Kuncin zuci
by @bintuuu
A daren Na'ima suka fara shirin tafiya Rome tareda Ahmad, tana zaune bakin gado Nafisa sai jeka dawo take a dakin tana hada musu kayansu, sai da tayi arranging creams and oils dinsu sannan ta kalli Na'ima tace "Bobo please dubamin weather forecast dinsu, in da dan sanyi sai in hada mana da light jackets" dauko waya Na'ima tayi ta fara dubawa sai taga wani message din Ahmad ne ya shigo wayan nata, murmushi tayi ta koma baya ta jingina da gadon suka fara chatting sama sama dashi, wanda mostly short and casual messages ne akan tafiyan nasu amma Na'ima jinsu take har ranta, sai da Nafisa ta fara jera kayan ta juyo tana kallonta tareda riqe qugu tace "Sannu Na'ima" da sauri tace "Eh?" Nafisa tace "The forecast?" sai sannan ta tuna, tana murmushi ta sake dubawa ta fada mata, kiranta video call yayi da kamar bazata dauka ba da farko, sai can ta dauka fuskanshi ya bayyana yana kwance akan three seater na falonsa, kallonta ya tsaya yi sai ta juya kai dan har ga Allah abunda yasa batason video call dashi kenan, direct take kallon idanunsa da suke mata kaifi dayawa, ganin taqi juyowa yasashi yin murmushi a nutse yace "Rowan fuskanki zakimin Babe" ta girgiza kai tana murmushi, dan juyowa tayi taqi kallonsa a ido, ganin kunya ya cikata yasashi kwantar da murya, ahankali yace "Inason kunyan nan naki Na'eemah" batace komai ba sai murmushin da yaqi barin fuskanta, wani farin muzurun mage ta gani ya hau kan fuskan Ahmad din sai ya fara lasan wayan, dariya ta fara ganin Ahmad na qoqarin tureshi daga kan fuskansa, shima dan dariyan yafara yace "Babe, meet Simba" ta dan daga hannu cikin sanyin murya tace "Hi Simba" kamar magen yaji me tace sai yayi meow, nan ma dan dariya sukayi Ahmad yace "Ya gane kin kirashi fa" ta sake cewa "Nice to meet you Simba" kirane ya shigo wayan Ahmad din yayi excusing kanshi a gurin ta sai ta gyada kai sukayi sallama, sai sannan ta dago kai taga har Nafisa ta gama hada musu kayan tsaf tana saka musu accessories dinsu acikin qaramin jaka....
Washegari sai karfe goma na safe suka fara shirin tafiyan, Na'ima ta shirya cikin wani classy black abaya da ya haska farin fatarta sosai, nan bakin mirror ta tsaya tareda yin light makeup na lip gloss and powder a fuskanta, Nafisa ma abayan ta saka amma nata milk color, Kiran Mami ne ya shigo wayan Nafisan sai tace ta saka a handsfree, bayan sun gaisa ta tambayesu ko sun shirya tafiyan, dan sun kirata har Abba sun sanar musu da tafiyan tun jiyan, bayan sun amsa mata sai tace "Ku kula sosai fa, banason shiririta" suka amsa da toh sannan tace "Allah ya kaiku lafiya, Allah yayi albarka" da haka sukayi sallama suna amsa addu'an nata...Ahmad ne ya zo daukansu shida drivern sa, Antyn Amnah na gida lokacin dan ranan bata je asibitin bama wai batajin dadin jikinta su twins kuma suna school, har bakin motan ta rakasu sukayi sallama tayi hugging dinsu, sai da suka biya aka dauki Lauren sannan suka wuce airport din, acan suka tadda Lamin a tsaye yana jiransu a waiting lounge, handshake sukayi da Ahmad, Lamin na cewa "Hey man" Ahmad ya gyada kai kawai, sai Lamin din ya kalli Na'ima yana murmushi yace "Our sleeping beauty princess" Ahmad ya kalli Na'iman yace "Karki kulashi" sai