KOMAI YAYI FARKO...

10

by @rahmakabir13

KOMAI YAYI FARKO...

Na

©®Rahma Kabir MrsMG.

Page 10.

Sarac Stars R Pen...✍️

Ko da na isa gida na tadda mashin ɗin Umar a ƙofar gidanmu, na shiga na samu har sun fara magana da Mamanmu, ya sanar da ita ya bani hutu zan zauna a gida saboda ba ni da lafiya, akan zubar jinin dana fara mara dalili, dan haka mama bata ja ba ta ce masa to, sai yayi mata sallama ya tafi, Mamanmu kuma sai ta samu damar yi mini faɗa.

Amma farida ya kamata ki tashi ki ni ma magani. Dama wani namiji ne zai zauna dake da wannan matsalar.

Na yi shuru ina nazarin maganarta tare da mamakin furucinta na inda take shiga ba ta an take fita ba, wanda ni na san a shakeruna da bai wuce ashirin ba ban san ta ina zan fara niman wani magani ba, saboda bani da wayon da zan iya yiwa kaina abu, musamman akan abunda bani da ilimi a kansa, tun da ban taɓa sanin ya zubar jini ya yake ba da kuma yadda zan san ina zan samu maganinsa na gargajiya, wanda wasu da yawan masu maganin niman kuɗi suke yi da shi ba maganin gaskiya suke badawa ba, wasu kuma suna saɓon Allah da sunan magani suke badawa, irin wannan tunanin nake yi a cikin kai da lissafin waye zan tunkara ya kai ni gurin da zan amsa magani na haƙiƙa, a wannan halin Kakarmu mahaifiyar mama ta kirata a waya, akan ga ƙannenta nan sun shirya ni suke jira na zo mu wuce gidan biki, dan Mamanmu ta sanar dasu ita ba zata je ba sai ni, tace mata ganin nan zuwa sai ta kashe wayar tana sanar da ni na tashi na shirya, ba musu na fita na ɗauraye fuskata na dawo na gyara na ɗaura ɗankwali na mayar da hijab ɗina na yi mata sallama na fita na samu abun hawa ya kai ni gidan Kakarmu dake unguwar Sarki, nan na haɗu da ƙannen mama muka wuce gidan biki.

Wajen ƙarfe tara na dare muna gurin dinner, sai ga kiran Babanmu akan duk inda nake na dawo gida, nace masa to dan na san ya dawo ya samu labarin abunda yake faruwa, nayi sallama da ƙannen mama dan suma sun fito akan mu wuce tare, na samu abun hawa suma suka samu nasu kowanne ya kama hanyar gida. Ashe kafin na isa baba ya kira Umar akan yazo nan gidanmu, dan haka ba ɓata lokaci ya je suka yi maganar. Na dawo na taddasu na zauna a ƙasa ina gaishe da Babanmu, amma bai amsa mini ba sai ya fara yi mini faɗa wanda ban san akan na miye ba, sunne kai nayi ƙasa ina wasa da hannun Jakata ga hawaye ya cika mini ido, yace na shirya maza-maza na bi mijina na koma gidana, nace to kafin na miƙe na shiga ɗakin Mamanmu na ɗauki sauran handouts ɗina dana aje su na fito nayi musu sallama nabi Umar muka koma gida.

...

A haka rayuwa ta cigaba da tafiya zaman namu babu daɗi ba farin ciki, tun da har lokacin Umar bai cigaba da kwana a ɗakina ba ya riga ya raba mana, nima kuma ban bi ta kansa ba na mayar da hankalina kan karatu, in ya siyo abinci na dafa in bai siyo ba inna je makaranta sai na siyan abu naci, wani lokacin har da ɗan saura nake ragewa a jakata wanda zan ci da dare tun da na san ga halin da muke ciki na zaman yunwa, kuma yadda na godewa Allah Babanmu yana turo mini kuɗin mota akai-akai, shi yasa bana shiga damuwa saboda Umar ɗin shi ke kai ni makaranta ya aje, sannan in ya gadama ya zo ya ɗaukeni in mun tashi, in kuma bai so ba sai ya kirani yace na dawo.

