KOMAI YAYI FARKO...

12

by @rahmakabir13

KOMAI YAYI FARKO...

Na

©®Rahma Kabir MrsMG.

Page 12.

Sarac Stars R Pen...✍️

Ko da muka isa gida Umar bai mini maganar gyalen dana siyo ba, nima ban kawo zancen ba ya gama abunda zai yi ya fita, ni kuma na ɗauki gyalen na kaiwa matar, sai ta ba ni kuɗina na dawo gida. A haka na cigaba da sana'ar gyale ina juya kuɗin tare da adana ribata, asusu guda na buɗe ina zubawa a ciki. Da ƙaramar sallah ta zo haka na siyawa kaina atamfa na biya kuɗin ɗinki sannan na ɗinka hijab da takalmi mai sauƙin kuɗi na siya, Amir ma na siya masa kaya kala ɗaya sannan na siya kaza guda ɗaya a gurin Mamanmu ta ƙara mini ɗaya shi ma Umar ya siya guda ɗaya, ya zama kaji uku sai na siya fulawa da kayan haɗin cin-cin na yi, zan iya cewa ban taɓa yin sallah irin wannan ba duba da na yi abun da ban taɓa yi ba, a lokacin na ƙara fahimtar sana'a rufin asiri ne, dan kuwa ba dan na fara shi ba da ina nan zaune ba abun arzikin da zan taɓuka, hakan yasa na ƙara ɗaura ɗamarar kama sana'ata domin nasan zai zame mini tsanin yayewar baƙin cikin da Umar yake ƙunsa mini. Haka na ɗiba nama da cin-cin na kai gidanmu wanda har a fuskar Mamanmu naga taji daɗin ganin wannan sauyi, duk a zatonsu Umar ne yayi cefanen saboda ban buɗe cikina na fallasa komai ba, suma gidansu Umar na kai musu nama da cin-cin kamar yawan na gidanmu, Umar kuwa baki har kunne dan yaji daɗin abunda nayi kuma har ila yau bai tambaye ni inda na samu kuɗi ba nima sai na bishi da ido. Kuma a wannan lokacin Umar ya samu koyarwa a wani boko da wata islamiyya, sannan yana koyar da lesson a gida kuma yana fita yin buga bugansa yana samun kuɗi, amma bai damu da ya siya mini abun amfanina ba sai dai abinci da yake siya ya aje, dan ya soma wadatamu da abinci shi yasa ma sana'ata tayi kwari, abu ɗaya ne zanyi shaidar Umar akai shi ne baya niman mata, dan da yana yi to samun kuɗin daya fara ba zan riƙa gani ba ko na gane yana samun kuɗin, kuma ba ni da shamaki da wayarsa sai dai in bai gadama ba ya hanani.

Sai ya zamana in biki ya taso a danginmu ina ƙoƙarin siyan anko na ɗinka, irin atamfa roba haka na biya kuɗin ɗinki ayi mini mai kyau, saboda kawai dan na samu ƙarin kaya musamman dan makarantar da nake zuwa, ya dace na samu isassun kayan sakawa, jefi-jefi kuma ina siyan takalmi masu sauƙin kuɗi na ƙara, haka nake kwaskwarimar kaya ina maneji dan fita kunyar shiga jama'a.

Ranar Alhamis naje makaranta sai ga wata 'yar ajinmu mai suna A'isha ta kawo takalma irin na sosa ɗin nan fashion, sai suka burgini na ɗauki wani mai ruwan pink akan zan bata kuɗin daga baya, tace ba matsala dan tasan business ɗin mata dole akwai bashi kuma bani kaɗai bace ma na ɗauki takalmin. Bayan mun dawo daga makaranta Amir ya ɗauki takalmin ya saka a ƙafarsa yanata yawo da shi har ya fita dasu falo ya barsu a can, yana cewa takalmi me kyau saboda yayi wayo sosai dan yana cikin shekara na uku.

Bayan sallar isha'i Umar ya dawo yayi arba da takalmin dana siya wanda Amir ya bar su a gefe, ko sallama bai yi ba amma buɗan bakin Umar sai ya ce.

Ke takalmin waye wannan.?

Sai na ce masa cikin zumuɗi takalmi na ne.

Ina kika same shi.?

Siya nayi amma ko kuɗin ban biya ba wata course mate ɗinmu ce ta kawo su shi ne na ɗauka.

To ba zaki saka takalmin nan ba, in banda zubar da kai da ɗaukar kanki ba a matar aure ba ina ke ina saka wannan takalmin, ki saka ki yima waye gayu, wa zaki burge.?

