Page-29
*FASAHA WRITER'S ASSOCIATION*
(*F.W.A)*©✍️
⭐⭐⭐
Ƙungiya masu aiki cikin salon hikima da fasaha gurin juya tunanin al-umma, kaifin alƙalumansu ya zarta takobi ©✍
___________________________________________________
بسم الله الرحمن الرحيم.
اللهم صلي وسلم على نبينا محمد.
❁ 𝐒𝐀𝐍𝐀𝐃𝐈𝐍 Ƙ𝐀𝐃𝐃𝐀𝐑𝐀𝐓𝐀 ❁
Free book📓
By
_*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_
Page2️⃣9️⃣
Lantana ta sake cewa, "za ki ƙyale shi ko mu sanar mata ta aikata abun da ta ce ɗin?" "Anty Lantana!" Faruq ya furta cikin ɓacin rai yana kallonsu gami da ƙarasowa, ji ya yi ya kamata ya dawo da wuri saboda bai ji daɗin yadda ya bar Sadiyar ɗazun ba, duk da ya kirata sosai har ya ce zau dawo amma ta hanasa.
Fiskarsa à haɗe ya ke ƙare musu kallo, su kuwa sun yi ɗip suna kallonsa, juyawa ya yi gun matarsa ganin hawayen da ya ke ta sarara akan fiskarta, ga alamu sun nuna tana cikin tashin hankali, da sauri ya yi inda ta ke ya rugumeta zuciyarsa ba daɗi yana sake binsu Fatima da kallon haushi, su kuma sun yi ƙasa da kansu sai lantana da ta ke kallonsa.
"Anty Lantana me ya kawoku sashina?" Ya yi tambayar wa Lantana, ita kuwa kallon renin wayo ta yi masa sannan ta ce, "yau na sake tabbatar da ba lafiya Sadiya ta barka ba, yanzu ni ka ke cewa me ya kawoni sashinka? Wato ka samu mata ka gusar da 'yan uwanka ko? Kuma matar ma sai irin wannan juyar?" "Ya isa Anty Lantana! Wa ki ke cewa juyar?" Sadiya da har yanzu so ta ke ta yi kuka amma ya ƙi zuwar mata sai hawaye da su ke tsiyaya tana ƙoƙarin dakatar da Faruq ya ɗaga mata hannu.
Ya cigaba da cewa Lantana, "eh wace juyar da ki ke magana akai? Idan ban manta ba lokacin da ki ka yi aure kin shafe kusan shekara biyu amma baki haihu ba, to idan ita Sadiya juya ce ke kuma wa ce a lokacin?" Lantana da ta ƙwalalo idanu tana kallon Faruq, suma su Badiyya hakan su ka yi, Aisha kuma ta giɗa kai alamar yauwa!.
Faruq bai tsaya ba sai ma ciga da cewa, "haka zalika idan ban kuma mantawa ba, kin fi shekara uku da ki ka rabu da mijinki, ki ka dawo gidan nan da zama kina zawarci, ke ba ki koma gidan mijinki ba sannan ba ki auri wani ba, to Anty Lantana faɗa min! Akwai wanda ya taɓa takura miki lokacin da baki haihu da wuri ba? Ko akwai wanda ya takura miki yanzu akan ba ki yi aure ba kina zaune?".
"Yanzu Faruq abun na ka har da cin mutunci? Yanzu ni za ka dubi idona ka faɗa min magana haka?" Bai ce mata komai ba Fatima kuma ta ce, "haba Faruq anty Lanta..." "yi min shiru à wurin nan! Ina zuwa kanki dama ai, wallahi daga ke har Badiyya ku kiyayeni, don kunfi kowa sanin ko ni waye idan raina ya ɓaci!". "Duk abun da za ka yi ka aikata Faruq! To bari ka ji, Baaba ce ta aiko mu ba zuwan kanmu ba ne, ta ce ko ka rabu da Sadiya ko ta tsine maka!" Cewar Lantana.
