Kuncin zuci
by @bintuuu
Back to main story....
A wannan lokacin Na'ima kasa daukan wayan hannunta tayi, ta rinqa kallon duka maza biyun da ke da alaqa da ita, dukansu tsaye anan street din, gani tayi Ahmad ya sauqar da wayan daga kunne yana kallon screen din dalilin bata dauki kiran ba sai ya maida wayan cikin aljihunsa ya fara takawa alamun zai taho cikin building din nasu sai tayi saurin kiransa ya sake ciro wayan ya daga, cikin kwantar da murya yace "Babe i'm outside" kintsa muryan ta tayi tace "Yanzu zan sauqo, kayan nake hadawa" sai yace "Bari nazo in tayaki dauka" Na'ima tayi saurin girgiza kai tareda cewa "No no no..ai ba yawa ma, ganinan zuwa" Ahmad yace "Okay", sai lokacin Bilal ya samu abun hawa, tana gani ya shiga suka tafi, cikin sauri ta juya ta nufi dakin Nafisa dan nata mirro yayi kaca kaca a tsakar dakin, jawo jaka tayi kawai ta rinqa tula kaya aciki batareda sanin ma wanne take diba ba, tana hawaye ta qarasa gaban madubin dakin ta kalli fuskanta, gefen lips dinta ne yadan fashe sai can saman goshinta da ya dan tashi sanadin bugata da kujeran da Bilal din yayi, dago hannunta tayi tana kallon yanda glass din ya yanke ta, sai ta fashe da kuka tana kallon kanta a madubin, share hawayen ta tayi da bayan hannu afili tace "You won't see fall Bilal...You will never see me fall" ta qarasa maganan tana fashewa da wani sabon kukan, sai tayi saurin shiga bandaki ta wanko hannun nata da ya dan baci da jini tareda wanko har fuskanta ta gyara gashinta, face mask ta nema bayan ta fito, anan falon ta dauki veil dinta da ke yashe a qasa sannan ta fice riqe da jakan a hannunta, kanta a kasa ta fito wajen, Ahmad dake tsaye jikin mota har sannan yayi saurin qarasowa gurinta tareda karban jakan yana kallonta yace "Kin dade Babe, meya faru?" kanta a qasa tace "Kayan na rasa" sai ya tsaya kallonta ganin tana ta sunkuyar da kai, ganin yana kallonta yasa ta fara nufan motan ya biyota ya bude mata front seat din, a back seat ya saka jakan sannan ya shigo bai daina kallonta ba, ahankali yace "What happen Na'eemah?" juyowa tayi ta kallesa sai tayi murmushi tacikin face mask din tace "Babu komai, kaine kemin ciwo na dan buge a daki ne dazu" da sauri yace "Subhan Allah, sannu Babe" ta gyada kai kawai tajuya tana kallon window, a hanyarsu ta tafiyan bini bini Ahmad zai juya ya kalleta har sannan kanta yana jingine jikin window din and she was trying so hard not to tear up a gabansa, sai da suka koma school din Ahmad ya kira Nafisan a waya ta fada musu tanacan wani underground parking lot, takai ajiyan motan nasu saboda zasu koma acikin na Ahmad din, lokacin da ya faka a gurin da suke hango Nafisan na tahowa sai ya kalli Na'iman, cikin kwantar da murya yace "Babe are you sure you're Okay?" dan yanayin nata yasa jikin sa ya bashi she's not alright, kallonsa tayi sai ta kasa jure irin kallon da yake matan tayi saurin sauqe idonta tace "I'm fine" sai ya duqo kansa ze sake magana Nafisa ta iso, dan gyara zama yayi ya juya yana kallon street, shiga backseat Nafisa tayi tareda sallama sannan ta gaishe da Ahmad, a nutse yace "Lafiya Nafisa, ya school?" ta amsa da "Alhamdulillah" sannan ta kalli Na'ima tace "Sorry Bobo I've missed your call dazu, ina gurin supervisor na lokacin" dago kanta Na'iman tayi wanda hakan sai da yasa zuciyar Nafisa bugawa ganinta da face mask, a iya saninta da Na'iman tasan bata saka face mask sai in tana son rufe ciwo a fuskanta, dan tsayawa kallon kallo sukayi sai Na'ima tayi saurin kauda kanta ta koma kallon window gudun kar tayi kuka, sai sannan Ahmad ya tada motan suka dau hanyan barin Oxford, shiru motan yayi babu me cewa qala acikinsu kowa da abunda yake saqawa a zuciya, basu tsaya da tafiyan ba sai da suka isa Beaconsfield town dake kan hanyarsu na tafiyan, nan wani filling station Ahmad ya tsaya zai qara mai a motan yace "I'm coming please" Na'ima ta gyada kai, yana fita Nafisa ta sako kanta gaban motan tace "Na'ima ina kikaje?" sai tace "Not now Nafisa" ta juya kanta, sanyi jikin Nafisan yayi ta koma ta zauna....Lokacin da Ahmad yayi parking a kofar gidan Anty Amnah da dan sauri Na'ima ta yi masa sallama ta fita ya bita da kallo yana dan jin wani iri, sai Nafisan ta masa sallama itama, kafin ta fita ya miqo mata ledan maganin da ya siyawa Na'iman na ciwon kai, bayan sun shiga gidan sai ya kasa tafiya ya fito shima ya rufa musu baya...