tayi murmushi tace "Ina kwana" dan dariya Lamin yayi sannan ya amsa tareda kallon Nafisa da Lauren, gaisawa sukayi Nafisa na magana cikin nutsuwa wanda se da Na'iman tadan kalleta dan mamaki, basu dade ba akayi kiran jirgin su, a first class suka zauna amma seats dinsu Na'iman daban da nasu Ahmad shida Lamin, within 3 hours din suka isa Rome, Na'ima nata kallon city din through window...kamar yanda Nafisan ta fada din ne kuwa, a wani tsadadden Beach resort Ahmad ya kama musu babban daki me hade da falo har da balcony da ke facing beach me ban sha'awa, sai da ya tabbatar sun shiga dakin nasu sannan ya juya zai koma nashi masauqin, shigan su dakin Nafisa ta wullar da jakanta tayi tsalle tareda kifewa kan gadon tace "Wow...this is life" Lauren sai videon dakin takeyi itama bakinta yaqi rufuwa tace "This is beautiful", tafiya wajen balcony Na'ima tayi ta dafa rail din tana kallon cikin resort din cikin ban sha'awa, dan kallon qasa tayi sai ta ware Ido tana murmushi da dan mamakin ganin Ahmad dake kallonta, yana tafiya da baya da baya tareda dago mata hannu alamun bye bye, daga masa nata hannun tayi tana fadada murmushinta har hakoranta na bayyana, sai sannan ya juya ya cigaba da tafiya tareda da sa hannuwansa a aljihu sai ta tsaya kallon bayansa bata ko kifta ido tanajin zuciyarta na amsawa da abunda takeji akansa....
Har dare basu fita daga dakin ba sun baje anan falon sai ciye ciye suke suna hira, washegari ma da sukayi waya da Ahmad da safe sai yace musu yana da aikin da zeyi suyi hakuri baza su gansa ba, Nafisa tace "Yaya ai dama aiki kazo yi, mu kuma hutu" yana murmushi yace "Ku huta Nafisa" tayi dariya Na'ima na girgiza kai tana murmushi, haka suka wuni a beach ranan Lauren na ta musu video a bakin sea na beach din, babu yanda Nafisa batayi ba dan Na'iman ta shiga ruwan amma taqi, haka tana ganinsu suka rinqa video acikin sea din, har abincin da zasuci a restaurant din sai Lauren tayi video'n sa, wanda hakan ba qaramin ba wa Na'ima mamaki yake ba tana ganin qoqarin content creators, har dare babu labarin Ahmad sai dai waya da sukeyi, washegari ma haka suka wuni gurin shopping wanda Ahmad dinne ya aiko musu card dinsa, hannunsu cike da shopping bags suka koma masauqinsu, A kwana na ukun ne da dare ya kira Na'ima bayan ta fito daga wanka ahankali tace "Aiki ne ya maka yawa?" daga daya bangaren Ahmad yadan sosa girarsa da yatsa yana kallon laptop din da yake aiki da ita a gabansa, sai ya sauke numfashi yace "I'm almost done in sha Allah" ta gyada kai bata ce komai ba, sai ya sake cewa "I'm trying to finish everything soon, so we could have time together Babe" sai sannan tace "Allah ya taimaka" da haka sukayi shiru, can Ahmad yace "Can i video call you?" da sauri ta kalli towel din da ke daure a jikinta tace "No..um..um" yana murmushi shima a hankali yace "Are you wearing your night dress?" tace "No..it's, uh.." sai ta daure kawai tace "Nayi wanka ne" shiru yayi yanajin wani sauyi a yanayin sa, kawai sai ya kashe wayan, dago wayan tayi daga kunnenta jin shiru sai taga kiran ne ya katse ashe, kawai sai ta ajiye wayan ta nufi jakan kayansu zata yi shirin bacci dan har sannan su Nafisa basu dawo daga restaurant din cikin resort din ba....
