KOMAI YAYI FARKO...

11

by @rahmakabir13

KOMAI YAYI FARKO...

Na

©®Rahma Kabir MrsMG.

Page 11.

Sarac Stars R Pen...✍️

Bayan makonni, maganar tashinmu ya taso, dan haka Umar ya samo mota ta kwashe mini kayana tas zuwa gidan da babanmu ya bashi haya, sai gashi gadon da Abida take yi mini gorinsa an mayar musu da abun su dan hatta carpet ɗin shima an mayar saboda inda muka koma akwai tiles, sai dai da yawan kayana sun lalace musamman katakon gadona saboda gidan da muka taso yana da ruma, wasu kayan kitchen ɗin sai dai na adana su a wardrobe wasu kuma na mayar gidanmu saboda kitchen ɗina a tsakar gida yake ba yi da girma sannan babu kitchen cabinet, muka gama shirya kaya, gida yayi tsaf kafin na dafa mana abinci muka ci da ƙanwata da Usman ɗinmu, da suka gama suka wuce gida suka banni ina ƙara gyara ɗakin. Kwana biyar da dawowarmu muka ƙare hutun makaranta wanda ranar Monday zamu koma, dan haka yau juma'a Umar ya ce na shirya ya kai ni gidansu na gaishe da babansu saboda ya yi rashin lafiya a kwana biyun da ya wuce, ban yi masa musu ba tun da har zuwa yanzu bai tayar da maganar abunda ya faru na gidansu ba, shi yasa na shirya ya ɗauke ni ya kai ni ya barni a gidan, ina nan zaune a falon tun bayan dana gaisa ba babansu da kuma Hajiya, na rakuɓe kamar wata baƙuwa, babu wanda ya sake shiga sabgata sai Abida da take zuwa tana gibtani tana waƙe-waƙen habaici, ni dai ban kulata ba na yi kamar ba da ni take yi ba, daga bisani ma sai na fito tsakar gidana na zauna, ba jimawa Umar ya dawo sai na yi sallama da Hajiya muka kama hanyar gida.

Ranar Monday tun kiran sallar farko na farka dan na saka alerm a ƙaramar wayata domin ina so ya tashe ni, na saka ruwa a kettle sannan na ɗauro alwala nazo na gabatar da nafila raka'a biyu, dana idar na yi addu'a sai na miƙe, nan take kuma nepa suka ɗauke wuta dan haka dole na fita zuwa kitchen na ɗauko murhun gawayi dana siya, na haɗa gawayi, da wutar ta ruru na mayar da ruwan zafin akai, bayan ya tausa na saka a flakes sai na ƙara mayar da wani, shima da yayi zafi na sauke na ɗaura sanwar dafadukan taliyar manja wanda a lokacin an kira sallar shiga masallaci, na sake wata alwalar na koma ciki na gabatar da sallah, dana idar na fito na duba abinci naga ya kusa ƙarasawa sai na juye ruwa na je nayi wanka na fito na shirya lokacin Umar yana masallaci, na sauke a abincin na ɗaura ruwan wankan Amir, da ya yi zafi na yi masa wanka na shirya shi na zuba taliya naci, sauran na zuba a kula. Lokacin da Umar ya shigo na gabatar masa da abincin yace ba zai ci ba dan haka sai na ƙarasa shiryawa ya ɗauke ni muka wuce gidanmu na aje Amir kafin yaje ya sauke ni a makaranta, na yi zaton da ya aje ni zai tafi ne amma sai na ga ya share guri ya zauna, hakan bai dame ni ba dan na saba da halinsa.

A haka muka cigaba da rayuwa da maneji, wanda tun ban saba da tashin asubahin fari ba har nazo na saba, haka zan yi girki da wuri na karya da shi sauran da ya rage na aje a kula inna dawo makaranta shi zan ci a matsayin na dare, in kuma aka yi rashin sa'a abincin ya jiƙe ko ya soma lalacewa to haka zan kwana da yunwa sai wani safiyar inna dafa naci.

