Chapter 10
by @zmchubado
Fitowa Aisha ta yi daga cikin motar ta tsaya a gaban Doctor Umar tana kallon idanunsa ba tareda kunya ba, hannu ta ɗora a ƙugunta ta na binsa da kallon raini, ba ta damu da zirga-zirgan da mutane keyi a gurin ba ta ce,"wllhi sai dai a fasa dinner ɗin nan ko wani shege ya tafi gidan Ubansa indai yace ni kaɗai zan shiga gurin nan. Wannan ai rainin hankaline da rainin wayo, sai kace wanda mukai auren ƙiyayya da shi?" ta firta haka hawayen baƙin cikin da take ɓoyewa suka zubo. Tun da ta fara magana Doctor ke kallonta har ta dasa aya ya kasa ce mata komai, har ga Allah bai san abinda ya kamata yace mata ba, saboda ya gama karantar tsantsar rashin kunyarta tun daga irin kallon da take masa. Mamaki gami da al'ajabin dalilin da ya sa Yusuf ya zaɓi auren Aisha suka haɗu suka mamamaye masa zuciya. Daga can ƙasan zuciyarsa mamakin yanda akai wannan marakunyar yarinyar ta samu gurbi mai girma a zuciyar Yusuf ya keyi, a nitse ya ɗaga Idanunsa yana kallon ƴan bikin dake kai komo a harabar gurin. Yayinda wasu daga ciki suka zuba masu idanu suna kallon yanda take zazzaga masu bala'i kamar ta ari baki, kunya ce ta kama Doctor ganin yanda duk ta tara musu jama'a aka.
"Ku koma ku gaya masa wallahi ba inda zan je, saboda ni ba ƴar iska bace da zai raina mini hankali ya turo ku da sunan in shiga gurin bikina ni kaɗai ba tareda shi. Kai ko a bazawara ya nemi aurena aka bashi ba zan ɗauki wannan cin kashin daga gareshi ba, Na rantse da Allah sai dai yayi asarar kuɗin hall ɗin don zai mai dani tambaɗaɗɗiya mara galihu a idanun mutane ba," Aisha ta sake katsewa Doctor tunani ta hanyar faɗar haka.
Ajiyar zuciya Doctor Umar ya sauke tareda gyara natuwarsa ya ce,"Aisha meye amfanin wannan abinda kikeyi don Allah? So kike ki tara mana mutane akan ɗan ƙaramin abu?" cewar Doctor Umar. Harara ta watsa masa sannan ta ɗauke kai ta fara ƙoƙarin share hawayenta da tissue gudin kar ta ɓata makeup ɗinta, sai da ta ɗan ja majinar data fara taruwa a cikin hancinta sannan ta ce,"wllh Umar ba zan shiga gurin nan ba har Sai Yusuf ya zo da kansa, idan ba haka ba sai dai gaiyar ta watse kamar yanda na gaya maka tun farko."
Doctor Umar da har lokacin yake tsaye kamar an dasa shi ya juya ya kalli Fahad wanda mamakin halinta ya hanashi magana ya ce,
"Fahad kana jin abinda take cewa ko? Don Allah ka saka baki ko kai za ta ji maganarka"
Taɓe baki Fahad yayi sannan ya ɗauke kai gefe ya ce,"so kake yanda ta rufe ido tana gaya maka maganar banza nima ta gaya min ko me?"
"don Allah Fahad ka saka baki wataƙila kai ta raga maka." cewar Doctor.