Shigan su Na'iman falo suka ga Laila zaune da Anty Amnahn suna hira, ita Na'ima har ta manta ma Lailan tazo garin, Anty Amnah tace "Kun dawo" suka qarasa Nafisa nacewa "Eh Anty", Laila da bata kulasu ba sai kallon Na'iman take gashi har sannan bata cire face mask din ba, basu zauna ba Nafisa tasake cewa "Anty bari mu watso ruwa mu dawo, duk mun gaji wallahi" Anty Amnah ta amsa da "Toh, in kun huta ga abinci can a kitchen" kafin su amsa Ahmad ya shigo sai Laila ta miqe tana masa murmushi, Nafisa ta amsa da toh tareda dan riqo hannun Na'iman suka shige dakin nasu, saida Nafisa ta rufe kofan dakin da key sannan ta juyo tana kallon Na'iman dake zaune bakin gado tace "Ina kikaje Na'ima?" sai lokacin Na'ima ta cire face mask din nata tafara hawaye tace "Meyasa zaki boyemin Bilal yazo London Nafisa?" cikin shock Nafisa ta ware ido tace "innalillahi... did that idiot hit again?" Na'ima bata amsa tambayan ba ta sake cewa "You should've told me Nafisa" dan stiff Nafisa tayi sai ta zauna gefen Na'iman tace "I'm doing this for you Na'ima, billah na boye miki ne for your sanity, i don't want you to get worried" hawayen Na'ima ta cigaba dayi tace "He beat me Nafisa, wai saina bishi" Nafisa ta riqo hannunta tanajin zuciyar ta babu dadi sannan tace "Babu inda zaki bisa wallahi, shi din banza" sai ta dago wayanta tareda cewa "I'm calling Mami now" da sauri Na'ima tace "Karki kirata please" tace "We have to tell them Na'ima, har Yaya Ahmad ma" girgiza kai Na'ima tayi cikin sauri tace "Dan Allah karki fada masa komai Nafisa, na shiga uku" kawai ta fashe da kuka, sanyi jikin Nafisa yayi sai ta rungumota tace "it's Okay, it's Okay, i won't tell him har saikin amince" ta dago Na'ima tana kallonta tace "Amma ki fadamin dalilin da bakya so ya sani" Na'ima na share hawaye tace "I just...I just" ganin haka yasa Nafisan cewa "Don't tell me kina tsoron yasan kin taba aure Na'ima" ta girgiza kai ahankali tace "A'a" sai Nafisa tace "Then what?" shiru Na'ima tayi at first sai can tace "Nasir...i don't even know how he'll take that Nafisa, I'm not ready" tsayawa kallonta kawai Nafisa tayi takasa cewa komai, can ta sauqe numfashi tace "Do you really think Ahmad zai gujeki akan haka Na'ima? what are you even thinking? Do you see the way he look at you everytime? That guy loose his guard anytime he's in front of you Na'ima, wanda cikin mu kaf danginsa babu wanda ya taba ganin wannan side din nashi sai ke, why are you even thinking of hiding such thing from him?" Na'ima ta kasa magana ma at that time, sai Nafisan ta cigaba "I know you like him too Na'ima but stop holding yourself back akan pig dincan, sannan kisani...this time around Bilal has found a match beyond him, kiyi addu'a kar Ahmad ya kashe shi in yaji abunda yayi wallahi" shiru Na'ima tayi har sannan batace komai, sai Nafisa ta tashi ta fita, study room din Anty Amnah ta nufa ta wuce Ahmad dake sallah a falon, Anty Amnah da Laila suna