Part 8
by @chefmuaysh
BADAKALA BOOK1 ✍️ ✍️ AISHA HAMZA CHEFMUAYSH
Mai tukin ne da fuskarsa take a rufe yadan kallasu ta mudubi kafin yace sir wacece surukar tamu ne anan
Shiiit yayi masa alamar shuru hakan yasa bai ƙara tankawa ba suka ɗauki hanya Ayrah dai ta zuba ido akan tituna don tana gefen glass duk wani symbol data gani saita karanta kunsan mu yan boko yanda muke har waige muke idan muka fara karanta abu bamu gama ba ana neman wucewa 😆
Tafiyar tasu batayi tsawo sosai ba sai gasu cikin wata unguwa wadda basai an faɗa maka ta masu hannu da shuni bace ba zaka fahimci hakan
Khairiyya dai tunda ta kwantar da kanta saman kafadar uncle Sameer bata ƙara dagowa ba sai Ayrah da take ta faman raba idanu a duk inda aka bi
Wangamemen get ne aka buɗe musu wanda iya get ɗin zai tabbatar maka da an kashe kuɗi wajen siyansa Saida motar ta kutsa kai cikin gidan kafin nace Alhamdulillah Astagfirullah wannan gidan anya ba'a sallami masu shiba don wannan aljannar duniya za'a kirashi
Ayrah dai ta saki baki tana kallon ikon Allah takasa magantuwa da tsaruwar wannan gidan don tafara tunanin mafarki takeyi saboda saka ran kullum za'a dauke su zuwa makaranta amma nan fa anya ba'a mafarki sukazo ba
Sunanta daya kira ne ya dawo da'ita daga hayyacinta yana rike da Khairiyya da take ta faman kankameshi don taki sakin shi gani take wani abu zai kamata don takasa nutsuwa bare ma taga irin gidan da suka shigo
Magana sukayi cikin turanci shida driver daya dauko su kafin yace su shiga ciki ita dai Ayrah kamar sakara sai bin gidan da kallo takeyi har suka isa wata ƙofa daga ɗaya daga cikin kofofin da zata iya cewa taga biyu a ta gaba su kuma Saida suka ɗan zagayo ta wani gefen
Faɗin haduwar parlour bata lokaci ne amma daga gani kasan an kashe kuɗi a wajen siyan kayan ciki tun daga kan faskekiyar plasma da take kamar a cikin bangon akayi ginin da'ita sai wasu shegun kujeru lallausan carpet ɗin kaɗai idan ka taka saika lumshe ido saboda taushin sa
Bakowa a cikinsa sai wani kamshi mai dan karen daɗi ga AC mai ratsa fatar wanda ya zauna a cikinta nanfa Khairiyya tafara baza idanu tuni tasaki uncle Sameer tasaki baki tana kallon haduwar parlour hada murza idanuwanta don taga da gaske ne
Hajiya Ayrah kuwa daga ta ciki ne ta shiga almara amma kallon fuskarta bazai nuna maka asalin mamakin abinda take gani ba
Morning sir shine abinda ya dawo da hankalinsu ga wata hadaddiyar budurwa wadda take sanye cikin shiga ta chef's
Morning hayrana ya faɗa tare da faɗin ga baƙin oga nan a basu kulawar data dace zuwa jibi zasu wuce ki kira Imran ki faɗa masa yazo ina jiransa yanzu
Ok sir ta ƙara faɗa hada ɗan dukawa kafin takai dubanta ga su Ayrah da suke ta faman yan kalle kalle
Tace zamu iya tafiya tana ƙoƙarin kama hannun Khairiyya ai da sauri ta fisge tana hararar ta irin ina zaki kaini
Murmushi ta saki takai dubanta ga Sameer shima martanin Murmushin ya maida mata kafin yace Ayrah ku bita kuje zata baku kulawa zuwa gobe zandawo karku wani damu
Itadai Ayrah tagama sallamawa da ko menene ma zai faru hakan yasa ta gyada masa kai alamar gamsuwa
Khairiyya tace tab wallahi saidai katafi damu wannan gidan kamar na yan yankan kai zaka barmu ka haɗa mu da wannan matar da bamusanta ba
