KOMAI YAYI FARKO...

13

by @rahmakabir13

KOMAI YAYI FARKO...

Na

©®Rahma Kabir MrsMG.

Page 13.

Sarac Stars R Pen...✍️

Ko da Umar ya dawo bai sake yi mini maganar ba sai ya yi shiru nima na bishi da ido. Ranar monady da safe sai ga Usman ɗinmu da kuɗin motar makaranta ya kawo mini, na amsa cikin farin ciki dan na tabbatar tunda Babanmu ya aiko da kuɗin to ya sauko, Allah kaɗai ya san me Mamanmu tace masa ya yarda na cigaba da zuwa makaranta, na ƙarasa shirya Amir na bawa Usman nace ya wuce da shi gida in mun taso zan biyo na ɗauke shi, sai ya ke ce mini ai Mamanmu tace ma na haɗo masa kayansa ya kwana biyu a gunsu, ba karamin murna nayi ba dan hakan ya tabbatar mini iyayena sun daina fushi da ni, na haɗa masa kaya na bashi ya wuce da Amir yana ɗaga mini hannu yana cewa bye bye Mami, na ce masa bye Amir ɗin Mami, suka wuce sai na koma na ƙarasa shirina na sami Umar a falo yayi ɗai-ɗai akan Cushing, daya ganni Sai ya tashi ya Zauna tare da miƙa mini hannunsa, na kalle shi fuska a ɗan haɗe dan na fahimci me yake nufi, ganin nayi banza da shi ya ce a ƙufule.

Ki bani kuɗin motar da baba ya aiko miki da shi na saka mai a mashin.

Hmmm kawai na ce masa na zare ɗari biyar a ciki na bashi, ya miƙe yana mayar da rigarsa ya fita sai na bishi da harara, ba yau bane ya saba yi mini haka, a tun baya idan zai kaini makaranta haka yake fakewa da bashi da kuɗi har sai na ɗauka daga cikin kuɗin motar da Babanmu ya aiko mini dasu na bashi ya zuba mai a mashin kafin ya kaini makaranta, ada ban ɗauki hakan komai ba amma a yanzu na fahimci tsabar mugunta ce na ƙiyayyar da yake yi wa karatu na, ba zai jure kashe kuɗinsa akan kai ni makaranta ba, dan haka ya dace na ɗauki mataki akan haka na nuna masa zan iya yiwa kaina komai akan karatuna ba tare da sa hannunsa ba, haka muka je makaranta ya sauke ni na wuce cikin ajinmu na samu guri na zauna, sai ga Fahima Ango ta shigo ajin, ta ƙaraso gurina muka gaisa kafin tace.

Yau fa ina tare da ke dan wlh ban samu nayin karatun test ɗin da malam Hadi zai yi ba, jiya Honourable ya dawo gari na tsaya kulawa da shi.

Ayya ba damuwa.

Nace mata sai ta yi mini godiya muka cigaba da hira, can sai ga Rahma ta zo muka haɗu muka fara bitar littafin da za a yi test ɗinsa.

Lokacin tashi makaranta yayi Umar ya ɗauke ni muka wuce gida. Na samu na gama girkin da zanyi na zauna ina bitar karatun mu na yau dan mun fara test an kusa exam. Bayan sallar Isha'i sai ga Umar ya shigo da Leda, ban bi ta kansa ba tun bayan dana ce masa sannu da zuwa na miƙe na shige uwar ɗaka ina bitar karatu, sai ya kwala mini kira, kamar bazan amsa ba amma na amsa ciki-ciki na fito na tsaya.

Ki ƙaraso, magana zamu yi.

OK na ce na samu yana cin tsire, har ga Allah sai da na haɗiye miyau amma kuma sai na fuska nayi kamar ban gani ba, buɗar bakinsa sai cewa yayi.

Farida idan har kina so ki cigaba da karatunki to dole sai kin rabu da Rahma 'yar ajinku, dan na samu labari itace take hure miki kunne kike abinda kika ga dama a ajinku, kin mayar da kanka kamar ba matar aure ba, sannan itace ke janki yawo ku fita daga makaranta shi yasa na fara tunanin a ina kike samun kuɗin da kike cin abinci a makarantar, ina da labarin komai, to gwara ita budurwa ce ke kuma matar aure, dan haka na datse alaƙarku da ita, idan kuma ban isa ba, to kin san abunda zan yi akai.

Allah ya kyauta na ambata rai na yana tuƙuƙin baƙin ciki, na miƙe ba tare da na jira me zai cigaba da cewa ba na koma uwar ɗaka, ina jinsa ya ja tsaki ya cigaba da cin tsirensa ba tare da yayi mini tayi ba, ko da yake ma koda ya ce naci bazan iya ci ba dan ina jin haushinsa sosai.