Sai da Sadiya ta sake manne idonta jin kalmar, shi kuwa Faruq cike da mamaki ya ce, "whatt!!" Lantana ta cigaba da cewa, "wannan shine umarninta kuma dole ka san wa zaka zaɓa tsakanin mahaifiyarka ko matarka!". Sai a lokacin kukan da ta ke riƙeta tun ɗazu ya fito, sosai Sadiya ke kuka da tausayin kanta, tana matuƙar son mijinta, domin à wannan watannin da ta yi tare da shi ya nuna mata ƙauna ta gaskiya, kuma itama ta nuna masa, idan har ta rabu da shi to ba ta san ya za ta yi ba.
Rarrashinta ya shiga yi shima cikin tashin hankali, domin da so samu ne shima ya yi kukan, yana son Sadiya matarsa ba zai iya rabuwa da ita ba. "Wace amsa za mu je mu sanarwa Baabar?" Cewar Fatima tana murmushi, domin ta ga shima ya ruɗe da jin batun. Kafin ya amsa mata Sadiya ta ɗago ta dubesa cikin kuka ta ke faɗin, "mijina don Allah ka bi umurnin Baaba ka sauwaƙe min, ita ta haifeka kuma ta san zafinka, ta raineka har ka girma sannan ni daga baya na haɗu da kai, ka bi umarninta don Allah"
Tana kaiwa ƙarshe ta kuma sakin kuka tana zamewa daga hannunsa zuwa ƙasa, Aisha ta durƙusa tana dafata itama tana fitar da hawaye, idon Faruq dam da ƙwallah ya juya gurinsu Lantana, su kuwa ko ajikinsu sai ma jiran amsar da zai ce musu su ke, Faruq ya fara cewa, "na...na yarda zan..."..
Sadiya babu abun da ta ke jira sai jin saki nawa Faruq zai mata, ta rintse idanunta zuciyarta na ta ba da amshi. Yayin da a ɓangarensu Lantana ko wannensu ya fitar da murmushinsa. "na yarda zan auri Nusaiba, amma ba zan iya sakin matata ba", Faruq ya ƙarisa maganar, da sauri Sadiya ta buɗe ido, shi kuwa sa hannu ya yi ya ɗago Sadiya ya shige da ita ɗaki tare zaunar da ita akan kujera, wanda ita kam kallonsa kawai ta ke kukan ma ya tsaya jin abun da ya ce ba zai saketa ba, duk da kuwa ta ji zafin amsa auren Nusaiba da ya yi, amma jin ba zai saketa ba ta ji daɗi, to amma idan Baaba ba ta amince ba ta tsine masan fa?.
"Dear me yasa ba za ka sakeni ba? Wai ko ba ka ji abun da Baaban ta ce ba?" Ahalin yanzu hatta idanuwansa sun yi jazir saboda ɓacin rai, amma ya share mata hawayen idonta, yasa hannunsa duka biyu ya kama hannayenta yana cewa, "ki kwantar da hankalinki, tun tuni abun da ta ke so na yi kenan, saboda na ƙi amincewa shiyasa ta biyo ta wannan hanyar, tun da na amince yanzu ba za ta tsine min ba, kwantar da hankali" ya faɗi yana janta jikinsa tare da lumshe ido.
Shi kwata-kwata ma bai ga me zai yi da mata biyu ba, ba ya buƙata Sadiyarsa ta ishesa amma akan ya rabu da ita gwara ya auri Nusaibar. Ita kuwa Sadiya ajiyar zuciya kawai ta ke saukewa à jere a jere.
Girgiza kai Aisha ta yi tana share hawayenta sannan ta wuce sashin Baabar ta barsu Lantana da su ka rasa ma me za su yi, haka dai su ka juya don kaiwa Baaba amsar saƙonta. Zuwa Aisha ta yi ta samu Baaba zaune akan kujera tsakar gida, zata mata magana kenan Lantana ta katseta, su ka ƙaraso suna bin Aishar da kallo Badiyya ta ce, "zuwa ki ka yi ki cewa Baaba itama bai kamata ba ko? Wai ke Aisha menene matsalarki wai?" "Ku rabu da Aisha ita dama babu abun da ta sani, kawai ku sanar da ni me ya faru bayan kun je?" Cewar Baaba.
