Chapter : 9
by @zmchubado
Nan muka fara kallon kallo aka rasa wanda zai ce ƙala! Ya Zainab ce ta yi ƙarfin halin fitowa da ga cikin motar already Ahmad yana hannun ya Naima, miƙo min Ahmad ta yi sannan ta rage sautin muryarta ta kalleni ta ce,"Stay in the car Bilqis, don't dare come out sai nace ki fito sannan zaki fita a matar nan kina ji ko?"
Ɗaga mata kai na yi jikina a sanyaye, ganin haka ya sa ta yi murmushi ta ƙara cewa,"karki sakama kanki damuwa in sha Allah komai zai yi dedai." tana gama faɗin haka ta buɗe murfin motar ta fita sannan ta kalli ya Zainab ta ce,"karki ce musu komai ki bari in kira Yusuf da kaina muji dalilin da yasa aka fito da kujerun, it maybe ma bai san sun aikata hakan ba wllh"
"hmmm ya Naimah kenan! Wllahi zan iya rantsuwa da Allah saboda su wulaƙanta Bilqis ne yasa suka buɗe mata ɗaki ba tareda saninta ba." ya Zainab ta faɗi hakan cikin ɓacin rai sosai
"What is your assurance about that? Su da kansu ne suka gaya miki hakan?" ya Naimah ta jera mata waƴannan tambayoyin.
"ba su suka gaya min ba amma ba na raba ɗayan biyu wulaƙanci ne ya sa su kai mata haka, saboda na jima da fahimtar mutanan nan basu san mutunci ba."
"To naji uwar marasa haƙuri but Don't do anything until we know why they opened her parlour without her permission tukunna, ni banson damuwa ki bari mubi komai a hankali." ta faɗi hakan dedai lokacin da take ƙoƙarin lalubar number Yusuf a wayanta. Bugu ɗaya tai masa ya ɗauka, cikin girmamawa ya ce,"ya Naimah barka da yamma."
"barka dai Yusuf ya hidima da jama'a?"
Ɗan murmushi ya yi mai sauti sannan ya ce,"Alhamdulillah dama tun ɗazu nake ta ƙoƙarin na kiraki Amma Ubangiji bai nufa ba."
"Eyyah! Shirin Allah ai shine shiri malam Yusuf, karka damu ba komai wllhi."
Ɗan jim ya yi kaɗan sannan ya rage sautin muryarsa ya ce,"Ya Naimah maganar Dinner don Allah ki sa Bilqis ta shirya zan turo Doctor Umar bayan magrib ya ɗauke ku zuwa in da za'ayi."
Jikin ya Naimah ne ya yi sanyi saboda jin abinda Yusuf ke gaya mata wai zai turo wani ya ɗauki Bilqis ya kaita gurin Diner ɗin bikinsa saɓanin shi da kansa, amma a zahiri sai ta yi murmushi ta ce,"ba matsala in sha Allah, Allah dai ya nuna mana anjima ɗin da rai da lafiya zan kaimu da kaina a Motar Zainab, amma kafin nan ina da magana wadda nake son muyi da kai idan har babu damuwa kuma kana da lokaci."
Zama ya yi a kan kujerar da ke facing Doctor Umar ya ce,"ina sauraronki Ya Naimah" ya firta hakan cikin nutsattsen sauti mai cike da girmamawa.
Shiru ne ya biyo baya na ƴan sakanni sannan ya Naima ta ce,"Yusuf da saninka aka fito da kujerun Bilqis waje?"
Gabansa ne ya yi wata irin faɗuwa cikin azama ya miƙe yana ƙoƙarin gyara Babbar rigar shaddar da ke jikinsa ya ce,"gani nan zuwa gidan yanzu, but don Allah yaya Naimah don't talk to anyone akan wannan maganar karku tanka musu pls." ya faɗi hakan a hargitse sannan ya katse wayar ya kalli Doctor Umar ya ce,"Mutumina akwai matsala muje gida kamin rakiya pls." bai jira jin amsar da Doctor Umar zai ba shi ba ya fice da ga falon zuciyarsa na harbawa, haka nan sai ya ji ransa ya sosu duk da cewa bai san ainihin abinda ke faruwa ba. amma tabbas ya san akwai wani abu a ƙasa wanda ya ke da tabbacin cewa shirin hajiya ne da sauran ƴan uwansa waƴanda basa son a zauna lfy.