A wannan lokacin ne aka sallami Babansu Umar a gurin aiki saboda Gonma mai ci a yanzu duk ya sallami malamai tun daga na primary har zuwa jami'a, dan haka suma korar ya biyo ta kan Babansu sannan duk wanda yake gidan gomnati dole ya tashi, hakan yasa mutane suka dinga maganganu marasa daɗi akan wannan sauyi da aka samu, ciki kuwa har da babansu dan sosai rayuwar ta fara sauya musu, shiyasa dole Babansu ya sayar da gidan da suke ciki ya fara niman gida ƙarami, Umar shi ne ya yi jagora har suka samu gida a Badikko, ƙaramin filat ne mai ɗauke da ɗaki biyu da falo madaidaici sai kuma wani ɗaki a tsakar gida, da kuma bayi a kowanne ɗaki, sai filin tsakar gida, haka suka fara rayuwa a takure dan ɗakunan su yi musu kaɗan ba kamar wancen gidan nasu ba da kowa yana da ɗakinsa, shi yasa ko kayansu ma bai ɗauke ba babu in da za a saka su, akwai wani ƙaton carpet na falonsu na wancen gidan to bai samu guri ba duba da nan inda suka dawo duk tiles ne, dan haka sai suka ce ai gidana a falon ledan shakar ɗaki ne, dan haka a kai carpet ɗin can mu shimfiɗa dan zai ɗauke tun da falo akwai girma.

Da na dawo daga makaranta sai naga kaya har da gado da katifa da wasu tarkacen kayan, na aje jaka na fito na samu Umar a ɗakin da ya mayar nashi muka gaisa, sai ya shiga yi mini bayanin kayan wai an bashi carpet ɗin ne, gado kuma zamu aje musu amma zamu kafa shi a ɗakin da yake ciki, kai tsaye nace masa bana so tun da ni dai ba kwana a gadon zanyi ba, meye amfanin saka shi gwara a jingine shi har sadda buƙatarsa ya taso musu su zo su ɗauka, tunda gashi nan ma yana da kyankyasai a ciki, sai yace shi lallai sai an saka, nace masa to dan yafi ƙarfina shi ke sama dani, nace shi kenan na bashi guri. Washe gari ya kafa gadon a ɗakin ban ce masa ƙala ba, sai na sanar da shi na gama shirin makaranta ya ɗauke ni ya wuce da ni.

Tunda aka saka gado a ɗayan ɗakin sai raba ɗaki ya tabbata da gaske, dan baya kwana tare da ni, idan kuwa yazo ɗakina to wani rashin mutunci ne ya kawo shi, maganar kusancin aure kuwa tuni ya jingine ya daina niman haƙƙinsa, ni kuma ban taɓa kai kaina ɗikinsa ba kuma ya san jini ya tsaya ina ibada na. Duk da haka ban fasa gyara masa ba dan hatta zanin gado ina zuwa na shimfiɗa masa na share ɗakin, tunda gidan nawa ne in ban gyara bama wani ya gani sai ayi zaton ƙazanta ce nake yi. Muna a irin wannan zaman ne muka samu hutun makaranta bayan mun yi jarabawar first semester, kuma an fara azumin watan Ramadan, kullun ina gida sai fita mai dalili ya kama nake fita.

Lokacin da Sallah ya ƙarato na fita siyan abu sai hanya ya biyo dani ta layinsu, sai na shiga gidansu dan na gaishesu, to bayan mun gaisa ina shirin tafiya sai ƙanwarsa Abida ta tare ni tana cewa.

Dan Allah Farida ki ara mini DVD ɗinki.

Me zaki yi da shi.?

To idan ba zaki bani aro ba, ki bani kyauta mana ina so.

Abida idan na baki ni inyi amfani da wanne.? Amma ki tambayi Yayanki.

Sai ta yi mini godiya na fito daga gidan ina mamakin Abida, wanda kuma DVD da TV plasma Babanmu ne ya siya mini a lokacin aurena, dan haka duk wani abu a gidan nan nawa ne, saboda Umar kayansa ne kaɗai abunda yazo da shi sai gadon da ya kawo kwanaki da carpet.

....

Bayan an kwana biyu ashe Abida ta tambayi Umar maganar DVD Sai yace mata ai ba nashi bane ta tambaye ni. To dana ƙara zuwa gidan ne take faɗa mini ai tayi magana da yayanta ya ce mata DVD nawa ne, sai ta ɗaura da cewa.