"Saboda Ubanta ne ni ai dole taji maganata, ka ga malam da mutuncina wllh ba zan tsaya ina roƙon wannan abar da ba tai macen ƙwarai ba, dama Bilkisu ce har risina mata zanyi saboda ita mai mutunci ce kuma ƴar masu mutunci." Fahad ya faɗi haka yana watsa mata wani wulaƙantaccen kallo wanda ya sa taji ta muzanta a gabansa. Hannunsa Doctor ya kama alamar yayi shiru amma fahad ya ƙeƙashe ƙasa ya dinga gasa mata maganganu sannan ya fizge hannunsa, gabaɗaya bega amfanin aurenta da yusuf ke son yi ba sam. Baƙin ciki da takaicine sukai mata rubdugu a zuciya, amma haka ta danne saboda ko giyar wake ta sha ba ta isa ta yiwa Fahad martani ba, becouse duk wani tashen rashin kunyarta shi Ubanta ne a wannan fannin. Sannan ya san duk wata badaƙala da suke aikatawa wadda ba za ta so ya baiyanata wa duniya ba. Rintse idanu tayi da ƙarfi zuciyarta a turniƙe da baƙin cikin maganganun da ya gasa mata. Tsaki ya ƙara ja for the scond time da ya tuna yanda Yusuf ya ɗauki lamarinta a cikin zuciyarsa, sai kawai ya matsa gefe ya zaro wayarsa ya fara dannawa yana huci, saboda He had no time to waste listening to that shameless girl, wadda bata san mutuncin mutane ba. A can ɓangaren mu kuwa tunda Fahad da Doctor suka nufi inda motar da aka ɗakko amarya a ciki take hankalina ya ke kansu, wannan dalilin yasa na gaza cewa komai. A hankali na motsa hannuna dake cikin nasa, hakanne ya taimaka wajan breaking shirun da ya samu gurbi a tsakanin mu duk da kowa da abinda ya ke saƙawa a cikin ransa, gabaɗaya Hankalina baya tareda shi na tattarashi a kan abin da ke faruwa a waje tsakanin Aysha da su Doctor Umar. Lumshe idanu nayi a hankali zuciyata na harbawa tamkar wadda na fafata tsere da ingarman doki, Ganin yanayin da na shiga a lokaci guda yasa ya matsa hannuna dake cikin nasa a hankali kamar mai raɗa ya ce,"ki kwantar da hankalinki Abarso, ina tare dake cikin ko wani irin yanayi, alƙawarina ne cewa ba zan taɓa bari wani ya keta alfarmaki a gaban idanuna ba. Har yanzu kece dai-dai da Ra'ayin wannan Zuciyar." ya firta haka yana nuna mini saitin zuciyarsa da duk wani yaƙininsa, jin nayi shiru bance komai ba yasa ya ƙara jana jikinsa in a romantic way.
"Ya Allah! Why do you always keep repeating the same thing a cikin maganarka? Kullum abu ɗaya kake maimaita mini sai kace karatu, Yusuf ya kamata ka ƙyale zuciyata taa huta haka don girman Allah." na faɗi haka ina ƙokarin janyewa daga ruƙon da yayi mini. Ƙura mini idanu ya yi ta cikin ƙaramin hasken da ya haska cikin motar, a hankali ya ƙara matsowa jikina sannan ya haɗa forehead ɗinmu guri guda, cikin gajeran likaci numfashin mu ya haɗu ya cakuɗe, da wani kalan murya ya ce,"har abada ba za ki taɓa canzawa daga abar sona ba." ya yi maganar yana lalubar lips ɗina da nufin ya sumɓaceni. Rintse idanu nayi da ƙarfi tun kafin ya ida manufarsa, cikin sa'a wayarsa ta fara ihun naiman agaji, murmushi ya yi mai sauti sannan ya janye fuskarsa a hankali ya ce,"karki ɗaga wa kanki hankali akan Aisha, wllahi ta na da kirki sosai kamar ke ɗinnan."
Buɗe idanuna nayi tar akansa tamkar an tsikareni da allura, sosai maganarsa tayiwa zuciyata wani irin duka. Zame hannuna nayi daga cikin nasa sannan na jingina bayana da sit ɗin motar nayi shiru ina maida numfashin dake ƙoƙarin subuce mini, na daɗe a haka kafin na mayar da idanuna na ƙara lumshewa. Ina jin yanda zuciyata ke ƙara nanata mini maganarsa ta ƙarshe, hmmm lallai sha'anin namiji sai dai a barshi kawai.