Yana fita mota ya shiga yana ƙoƙarin kunna motar Doctor ya cinmasa, shiga matar ya yi sannan suka fice daga gidan ba tareda sun sanar da sauran abokan su cewa sun fita ba. Sai da suka bar harabar gida sannan Doctor ya kalli Yusuf ya ce,"Mutumina wai mai ya ke faruwa ne?"
Hankalinsa yana kan tuƙin da ya ke amma sai da ya juya ya kalli Doctor ya ce,"Umar Hajiya so take ta ɗaga min hankali bata son ayi taron nan lfy a gama lfy kamar yanda nake fata." ya yi maganar yanayin fuskarsa na sauyawa.
"Subahanallah! Ya zaka faɗi haka da hankalinka Yusuf? Pls kada ka ƙara faɗin haka don Allah" cewar Doctor Umar
Shiru Yusuf ya yi bai ƙara cewa komai ba har suka iso ƙofar get ɗin gidan, horn ya yi sannan aka buɗe masa get ya shiga ciki bisa ga mamakinsa sai ya ga all abinda ya Naimah ta sanar dashi a waya da idanunsa, cikin nutsuwa ya yi parking motar sannan ya fito a hanzarce ya iso inda motar mu ke tsaye. Kasa magana ya yi sai kwai ya juya da ɗan sarsarfa ya nufi inda aka zube kayan fuskarsa babu alamun ɓacin rai, ya jima a tsaye yana ƙarema kayan kallo sannan ya nufi maine ƙofar da zata kaishi cikin falona, yana shiga da Munirah Sulaiman ya fara cin karo wadda ta kasance yaya ga Aysha Matar da aka ɗaura masa aure da ita. Fuskarsa a ɗaure ya dubeta ya ce," ina Hajiya Habibah?"
"Ta na ɓangaren Hajiya ba ka ganta a can ba?"
Bai bata amsa ba ya juya zuwa ɓangaren Hajiya Doctor na take mishi baya, da sallama suka shiga falon lokacin ba mutane sosai duk sun shiga salla sai ɗaiɗaiku ne suka rage, kai tsaye ɗaki ya nufa in da yake jiyo muryar mutane sosai.., shi kuma Doctor ya yima kansa mazauni a kan ɗaya daga cikin kujerun falon yana jiran futowar abokin nasa.
Hajiya Halima wadda ke facing ƙofar daga inda take zaune ita ta fara hangen Yusuf ɗin, ta na kallon fuskarsa ta fahimci akwai matsala, saboda Yusuf mutum ne mai haƙuri da biyayya amma idan ransa ya ɓaci ba shi da daɗin sha'ani ko kaɗan, wani murɗaɗɗen mutum ya ke komawa mai taurin kai da rufewar idanu. Cikin azama ta zunguri Hajiya ta ce,"ga Yusufa nan ga dukkan alamu shegiyar ce ta zigo shi, na san ba zai wuce zan ce musayar ɗakin da mukai mata bane ya janyo wannan matsalar."
Taɓe baki Hajiya ta yi sannan ta ce,"to sai me idan ta zugo shi? In zata iya zama a wancan ɗakin ta zauna idan kuma ba zata iya ba ta koma gidan Ubanta."
A dai'dai wannan gaɓar Yusuf ya shiga ɗakin da sallama, sai da ya rusuna sannan ya gaishe su mafi yawa da ga cikin mutanan ɗakin sun amsa gaisuwar amma banda Hajiyarsa, wadda ke zaune kusa da Hajiya Halima. Ganin acting ɗin hajiyar da ya gani ne ya sa ya ƙara dedaita sautin muryarsa ya ce,"Hajiya ina yini?"
A daƙile ta amsa a ransa ya na mamakin hali irin nata, amma sai ya daure ya dubi Hajiya Habibah wadda ke zaune akan sallaya ya ce,"Aunty Habibah ina son magana da ke." ya na gama faɗin haka ya fice daga ɗakin zuwa falo inda ya bar Doctor Umar.
A falon Hajiya Habibah ta samesu shi da Doctor a zaune, cikin sakin fuska ta zauna a kujerar dake facing ɗin su, ganin haka ya sa Dr. Umar ya zamo ƙasa ya gaisheda da girmamawa.
Fuskarta a sake ta amsa sannan ta maida dubanta ga Yusuf ta ce,"na san wannan zaman ba zai wuce akan musayar ɗakin da Hajiya tasa akayiwa Bilkisu bane ko?"