Basu sake waya ba sai washegari da dare ya kirata, da ta dauka yace "I'm outside, can you come out?" ta gyada kai tareda cewa "Okay" sai da ta sake shiri ta dan fesa turare sama sama sannan ta fice, a lobby ta gansa tsaye sanye cikin black three quarter da T-shirt me dogon hannu, hannunsa daya cikin aljihu dayan kuma yana danna wayarsa, dago kai yayi suka kalli juna sai ya dan yi murmushi, sai da ta qaraso gabansa sannan yace "How i missed you Babe" cikin kunya ta juya kanta tana murmushi, sai yace "Should i order us food?" ta girgiza kai tace "Na qoshi" ya gyada kai, ta sake cewa "kaifa? bakajin yunwan" yace "i'm okay" da haka suka fita wajen resort din suka nufi can bakin ruwan beach din suna tafiya a hankali, Ahmad ne yafara magana tareda kallonta, yace "Can i ask you something Na'eemah?" ta kallesa itama tace "Yes" yace "Shekaru nawa kikayi da ex husband dinki?" sai ta kauda kai tana kallon sea din tace "About four years" ya gyada kai sannan ya sake cewa "What about kids? kin taba haihuwa dashi?" dan stiff Na'ima tayi na tuna Bilal bai taba saninta ba ma balle ta haihun, sai tayi kasa da kanta tana girgiza kai alamun "A'a", ganin kamar mood dinta ya fara chanjawa yasa Ahmad barin maganan, yace "Do you like Rome?" ta juya ta kalli resort din tace "I love it, the place is beautiful" yace "Zamu dawo mu kadai watarana, tunda kinaso" tayi murmushi tana kallonsa sai ya miqo mata hannunsa yace "Here, mutafi kar sanyin ruwan nan yasaki mura" ta gyada kai tareda kama hannun nasa suka bar bakin ruwan tareda komawa cikin resort din zuciyarsu cike da annushuwan kasancewa tare da junansu...
Sai da suka qara wasu kwanaki biyar suna hutawansu a Rome kafin wani tafiyan Ahmad din zuwa Venice ya taso masa, zuwa sannan duk wani ancient gurare sai da su kaje, siye siye dai kam sunyi shi da card din Ahmad har sun gaji, ana gobe zasu tafi shima tareda dasu Ahmad da Lamin din suka fita, wani finest restaurant in town din suka je cin abinci suka sha hira cikin raha, washegari da zasu koma Ahmad sukazo kaisu airport dan shida Lamin din zasu wuce Venice sai wani satin zasu koma London, A airport din Na'ima sai kallon Nafisa take tana danne murmushi ganin yanda take sunkuyar da kai suna magana da Lamin, Ahmad dake gefenta sai ya kamo hannunta ya rada mata "They'll make a good couple, Lamin is a good guy" bakin Na'ima kamar ze yanke dan murmushi tana kallonsu, gani tayi Lamin ya dan sunkuyo yana fadawa Nafisan wani abu sai ta fara dan dariya tana rufe bakinta da hannu, Lauren ce ta qaraso gurinsu hannunta riqe da cocktails ta miqawa Nafisan sannan ta kawowa Na'ima ta karba tace "Thank you Lau" sai ta gyada kai sannan ta kalli Ahmad tana murmushi tace "Thank you so much for this trip, it's surely unforgettable" ya dan girgiza kai yace "No thanks", sai da ta koma gurinsu Nafisan sannan Na'ima ta kallesa zatayi masa godiya sai taga ya saka yatsansa a baki alamun tayi shiru, da aka kira jirginsu suka yi sallama zasu tafi, sai ta juyo tana kallonsa yana tsaye shida Lamin din sai ya daga ma ta hannu yana murmushi yakai hannunsa kunne alamun "Sai munyi waya" ta gyada kai cikin sanyin jiki ta juya suka tafi....
Bayan sun koma London nan gidan Anty Amnah suka fara tsumayin lokacin graduation din nasu wanda ji suke kamar lokacin bazai zo ba, dan suma suna son komawa gida hakanan, Ahmad ma bai cika satin ba ya dawo a kwana na biyar, ranan da ya iso gidan Amnah'n ya fara zuwa yasamu daga ita sai Na'ima dan ko twins ma sun fita tareda Abban su, da suka gaisa anan falon sai ya miqe akan zai tafi, da tayi masa tayin abinci ma yace ya qoshi, sai da ya qarasa gaban motan sa sannan yayi texting Na'ima, tana zaune falon tagani, da farko kunyan magana da Anty Amnahn tayi sai can ta daure ahankali tace "Anty zanje yana kirana" Anty Amnah na murmushin tace "Je ki abunki daughter" ta miqe tana gyara veil din jikinta ta fita, bin ta da kallo Anty Amnah'n tayi har sannan tana murmushi, dan lamarin nasu na burgeta, tana matuqar son alaqan tasu takai da gaci...