Kiran Doctor Umar ne ya ƙara shigowa, a nitse yayi picking call ɗin. Shiru yayi yana sauraron abinda Doctor ke cewa ba tareda ya yi kyakkyawan motsi ba, ina kallonsa ta gefan idona ya juyo ya kalleni tamkar mara gaskiya sannan ya sauke wayar daga kunnensa ba tareda yace da shi komai ba. Ganin haka ya sa na buɗe idanuna na kalleshi ba tareda nayi magana ba, yanayinsa na kalla kawai na fahimci akwai wani abu saboda na lura da yanda ya riƙe sit ɗin motar da ƙarfi, sosai jijiyoyin hannunsa suka nuna kansu a fili.
"Abin so!" na kira sunansa a hankali.
Jin sunan dana kira shi da shi ne yasa ya juyo ya kalle ni, murmushi ya ɗora akan fuskarsa amma duk da haka ban kasa gano ɓacin ran da yake ƙoƙarin ɓoyewa a cikin zuciyarsa ba.
"Me ke faruwa?" na tambayeshi ba tare da na raba ƙwayar idanuna da tasa ba. Shiru ya yi na ƴan daƙiƙu, sannan ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Aysha ce… ta tada rigina wai tana so mu shiga cikin holl ɗin tare."
Jin maganar nayi ta faɗo cikin kunnuwana tamkar saukar aradu. Ban ce komai ba, saboda yanda zuciyata ke bugawa da ƙarfi. Sai kawai nayi murmushi sannan na dafa kafaɗarsa nace,"ai dama tare ya kamata ku shiga"
"Saboda ita ta haɗamin dinner ɗin da kuɗinta ko?" ya gaya mini haka muryarsa ɗauke da hasala a cikinta
Murmushi na ƙarayi sannan na ce,"A'a ba haka nake nufi ba, karka manta fa bikin nata ne kuma ita ce amarya. Don haka tana da cikakken ikon da za ta nemi haƙƙinta na shiga tareda Angonta." na gaya masa haka still fuskata da murmushi. Amma a cikin raina ji nake tamkar ana ɗana mini ƙarfen da aka saka a cikin wuta ya ɗau zafii, wanda ko ba'a fassara mini ba na san kishi ne. Kiran Doctor Umar ne ya ƙara shigowa. Sai da kiran ya kusa katsewa sannan yayi picking ya ce,"Ka jirani a nan," ya faɗa yana buɗe ƙofar motar sannan ya kalleni ya ce."Ina zuwa zan je na warware waccan matsalar."
Ban amsa ba ya rufe motar walking slowly ya nufi inda yake hangensu. Ni kuma na raka bayansa da kallo har ya isa gurin ban dena kallonsa ba. Fuskarsa a ɗaure ya isa gurin tana ganinsa ta matsa kusa da shi tayi hugging ɗinsa, ga mamakina sai naga yayi hugging ɗinta back. Nan take ƙawayen amarya suka fiddo wayoyinsu suka fara ɗaukarsu hotunan suna ihu alamar an birgesu. yawun bakina ne ya ƙafe lokaci guda kuma ya kaure da wani irin ɗaci, tamkar mai zazzaɓi haka kishin da baƙin cikin da abin ya bani ya fara ƙokarin saukar mini da zazzaɓi mai zafi. Ya subahanallah! Ganin su daga nesa sai naji yana ƙara mini raɗaɗi a zuciya, wani ƙaton abu mai kama da ƙululu ne ya tokare mun wuya naji na kasa numfashi. Shikenan ya tabbata mijina munafikine mai lasisi, dafe ƙirjina nayi lokaci da naji zuciyata tana barazanar tarwatsewa in to pieces. Da na sani da nadamar auren Yusuf ne suka haɗu sukai mini rubdugu.