Kawai dai in ba zaki bani bane ki fito fili ki faɗa mini na cire rai, ki daina yi mini wala-wala da hankali. Ok ba a kyauta ne muka ɗauki gado da carpet muka baki.

Abida ba ni kuka bawa gado ba, dan Yayanki shi ke kwana a kai, sannan kuma koda baku ba ni gado ba, ba a katifa nake kwana ba ina da nawa gadon, shi kuma carpet akan ledana mai kyau na saka shi, dan haka ba kida dalilin da zaki yi mini gori akan an bani kaya, kuma koda aka kai kayan bana gida zuwa nayi na same su, to bari ki ji, ni amfanin da DVD yake yi mini ya fiye mini gado da carpet ɗin da aka bani.

Sai na ɗauki Amir na goya shi dan lokacin na amso shi ya dawo hannuna, na cewa matar Babansu sai anjima wacce duk tana jin abunda ya wakana tsakanina da Abida bata tanka mana ba, na fice na nufi gida. To da Umar ya dawo bayan ya ci abinci sai na zauna nake faɗa masa abunda ya faru tsakanina da ƙanwarsa, sai na cigaba da cewa.

To ka faɗa mata ba ni nace a kawo mini kaya ba, kuma in da ta ni ne ba zan yi amfani da su ba, dan haka ba ta da dalilin da zata ci mutuncina akan tsofaffin kaya.

Sai yace nayi haƙuri zai je ya same ta, ni kuma sai ban sake cewa komai ba na miƙe na je na kwantar da Amir.

Washegari yaje gidansu ban san ya suka yi ba, ni dai na san dole na gyara zamana da ita dan ko da ta girme ni ba zan ɗauki raini ba, banda zuciya mai mance alkhairi ai ban cancanci Abida ta yi mini wannan wulaƙancin ba duba da irin kyautatawar da nake yi mata, tasha kwanciya asibiti nike zuwa nayi jinyarta. Akwai lokacin da ina da tsohon cikin Amir tayi wani rashin lafiya wlh babu wanda ya zauna da ita sai ni, haka muka yi kwanaki a asibiti har aka sallameta kafin na koma gidana, kuma ba dan ba su da 'yan uwa mata ba, yayyinsu mata biyu sun yi aure sannan suna da kannai mata a dangi waɗanda suka tasa ga kuma matar Babansu amma ni duk na ɗauke musu na zauna mata. Umar da ya dawo ya ce mini yayi mata faɗa, kuma sai da ya mai da mata zancen jinyarta dana yi mata a asibiti, akan bata kyauta ba ko dan wannan yaci ace ta riƙe ni da mutunci, sosai na yaba masa dan ban taɓa tunani zai iya kare ni ba a gurin 'yan uwasa duba da ga irin zaman da muke yi.

***

Lokacin bikin sallah, haka naci sallah bada sabon kaya ba, dan tun da muka yi aure da Umar bai taɓa siyan mini koda pant ba, kayan akwati sune nake ta murza wanda har na gama ɗinka sauran na ciki, batun naman sallah kuwa kaza ce guda ɗaya yake haɗamu, da yake Mamanmu tana kiyon kaji agiric to duk sallah a gurinta yake siyan guda ɗaya sai ta ƙara mana da guda ɗaya, inna gyarasu a ciki nake ɗibar wa gidansu na kai musu, sannan gidanmu ma na ɗiba na kai musu, duk da bana haɗa musu da abinci, dan tun da ake yin bikin sallah ban taɓa girka abinci na kai gidanmu ba saboda babu, kuma ban da halin ni na siya na dafa na kai musu, sai dai wannan tsurar naman nake kaiwa, suma baifi a ƙidayasu ba, bana damuwa tun da gidanmu akwai wadataccen abinci Babanmu yana noma, sai dai ma su ba ni.

Ranar uku da sallah na je can tsohuwar unguwarsu Umar, saboda akwai mutanen dana sani musamman 'yan Islamiyanmu, ga kuma matan abokan Umar, haka na shishshiga na sada zumunci dan har gidan Haj. Dada naje matar da ta zauna mini lokacin haihuwar Amir, na gaisheta kafin na fito da nufin na kama hanyar gida, sai na hango ƙanin Umar mai suna Jafar yana hira da abokinsa sai na matsa wajen nace masa mun zo karɓan barka da sallah tare da gaishe shi, sai ya murtuke fuska bai tanka mini ba bai kuma nuna yaga Amir ba balle ya karɓe shi, sai dai na gaisa da abokinsa, da ma shi nasa halinsa ko gidansu naje in dai ba nice na gaishe shi ba to ba zai taɓa gaishe ni ba sai dai muyi kallon kallo. Ganin irin tarbar dana samu a gurinsa sai na ja jikina na matsa gefe dan Umar ya kira ni yace na jira shi. Ba a jima ba yazo, sai ya miƙa mini kuɗi wai na hau mashin ɗin haya shi zai ɗauki Jafar ne mu haɗu a gidansu.