Da ta samesa a wajen suka gaisa sai yace "Babe ki rakani restaurant inci abinci" sai ta dan ware Ido tace "Yanzu fa aka gama maka tayin abincin" ya gyada kafada yace "I want to have time with you" da haka ya bude mata front seat ta shiga sannan ya shiga ya tada motan suka tafi, tun kafin su qarasa restaurant din ya nemi wajen parking dan cikin gari ne tsundum jama'a sai bustling suke kowa na harkan gabansa, a kafa suka taka zasu qarasa, sai da suka je daf da restaurant din kiran Mamma ya shigo wayan Ahmad din, bayan ya ciro wayan daga aljihu sai yace da Na'ima "Sorry i have to take this" ta gyada kai, yana cikin wayan ta masa alama da hannu akan zata shiga cikin gurin kafin ya gama, sai ya gyada ma ta kai ta juya ta shige restaurant din, yana nan tsaye yana waya sai wani ya zo ya wuce ta gabansa zai shige restaurant din, dan binsa da kallo Ahmad yayi sannan ya cigaba da amsa maganar da Mamma'n ke masa, ba'a fi minti biyu ba Na'ima ta fito a rikice daga cikin restaurant din Bilal ya biyo bayanta yana kamo gyalenta yace "Ki tsaya ko in ji miki ciwo wallahi" Ahmad bai qarasa Jin ma abunda ake fada a wayan ba ya taho da hanzari ya tura Bilal din baya da karfi yana cewa "Back off Man, who are you?" da sauri Na'ima ta miqe bata ma san ina take nufa ba, sai Bilal ya ture hannun Ahmad din daga qirjinsa da bacin rai shima yace "Kai zan tambaya, who da f"ck are you?" Ahmad was taking aback with suprise da kalman Bilal din, gashi turawan da ke wucewa suna kallonsu sai ya juya yaga Na'ima na tafiya da sauri sauri tana gyara gyalenta, hankali a dan tashe ya bi bayanta, shima Bilal ganin hankalin mutane yadawo kansu harda mutanen dake cikin restaurant din ne yasa bai bi bayansu ba ya tsaya...da sauri Ahmad ya iddata tana tafiyan, ya kai hannunsa zai riqe nata ta kwace hannunta da qarfi tace "Don't touch me Bilal" sannan ta juyo taga Ahmad, ganin hawaye a idonta yasa hankalinsa tashi, ya kwantar da murya yace "Babe don't cry here, muje mota" sai sannan ta fara bin mutanen dake zirya a wajen da kallo, ahankali ya sake cewa "Not here Na'eemah" sai ta gyada kai tafara goge hawayenta suka juya, idon Ahmad ne ya fada cikin na Bilal dake tsaye a bakin restaurant din har sannan yana kallonsu fuskar nan kamar hadari, Ahmad na kallon cikin idonsa ya miqa hannusa ya damqe hannun Na'ima da take kallon Bilal din itama, sai ya juya ya tafi cikin bacin rai, tana riqe da hannun Ahmad suka qarasa gurin motarsa, bayan ya bude mata ta shiga ta zauna sai yakai hannu yana gyara mata qasan riganta da ya sauqo wajen motan sannan ya rufe motan ya zagaya ya shiga suka tafi, Har suka isa gida hannunsa yana cikin nata tana kallon window, baya seconds goma bai juya ya kalleta ba, bayan yayi parking sai ya dan duqo ya tayata gyara gyalen nata da take ta faman yi, ahankali yace "Shine tsohon mijin naki?" ta gyada kai hawaye na zuwa mata tace "Banason ganinsa, he hurt me" sai yayi saurin gyada kai yace "Bazaki sake ganinsa ba, I'm here kinji" ya sake cewa "Me ya miki Na'eemah?" anan kuma ta fashe da kuka wanda yake jin zafin hakan a ransa, sannan hakan ya nuna masa the guy did bad things to her that still hurts her har yanzu in ta tuna, cikin lallami yace "It's Okay dear, muje ciki ki huta" zai kai hannu fuskanta sai ta rigashi share hawayen, da haka suka fito daga motan amma Ahmad ya kasa shiga gidan yace ta shiga tukunna, sai da ya jira shiganta gidan sannan ya koma motan nasa, da sauri ya dauki hanyar komawa restaurant din dan su bashi cctv record dinsu....