Dariya taso basu amma saboda yasan halinta nan ya shiga lallaba ta akan zai dawo zuwa da safe karta wani damu nan ɗin gidan su ne kuma ba gashi ya haɗa ta da Kanwar sa ba ya faɗa yana nuna hayrana
Murmushi tasaki itama hayrana kafin suka ɗan kyafta ma juna ido itada shi cikin rashin Sa'a kuwa Ayrah takara ganinsu duk yanda zan faɗa muku tashin hankalin mutuniyar taku daga ta ciki abin bai misaltuwa saboda tafara zargin uncle ɗin nata amma saboda shegen wayau irin nata baka isa ka fahimci hakan daga gare ta ba
Daƙyar yasamu Khairiyya tabi hayrana suka wuce ta wani dan corridor da yake a parlour ɗin daga gefensa kuma stairs ne
Dakuna ne a jere guda biyu ɗaya ta buɗe suka shiga nan suka samu wani sabon abin kallon don shima dakin kujeru ne purple da curtains purple ga wasu kofofin har guda uku a cikinsa shima ga tv madaidaiciya ba kamar ta parlour ba amma
Bayanin data fara musu ne ya dawo dasu hayyacinsu suna dubanta nan shine parlour ɗin da zaku zauna ga tv nan ta faɗa tana nuna inda take ɗaya daga cikin kofofin ta nufa wannan shine dakin bacci sai ta buɗe ta kusa dashi wannan kuma kitchen ne amma bakuda bukatar sa komai za'a kawo muku sai dayan da yake daga gefe tace ga toilet nan ta musu bayanai akan komai da yanda ake amfani dasu a parlour da kuma toilet ɗin
Dukda da bakomai suka fahimta ba saboda tanayi tana haɗa musu da turanci dakin da tace na bacci ne ta kuma buɗewa tare da faɗin ku shigo kugani kamar sakarkaru suka bita suna kallon ko'ina na dakin
Masha Allah Ayrah ta faɗa azuciyarta ganin faskeken gadon da ke cikin dakin ga wata ƙatuwar closet daga gefensa daga gaba kuma mirror ne wanda yake shirye da mayukan shafawa da abubuwan buƙata na mata
Bayan hayrana tagama musu bayani tace to zata tafi tagama aikinta sai gobe zata dawo Khairiyya tace ina kuma zaki tafi ki barmu tana zaro mata idanu
Hayrana tayi Murmushi tace Karki damu sister yanzu za'a zo a kula daku bakuda matsalar komai anan ai
Gamm taja musu kofar wata nannauyar ajiyar zuciya Ayrah ta sauke wadda batasan dalili ba kafin ta juya tana ƙare ma ko'ina kallo, parlour dakin da suke tafito ta nufa hanyar da aka ce mata toilet ne ta shiga kamar yanda aka musu bayanin komai haka ta shiga yin alwala domin tayi sallah zuhr da Asr data kamasu a hanya
Ganin Khairiyya zaune Kasan carpet ɗin ne duk a tsorace yaso ya bata dariya tace kije kiyi alwala Khairiyya muyi sallah Koh
Ta buɗe baki zatayi magana aka turo kofar gaba ɗaya hankalin su ya koma ga mai shigowa da Murmushi ya dube su kafin yace sorry na shigo muku ba tareda izini ba wayaga wuƙi wuƙi duk sun zuba masa ido sun kasa furta kalma hakan bai dame shi ba saima ledojin daya shigo dasu yafara saukewa saman dan madaidaicin stool ɗin dakin yana faɗin ga abinci nan idan akwai abinda kuke buƙata ga wata abu nan da kun danna za'a zo aji menene ya faɗa yana nuna musu wani dan ƙaramin abu a jikin bango mai madannai
Ba wadda tayi magana dai har ya gama ya fice abinsa kamar jira Khairiyya take ta nufa ledojin tana faɗin wallahi dama ce maki zanyi yunwa nakeji Bazan iya Sallah nan ba sai naci to Allah ya taimake ni gashinan inajin abincin ne tana buɗe ledojin