Da ya kai aya a maganarsa ban ɗaga kai na kalle shi ba balle na tanka masa, sai shima bai kuma cewa komai ba ya wuce ya zauna Cushing fuskarsa a haɗe, haka muka kwana a daren kowa rai ba daɗi. Washegari da safe na ɗauki takalmin na sa a jaka muka tafi makaranta ya sauke ni, sai na shiga aji na samu Fahima ta zo, wata matar aure ce da muke gaisuwar mutunci, duk da ita bata shiga harkar kowa duba da ita Hajiya ce mijina babban ɗan siyasa ne ɗan majalisan Dattijai na ƙasa, na zauna a kusa da ita muka gaisa sai nake ce mata.

Dan Allah Hajiya Fahima ko zaki sayi wannan takalmin.? Jiya na ɗauke shi a gurin Aisha to sai da naje gida na gwada tafiya da shi naga yayi mini tudu sosai, ni kuma kinga ina da tsayi.

OK nawa ne kuɗinsa.?

Dubu ɗaya da ɗari biyar ne.

To shi kenan ba matsala zan siya, amma ba yau zan baki kuɗin ba.

Ba matsala na gode sosai.

Na ambata cikin fara'a, tayi murmushi bata ce komai ba ta amsa takalmin, ni kuma na wuce mazauni na. Cikin ikon Allah sai gashi washegari Fahima takalmin ta saka ta zo da shi makaranta, kuma yayi mata kyau sosai dan itama fara ce, muna zaune tare da Rahma ta ƙaraso inda muke muka gaisa, ta bani kuɗin takalmin na amsa ina yi mata godiya, sai na tashi naje na bawa mai takalmi kuɗinta, daga nan magana ta ƙare.

A hankali na riƙa fahimtar mutanen ajinmu maza da matan, musamman da ya zamana suna yawan nace mini saboda ƙoƙarina tun sadda na samu highers mark a 100level, dan wani lokacin lecturer yana fita zasu taso su zo gurina dan in ƙara yi musu bayani abunda aka karanta ba, to akwai wani Usman da ya nace mini duk in ba Malami a aji to zai taso yazo nayi masa karatu gashi da yawan tambaya, haka sauran suma zasu zo su zagaye ni ina yi musu bayani, muna yin karatun wasu suka ɗan sako zolaya a ciki muna raha, ashe wannan da'irar da nake haɗawa shi ne zancen da Umar yake faɗa na ina hira da maza a makaranta, sannan ana ɗaukar masa hoto ko video ɗinmu a tura masa, sannan duk wani shige da ficena duk ya sani, ban gane ana yi mini zagon ƙasa ba sai sadda na taɓa kama Khalid class rep ɗinmu tare da Umar can bayan wani aji suna magana, sai na ɓoye dan kar su ganni, naga hira suke yi sosai har da tafa hannu wanda ya nuna sun saba sosai, na ji raina ya ɓaci sosai dan na fahimci Khalid shi ne munafukin daya ke ɗaukar maganata ya kaiwa Umar, ko da yake banga laifinsa ba domin nasan Umar shi ne zai saka shi yayi masa aiki a kaina tun da zuciyarsa ta kasa natsuwa da ni, ban san so ne ko ƙiyayya Umar yake yi mini ba, sai na wuce su na koma aji na cigaba da lamarin gabana amma abun yana cina a rai, haka na danne ban yiwa Umar maganar ba.

To kwatsam sai ga wata magana ta fito wai ina soyayya da Usman, wanda Umar ya tare ni a ɗaki yana tuhumata akan yaron dana girme masa, kuma ma da aurena me zai sa na kula wani namiji da sunan soyayya, sai kawai na ɗaura zargina akan Khalid ne ya haɗa wannan munafurcin, dan har da hotunanmu duk Umar ya nuna mini, wani muna dariya wani kuma muna karatu sai dai duk hotunan Usman yana kusa da ni kuma ba mu kaɗai bane a gurin kusan duk 'yan ajin ne muna class discussion, dan in mutum ya lura da hoton an ɗauki hoton ma bamu sani ba muna sabgogin gabanmu, sai hankalina yayi mugun tashi domin na san wani sharrin Umar zai ƙulla mini dan ya tabbatar mini zai je gidanmu, ban iya ce masa komai ba har ya fice zuwa can gidanmu.