Ɓangaren Umar kuwa bai fasa in ya kawo ni makaranta ba ya zauna zaman jirana har sai an tashe mu ba, ko da kuwa tun safe ne har yamma. 'Yan ajinmu suka zo suka buɗe mana WhatsApp group, kowa ya bada number ɗinsa saboda suna da babbar waya sai ni ce ban bayar ba, ganin haka sai na bada number ɗin Umar suka saka shi a ciki, saboda shi yana da waya tun wacce ya amshe a hannuna, ko da muka je gida na sanar da shi na bada number ɗinsa an saka shi a group ɗin 'yan ajinmu saboda discussion da ake yi na karatu, yace to, dan haka in ya dawo gida wani lokacin yana bani wayar na duba group ɗin, idan an bayar da assignment ko text ko wani abu anan zan ga tattaunawarsu, daga baya ma ya daina bani sai ya zama bana sanin abun da ke faruwa a group ɗin sai idan Umar ya sanar dani.

Muna a haka sai kwatsam rashin lafiya ya taso ni a gaba na wannan zubar jinin dana yi kwanaki, sai Umar yaji tsoro yaje har gidanmu ya faɗawa iyayena akan yana so na koma gida nayi jinya, Babanmu ya amince masa ya dawo ya taya ni shiryawa muka tafi gidanmu na zauna zaman jinya. Sai ya zamana kullun safe Umar shi ne yake zuwa gidanmu ya ɗauke ni ya kai ni makaranta ya kuma zauna zaman jirana har mu tashi. To bayan kwanaki sai jini ya ɗauke saboda na yi amfani da wani magani da Mamanmu ta amso mini a Islamic chemist, to ganin jikina yayi kyau Babanmu ya ce na shirya na koma gidana, ni kuma a lokacin nace masa bazan koma ba dan na gama auren Umar, Baba ya fara yi mini faɗa yace na tashi na bashi guri, sai na miƙe na koma ɗaki ina jin ba zan koma ba saboda ɗan zaman dana yi a gida yasa naji auren Umar ya fice mini a rai, duba da babu abunda na rasa a gidanmu, amma gidansa daga yunwa zai zargi da rashin jituwa, babu soyayya kwata-kwata ko tausayi a zamanmu, dama ni na aure shi bisa biyayyar iyaye ne ba dan ina sonshi ba, kuma da farko nayi zaton in muka yi aure zan so shi duba da naga ansha yin auren ƙiyayya mace tace bata son miji amma daga baya ta dawo tana sonsa saboda irin kyautatawarsa gareta, to ni babu kyautatawar balle na ji sonsa a cikin raina, sai dai sabon halayyar da ya nuna mini shi ne yake ƙara sakawa nake jin tsanarsa a raina, shiyasa na yanke shawarar ba zan koma ba. Bayan sallar isha'i na idar da sallah ina cikin ɗakinmu naji mama ta kwala mini kira, na amsa na fito, sai na ji muryar Umar a ɗakin babanmu, ashe ya kira shi ne akan maganar dana yi masa ɗazun. Na shiga ɗakin na zauna muka gaisa, sai Babanmu ya ce masa.

Umar ina so ka sanar da ni menene yake haɗa ka da Farida.?

Baba abunda yake haɗa ni da Farida gaskiya tana mu'amala da maza a makaranta, sannan kuma a gida ma ba tada aiki sai dai tayi charting da maza.

Cewar Umar fuskarsa ɗaukar da damuwa, Babanmu ya saki salati sai ya rufe ni da faɗa ba tare da yayi bincike ba, suka haɗu shida Mamanmu suka zage ni tas, sai ruwan hawaye kawai nake fitarwa dan basu bani damar kare kai na ba. Babanmu ya ce.

Dole zaki koma ɗakin ki, domin in wannan rayuwar kike so to sai dai ki mutu a ɗakin mijinki.

Ya ƙare maganar ya sallami Umar ya tafi, sai suka ce da safe na shirya na koma gidana, nace to kafin na koma ɗaki ina share hawayena.

Washegri da wuri na shirya na wuce gidana ni kaɗai na bar Amir anan saboda bai ma cika zama a hannuna ba saboda makaranta. Haka muka cigaba da rayuwa zaman ba daɗi sai dai haƙuri nake yi tunda ban isa na kaucewa ƙaddarata ba, sannan kuma iyayena basu taɓa karɓan kokena ba shiyasa na ke jure zaman bisa umarninsu. Na cigaba da zuwa makaranta wanda a yanzu shi ne kaɗai gatana da nake da shi, kamar yadda na saba da wuri nake dafa abinci na tafi, yau ma ranar talata haka na gama dafa dafadukan taliyan manja da busasshen kifin da Mamanmu ta bani, na zuba a kula sai na jawo ƙofar kitchen ɗin da ƙarfi na rufe, da yake ba ni da kwaɗon da zan rufe saboda ba mai key a jiki bane, ina son na siya kwaɗo amma ba ni da kuɗi, Umar kuma ko na faɗa masa ba siya zai yi ba, haka na bar ƙofar tunda na saba rufe shi haka, kuma duk da ba kwaɗo ba kowa ne zai iya buɗe shi ba saboda ina datse shi da ƙarfi.