Nan su ka kwashe komai su ka rangaɗa mata, "me!? Wato shi Faruq ko me zai faru sai dai ya faru rabuwa da matarsa ne ba zai yi ba ko? Shikenan wannan ɗin ma ya yi, ai da na san zai amince da tuntuni na bi hanyar nan, yanzu zan kira Mairo insanar da ita a fara shirin biki, ko sati ɗaya ba zai kai ba", Fatima ta ce, "amma Baaba malam fa?" "Ba dai Faruq ya ce ya yarda da auren ba? Ai Malam bai da matsala rashin amincewar Faruq ɗin ne yasa ya ƙi amincewa, ku bar min komai ku kam" faɗin Baaba ta wuce ɗauko wayarta da ke falo cike da farin ciki.
Badiyya ta ce, "ni wallahi so na yi ya saketa ma" "ba komai hakan ma ai dama ce, Allah ya kaimu lokacin da Nusaiba za ta zo gidan nan, sai ta fi gane kuranta, ai lokacin da kanta ma za ta ce da sakinta Faruq ɗin ya yi da zamanta" Aisha cike da haushi ta murya ƙasa-ƙasa ta ce, "Allah yasa kuma ai muku àbun da ku ke yiwa anty Sadiya, anaku gidan in kun yi aure".
Da sauri su ka juyo suna faɗin, "me ki ka ce?" "Ba komai" ta faɗi sannan ta wuce ɗakinsu. Lantana dai shiru ta yi don maganar da ɗan uwan na ta ya ɓata mata rai, cikin ranta ta ce, "Sadiya? Akan Sadiya matarsa zai faɗa min haka? Wallahi sai na yi mata abun da ba ta taɓa zata ba!".
Baaba kuwa ba ɓata lokaci ta kira ƙawarta Mero ta sanar da ita Faruq ya amince da auren Nusaiba, don haka tana son su shirya kada abun ya wuce mako ɗaya, da murna Mairo ta ce, "an gama ƙawata ba ki da matsala, kin san ita Nusaiba tana matuƙar sonshi tuntuni, don haka abun farin ciki ne a wurinta" nan dai su ka cigaba da tsara yadda za su yi.
A ɓangaren MAIRO kuwa.
Ko da ta gama waya da Baaba ta kira Nusaiba, wacche da ka ganta ba ka neman ƙarin bayani akanta, kasancewar mahaifiyarta Mairo mace ce mai son duniya, da kuma bin malaman tsubbu, hakan yasa Nusaiba ma ba ta baro halin Mairo ba, ga ta masifaffiya ba ta ganin girman kowa kuwa, ba komai ba ne yasa ta ke son Faruq sai don yana da 'yan canji, sannan kyakykyawa ne shi, hakan yasa Nusaiba ta ke da burin ta ga ta mallakeshi, babu yadda Mairo ba ta yi don ganin Faruq bai auri wata ba sai 'yarta bayan jin ansa rana, amma kuma da ya ke Allah ya fisu, sai duk ɓaɓatunsu ya tafi abanza ba su ci nasara ba, kuma fa duk wannan labarin Baaba Talatu ba ta san da shi ba.....
NURIYYAH.
"Na ce me ki ke ɓoyewa à hannunki!" Mama ta ƙara faɗi da ƙarfi, gaba ɗaya gumi ya gama tsatsafo min, kafin na nemo me zan ce mata kawai ta sa hannayenta ta juyar da ni, lokaci ɗaya ni da ita mu ka zare ido, ita na ganin sarƙar da ta yi kama da na ta, ni kuma na tsoron tawa ta ƙare.
Wani irin fisga ta yiwa sarƙar 'yan kunnensa su ka zube ƙasa, da sauri na juyo ina kallonta cike da tsoro, yayin da ita kuma idonta ke kan sarƙar tana son gasgata tunaninta, "wannan!...wannan ba sarƙata ba ne Nuriyyah?" Ta yi min tambayar tana ɗagowa kaina, bakina rawa ya ke yi na kasa furta ko wace iriyar amsa.
Hannu ta sa ta ɗauki 'yan kunnen da su ka faɗi ƙasa, sannan ta ɗago tana aika min da kallon wanda ya sake tunzura tsorona, tana faɗin, "ba za ki ban amsa ba, na ce wannan ba sarƙata ba ne!?". Ƙasa na yi da kaina ban iya furta ƙala ba. Nan take Mama ta gamtse fiskarta cike da tsana ta kama hannuna ba tare da ta ce komai ba, sai da na kalli hannunta da ta damƙe hannuna sannan na maida idona akanta, 'inna lillahi wa inna ilaihi raju uun' na furta a cikin zuciyata.
