WATA RAYUWA

2-3

by @annafiyo

*WATA RAYUWA*
  _BY ZAYNAB ABDULRAZAK_
*PAGE 2-3*
Goge idanunta tayi sannan ta kama hannun Mamie ta Fara kokarin tada ita, Cike da karfin Hali Mamie ta mike tare da goge hawayen da ya bata mata fuska tana kakalo murmushin dole. ya isa haka amma Mamie banji ciwo ba kalli natashi da kaina ,Dan bigewa nayi da kujera". kallanta amatullah take cike da tausayawa da Kuma jinjina Halin Mamie a koda yaushe abba ya daketa bata fushi ko nuna laifin sa,  kullum Yi take kamar ba abinda yake faruwa tsakaninsu.

 Kama hannun Mamie tayi ta kaita har dakinta ta zaunar da  ita a bakin gado, wani dakine da idan ba an fada maka ba bazakace a Nigeria dakin yake ba tsabar yadda yayi kyau royal bed NE da kayan da suka amsa sunan kayan daki a ciki,masha Allah fadar kyawun dakin ma bata lokaci ne dan kyawun da dakin yayi abin ba a cewa komai, .fice wa tayi daga dakin bayan mintuna kadan ta dawo da first aid box a hannunta, Ta dauki Dettol da cotton ta Fara gogewa Mamie ciwon da  Abba yaji mata , kallan Mamie tayi ganin yadda taga mahaifiyarta ta, ke yamutse fuska tasan tana Jin ciwon sosai hawaye ne suka sauko daga idanunta. Yadauketa minti hudu sannan ta tattare kayan ta mayar cikin box din. Magani ta balla ta bawa Mamie tasha sannan ta tashi ta fita daga dakin ba tareda ta kalli Mamie ba.
Fitowa Tayi daga dakin tana duba falonsu daya sha kayan alfarma masu kyau da daukar hankalin duk Mai kallo. Dankara -dankaran kujerune na alfarma da carpet shimfide a kasa daga dayan bangaren TV ce plasma Mai girman gaske.

    Can daga gefe akwai dining area Mai matukar kyawun gaske . Palon ya kawatu da kaya na Alfarma masu kyau da matukar tsada.
  A hankali take tafiya harta isa dakinta . Shiga tayi ta zauna a matsakaicin gadonta Mai kyau . Ba laipi dakinta yayi kyau yayi irin na yayan masu kudi, yayi kyau sosai . Takai mintina a zaune tana tausayawa rayuwarta da ta mahaifiyarta,
Idanunta sun  kumbura sosai saboda yadda Tasha kuka. Goge idannunta tayi ta janyo wayarta da take kara , kirar iPhone 13 ce . 
Bin wayar tayi da kallo saboda ganin sunan da yake yawo akan screen din wayar . Harta katse bata daukaba wani Kiran NE ya sake shigowa ,dauka tayi a hankali takai kunnanta , daga can bangaren Rufaida ke mata magana "amatullah kina Ina NE har yanzu Baki shigo ba saura minti talatin fa doctor sadam ya shigo , kuma kinsan halin sa yana shigowa sai dai ki hakura da  test din sa.

Shiru amatullah tayi  hakane yasa Rufaida cewa hello kina jina kuwa ?.
Yanzu zan taho , amsar da ta iya  bawa Rufaida kenan ta  katse wayar. 

Tashi tayi ta fada bandakin da ke cikin dakin, a gurguje tayi wanka ta fito, Shiryawa tayi cikin tsadaddar abaya baka Mai kyau wadda ta haska farar fatarta, tadan gyara fuskarta sannan ta dauki key din motar ta da Jakarta ta fito compound din  gidan ta shiga mota, horn tayi wa mai gadi ya bude mata ta fice .
  Mension NE gidan dankarere Mai kyan gaske bangarori biyune a gidan Amma yana da girma Kuma ya tsaru sosai . Compound din gidan za’a iya parking din motoci kamar goma Sha biyu.
 Masha Allah gidane da ya amsa sunan hadadden gida.
 Gudu take sosai akan titin tarauni , kwana ta shiga Inda ya sadata da titin UDB. Minti baifi biyar ta dauka ba, ta iso makarantar MARYAM ABACHA AMERICAN UNIVERSERTY KANO.

  A waje tayi parking motarta kirar Mercedes baka Mai kyau. Da sauri ta shiga tana hadawa da gudu . Tsakanin kofar gate da main building na makarantar akwai tafiya sosai hakanne yasa tadan bata lokaci kafin ta karasa. Da sauri ta fada cikin ajin Daya hada dalibai da Dan dama .
  
 Fariderh ce ta karasa wajenta da Dan sauri tana mata hararar Wasa."sai yanzu sarkin latti?" Shiru tayi mata sannan ta Mika mata Hannu tana karbar labcoat dinta tana sawa ., amsa ta bata a takaice "eh Natashi a makarane shiyasa.

  Doctor sadam ne ya doshi hanyar class din da yasan yana da lecture kai tsaye ya wuce cikin class din bakin sa dauke da sallama, a sannu kowa ke Neman gurin zama , cikin Yan mintuna ajin yayi shiru sannan ya Fara lecture.