Washegari kamar kullun na gama shiri yace na bashi kuɗin da zai saka mai, sai na shafawa idona toka nace ban da shi, sai yace ba zai kaini makaranta ba naja guntun tsaki nace yafi nono fari, dan ya kamata na nuna masa nima da zuciya a ƙirjina kuma na fara sanin ciwon kai na, na ɗauki jakata na fice daga gidan na je na samu napep na hau na wuce makaranta, ashe bayan fitowa ta Umar ya biyo bayana da mashin, sai da na isa makaranta na sauka na sallama mai napep, juyawar da zanyi sai na hango Umar, naji gabana ya faɗi amma na dake nayi kamar ban ganshi ba, na juya zan shiga makaranta Rahma ta kwala mini kira na tsaya na jiranta ta ƙaraso muka shiga tare, to wannan ganin da Umar yayi mini da Rahma sai ya ɗauka da zafi cewar naƙi jin maganar sa. Dana koma gida ya tasani a gaba da masifa akan dole na rabu da Rahma dan ya ji labarin ba tada kamun kai, idan kuma naƙi zai je har makarantar ya saka a ja mana layi kuma zai samu Babanmu da maganar, ya kafa mini ƙafar zuka har sai da na saduda na haƙura da mu'amala da Rahma, na janye jiki da ita bayan nayi mata guntun bayanin da zata fahimce ni, sai muka koma mutunci muna gaisawa kawai, a wannan lokacin sai na koma ina zama kusa da Fahima tun da ita matar aure ce, bazan samu matsala da Umar ba koda ya samu labari, sannan na dai na class discussion ya zamana bana sakewa sam a cikin aji, da zarar lecturer ya fita zan fito nima na zauna a kofar aji ko kuma naje wajen abinci na siya abunda zan iya ci, to a haka ne Fahima ta shigo rayuwata sosai dan duk in zan fito sai ta biyo ni mu je duk inda zani tare da ita, wani lokacin ma ita ce take siya mini abinci ta biya, sai nayi mata godiya dan na saba da halinta, mace ce mai kyauta dan tasha siyan wa 'yan ajinmu handouts mu duka ta biya kuɗin, saboda mijina babbane suna da kuɗi dan da motar kanta take zuwa makarantar. To Fahima tunda ta samu damar kusanci da ni sai take jin daɗi domin tana mugun ƙaruwa dani tunda ita gaskiya ba tada wani ƙoƙari, ba wani gane karatun take yi ba, sai dai akwai ta da gayu da kwalliya ga shigar kece raini tunda dama matar manya ce, sai dai ba tada girman kai tana son zama cikinmu shiyasa muka shuƙu sosai fiye da yadda na saba da Rahma a baya, dan yanzu kullun in mun zo makaranta ita ce take rage mana hanya in zamu koma gida ta sauke kowanne a junction ɗin unguwarsu, saboda na nunawa Umar na waye bai isa ya juya ni kamar da ba, dan na dai na bashi kuɗin mota balle ya ɗaukeni ya kaini makaranta, na riga na yiwa kaina alƙawarin in har sai na bashi kuɗin motar da baba yake bani kafin zai kai ni, to wlh sai dai ya dai na kaini makarantar, kuma a hankali sai ga shi hakan ya tabbata sai dai nasan ya ƙara tsaurara matakan tsaro a kaina, amma hakan bai dame ni ba domin a wannan lokacin Allah shi kaɗai nake tsoro ba wani abun halitta ba.

Sai ya zama duk in muka zana test Fahima taga ta ci sosai sai ta dinga yi mini godiya tana jin daɗi, dan haka sai ta ja ni wajen abinci ta siya mini abinci mai kyau mu ci mu koma class. Daga haka kuma sai ta amsa number ɗin mijina tana kiransa akan in muna da lectures ta faɗa masa ya gaya min saboda ni bana sanin abubuwa, duba da bani da babbar waya, kuma Umar ya fita daga group ɗin ajinmu a wayarsa, shiyasa bani da labarin komai sai dai wani lokacin haka nake kashe kuɗin mota naje makaranta na samu an seko lecture ɗin ranar sai washegari ko kuma sai zuwa rana, dan haka kiran da Fahima take yi wa Umar ta faɗa masa sai ya samar mini da sauƙi, ita kuma sai ta samu damar da zata ƙara jana a jiki, watarana bamu da lecture da wuri amma zata ce masa na fito, tana gaya masa ne domin tasan shi ne shugaba dole sai da izininsa zan fito, ni kuma daya faɗa mini zan shirya, sai na kama hanya zata sanar da ni a ƙaramar wayata cewar na ƙaraso gidanta ba mu da lecture da wuri, haka zan je gidanta a Kinkinau ta haɗa mini sha tara na arziki mu zauna musha hira, dan gaskiya Fahima tana da mugun kirki da kuma son mutane. Sai hakan ya jawo mugun shaƙuwa a tsakaninmu dan duk wani abu da zai taso a ajinmu na maganar kuɗi to Fahima ita ce take biya mini.