kitchen, dauko maganin shafawa tayi ta koma daki, nan kan gadon ta zauna taja veil din Na'iman data rufa goshinta sannan ta fara shafa mata, rufe Ido Na'ima tayi tanajin komai na dawo mata sabo, dukan da Bilal din ya mata a baya ta fara tunawa har sannan bata bar hawaye ba, Nafisa na kallonta cikin karyewan zuciya tace "Ki fadamin me ya miki Dan Allah" cikin rawan murya ta fara fada mata abunda tayiwa Bilal din, har ta gama magana Nafisa na kallonta cikin mamaki, sai tace "Abunda nakeson kiyi tun shekarun baya ne Allah ya baki ikon yi yau" ta kamo kafadan Na'iman tace "And you did the right thing Bobo, I'm so proud of whom you're becoming"...Bayan sunyi sallah sai Na'iman ta kwanta nan kan gadon tace ba yanzu zata fita ba kanta yana ciwo, da haka Nafisa ta fita falon tasamu su Ahmad din a dining area Laila na serving dinsa, dan bin bayan Nafisan yayi da kallo amma baiga Na'ima ba, Anty Amnah tace "Ina Na'iman fah" tace "Ta dan kwanta kanta na ciwo" Jan kujera tayi tana kallon Laila dake serving Ahmad din cikin yanga, dan kadan ya ci abincin sannan yasha ruwa yanajin zuciyar babu dadi ya miqe, Laila tace "Haba Yaya, bakaci sosai ba fa" bai ce komai ba Anty Amnah tace "Na fada miki cin abincinsa ba sosai bane ai kika dafa dayawa" Nafisa dai sai kallon Lailan take ganin ta wani shagwabe fuska, aranta tana fadin "iska na wahalar da me kayan kara"...Na'ima bata fito taci abincin ba har dare, dan nan dakin Anty Amnah ta shigo tareda twins suka kawo mata abincin jin shiru bata fito ba, bayan ta mata sannu ta gyara mata blanket din sannan ta kama hannunsu suka fice, har lokacin Na'ima ba baccin tayi ba kawai ji take komai baya mata dadi, tana kallon kiran Ahmad na shigowa wayanta amma bata dauka ba, har Nafisa tayi bacci a gefenta idonta biyu, ganin hakan yasa ta tashi tayo alwala, sai bayan ta idar da sallan ta daga hannu zatayi addua taji kuka yazo mata, har ta gama ta koma gadon ta zauna bata daina hawaye ba dan ganin Bilal din da tayi yau din ya tada mata abubuwa da dama da tayi tsammanin sun wuce a rayuwanta, wani kiran Ahmad din ne ya sake shigowa wayan nata, sai sannan ta dauka takai kunne, shiru sukayi..daga daya bangaren Ahmad na tsaye bakin pool din gidansa sanye da Pj's hannunsa riqe da glass cup me dauke da champagne yana kurba kadan kadan, shiru sukayi na tsahon seconds kafin yace "Ya kan naki fa?" ahankali tace "Yayi sauqi" cikin nutsuwa shima yace "Sorry dear" bata amsa ba, ya sake cewa "Bakiyi bacci ba, ko na tadake?" tace "Uhm uhm" suka sakeyin shiru, cikin sanyin murya ta sake cewa "I want to tell you something" Jin yayi shiru yasata cewa "I'm sorry i didn't tell y.." bata qarasa ba taji yace "Shhhh, get some sleep now okay, we'll talk tomorrow" da sanyin jiki tace "Toh" yace "Allah ya baki lafiya" da haka sukayi sallama, ta bangaren Ahmad bayan ya kashe wayan sai ya tsaya nan riqe da cup din yana kallon cikin pool din like he was lost in thoughts.....