Jin haka sai yasa ran Yusuf ya ƙara ɓaci, hular kansa ya zame cikin matsananciyar damuwa ya ke motsa idanunsa waƴanda su ka faɗa saboda fitinar Hajiya ya ce," Aunty Habibah na rasa inda zan tsoma raina wllhi, kullum cikin ɓacin rai da damuwa nake rayuwa a cikin gidannan, kullum ji nake a raina kamar na gaza bawa matata farin cikin daya kamata ace na bata. Ban san meye matsalar Hajiya akan Bilkisu ba, duk wata biyayya da kyautatawa tana yi mata fiye da yanda nake mata, tun da na auri Bilkisu yau kimanin shekara biyar muna neman ta shida hajiya bata taɓa barin yarinyar nan ta zauna lfy ba. Ban san abinda ya kamata inyi akan wannan lamarin ba wllh kaina ya kulle, but pls don Allah Aunty Habibah ki taimaka min ki shiga maganar nan pls!"
Shiru Hajiya Habibah ta yi tana tunanin ta inda zata ɓullowa lamarin, a hankali ta ɗaga kai ta kalleshi ta ce," Yusuf a duk duniyar nan ba wanda ya isa ya takawa Hajiyarka birki akan al'amarin gidanka sai Baffa Hashimu. Shi ka ɗai take shakka kuma take jin maganarsa, bayan haka babu wanda ya isa ya gaya mata magana taji. Amma ka kwantar da hankalinka yau ɗinnan zan kirashi in sanar dashi komai, na tabbata zai shiga maganar."
Ajiyar zuciya Yusuf ya sauke mai zurfi sannan ya langaɓar da kai cikin alamun karaya ya ce,"ina jin tsoro kar daga baya ta tuhume ni da laifin na kai ƙararta."
"I'll handle everything, don't worry about that. You just go and take care of what you need to do, kafin a tafi gurin Dinner ɗinan zan tabbatar da cewa an mayarwa da Bilkisu kayanta cikin falonta."
Jinjina kai ya yi cike da gamsuwa da maganarta ya dubi Doctor Umar ya ce,"Muje."
Sallama su kai mata sannan suka fita daga falon cike da ƙarfin gwiwar samun mafita.
Hannunsa Doctor Umar ya kama alamar ya tsaya, cikin nutsuwa Yusuf ya juya ya fuskance shi sosai ya ce," Doctor ya akayi?"
Ɗan jim Doctor ya yi sannan ya ce,"Yusuf, do you really think putting Aisha and Bilkisu together in one place will bring you peace? Ka fi kowa sanin fitinar Aisha tun kafin ka aureta, haɗasu guri ɗaya sai nake gani kamar hakan zai iya zama matsa ga Bilkusu."
Zame hannunsa yusuf ya yi daga ruƙon da Doctor ya yi masa, cikin sanyin jiki da rashin ƙarfin gwiwa akan hukuncin da ya zartar ya ce,"na riga na yanke hukunci, kuma bana zaton hakan zai zama matsala a gurin Bilqis."
"amma sai nake ganin kamar akwai cutarwa a cikin wannan hukuncin naka." cewar Doctor
"Don Allah Doctor Umar kayi shiru akan wannan maganar pls. Long before I married Bilkisu, she already knew there was a relationship between me and Aisha Sulaiman, already ta san da maganar ba sabon abu bane. A baya Aisha iyayena suka zaɓa min matsayin wadda zan aura, amma da yake a lokacin Allah bai ƙaddara zan aureta ba sai na fara auren Bilqis saboda ina sonta sosai. Yanzu da Allah ya ƙaddara itama matata ce ai gashi zan aureta kuma in haɗasu gida ɗaya, na tabbata dole Bilkisu ta kwantar da hankalinta su zauna lfy tunda tana son zama dani." Yusuf ya ƙare maganar cikin nuna jin haushi.
Tun da ya fara magana Doctor ke masa wani irin kallo wanda yafi kama da na rainin wayo sannan ya ce,"wllhi ƙarya kake baka gayama Bilkisu kunyi soyayya da Aisha Sulaiman ba, baka gaya mata gaskiya ba kawai nuna mata kai Aisha ce ke sonka alhalin kuma ƙarya kake yi. Duk sanda ka zauna da Bilkisu nana mata kake hajiya ce take tilasta maka akan maganar auren Aisha. But honestly, I fear for you on the day Bilkisu will find out the real reason why you married her, ranar data gane haka sunanka mayaudarin masoyi kuma wallahi ba zatayi la'akari da girman son da kake iƙirarin kana yi mata ba."