Haka Umar ya samu Mamanmu ya nuna mata hotunan tare da yi mata bayani, ban san ya suka yi ba sai dai ni ina nan gidana zuciyata ta gama tsinkewa tare da tsoron irin hukuncin da iyayena zasu ɗauka akan maganar. Ban iya yin bacci ba dan Umar ya ɗauki lokaci kafin ya dawo, bai ce mini ba nima ban ce masa ba duk muka kwanta ina saƙar zuci, zan iya cewa wlh ban san sadda bacci ya ɗauke ni ba duba da tashin hankalin da na samu kaina a ciki.

Washegari da safe sai ga Mamanmu ta zo, wanda ganin dana yi mata sai da ya saka hantar cikina ta kaɗa, ga alamar idanunta sun yi ja duk sun kumbura wanda ya nuna taci kuka sannan bata samu bacci isasshe ba, ta tsaya ko zama bata yi ba suka gaisa da Umar, koda na gaishe ta bata amsa mini ba sai ta rufe ni da faɗa tana zagina. Mamanmu taci mini mutunci sosai a gaban Umar, ta kuma ce Babanmu idan ya dawo daga tafiya zata nuna masa iskancin da nake yi a makaranta ya gani dan ya ɗauki mataki, sannan ta ce na gama riƙe waya a rayuwata, ban iya cewa komai ba sai zubar da ruwan hawaye nake yi har ta tafi. Umar ma ya fita saboda ya gama ƙulla mini makirci.

A daren ranar Babanmu ya dawo daga tafiya, washegari da safe sai ga Babanmu da Mama sun zo gidana, suka shigo cikin ɗakinmu, ko kafin in yi magana naji Babanmu ya rufe ni da duka, ga matar gidanmu tana jin duk abunda ke faruwa, baba yayi mini dukan tsiya kamar ba zai bar ni da rai ba, Umar da Mamanmu suna tsaye suna kallonmu, ganin babu sarki sai Allah sai na ruga uwar ɗakana na ɓoye ina kuka. Babanmu ya cigaba da zagina yana kumfar baki tare da cewa.

Daga yanzu kin dai na zuwa makarantar kenan, kuma duk inda yaron nan yake zan saka a nemo shi a kama shi.

Ya gama bambamin faɗa ya fice, Mamanmu ta rufa masa baya tare da Umar. Wannan dukan da Baba yayi mini sai da nayi jinyarsa, dan da wayar wuta ya dake ni ga shashin bulala ruɗu-ruɗu jajir a jikina kasanturar ni fara ce sosai. Wannan baƙin cikin da Umar ya ƙunna mini yasa naji karatun ya fice mini a rai, ban sake marmarin zuwa makarantar ba.

Da aka kwana biyu ban je ba 'yan ajinmu duk sun damu sunata kiran Umar a wayarsa suna tambayar meyasa bana zuwa.? Sai ce musu yayi nayi tafiya ne shi yasa ban zo ba, wanda in da ya faɗi ba ni da lafiya ne dole sai an samu waɗanda zasu bincika gidana su zo dubiya, sannan Malamanmu ma sun damu da rashin zuwana suma sun tuntuɓi Umar, wanda amsa ɗaya ya basu cewar na yi tafiya, kuma duk basu da numbern wayata sai Rahma ce kaɗai ke da shi sannan na kashe wayata shi yasa suke kiran Umar, kuma komai na makaranta hatta yin registration da number Umar nake amfani wajen da aka buƙaci na saka, amma duk da hakan Umar ya kasa yarda dani ko ya samu natsuwar ruhi akan ba zan ci amanar aurensa ba.

Bayan mako guda, zamanmu ya koma zaman doya da manja dan ko kaɗan bana son ganin fuskar Umar, na tsane shi irin tsanar da baya misaltuwa, kallon maƙiyina nake yi masa wanda ba ya ƙaunata face son ganin bayana, shi yasa ko magana bana iya yi masa babu abunda ke haɗani da shi daga ido sai ido. Ɓangaren Mamanmu kuwa washegarin da Baba ya zo ya dake ni, ta tattara kayan yarona Amir ta bawa ƙanwata ta kawo shi tare da saƙon wai ga tsiyata nan kar in ƙara doso inda take, dan ko yarona ma bata son ganinsa.

....

Yau Asabar muna cikin sati na biyu da faruwar abun nan, sai na tashi da kwalimar kitchen ɗina, na tsuguna Ina yin wanke-wanke sai ga ƙanwata Sakina ta shigo da sallama, na amsa fuska sake, ta ƙaraso ta zo ta zauna bakin rijiya muka gaisa, sai take ce mini.

