Kuncin zuci
by @bintuuu
Kallon sa ta rinqa yi tanajin zuciyarta na bugu, shima bai daina kallonta cikin ido ba, sunkai 5 secs a haka kafin ta juya kanta tana dan gyaran murya, murmushi Ahmad yayi yana kallonta ganin irin kunyanta, sai ya juya ya kalli river'n shima yayi sipping coffee din hannunsa still be daina murmushin ba, because he likes it when he made her uncomfortable, hakan na qara tabbatar masa da yana samun guri cikin zuciyarta kamar yanda yake bida, Na'ima ji tayi atmosphere din na saka wa zuciyarta wani irin yanayin, sai tace "Ya kamata mu koma kafin su tashi daga bacci" Ahmad yace "Zaki barni in shiga gidan tare dake yau?" sai tayi murmushi cikin sanyin murya tace "You'll still bail on me ko na hanaka" murmushi me fadi Ahmad yayi sannan yace "Inason kowa ya ganni tare dake Na'eemah" wani murmushin tayi dan har ga Allah duk wasu kalamai da Ahmad din yake fada mata direct suke samun waje cikin zuciyarta, she's new to it, bata taba jin haka akan kowa ba sai akansa shima bai taba jin haka akan kowacce mace ba sai itan...
Da Ahmad ya nemi yakaita nearby cafe suyi breakfast qi tayi, tace su tafi gida suyi breakfast din acan, babu yanda ya iya haka suka fara wani tafiyan zasu koma gurin motansa, a wani public dustin yayi dumping robber cups din coffee din nasu sannan suka shiga motan sa, cikin shiru suke tafe a motan jefi jefi suke juyawa su kalli juna, sai da yayi parking a qofar gidan Anty Amnah ya juyo yace "Yaushe ne graduation dinku?" Na'ima ta amsa da "In a month in sha Allah" yace "Ma Sha Allah, i'll be going to Italy for a work this week and in na dawo inason komawa Lagos" ahankali tace "Allah ya taimaka" cikin kwantar da murya ya sake cewa "Babe i hope after graduation din zaku koma Abuja" sai ta gyada kai idonta a qasa, ya dan matso yace "Then i'll transfer all my work back to Abuja kinji" sai sannan ta kallesa itama a hankali tace "I'll be waiting" da haka ta juya tareda da bude motan fuskanta dauke da murmushi, tanajin duk wani damuwan da ta shiga jiya akan Bilal din yana washewa daga zuciyarta, tare suka jera suka nufi shiga gidan, Na'ima ce farkon shiga falon, again yau ma Lailan ta fara gani tana tahowa cikin falo daga dakinta, Anty Amnah da Abban twins sannan Nafisa suna zaune a dining area having their breakfast, Ahmad da ya shigo bayan Na'iman ko kallon Lailan beyi ba ya nufi su Anty Amnah, itama Na'iman sai ta bi bayansa dan har ga Allah ita mantawa take da wata Laila ma a gidan, kasa motsawa Lailan tayi daga inda take tsaye sai Anty Amnah ta kalleta tace "Kin fasa cin abincin ne ko me?" Nafisa ta tabe baki sannan ta miqe tafara serving Ahmad dake zaune kusa da Na'iman yana magana da Abban twins kamar bai san da wata Laila a gurin ba, juyawa Laila tayi ta koma guest room din nasu, cikin bacin rai ta fara bincika akwatin ta, wani kwalba ta dauko me dauke da wani ruwa acikinsa, shafawa tarinqayi a tafin hannunta har jikinta kamar yanda mommy'nta ta umarce ta dayi sannan ta tafi falon, ganin Na'ima a gefen Ahmad din ba qaramin tsaya mata arai hakan yayi ba, sai taja kujeran dake facing din Ahmad ta zauna, itadai Na'ima kanta a qasa tana cin abincin ahankali bata ma sauraron hiran dasu Ahmad din ke yi sama sama da Abban twins..