Bayan na dawo makaranta na je kitchen dan na ɗauki abinci sai na ga wayam an cinye, na kira Umar a waya na tambaye shi ko shi ne ya cinye abincin.? sai yace ba shi bane domin a wata ƙaramar kula ya ga abinci kaɗan sai yaci, na cika da mamaki dan abincin da yawa na bari a babbar kula, haka na fito kitchen ɗin ina tunani, amma ban san waye zan ɗaura zargi akansa ba, dan haka na aje maganar a gefe na ɗauki alwashin ɗaukar mataki. Sai tun daga ranar in na yi girkin safe bana aje shi a kitchen ɗin, sai na saka shi a ɗakina na rufe da key na tafi makaranta, dan na tabbatar in ba Umar ne yazo ya buɗe ya ci ba babu wanda zai samu damar cin abincin.

....

A hankali nazo na shirya da dangin Umar, duk da ba wani shiri sosai nake da su ba kadaran kadaham ne, amma duk wani abu in ya taso nasu ina zuwa. To ranar Juma'a lecture ɗin safe muke da shi dan haka wajen sha biyu muka tashi, sai Umar ya ɗauke ni ya kai ni gidansu shi kuma ya wuce Masallacin juma'a, na gaisa da mutanen gidan kamar yadda na saba, sai Abida ta fito daga ɗaki itama muka gaisa sai take ce mini.

Matar Yayanmu gaskiya kinshiga uku da rowa. Rannan naje gidanku na ga kin yi abinci kin bar shi a kitchen sai na ɗiba na ci, to shi ne tun daga ranar naga baki sake barin wani abinci a kitchen ɗin ba.

Ayya kin san kitchen ɗin babu kwaɗo shiyasa nake kwashe abincin na aje a ɗaki, saboda tsaro ba dan tsoro ba.

Na bata amsa cikin raha saboda gudun fitina, duk da rai na ya ɓaci da ta ce mini na shiga uku da rowa, wanda da ace yayansu ya wadata ni da abinci ba zan yi kafa-kafa da abinci irin haka ba. Sai bata kuma tanka ni ba ta wuce nima na ɗauki wani takarda na soma dubawa saboda ana maganar ranar monady zamu fara Test, sai dai hankali na ya koma kan mamakin ƙarfin halin Abida, ashe rannan ita ce ya zo ta cinye mini abinci. Bayan sallar juma'a sai ga Umar ya dawo sai ya ɗauke ni muka wuce gida ya sauke ni sai ya sake fitowa ni kuma na bi lafiyar gado na yi bacci.