Fahad ne ya matsa kusa da Yusuf ya ɗan taɓashi da hannunsa alamar yana son yayi magana da shi, hakanne ya sa ya janye jikinsa daga ruƙon da su kaiwa juna ya juya yana facing Fahad ɗin fuskarsa da murmushi. Kallon gargaɗi yayi masa sannan ya yi ƙasa da murya ya ce,"don Allah Yusuf ka dinga rage wasu abubuwan akan wannan yarinyar ko dan saboda Bilkisu, ba sai ka nunawa duniya kana farin ciki zaka auri first love ɗinka ba, ka juya ka duba bayanka na tabbata Bilkisu tana kallon duk wani motsinka." Fahad ya faɗi haka cikin jin zafin abin da Yusuf ɗin ya yi. Tun da ya fara magana Yusuf ke kallonsa har sai da ya kai ƙarshe, murmushi ya yi sannan ya ce,"karka manta ina da good Understanding tsakanina da matata Fahad Ibrahim."
"Ok" kawai Fahad ya ce sannan ya miƙawa Doctor Umar hannu su kai musabaha, bai ƙara magana ba ya juya ya bar gurin, da ido Yusuf ya rakashi don ya tabbatar ba zai tsaya a gurin Dinner ɗin ba gida zai tafi.
"Allah ya raka taki Gona" Yusuf ya faɗa da ƙarfi ta yanda Fahad Ɗin zai ji. Amma haka yayi biris da shi ko waiwaye beyi ba. Sosai hakan ya yiwa Aisha Sulaiman daɗi a ranta saboda ta tsani Fahad Ibrahim tsana mai girma. Duk yadda abin da na gani ya sosai mini rai haka na daure na hana kaina kuka, saboda bana so na ƙara zubar da hawayena akan wannan auren. Jakata na buɗe na zaro wayata ina kallon time, sai kawai na fara ƙoƙarin neman number ya zainab amma sai jarumtata ta gaza. Raunina ya baiyana idanuna suka fara gani dishi-dishi tamkar mai lalurar hawan jinin dake gabda tashi, sai kawai na ɗora kaina a kan gwiwata na ce,"Hazbunallahuwani'imalwakil"
Haka nayita nanatawa ban tsagaita ba sai da naji zuciyata tayi sanyi sannan na ɗago na ƙara ɗaukar wayar, cikin ikon Allah sai naji nauyin da zuciyata tayi ya ragu sosai. Lambar ya zainab na laluɓo na danna kira, bugu ɗaya ta amsa ta ce,"wai kina ina ne naga har yanzu baku ƙaraso ba."
"mun zo tun ɗazu, jira nake amarya da ango su shiga da mintuna goma sannan twiny tazo mu shiga tare."
"Eh hakan ma ya yi, dama abinda ya Naima tace kenan idan sun shigo zan turo miki Hajar ɗin." cewar ya zainab.
"ok to." na amsa a sanyaye sannan na kashe wayar nayi shiru ba tareda na ƙara gigin kallon inda suke tsaye ba. Gabaɗaya ji nayi na daina gane komai saboda ƙunci da wutar kishi. Mintuna biyar aka kwashe sannan sauran abokanan angon suka hallara, Aisha ba ta bawa Yusuf damar da zai dawo gareni ba har suka shiga cikin hall ɗin bai waiwayeni ba. A wannan lokacin gabaɗaya na gama muzanta a cikin motar saboda ganin yanda ya wofantar dani ya bi sabuwar amaryarsa, jikina a mace na kai hannu na buɗe motar na sauka, kallon komai nake tamkar a mafarki saboda yanda zuciyata taƙi karɓar abin, rintse idanuna nayi da ƙarfi ina jin yanda ƙirjina ke bugawa tamkar zai tsage gida biyu. Jingina bayana nayi a jikin motar ina bin harabar gurin da kallo, ba kowa a harabar gurin sai mutanan dake wucewa jefi-jefi. Na jima a tsaye sannan na fara tafiya a hankali ina ƙara ƙanƙame ƙaramar jakar dake hannuna, wayata ce ta fara ƙara don haka na zarota a cikin jaka ina ƙoƙarin amsawa. Ya Naimah ce ke kira don haka nakai wayar kunne ina sauraron abinda da take cewa, ajiyar zuciya na sauke mai sannan na ce,"yamzu zan shigo ina gabda bakin holl ɗin."
