Part 3
by @chefmuaysh
RAYUWAR MARYAMA*
*_By Aisha Hamz_*
~BOOK 📚 1~
*Sharar take amma yunwar da take* *ƙwaƙularta tahanata yin sauri hawaye kawai take zubarwa tana haɗiyar zuciya domin tasan idan Balaraba tajiyo kukanta toh fa kashin ta ya bushe ba ruwanta da yunwar da takeji zata ƙara dukanta*
*koda tayi rabi kasa ƙarasawa tayi tazauna ƙasa cikin ƙasa duk tayi buɗu buɗu da,ita idonta takai duba izuwa inda balaraba ta sauke* *Abincin safe tasan ba za,a rasa komai a ciki ba shiyasa da zatayi wanke wanke balaraba tace karta wanke da tukunyar safen a hankali take jan jikinta harta isa bakin tukunyar*
*tabuɗe shinkafa ce dafa duka ƴar kaɗan a ciki dukta bushe saboda buɗewar da murfin tukunyar yayi daga gefe haka ya tabbatar mata da shine abincin nata bata jira komai ba tasaka hannu tafara hannu baka hannu ƙwarya har tana ƙwarewa saidai saboda ƙarancin Abincin nan da nan ya ƙare*
*Batasan sanda tasaki gorar ruwan da yake hannunta ba sakamakon jiyo Muryar Balaraba da tayi tana faɗin iyeee eh lallai yarinyar nan wato kin nunaman ban isa dake ba ke kin girma wuyanki ya,isa yanka ince sai kingama sharar sana kici Abincin amma saboda kin rainani shine zanganki akan tulun ruwa wato ke har kin ƙoshi ma ko*
_Kyarma tafarayi tana haɗa hannuwa tana faɗin don Allah kiyi haquri maman Hafizu wlh wlh ……….tassss taƙara mata tassss mari biyu sana tasanya ƙafa ta harba ta tadauki iccen geza ta cigaba da dukanta tun tana iya_ _magana tana bata haƙuri har ta kaida ta kasa yi mata magana sai numfashi da take sama sama saida maƙociyarsu Indo ta shigo tana faɗin haba maman Hafizu wannan duka haka sai_ _kace kina dukan wata babba haba don Allah tafaɗa tana amsar Maryama daga hannunta_
*Balaraba tana miƙa hannu tana kokarin kara jawo Maryama domin tana ganin dukan bai isheta hakanan ba sai ta ƙara tana faɗin ina ruwanki wato dama na lura kina shiga harkar da Babu ruwanki ko Indo toh ki kifita harkata ki miƙomin ita nan*
*Indo bata ce mata komai ba ta saɓi Maryama a kafaɗa wadda duka yasa takoma kamar wata gawa tayi gaba tabar Balaraba da surutai*
_Zata dawo gidan ta sameni sai naga ubanda ya tsaya mata a garin nan balaraba ta faÉ—a tana shigewa cikin É—akinta tanata Ć´an surutanta_
*Wajen ƙarfe uku saura malam habu da yaransa'' suka dawo daga gona ya cike balaraba take domin bata huce da dukan da takeson takara yiwa Maryama ba*
_Malam habu yace balaraba yau kuma me yafaru keda baki gajiya da fushi a fusace ta kalleshi au haka ma zakace ko malam shiyasa gaba É—aya yaran nan naka suka rainani ashe dama kai kake basu goyon baya kenan wato Ni sarkin fushi ta inda take shiga ba tanan take fita ba_
*Saeda malam yaga tagama faÉ—an nata sana ya dubeta yace haba Balaraba tayaya za,ayi dakaina insanya yarana su rainaki don Allah kibar ma wannan zancen idan kuma baki yarda ba ki gayamin me kike so yanzu ayi*
_Malam ga Sadiqu nan ya girma yanzu yawuce zaman gida gsky malam ka kaishi almajiranta kaga sai yaƙara ilimi ko_
Malam ya dubeta da fara'a yace angama Balaraba indai wannan shine damuwan ai kamar É—anki ne kuma ai ilimi ma kike so ya samu
*Duk abinnan a cikin kunnen Sadiqu da najibu da sauri ya shige daki domin yau yaƙara tabbatar da yayi rashin mahaifiya ba abinda yake tunani sai ƴan ƙannensa da za'a rabasu dashi Abinda yafara zo masa a rai shine najibu da Maryama*
*idan yatafi wazai kula masa da Amanar da mahaifiyar su tabashi akan Maryama yanajin tausayin qannen nashi domin kuwa kallon su kaÉ—ai yakan rage masa wani radaÉ—in baya so yayi nisa da maryama*
*Toh ina jiran comment ɗinku masoyana❤️ shin littafin nan yana muku daɗi sosai🥰 yaya zata kaya idan aka ɗauke sadiƙu aka kaishi almajiranta🙄*
*Shin yaya rayuwar zata* *kasance🥺 ku biyoni gobe inshaa Allah domin jin yadda zata kasance👍*
_Na sadaukar da wannan page ga ƙawayena na amana ƴan Ajiwa 2k21 🥰💋_
Karki bari karku bari kar mu bari abamu labari top 3 Na A'ishatu Hamza wadda kuka fi sani da Muaysh graphics 🤟 🤗 basai na faɗa muku ba littafaine wanda daga jin sunayen su zaka gane cewa na musamman ne
(UMMU OR SALMA) UMMU kO SALMA
(ORPHANAGE HOME) GIDAN MARAYU
(MARYAM’S LIFE) RAYUWAR MARYAMA
Wannan shine account details din mu 👇
3201868037 A'isha Hamza First bank
Ko kuma 9131096058 A'isha Hamza Opay bank
RAYUWAR MARYAMA akan 400 kacal GIDAN MARAYU akan 400 sai kuma UMMU KO SALMA akan 400 ga wanda yake buqatar duka zai biya 1000 instead of 1200 sana zaka tura receipt after payment a wannan number *** ta whatsapp