Jikinsa ne ya yi sanyi a lokacin da ya yi realizing abinda Doctor yake hango masa a gaba, rasa abinda zaice ya yi sai kawai ya juya ya fara tafiya a hankali cikin rashin guzari, a haka ya ƙarasa inda motar ya zainab ke ajiye.
A wannan lokacin muna cikin mota ni da Ahmad sai ya zainab dake zaune a Driver sit ta zubawa waje ɗaya idanu, wayarta ce ta fara ringing don haka ta miƙa hannu ta ɗauka tana kallon screen ɗin wayar.
Murmushi ta yi sannan ta kalleni ta ce," its your twiny. Fitinanniya barin ɗaga naji dalilin da ya hanata ƙarasowa har yanzu." ta ƙare maganar tana picking call ɗin ta ce,
"Hajar na jiki shiru har yanzu baki ƙaraso ba. Hala kin manta da maganar Dinner ɗin ne?"
Da ga can ɓangaren Hajar langaɓar da kai tayi sannan ta kalli Inno wadda ke zaune akan Sallaya ta ce,"wllhi ya zainab tun ɗazu na gama shiryawa amma Inno ta hanani mukullin mota wai ba zan fita da ita ba, ni kuma bana so na hau keke napep da wannan uban make-up ɗin dake fuskana, idan da hali don Allah ki sa baki ki nuna mata mahimmancin zuwa dinner da mota pls." ta ƙare maganar cikin marairaicewa.
"bata wayar" cewa ya Zainab, miƙawa Inno wayan ta yi sannan ta matsa baya ta kafeta da idanu tana jiran taji abinda zata ce.
Da murmushi kwance a kyakkyawar fuskarta ya zainab ta ce,"inno barka da yamma"
"barka dai zainabu Ashe har kun iso gari." cewar Inno.
"Eh wllh tun jiya muka iso amma ko gida bamuje ba muka sauka a gidan ƴar gaban goshin ki." ya zainab ta faɗi haka cikin zolaya da dariya mara sauti.
Itama inno dariyan ta yi sannan ta ce,"ai saisa na yafe muku rashin zuwan da bakuyi ba, saboda na san hidimar Bilkisu ce ta kawo ku kaduna, ni kuma indai akan lamarinta ne ni mai yawan afuwa ce."
"saisa nace Hajar ta baki wayar in tuna miki hidimar Fafah ce bata kowa ba."
Murmushi Inno tayi har sai dahaƙoranta sika baiyana sannan ta jefawa Hajar Makullin motar ta ce,"jeki ubangiji ya tsare hanya don Allah banda tuƙin ganganci, ke kuma zainab ku maida hankali sosai ku rarrashi Bilkisu karta saka damuwa a ranta, karku dinga barinta ita kaɗai don Allah."
"In sha Allahu Inno zamu kula da ita." cewar ya zainab sannan su kai sallama da juna akan gobe zata shigo kafin ɗaurin aure.
A haka Yusuf ya ƙaraso ya samemu, da girmamawa ya ce,"ya Naimah ku shiga ciki kuyi sallah dama ba wata matsala bace ƙurar falon aka karkaɗe, amma yanzu za'a mayar da kayan ciki dama wai zuwan mai fenti ne yasa aka fitar da kayan waje."
Mamaki ne ya kamani jin ƙaryar da yayi don ya ɓoye rashin kyautawar danginsa. Murmushi ya Na'imah ta yi sannan ta ce,"masha Allah! Bari mu shiga muyi sallah kafin lokacin tafiya Dinner ɗin yayi" ta firta hakan tana buɗe mini ƙofar bayan motar.
A hankali na ziro ƙafata waje wadda tasha baƙin lalle cikin wani Designer ɗin takalmi mai tsini, tun daga fatar ƙafata wadda ke shaining ya fara kallona zuwa fuskata, wadda aka cancaɗa min ado mai kyau da burgewa.
Da ga can ƙasan zuciyarsa tazbihi yake ga Allah wanda ya azurta shi da samun mace kyakkyawa irina, amma a zahiri sai ya yi murmushi ya matsa dab da kunnena bayan na sauka daga motar ya ce,"You look very beautiful, so I will personally pick you up in my car and take you to the dinner. Na ɗaukewa ya Na'imah wannan nauyin a kanta."
Takaici ne ya kamani na kasa ɗaga kai na kalleshi, ganin irin kusancin dake tsakaninmu ya sa su ya Na'ima sukai gaba suka barni don mufi sakewa da juna, ganin haka yasa ya janyoni jikinsa ya rungumeni yana shaƙar ƙamshin jikina. A wannan lokacin tuni Doctor Umar ya shige mota yana jiran isowarsa.