Ahmad sai cin abincin sa yake cikin kwanciyar hankali, can ya juya ya kalli Na'iman dake cakulan abincin sama sama, kasa cin abincin Laila tayi tana kallon su ranta na baci, ita dai Nafisa sai kallonsu take tana danne murmushi, sai da Na'ima takai cup bakinta tana sipping tea din ta hada ido da Nafisan dake kallonta tana murmushi, kwaruwa tayi da tea din ta dan fara tari, da hanzari Ahmad ya zuba ruwa a cup ya miqa mata tareda cewa "Sorry" daga Anty Amnah har Abban kallonsu suka tsaya yi, gyada kai Na'ima tayi ta karbi cup din sai ya miqa hannu ya ciro tissue dake gurin still ya miqa mata bai ma lura da kallon da mutanen gurin ke masa ba, kadan ya hana Nafisa kwashewa da dariya ganin yanda Laila ta daskare a zaune tana kallon Ahmad, sai da Na'ima ta gama shan ruwan Anty Amnah tace "Sannu Na'ima" Abba ma yace "Sannu" gyada kai tayi sai ta miqe Ahmad na kallonta zata bar gurin, Anty Amnah ta sake cewa "Har kin qoshi daughter" tace "Uhm Anty"
da haka ta nufi hanyar dakinsu, Nafisa da ta kasa shiru ta kalli Laila tace "Ke ma kin qoshi ne" sai ta juya tana wani irin kallo a Nafisan...Bayan sun gama Ahmad ya miqe tareda fada musu zai wuce office shima, yana fita Lailan ta bi bayansa su Anty Amnah suka bita da kallo suna ganin ikon Allah, a gurin motansa ta idda sa rai a bace tace "Yaya" ya juyo yana kallonta bai amsa ba sai ta tsaya nan gabansa tace "Jiya naje gidanka nasamu ka chanja gate pin din ka fa" ya dan daga kafada yace "Yes.. meya faru?" ranta adan bace tace "Sai abu ya faru ne zanje gidan ka Yaya?" bai amsa ta ba ya tsaya yana kallonta fuskansa a dinke kamar be taba dariya ba, ganin haka sai ta sassauta bacin ran nata ta shagwabe fuska tareda matsowa zata kamo hannunsa, kauda hannun nasa yayi a nutse yace "Why are you even here? fadamin me kikazo yi a London" tace "Shikenan sai bazan zo gurin 'yan uwana ba, naga har bare ma suna zama a gurinsu" bai ce komai ba ya cigaba da kallonta coldly yana jin ransa ya fara baci kuma, nan tasha jinin jikinta tace "Hutu fa nazo yi gurin Anty Amnah" sai sannan yace "Pack your things and go back home before i loose my temper with you Laila" kuka ta fara tace "Yaya ga bare ma tana zama a gidan 'yan uwan mu sai nice zakace in tafi, wallahi nikam a'a" juyawa Ahmad yayi ya bude front seat na motan zai shiga sai Lailan ta matso zata kama hannunsa yayi baya yace "Kika tabani sai na saba miki, bazan maimaita abunda nace miki ba, in kinga dama ki bari in sake dawowa in sameki" Tananan tsaye ya ja motansa ya bar street din sai ta juya rai a bace ta koma cikin gidan tana fadin "Babu inda zanje wallahi, saidai sh*giyar nan tabar gidan"
Bayan su Anty Amnah sun gama breakfast din suka shige part dinsu ita da mijin nata yayi shirin fita aiki dan ita sai night, saida Nafisa ta gama tattare gurin takai kitchen zata wanke Na'ima ta shigo, basu ce komai ba suka fada cleansing plates din, saida suka koma daki Nafisan ta tambaye ta yanda sukayi da Ahmad din, a sannu ta fada mata yanda sukayi dashi, sai Nafisa takai hannu baki tana blushing tace "Ya Allah" Na'ima na murmushi itama batace komai ba, kafin Nafisan tayi magana Laila ta turo kofan tareda shigowa da babban akwatinta, miqewa Nafisa tayi tace "Meya haka ke kuma" Laila tace "Me kuwa..zama zanyi anan ita baren sai ta tafi guest room" da dan mamaki Nafisa ta bude baki tace "Laila anya lafiyan ki, na rantse bazaki zauna a dakin nan ba" cikin bacin rai tace "Toh naga abunda zai hanani wallahi" ta kalli Na'ima tace "Ke wai baki da dangi ne sai nawa" Nafisa bata san lokacin da ta mulmulo zagi