Washegari da sassafe sai ga kiran wayan shi lokacin da Na'iman ta shiga toilet, data fito sai taga Nafisan na miqo mata wayan tace "He's calling" karba tayi ta kai kunne bayan ta amsa kiran, bayan ya amsa gaisuwan ta yace "I'm outside, I'll be waiting for you" shiru tayi sai ya sake kwantar da murya yace "Babe" tace "Toh", shiryawa tayi cikin riga da wando me fadi sai ta saka dogon jacket daya wuce gwiwanta sannan tayi rolling veil, Nafisa na kwance kan gadon tana danna wayanta, sai da Na'iman tace mata zata fitan sannan ta miqe zaune tace "Please Na'ima try and tell him what he needs to know, bance sai kin fada masa komai ba tunda baki shirya hakan ba, but i know Yaya Ahmad will be ready to cross that river with you when the time comes" gyada kai Na'ima tayi tareda cewa "Toh" sannan ta fita, babu wanda ya tashi a gidan dan har Hajiya Laila tana can guest room tana bacci har sannan itama, tun fitowanta Ahmad dake jingine da motan yake kallonta har ta qarasa ta tsaya nan gabansa, sai taga ya bude mata front seat, bata ja ba ta shiga sannan ya zagaya shima ya shiga, cikin twenty minutes Ahmad yayi parking motan a arean Westminster bridge, kallon gurin Na'iman ta rinqa yi tanajin fresh view din na saka mata nutsuwa, saida Ahmad ya dauko packet din da ya taho dashi na hot coffee sannan suka fara takawa asannu, tafiyan suke a sannun cikin shiru, sai can Ahmad yace "This is one of my favorite places in London" Na'ima na kallon yanda boats suke wucewa akan ruwan tace "It's beautiful" tsayawa sukayi jikin rail na bridge din yace "I always come here when i needed some 'alone time' for myself", coffee yaciro ya miqa mata ta karba amma bata sha ba, tana kallonsa tace "I'm sorry for how i acted yesterday" yana kallonta shima yace "Babe, me yake damunki?" sai ta juya ta kalli river'n, cikin kwantar da murya Ahmad ya sake cewa "You can tell me" bata kallesan ba cikin sanyin murya tace "I was married before"...jin yayi shiru yasata juyowa ta kallesa sai taga kallon ruwan yake kamar me tunani, ta sake cewa "Ba daga nijar nazo ba, ni 'yar asalin qauyen Adamawa ce amma na rayu a Kano" sai sannan taga ya kalleta wanda hakan yasa ta kasa jure kallon idonsa ta sauqe idonta, a nutse yace "Na'eemah look at me" bata dago kan nata ba sai ya kai yatsansa ya dago habarta ta kallesa idonta na kawowan hawaye, bai bar kallontan ba yace "Were you afraid to tell me this?" ahankali ta gyada kai sai ya kamo hannunta ya damqe cikin nashi, dan stiff Na'ima tayi Jin haduwan hannun nasu kamar an jona mata electric wire, yana riqe da hannun nata yace "Even if you had to marry a hundred times, I'd choose you a thousand times Na'eemah" ji tayi zuciyarta na melting da wani irin feelings a lokacin, sai ga hawaye na fitowa daga idonta, ya kai hannu yana share mata su, yana dan murmushi yace "You're a cry baby Na'eemah, how do you even survived in marriage da wannan kukan naki" murmushi ta fara idonta da hawayen batace komai ba, coffee din suka fara sha suna kallon ruwan sai can yace "Did he hurt you?" da sauri ta kallesa takasa cewa komai, sai ya kalleta yace "Shi ya yanka miki hannu?" nan ma da sauri ta girgiza kai tace "A'a, yankewa nayi" sai Ahmad ya gyada kai, ganin ya fara mata tambayoyi yasa Na'iman cewa "Ya akayi accent dinka yazama haka?" yayi murmushi yana kallonta yace "A Canada na tashi, iyayena sunyi zama acan tun ina yaro" ta gyada kai sai ya sake cewa "Na taba ganinki a Kano" ta ware Ido da dan mamaki tace "Anya ni ka gani, ban taba saninka a baya ba" dan duqawa yayi ya jingina da rail din bridge din, yana kallonta yace "I never forget a face, more especially naki, kinje gidan Abba ranan" ta gyada kai tana qoqarin tunowa amma ta kasa, yace "Kinada auren a lokacin?" cikin sanyin jiki ta sake gyada kai, yana kallon cikin idonta yace "Daga wannan ranan zuwa yanzu shekara daya kenan, da wata takwas da kwana uku Na'eemah, Astaghfirullah, but you've been on my mind since that day".......
Don't forget to follow my account and like this story please