"Zo mu je!" Ta faɗi tana ja na mu ka bar ɗakin, sai kuma ta fara ƙwalawa Momy kira, "Rahama kina ina? Kina Ina Rahama?!" Ta faɗi tana cigaba da ja na tana nufar falo da ni, da ya ke tozartani ta ke son yi. "Wayyo na shiga uku!" Cewar Wasila da ta hangi Mama na jana kuma hannunta riƙe da sarƙar, bayan sun ji kiran da Mamar ta ke yi sun fito.
Mama ba ta tsaya a kiran Momy kaɗai ba, da yake kusan kowa ya dawo gida, sai da ta tabbatar da ta haɗa kowa à falon Momy ciki kuwa har da Abba, da Dady. Uncle Usman ne kaɗai ba ya nan à cikin mazan. Kowa ya hallara idonsa kan Mama da kuma ni da na yi ƙasa da kai tun ɗazu ba na kallon kowa, jikina kuwa sai ɓari ya ke yana ƙarawa.
Momy da ke bin Mama da kallon rashin fahimta tun ɗazu, saboda ta tambayi Mamar me ya faru amma ta ƙi sanar da ita sai kiran mutane ta ke yi, sai yanzu Momy ta kuma tambayarta, "Mama na tambayeki me ya faru amma ba ki sanar da ni ba, kuma sai tara mutane ki ke, duk akan me ki ke yin hakan Hajja Mama? Sannan kin saka Nur a gaba".
Kowa jiran abun da Mama za ta ce ya ke yi, amma Wasila kam tuni ido ya raina fata, saboda ta san ko shakka babu wannan sarƙar da Mama ta gani a hannun Nuriyyah ne. "Wato wancan karon ance ba ita ta sace na Fatima ba, kuma zai yi wuya idan ba ita ba ce ma ta haɗa wani plan ɗinta, ta sa aka ga ni a hannun wata, zan faɗa yau kamar yadda na faɗi a baya, yarinyar nan ba alkhairi ba ce ta kasancewa a cikin zuri'armu, domin kuwa kura ce da fatar akuya", cewar Mama tana taɓe fiska da kallona.
Yayin da ni kuwa kalamanta kamar saukan dutse na ji su cikin raina, zuciyata ta cigaba da bugawan tsoron da ta fara tun ɗazu, kafin wani ya yi magana wannan karon Dady ya kalli Mama da rashin fahimta ya ce, "Hajja Mama what's wrong? Ni fa ban fahimci me ki ke cewa ba, taya za ki faɗi kalamai haka akan Nuriyyah?". Hajiya Kaka ma ta ce, "ƙwarai kuwa akan wani dalili za ki jefeta da wannan maganar mai muni? Wannan abun bai da ce ba".
Momy ba ta yi magana ba domin kuwa su Dady sun faɗi abun da za ta ce, sai dai jiran jin amsar da Mama za ta ba da, Nusaiba da ma ba abun da ya dameta da ni, sai ma haushi da ya sake ratsata a kaina, Asma'u kuma fiskarta da mamaki itama. Sai shi kuwa Abba, idonsa kan Nuriyyah ya ke kawai ganin yanayinta, hakan bai yi masa daɗi ba ko kaɗan, jin zuciyarsa ya ke yi kamar ya je ya kwantar mata da hankali, saboda ya ga alamar kamar tsoro na tattare da ita.
Mama kuwa cewa ta yi, "to kafin ku sake cewa komai, bari ku ji abun da yarinyar nan Nuriyyah ta aikata, ko da yaushe ku kareta ku ke yi, to yau ba abakin wani na ji ko na gani ba, ina shiga ɗakin ta yi saurin tashi ta ɓoye hannunta a baya, ko da na juyo da ita sarƙata na gani a hannunta! Gashi nan" Ta faɗi tana nuna musu sarƙar, "à hannunta?!!" Duk kowa ya ambata tare da zare ido inka ɗauke Nusaiba 'yar Mamar.