Amma ai ni gida zan wuce.

Na ce masa ina saka Amir a bayana na saka zani na ɗaure shi, sai Umar ya ce.

Zamu je gidanmu ne za muyi magana akan abunda ya faru tsakaninki da Abida, dan maganar ta zama babba ana buƙatar a tattauna.

Nace masa to kawai na ɗauki jakata nayi hanya dan na samu abun hawa, shi kuma suka wuce. Sun riga ni kaiwa dan haka ba ɓata lokaci na sallami mai mashin na shiga cikin gidansu. Na samu duka familyn gidan sun haɗu sai na zauna muka gaisa babansu ya karɓa Amir, kafin aka shiga mayar da magana, ni dai ban ce komai ba ina saurarensu, nan yayarsu Hasiya ta bawa Abida damar ta fara yin magana saboda ita tasu ce sun fifita ta a kaina, sai Abida ta soma magana.

Dan kawai nace mata an kai kaya gidanta ko tana amfani da su kuwa.? sai kawai ta rufe ni da faɗa har tana cewa sai ta saka Umar ya ci Ubana.

Abida kiji tsoro Allah ki faɗi gaskiyar abunda ya faru, duk abunda zaki faɗa ki sani ba a nan zamu dauwama ba, wannan maganar da kika faɗa zamu tsaya ki maimaita shi a gaban Allah a ranar sakamako.

Ke karki ƙara magana a gurin nan, dama ke munafuka ce bamu sani ba. Kin shigo ne dan ki rusa mana family.? Abunda kika zo yi kenan. In ba munafunci ba miye na ɗaukar maganar da kika yi da Abida ki je ki faɗawa Umar.

Cewar babansu da ya dakatar da ni cikin tsawa, ban iya ɗaga kai na kalle su ba, na sunne kai ba tare da na kuma cewa komai ba, sai ita Abida ta miƙe tana cewa da ƙarfi.

Allah ya jiƙan Mamanmu, da ta na nan da wannan abun ba zai taɓa faru ba, daga shigowa wannan matsiyaciyar ta raba mana kai da ɗan uwana.

Abida ni ba matsiyaciya ba ce wlh.

Sai kawai Abida ta fara fusge-fusge zata zo ta duke ni Umar da matar Babansu suna riƙe ta tare da gargaɗinta akan kar ta aikata haka, sai kawai naji Jafar ya ce.

Tashi ki fita daga gidan nan kafin inci Ubanki.

Na miƙe na ɗauki jakata nace cikin ɓacin rai.

Wlh ba dai Ubana ba.

Sai nayi hanyar fita gate, sai Jafar ɗin yazo da sauri ya tunkuɗe ni na bugu da ƙofar gate, sai na fita suna zagina da matsiyaciya, nace da ƙarfi.

Ku ne matsiyata, saboda ko ba komai Ubana baya yawon haya.

Na tsaya suka cigaba da zagina ina mayar musu, mutane suka taru ana basu haƙuri da riƙe su akan zasu duke ni, musamman ma Jafar da yake hanƙoro ya cim mini, amma bai samu dama ba, sai kawai na kama hanya na wuce gida na bar Amir dan ba barshi a hannun babansu, ina cikin tafiya naji ƙafata ta riƙe sai na tsaya, can sai ga Umar tare da Amir ya biyo ni ya miƙa mini shi dan yana ta kuka, yace na jira shi yaje ya dawo, na tsaya daga gefe ya je ya ɗauko mashin yazo muka wuce gida. Ban zata Umar zai yi shuru da maganar nan ba domin kuwa ko da muka koma gida bai ce min komai ba nima ban kawo zancen ba, haka na zuba ido ina jiran ya yi maganar amma shuru har aka kwana biyu.

Rahma Kabir ce.