Ayrah girgiza kai kawai tayi don ita a yanzu bata da burin daya wuce tayi sallolin ta carpet tagani daga saman bedside ɗin dakin ta dauko ta dawo parlour don Khairiyya biyota tayi tana faɗin tadawo wallahi parlour ɗin kota biyota suci abincin anan dakin
Sanda ta idar da sallah ta dukufa addu'o'in da ta saba sosai tayiwa gwaggo addu'a da duk wanda ma ya jibance ta kafin tasamu nutsuwa lokacin Khairiyya ta dage sai cin naman kaza take hada taune kasusuwanta
Fried rice Ayrah ta buɗe cikin wani ɗan ƙaramin takeaway don ita take ganin zata iya ci duk abubuwan da yake a cikin nata ledar don kowa dai-daya ce tashi,gaba ɗaya cikinta hanta ce kamar me
Saida tadan ci takasa cinyewa ma kafin ta ɗauki ruwan roba mai sanyi tasha ita kuwa Khairiyya ga kayan daɗi me zatayi da ruwa taci kaza da fresh milk dinta ta ture sauran wai idan ta idar da sallah zata karasa cin abinda bataci ba
Zaman fira suka zauna yi akan gida da rayuwar makaranta amma hankalin Ayrah sosai yakasu gida biyu don zuciyar ta namata sake sake iri daban daban kasancewar wayansu dana Khairiyya ba ɗaya bane ba ma
Tanada matuƙar hangen nesa sana dawuya ka iya gane gabanta koda yaushe cikin canja salo take don bazaka iya siffanta halayenta gaba ɗaya ba saidai ɗaya da yariga ya zamar mata kamar jiki shine tambaya kamar yar jarida don bata fiye son yanke hukunci da kai ba sai tasan dalilin mutum na aikata abu
Hakan yasa yanzu ma take kullawa da warwara a zuciyar ta basu dade suna fira ba taji shurun Khairiyya ɗin tana juyawa taga ta baje sai uban bacci takeyi dama ansha tafiya ga anci an koshi kuma
Nan ta samu damar zancen zucinta wanda yasa tayi saurin mikewa jin zata fara tunanin da bai dace ba tafara addu'a
Kiran sallah Maghreb ne ya tadasu don anaji idan ana sallah kamar a kofar dakin nasu akeyi kasancewar koda suka shigo zata iya cewa ta hango wani waje kamar masallaci a ciki
Bayan ta fito ne ta tayarda Khairiyya akan ta tashi lokacin Sallah yayi saboda baccin bai isheta ba kau hada tsoki wai meyasa ita bazatayi ba ta kyale ta idan ta tashi ai tayi
Batabi ta kanta ba saboda tasan hali taje ta tayarda sallah ta a cikin dakin gadon nan Khairiyya ma ta fito itama tayi suna zaune Ayrah tana gefen gadon Khairiyya na zaune saman abin sallah kamar daga sama sukaji karar bullet daramm zo kaga tashin hankali
Ayrah ta rufe kunneta ita kuma Khairiyya ta makure jikin bedside tana zabga kuka jin shiru kamar kuma ana magana da faɗa faɗa yasa Ayrah buɗe ido tana sakin kunnenta tare da mikewa tsaye kamar mai nazarin wani abu can kuma sai tayi hanyar parlour dakin da suke ciki
Khairiyya data dan dago cikin tsawa tace wallahi Ayrah karki fita zasu kasheki ba ruwana Shikenan mun shiga uku mun kawo kanmu fuska tayi jage jage hada majina
Ayrah kuwa bata juyo ba gadan gadan ta nufi kofa don saita gane ma idonta abinda ya faru zata iya bacci a gidan
Tofah tashin hankali ƙarar bullet kuma daga ina ❓😳
Ko inane suka kawo kansu oho ❓
Gidan wanene SHAUBAN FAMILIES HOME ❓
Da alamar tambaya anan fa muje gaba nan zamuji tirka tirkar da za'ayi anan don mutuniyar ku Ayrah fa tace sai taje taga abinda ya turewa buzu nadi
Ina fans ɗin Khairiyya ne mutuniyar taku
fa sai kun kawo ɗauki da alama neman zarewa takeyi 😆
BADAƘALA ✍️
Sai daku 🤟 yan amana