"ok idan kin shigo ki miƙo sosai then look to your right and you’ll see us sitting opposite each other."
"Amma maiyasa Twiny ba za ta fito mu shiga tare ba?" nayi tambayar kamar zan rushe mata da kuka. "already ta fito ai ki duba da kyau za ki ganta a bakin ƙofar." ya Naimah ta faɗi hakan tareda katse wayar.
A hankali nake tafiya har na iso dabda ƙofar shiga hall ɗin, kamar haɗin baki sai naji kiɗan dake tashi a cikin holl ɗin ya tsaya. Twiny na ganina ta ƙaraso gareni tana murmushi ta kama hannuna ta ce,"Tsakani da Allah you’re extremely beautiful Twiny. kinga masifar kyan da kikayi kuwa?"
Murmushi nayi jin yanda ta koɗa ni, sai kawai ta kama hannuna muka fara tafiya majestically zuwa cikin holl ɗin, dedai lokacin kuma gabana ya tsananta bugu saboda ban cika son shiga cikin mutane da yawa ba. Ganin yanda holl ɗin ya cika da jama'a ne ya sa na ƙara damke hannun twiny, a haka na ɗaga ƙafata na ɗora a ciki, a hankali nake tafiya baka jin sautin komai sai na takalmina. Ƙarar takuna ita ce ta janyo attention ɗin mutane kanmu, sai kawai DJ ya saki wakar Uwargida mai Capacity ta Ali jita ta karaɗe gurin,haba ai sai twiny ta fara bada step tana taku cikin ƙwarewa. Sai kawai naga Yusuf ya nufo mu tareda ɓalle rafar ƴan dubu-dubu ya fara mini liƙi har muka isa tsakiyar hall ɗin. ya Zainab ma ta fito ta fara ɓarin nera ya Na'ima tana take mata baya, nan fa guri ya rikice Dije sai zuba banbaɗanci yakeyi har waƙar ta kai ƙarshe. Aisha kuwa wasu zafafan hawayen baƙin ciki ne suka fara zubo mata, saboda kallon abinda Yusuf yayi take a matsayin cin fuska mafi girma a gareta. Sai kawai ta miƙe da nufin ta fice daga gurin taron gabaɗaya, amma sai Faridah Attahiru ta riƙe hannunta ta ce,"karki ƴarfa kanki a idanun jama'a Aisha. Ki ƙara haƙuri a ɗaura auren tukunna na tabbata kece zaki mallaki zuciyarsa tunda dama can ke yake so ba ita ba, amma muddin kika fita daga holl ɗin nan zaki janyoma kanki abin magana a gurin mutane da sauran dangi."
Komawa Aisha tayi ta zauna amma har cikin ranta take jin zafin abinda Yusuf yayi mata.
Sinkuyawa Faridah tayi still tana murmushi ta ce,"idan Aski yazo gaban goshi yafi zafi Amarya, ke dai kawai ki jira daran da za ku haɗa gado da yaya, a washe garin ranar zaki mallake duk wani gurbi na zuciyarsa i Assure you."
Tafawa sukayi sannan aka ci gabaa da sauran shagali kamar yanda aka fara, sai ƙarfe 1:00am sannan aka tashi daga Dinner ɗin.Tun kafin a tashi daga Dinner ɗin Faridah take tufka maganganun da zata fimfa hajiya dasu wanda za tayi mana rashin mutunci a haka ta isa gida da wannan ƙudirin.......