****

A hankali rayuwa ta miƙa dan har mun wuce 100level wanda na samu maki mai kyau har 'yan ajinmu wasu mazan sai da suka yi mamaki, daya ke na mayar da hankali sosai a karatu bana wasa gaskiya, domin zuwa yanzu shi ne kaɗai gatana da nake hange nan gaba. Sai muka shiga 200level wanda a hankali na soma wayewa, duba da ina haɗuwa da mutane mabambanta halaye, sannan Jami'a gidan ban kashi kowa da irin rayuwarsa, a haka nayi Ƙawa 'yar ajinmu mai suna Rahma Muhammad 'yar unguwar Rimi ce, tun ina ƙin sake mata har na zo na saba da ita sosai, to wani lokaci muna fita zuwa gidansu Rahma mu zauna a can mu ci abinci, sai mun tabbatar da mun kusa komawa lectures sai mu fito mu hau napep mu koma makaranta, duba da ƙofofin shiga makarantar da yawa, haka zamu fita har mu dawo ba tare da Umar ya fahimta ba, domin zuwa lokacin na dai na jin tsoronsa kuma bai fasa bin diddigina ba, in ya kawo ni ya zauna gadin jirana har sai mun tashi, sai wannan halin nasa yabi jikina na daina fargaba da matsawar da yake yi mini, haka nake yin duk abunda nagadama tunda na san ba zan taɓa cin amanar aurena ba sannan ina ƙoƙarin riƙe martaba aurena tunda duk 'yan class ɗinmu sun san ina da aure, shiyasa ma mazan basa shige mini, basu ma fiye shigewa matan ajin ba sai in mace ta sake musu fuska. To yawan zuwa gidansu Rahma dana ke yi sai na saba da iyayenta sosai, dan mamanta tana da kishiya ita ce amarya kuma suma da yawa yaran gidan, akwai 'yan mata da yayyinsu maza, to ina ganin rayuwa daban-daban a gurinsu, dan duk wani style na ɗinki a jikin 'yan matan gidan nake fara gani gwanin sha'awa, ga yanayin shigarsu gwanin burgewa, suna amfani da gyale da takalma masu kyau da ɗankunne na 'yan mata, sun iya kwalliya sosai duk da bama su kuɗi bane sosai amma suna da sakewa da iyayensu wajen yin rayuwar da suka zaɓa cikin tarbiyya da sanin ya kamata. Ni kuma rayuwar nasu sai yake burgeni wani lokacin sai naji kamar na koma su, amma babu hali duba da igiyar auren Umar da ya ƙudundune ni. Dan haka sai na soma tara kuɗin motar da Babanmu yake bani, saboda duk mako yake aiko mini da kuɗin kuma gashi Umar shi yake kai ni ya dawo da ni, sai dai amfani kuɗin ina siyan abinci a makaranta naci da rana ko drinks da buns. To wani tunani ne ya faɗo mini a rai akan na fara kasuwanci musamman ga matan unguwarmu, dan layinmu manyan gidajene masu rufin asiri, dan haka gyaluluwan da aka saka mini a akwati kusan guda takwas duk suna nan a ajiye sababbi, dan bana sakawa Umar ya hana ni saboda baƙin kishinsa sai hijab.

Washegari na tafi makaranta da niyyar na je kasuwa, dan haka muna fita lecture ɗin farko sai na bi ta ƙofar baya na tafi kasuwar gari na siyo leda irin wanda ake parkeging kaya a ciki, ina gamawa na koma makaranta na shiga aji har lokacin Umar yana nan a zaune bai san na fita ba, ya manta cewar tsaron Allah shi ne tsaro bana mutum ba. To da muka koma gida ni na shiga shi kuma ya wuce, sai na sauke akwatuna na na ciro gyaluluwan na zauna na ninkesu na saka su a wannan ledan ɗaya bayan ɗaya, sai suka dawo tamkar sababbin da aka siyosu a kasuwa, na jerasu a cikin kwando da ake saka kulolin abinci, sai na fara shiga maƙota ina yi musu talla zuwa lungu da saƙon gidajen unguwarmu. Cikin sa'a wasu suka taya wasu kuma suka ɗauka akan ƙarshen wata zasu bayar da kuɗi,wasu kuma suka bayar da rabi akan nan da kwanaki zasu cika mini kuɗin, suka amsa number wayata wasu kuma nayi musu kwatancen gidana, a ranar ban dawo gida ba sai da gyale kwara biyu an siye guda shida, sannan ma mutum uku sun faɗa mini wasu kalar gyale da suke so na kawo musu. Dan haka kuɗin dake hannuna na yi amfani dasu washegari na shiga kasuwa na siyo musu na kai suka bani kuɗi na. A hankali sai kasuwar gyale ya fara ƙarfi kuma duk Umar bai sani ba, ban kuma bashi ƙofar da zai gane ba, da zuciyata na zauna nayi wannan shawarar ban faɗawa kowa ba, kuma cikin hukuncin Allah sai Allah ya saka mini albarka.

***

Kwatsam yau asabar naje makaranta da nufin ina son na fita na je kasuwa, amma ban samu hali ba har sai da aka tashe mu wajen ƙarfe uku na rana, sai na rasa yadda zan yi na fita tun da Umar yana nan ya kashe ya tsare yana jirana, haka na isa inda ya ke zaune na tsaya nace masa.

Dan Allah ina so zan je kasuwa.

Me zaki je yi a kasuwa.?

Gyale ne wata mata tace na kawo mata, shi ne zan je in siyan mata.

Bai yi mini musu ba ya ɗauke ni ya kai ni kasuwar bacci ba tare da ya tambaye ni sana'a na fara ba ko wace mata ce tace na siyo mata gyalen, haka na siya gyalen sai muka wuce gida.

Rahma Kabir ce.