a Lailan ba ta qara da "Idan ban gaura miki mari ba kin canja min suna" cikin daga murya ta cigaba "ki fita daga dakin nan Laila" Na'ima ta miqe tace "Nafee muje guest room din" cikin bacin rai Laila ta handakata tareda cewa "You don't get to say anything tunda ba gidan uw*rki bane nan din" nan Nafisan ta handaka Lailan itama suka fara dambe a dakin Na'ima na rabasu, da sauri Anty Amnah ta shigo dakin tana fadin "subahanallahi bakuda hankali ne" sai da ta musu tsawa suka rabu kowacce na maida numfashi Nafisa tace "Kuma wallahi sai kin bar London gaba daya bama gidan nan kadai ba" Laila tace "Ke kin isa, waccan mara galihun ce zata bar qasar wallahi, yar matsiyata kawai" cikin tsawa Anty Amnah tace "Sai naci ub*nku zaku nutsu tukunna?" shiru sukayi Na'ima tayi tsuru tsuru sanin fadan dan ita akeyi, neman ba'asin fadan Anty tayi, Nafisa tayi saurin fara fadin yanda akayi har da qarawa da "Wai sai tayi sanadin barin Na'ima garin nan bata gama karatu ba" dan kallon ta Na'iman tayi tana mamaki, Laila tace "Qarya take wallahi" Anty Amnah ta daga mata hannu tace "Duk naji, meyasa ke komai sai kinyi rashin da'a ne Laila, da kika zo nan din wato neman fada kikazo kenan, in hakane to ki hada kayanki anjima zan siya miki ticket ki koma gida bazaku sakamin ciwon kai ba da giramanku, kema Nafisa sai na saba miki wallahi, shashasha kawai, da ta fadi hakan sai bazaki fadamin ba kawai ku hau dambe ke gaki uwar masifa, toh duk ku kama kanku a gidan nan kuna jina" Laila ta juya fuu ta fice daga dakin ko akwatin nata bata dauka ba, Nafisa tace "Kiyi hakuri Anty" bata ce komai ba ta fita ranta a bace, Na'ima na kallon Nafisa tace "Yaushe tace haka Nafee" da masifa Nafisan tace "Ke bakisan Laila bane, in ba tafiya tayi ba bazata bari mu huta ba" ta qarasa maganan tareda daukan kiran Mami da ya shigo wayanta...Aikuwa tun kafin Anty Amnah ta siyawa Lailan ticket ta siya da kanta, jirgin su zai tashi da dare, ko mummynta bata kira ba ta hada sauran kayanta ta fito janye da akwatin ta, duk suna zaune a falon tace da Anty Amnah "Na tafi" sai jikin Antyn yayi sanyi kuma tace "Daughter fushi kikayi, toh ki koma nawa dakin da kwana tunda bancika kwana cikinsa ba" dauke kai Lailan tayi tace "Flight din anjima ne" ta yi maganan tareda nufan fita, miqewa Anty Amnah tayi ta bi bayan ta, Nafisa ta tabe baki ta juya tana kallon Na'iman da duk jikin ta yayi sanyi itama....
A washegarin ranan driver'n Ahmad ne ya kaisu makaranta suyi submitting dissertation dinsu, tare Na'ima taje ko ina da Nafisa ranan, tana sane Nafisan tayi haka ne gudun kar ta qara haduwa da Bilal, suna fitowa daga office din supervisor din Nafisan sai taga tayi tsalle tace "Finally, atmosphere din qasar nan ya fara isata" Na'ima tayi murmushi tace "Ki jira mu ga score din mu tukunna" tace "Ai ko na fadi dai na gama school din nan" Kiran Mami ne ya shigo wayan Na'iman ta dauka, bayan sun gaisa tace "Habibti kunyi submitting din" ta amsa da "Eh" sai Mami tace "Ma Sha Allah, may your graduation mark the beginning of a beautiful new chapter in your life Habibti" har ranta taji addu'an, tana murmushi tace "Amin, thank you Mami" tace "Wane kalan kaya kikeson sawa a graduation ceremony din?, Baby tace fitted kuma nasan fada tayi babu shawararki" dan kallon Nafisan tayi taga tana mata dariya, tace "ko wanne ma" Mami tace "No ki kira Meerah kuyi magana, zata turomin bill din" amsawa tayi sukayi sallama, sai da suka dauko motan su daga gurin ajiya sannan suka dauki hanyar komawa har sannan ba wanda yayi maganan zuwa apartment din nasu....