Ashe baki je makaranta ba.?

Sakina ai ni na haƙura da zuwa makarantar akan dai wannan cin mutuncin da ake yi mini akansa. Tun da haka Umar yake so, yaje yayi mini sharri a gurinsu to ni na haƙura da karatun.

Hmmm nima gidan Inna Maryam zani na biyo ta nan, ba a san ma nazo ba, dan in mama ta sani zata yi mini faɗa.

Karki damu, ki tafi kawai sai anjima.

Tace mini to sai ta miƙe ta wuce. Ashe Sakina da ta koma gida sai ta kwashe duk maganar da muka yi ta faɗawa Mamanmu, Allah yasa ban faɗi mai zafi akansu ba, sai ga Mamanmu ta kirani ta fara faɗa, akan me zance na haƙura da karatun.? memakon na zo na bawa Babanmu haƙuri ya yafe mini na koma amma zance haka, na share hawayen daya gangaro mini a kuncina nace.

Mamanmu saboda Umar ya ɓata mini suna shiyasa na haƙura da karatun, saboda ko da naje makarantar za a riƙa kallona da haka, dan Rahma ta tabbatar mini da tana ganin Umar yana zuwa makarantarmu duk da na dai na zuwa, shekaran jiya ta kira ni a waya take faɗa mini. To kinga Allah kaɗai ya san me yake faɗawa mutane.

Na ƙare maganar cikin rauni, Mamanmu ta sauke numfashi.

To ki shirya ki zo zan baki kuɗin mota ki tafi makarantar, ni zan san me zan faɗawa babanku.

Nace mata to sai ta kashe wayar, ban yi mamakin Mamanmu ba domin na san ta ɗaura buri akan karatuna saboda tana ganin zan zama wani abu nan gaba, domin nice babba kuma wacce ta fara karatu a jami'a, saboda ƙanwata ita bata samu admission ba duk da tare muka zana waec exam, shiyasa take goyan bayan na koma makarantar saboda tana son nayi karatun duk da abunda ya faru. Ina gama waya da ita naga ƙarfe goma ne da wani abu na safe, sai kawai na fita na rufe kitchen ɗina ba tare da na kife wanke-wanken dana yi ba na dawo na shirya cikin sauri, na ɗauko Amir da yake bacci na goya shi sai na saka hijab na ɗauki jakar makaranta na fito, na rufe ɗaki sai na tafi gidanmu, Mamanmu ta bani kuɗin mota na wuce cikin sauri na samu abun hawa na tafi makaranta dan nasan muna da lecture ƙarfe sha ɗaya na safe duk ranar Asabar.

Zuwa yamma na dawo makaranta na tadda Umar a gida, yana ganina ya miƙe ya fara tambayata ina naje.?

Daga makaranta nake, Mamanmu tace na shirya na tafi.

Amma ai Babanmu yace kin bar zuwa makarantar a haƙura da karatun, yanzu kuma akan wani dalili ne za a ce ki cigaba da zuwa.?

Hmmm, da farko dama bani na saka kaina a makarantar ba, Babanmu shi ne ya goya mini bayan karatun da kuma amincewar ka, sannan na biyu ba ni ce nace na daina zuwa ba su ne suka ce na daina zuwa, yanzu kuma sun dawo sun ce na koma, kaga ni bani da iko da kaina sai abunda kuka yanke, dan haka sai ka je ka same su.

Yayi kwafa bai sake magana ba ya fice a gidan. Ashe da ya fita gidanmu ya je ya samu Mamanmu da maganar, saboda Babanmu baya nan, Umar yayi mata ƙorafin na koma makaranta, Mamanmu ta wanke shi tas tayi masa kaca-kaca, haka ya fito daga gidan guiwa sake, wanda a lokacin ƙanwata ta kira ni a waya take faɗa mini, dariya kawai nayi na kashe wayar ina cewa a fili.

Ai dama mugun abu ɗan aike ne yadda ka tura shi wata rana sai ya waiwaye ka, a juri zuwa rafi In Sha Allah Umar ba zaka taɓa ganin bayana ba.

Na ƙare maganar da murmushi a fuskanta, dan na tabbatar Mamanmu ta gama da matsalar tun da ta ɗaura buri akan karatuna.

Hmmmm makashinki yana tare da ke Farida. Labarinki akwai taɓa zuciya. Ni kaina ina son sanin anya komai yayi farko zai yi ƙarshe kuwa.?.

Rahma Kabir ce.