"Ƙwarai à hannunta, ga ta ku tambayeta ta bada amsa, ɓarauniyar banza ɓarauniyar hofi", "Nuriyyah na san ba halinki ba ne, faɗa mana ya aka yi hakan ya faru?" Cewar Dady yana matsowa kusa da ni, hawaye suna rige-rige a fiskata à hankali na ɗago ina dubansa, sai kuma na kai kaina kan Wasila da idonta ya ke a zare cikin firgici.
Ko da ganin mun haɗa ido da ita sai hawaye ya gangaro a idonta, wanda ni kuma hakan bai min daɗi ba, sai na ji na kasa amsawa Dady tambayarsa kawai na yi ƙasa da kaina, "na ce muku ni fa na ƙwace a hannunta idan ba sacewa ta yi ba to me ta yi?" Momy ta dubi Mama ta ce, "Hajja Mama ya kamata ki bi komai a sannu kada ya zama rashin fahimta ne kamar na baya".
Hajiya Kaka ta giɗa kai, Abba ma ya samu damar buɗe baki ya ce, "maganar Momy gaskiya ne Mama, kada a sake yin kuskure kamar na baya, saboda na tabbata Nuriyyah ba ta yi satar nan ba", ban san lokacin da na ɗago idanuna da su ke fitar ruwa zuwa gun Abba ba, jin ya kirani da sunana wanda na san dai Gajera shine sunan da ya ke kirana ako da yaushe, sannan kuma yana kareni akan abun da bai ta tabbaci a akai?
"To yo na nawa kuma? Bayan ta riga ta aikata, idan ba haka ba ne ga ta nan ta kare kanta mana!" Cewar Mama tana nuna ni da yatsa, don ta ga alama kamar so su ke su ƙaryatata. Momy ta taho ta juyar da ni gefenta, ta ɗaga ido tana kallona ta ce, "yata Nur faɗa mana me ya faru? Yi magana" nan Dady, da Hajiya Kaka, har da Abba, su ma suka tambayeni akan na faɗi me ya faru, Asma'u shiru ta yi tana kallon kowa kawai, Wasila kuwa idonta bai bar fitar da hawaye ba, sai Nusaiba da ta ke ta yamutsa fiska sai ma ta fice ta bar wurin.
Ni dai na kasa cewa komai, ban san me zan ce ba, domin na sake haɗa ido da Wasila kuma na ga idanunwanta itama kuka ta ke yi, "ba ga shi ba ba ta da bakin magana, to me ma za ta ce bayan ta san ta aikata, ai ba za ta ce komai ba!" Sakina Momy ta yi tana cewa, "me yasa ba za ki faɗi gaskiya ba?" Su Dady kam shiru su ka yi sun ma kasa magana, tun da na ƙi ba da amsa hakan na nufin da gaske na ɗauka kenan? Abba dai bai yarda ba amma yana iya gane akwai abun da yasa ba zan faɗi gaskiyar ba, to menene?.
"Kai bai ma kamata ace na ma barki haka ba" cewar Mama tare da janyoni da ƙarfi ta ɗaga hannu za ta kifa min mari, na rintse idona da ƙarfi, haka shima Abba kamar shi za a mara, kafin ta kai ga sauke min hannun ta dakata ƙyam, sakamakon riƙeta da Wasila ta zo ta yi da ƙarfi sannan ta ce, "ka da ki mareta Mama don Allah!!". A hankali na fara buɗe idanuwa da na ke jiran saukar marin, haka Abba ma ya buɗe ta sa, su Momy da su ka fidda ido ganin Mama na shirin marina su ka maida kallonsu ga Wasila da ta yi magana da ƙarfi!!.
Last page
___________________________________________________
To fah, Faruq ya amince da auren Nusaiba, shin kuna ganin hukuncin Baaba zai zame musu alkhairi? Shin Sadiya za ta ji daɗi bayan wannan al'amari ya faru? Ko kuma wani sabon babin ƙaddararta ne. Idan kun lura, ita fa Sadiya sanadin ƙaddararta kalmar Momy ɗaya tak ne.
A gefe ɗaya, Wasila ta tsaida maihaifiyarta kuna ganin za ta faɗi komai da kanta? Ko kuwa?.
Ka da ku manta, bayan kun gama karantawa, ku dannan min like da comment, don insan ya ku ka ji sannan inji hasashenku. Idan so samu ne ku haɗa min da share fisabilillah 🥰
_*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_