A wahalce ya fara ƙoƙarin neman ƙwayar idanuna amma fir na hanashi wannan damar, saboda har ga Allah ban shirya karɓar baƙuncin fitinarsa ba. Murmushine ya ratsa ta tsakanin laɓɓansa sannan ya ƙara ƙwaƙumata har sai da na ɗanyi ƙara kaɗan, ya haɗe forehead ɗinmu guri guda cikin wata kasalalliyar murya ya ce,"You have dignity Bilqis. Yes, you truly have it." ya firta hakan yana ƙoƙarin kwance ɗankwalin kaina.
Ƙoƙarin janye jikina na fara amma sam ya hanani wannan damar, ganin ya fara wuce gona da iri ne yasa na fara kuka a hankali, sai da ya fara jin shash-sheƙar kukana sannan ya sakeni da sauri ya fara ja da baya, ban bashi damar magana ba na juya da sauri na bar harabar gidan, cikin rashin guzari ya yi mini rakiya da ƙwayar idanunsa.
A hankali nake tafiya ina share hawayen da suke zuba ba tareda na basu umarni ba har na ƙarasa ƙofar falon banyi gigin juyawa na kalleshi ba.
Sai dai na sa a raina cewa ba zan sauya kayan jikina ba kamar yanda ya buƙata dasu zanje taron dinner, ban damu da mutanan da na gani a falon ba kai tsaye na wuce bedroom ɗina, da dabara na zare mayafin jikina sannan na saka hijjabi na kabbara sallar magrib, mintuna biyar na ɗauka sannan na idar, ina nan zaune har aka kira sallar isha.
Sai wajan ƙarfe tara sannan motoci suka fara ɗibar mutane zuwa wajan Dinner ɗin, ni dai har lokacin ina ɗaki sai da na dena jin motsin mutane sannan na fito walking slowly zuwa ɗaya ɗakin in da su ya Naima suke, a hankali na tura ƙofan bakina ɗauke da sallama to my surprise ba kowa a ɗakin sai kayansu da suka cire a saƙale jikin hanger.
Jiki a sanyaye na koma ɗaki na ɗauka wayana na fara kiran ya zainab, bugu ɗaya ta ɗauka kamar zan fashe da kuka na ce,"Why are you leaving without talking to me?"
"Yusuf ne ya ce zai zaku tafi tare saisa muka tafi, ki kwantar da hankalinki uwar gida naki isowar mai Capacity ce." ta ƙare maganar tana dariya.
"Ya zainab Twiny ta ƙaraso kuwa?" na tambaya a sanyaye.
"Eh kin ganta duk muna tare amma bamu shiga holl ɗinba zamu jira ki ƙaraso tukunna."
"To ya Zainab thank u." na firta hakan tareda katse wayar, a hankali na miƙe na isa jikin mirror na ƙurama kaina ido ina kallon yanda kayan jikina suka zauna min ɗas, lumshe idanu nayi sannan n ƙara buɗewa na kai hannu na ɗauki sosin powder na ƙara gyara fuskata, sannan na ɗauki humra na ƙara shafawa a jikina na koma gefan gado na zauna.
Tunanin rayuwa ne ya fara karakaina a ƙwaƙwalwar kaina, nan da nan damuwar duniya ta isheni, sai na fara ji a raina tamkar duniyar ta juya min baya, cikin ƙanƙanin lokaci ruwan hawaye ya fara ƙoƙarin samawa kansa gurbi a tsakiyar idanuna, tissue na zara na goge saboda karna ɓata kwalliyata.
Kwanciya nayi tareda jan wayata na kunna data, ina kunnawa idona ta sauka akan status ɗin ya Khadir. Gyara kwanciya nayi na danna a hankali ina kallon hotunan da ya ɗora, jikina ne ya yi sanyi na dinga kallon caption ɗin ƙasa hoton ina maimaita kalmar a raina, sai kawai na kashe datar na miƙe a hankali na zauna dedai lokacin wayana ya fara ringing........
Kafin in amsa kiran na ji sallamar Yusuf daga bakin ƙofar dakin, walking slowly ya shigo cikin ɗakin sanye da farar shadda ɗinkin babbar riga, sosai shigar tayi masa kyau ta ƙara fito da kwarjinin da Allah ya yi masa. Murmushine kwance a saman fuskarsa sai dai hakan bai hana idanunsa fallasa damuwarsa ba. Tsayawa yayi cak yana kallona na tsahon minti ɗaya sannan na ɗago idanuna muka haɗa ido.