Laila ce zaune a falon gidansu, fuskan nan tayi jajir tana hawaye, Mummy dake gefenta ma rai a bace tace "Ita yarinyar me ya kaita gidan Amnah'n" Laila tace "Tare suke zama da Nafisa a gidan, Mummy har fita fa takeyi tareda Yaya Ahmad din" sai Mummy tace "Baki goga abunda na bakin bane?" tana share hawaye tace "Baya kulani fa Mummy, cewa yayi in bar gidan Anty Amnahn ma" cikin masifa Mummy tace "A matsayin gidan ub*nsa kenan, duk dani suke zancen, sha kurumin ki Auta, ina nan dake zai zo har gidan nan kinji, badai koroki sukayi ba, zasu san sunyi hakan dukansu har Amnah'n" Laila na kuka tace "Narantse ko bazan aureshi ba wannan sh*giyar bazata aureshi ba Mummy" cikin lallami Mummy tace "Balle ma zaki aureshi auta, duk abunda kikeso sai kin samu matuqar ina raye kinji" Laila ta gyada kai tareda kwanciya nan kan kujeran Mummy na shafa bayanta tunani iri iri nazuwa mata kanta, inaa ai dukiyar Ahmad 'yarta ce kawai zata moresu....
Ana gobe Ahmad zai tafi Italy din yazo gidan Anty Amnah da dare, Na'ima na daki jabeer ya shigo ya fada mata zuwan sa, Jafar dake gefen ta suna kallo a laptop ya tashi da gudunsa ya fita, kasa fita tayi kuma bata cigaba da kallon ba, can taji shigowan message dinsa awayanta dake gefenta, murmushi tayi bayan ta karanta content din, ta ajiye wayan batayi reply ba, can sai ga Nafisa ta shigo tana murmushi tace "Kinsa Yaya na yana ta raba idanu, na neman ta inda zaki fito" Na'ima na murmushi cikin sanyin murya tace "Ni ba gurina yazo ba" zama a bakin gadon Nafisan tayi tace "Kiji tsoron Allah Bobo, yaushe muke sanin lokacin tafiyan Yaya Ahmad har ya mana sallama" dan girgiza kai Na'ima tayi tace "Ku yazo yiwa sallama bani ba" dariya kawai Nafisan tayi sannan tace "Yanzu yake fada mana ashe Italy zai tafi gobe, da kamar zan fada masa zamu bisa amma nasan halinki shiyasa nakeson jin ta bakinki" aikuwa nan take Na'ima tace "kije abunki, nidai bandani" Nafisa ta hade gira tace "Haba Na'ima, Rome fa ake magana, it'll be like a vacation" Na'ima ta sake girgiza kai, cikin masifa Nafisa tace "Mufa beach resort zai kama mana, yana can yana aikinsa mu na hutawan mu, mun gama makaranta kuma me ya saura in ba yawon bude Ido ba" shiru Na'ima tayi at first sannan tace "Hakan bazai zamo burden ba, kinyi maganan dashi?" ta amsa da "Waa? burden ta ina, ai in qasa goma kikace muje Yaya zai kaimu, taso muje ni zan fada masa" da haka ta kama hannun Na'iman suka fice, ganin yana tare da Anty Amnah yasa Na'iman jin kunya saboda kallon da yake ma ta ko a jikinsa, sai da suka zauna tace "Ina wuni" yana kallonta yace "Lafiya Na'eemah" Anty Amnah ta cigaba da maganan da suke yi din tace "Son ai ka dade ma this time, ko ayyuka ne sukayi yawa a branch din ku na nan din?" Ahmad yadan shafa kansa a nutse yace "Eh momma, but in na dawo zan koma Lagos in sha Allah" Nafisa tace "Yaya ka tafi damu Rome din" Anty Amnah ta girgiza kai tana murmushi tace "Nafisa sarkin yawo" tana dariya tace "Graduation trip ne Anty" Ahmad ya gyara zama tareda dauko wayansa yace "It's settled then" dan daga hannu Nafisa tayi tana murna tace "Thank you Yaya, amma dan Allah muje da Lauren, wallahi in ba haka ba zatace naci amanan ta" daga Anty Amnahn har Ahmad din dariya sukayi wanda yasa Na'iman kallon Ahmad dan bata taba ganin dariyarsa haka ba, yana danna wayar tasa ya dago kai suka hada ido tayi saurin dauke kai tana murmushi, sai ya tura mata wani text din kamar haka.
"I know this will be the best working trip i've ever had"
Bayan ta karanta ta dago kanta taga yana kallonta fuskansa dauke da murmushi me kashe mata zuciya...