyar Diner ɗin Yusuf Attahiru da amaryarsa Aisha Sulaiman.
Wayata na zaro na miƙawa ya zainab na ce,"kiyi magana da inno naji tace hajar zata zo amma har yanzu bata ƙaraso ba."
"Ita tace miki miki zata zo ko kuma ke kika kira waya kika tilasta mata saita turo miki Hajar ɗin" cewar ya zainab.
Ɗan murmushi nayi sannan nace."no ba tilasta ta nayi ba wllh, kawai dai na nuna mata idan ta bar twiny tazo zanji daɗi sosai."
"uhmm to sannu uwar kinibibi, wato zuwan mu bai wadatar ba sai kin jajiɓo mana sarauniyar niman magana ko" ya Naima ta faɗi haka tana tsareni da idanu. Dariya mukayi ni da ya zainab ba wanda ya ƙara magana.
Light make-up aka min sannan ya Naimah ta zaɓar min kayan da zan saka cikin waƴanda muka taho da su, wani haɗaɗɗen jan less ta zaɓar min wanda hasken stones ɗin ya taimaka wajen ƙara fito hasken farar fatana. Bayan an gama shirya ni mukai sallama da matar muka tafi gida, sai dai, tun kafin mu kai ga shiga harabar gidan mukai karo da kujeruna an fito da su waje yayinda ƙofar falon ta ke a buɗe mutane sunata kaiwa da komowa..........!