A karo na farko ban iya ɗauke kaina ba, sai kawai na saki ajiyar zuciya.
"Kin shirya Bilqis?" Ya tambaya a sanyaye, yana ƙoƙarin ɓatar da musmushin da ya yima fuskarsa ado.
Kai na ɗaga a sanyaye na ce,"Eh na shirya."
Shiru ne ya ratsa gurin still idanunsa a kaina, cikin nutsuwa ya ƙaraso gabana ya kama hannuna cikin nasa ya fara matsawa a hankali, wani iri yake ji a ransa tamkar bashi ba, ji yake tamkar ya aikata kuskure mai'girma da yabi son zuciyarsa, gani yake tamkar ya keta alfarmar amanar da aka jima da danƙawa a hannunsa. Lumshe idanunsa ya yi a hankali sannan ya jani jikinsa ya rungumeni, lafewa nayi a jikinsa na ƙara riƙe hannunsa ƙam. Lokakaci guda hawaye masu zafi suka fara zubo min.
Janyeni ya yi daga jikinsa, sannan ya zaunar dani a gefan gado ya tafi gaban dressing mirror ya janyo Tissue ya durƙusa a gabana ya fara share min hawayen a hankali.
Da kulawa yake tsane hawayen gudin kar ya ɓata min kwalliyar, sai da ya gama tsaf sannan ya sassauta muryarsa ya ce,"kinyi kyau sosai ƙaunata, don Allah karki sake yin kuka zaki ɓata kwalliyar kinji?"
Ɗaga masa kai nayi sannan ya yi murmushi ya kai bakinsa ya sumbaci lips ɗina na ƙasa. Miƙewa ya yi sannan ya ɗagoni ya gya min mayafin jikina ya kama hannuna muka fita zuwa falo, mamakine ya cika min zuciya ganin an mayar min da kujeruna da aka fitar, komainan mayar dashi inda yake ba abinda aka saɓa.
Ganin yanda nake kallon falon da mamaki ne ya sa yayi murmushi ya ce,"All this that you are seeing is the work of Aunty Habibah. Ita ce ta tsaya kai da fata wajan ganin ba'a cutar dake ba."
Ni dai shiru nayi bance komai ba, yaja hannuna muka fita harabar gidan, ko ina shiru kowa ya tafi gurin Dinner sai mai gadi kawai da wasu daga cikin baƙi mazan da suka zo daga ƙauyen su Yusuf.
Shine ya buɗe min bayan motar na shiga na zauna, sannan ya zagaya ya shiga ta ɗaya ɓangaren, sai a lokacin na lura da Doctor Umar wanda ke zaune a Driver sit sanye da brown ɗin shadda. A hankali na ce,"Doctor ina yini."
Murmushi ya yi sannan ya amsa ya ce,"Uwargida Sarautar mata."
Wannan kalmar da ya faɗa sai naji tamkar ya sokeni da mashi ne, don haka sai nayi shiru na gaza cewa komai tamkar ruwa ya cinyeni. Ganin haka ya sa shima ƙara cewa komai ba ya tsuke bakinsa. A haka muka isa cikin Arewa Hausa inda ake Dinner ɗin.
Muna isa Doctor ya samu guri ya yi parking, sannan ya juyo baya ya kalli Yusuf ya ce,"Amarya fa ta iso tun ɗazu kai take jira ku shiga tare."
"No Doctor don Allah kaje ku rakata ciki ni zan taho tareda Bilqis." ya firta hakan a dake don kar Doctor Umar ya yi masa musu.
Ƙura masa ido Doctor ya yi yana kallon ikon Allah, ganin bashi da niyar sauka ne yasa don dole Doctor ya fita daga motar zuwa can inda motar amarya take.
Yana isa gurin ya samu amarya tareda Fahad da su Faridah Attahiru sai yauƙi ake ita a dole ƙanwar ango, hannun Fahad Doctor ya kama sannan ya yi masa raɗa a kunne, jinjina kai Fahad yayi sannan ya ce," ƙawayen amarya lokaciɓ shiga da amarya ya yi."
Wani kallo Aysha ta watsama Fahad sannan ta kalli Doctor ta ce," na rantse da Allah ba inda zani idan bezo mun shiga tare ba. Sai dai a fasa taron kowa ya kama gabansa."
***