Yau Juma'a tunda muka fito lecture Fahimta take faɗa mini mijina ya shigo gari ya dawo daga Jos, ya kawo tsarabar doya da irish har da naman talo-talo, dan haka in mun tashi zan bita na amsa nawa tsarabar, sai na ce mata to tare da yi mata godiya. Da muka tashi muka shiga motarta tare da wasu 'yan ajinmu su biyu mata ta rage musu hanya suka sauka akan babban titi, mu kuma muka wuce gidanta ta haɗa mini Irish, doya da kuma naman nan duk ta ɗibar mini kuma da yawa, ta kuma bani kuɗin mota, na amsa ina godiya na fito na hau napep na wuce gida. Bayan sallar la'asar sai ga Umar ya shigo ya ga kaya daga kefe dan bana aje su a kitchen saboda ba ɗan makulli, ya kalle ni ya ƙara kallon kayan yace.

Ina kika samo wannan kuma.?

Fahima Ango ce ta bani tsaraba, mijinta ya dawo daga tafiya.

Kwafa ya yi tare da girgiza kai ya wuce cikin uwar ɗaka, hmmm na fahimci Umar duk wanda zai taimake ni ne baya so, saboda yana ganin wannan taikamon kamar hure mini kunne ne suke yi, ko kuma yana ƙara buɗe mini ido ne ban gane masa ba, amma kuma abun takaici idan na gyara abunda ta bani da shi muke cinyewa bayan ya nuna a zahiri baya so.

Haka tafiya ta miƙa har muka zo muka fara exam, a ranar Alhamis muna aji muna zana jarabawa, sai Fahima tayi exchanging paper da wani ɗan ajinmu, wata lecturer ta kama su, to da yake ba malamanmu bane suke duba mu, wasu ake kawowa daga wani department ɗin, dan haka sai maganar tayi tsawo akan lecturer ɗin sun dage sai sun cika malpractice form, su kuma sun ƙi cikewa saboda ba su yarda da abunda ake zarginsu akai ba, sai hakan ya kawo delaying wajen rubuta exam ɗinmu, dukanmu 'yan aji muka saka baki muna ta basu haƙuri akan a yafe musu, hakan yasa duk sauran classes ɗin sun gama rubuta paper ɗinsu mu bamu gama ba, a wannan runtsun sai class rep ɗin mu ya yi sauri ya kai paper ɗinsa ya gama rubutawa sai ya sulale ya fita waje ya kira mijina a waya, jikinsa yana rawa ya sanar da shi ai an kama team ɗinmu muna malpractice, kuma yasan bani aka kama ba amma tsabar sharri yayi mini wannan ƙulli, da yake a ranar Umar ne ya kawo ni makaranta yana waje yana jiran na fito mu wuce gida, ai Umar daga jin haka ya buga mashin ɗinsa ya fice daga makarantar bai zame ko ina ba sai gidanmu. Haka yaje ya faɗawa iyayena wai akwai wata Fahima Ango 'yar lesbian ce kuma tana bin maza yanzu ita nake tare da ita, ga shi daga ƙarshe munyi satar amsa an kore ni a makaranta, da ya gama ɗagawa iyaye hankali sai ya yi sallama dasu ya sake fita ya buga mashin ya nufi gidansu, ya sanar da iyayensa wannan labarin, tare da ƙarin zancen yana zargin nima ina yin lesbians, Allah kaɗai ya san me iyayena suka faɗa suma iyayansa suka faɗa a kaina. Ni dai nasan bayan mun fito paper nayi ta kiransa a waya yaƙi ɗauka, to da yake ina da canji a Jakata sai nayi amfani da shi na wuce gida, kasantuwar su Fahima an wuce dasu wani malpractice community ban tsaya ba na wuce kawai ina binsu da addu'a Allah ya fidda su. Lokacin da muka kawo kwanar da zai sada mu da anguwarmu sai na hango Umar ya ɓullo daga hanyar gidansu, sai na saka mai mashin ya sauke ni a gurin, ya tsaya na sauka na sallame shi ya wuce, Umar ya ƙaraso ya tsaya ina cewa.

Ina ta kiranka amma baka ɗaga ba.

Eh ki hau mu wuce gidanku kawai.

Lafiya me ya faru kuma.?

Na tambaye shi cikin damuwa, sai yace na hau mu wuce kar na ɓata masa lokaci, sai na hau muka isa gidanmu na sauka muka shiga a tare, muka isa ɗakin babanmu dana ke jin hirarsu da mama, muna shiga suka rufe ni da faɗa tare da zagi kala-kala, dan naci zagin da bazan iya faɗarsa ba, Mamanmu tace.

Ai kin zama 'yar iska yanzu, abunda matan bariki ke yi shi ne kema kike yi.

Wlh Mamanmu bada ni aka samu matsalar ba, bama wajen zamanmu ɗaya ba, su Fahima ne aka kama da malpractice amsa babu ni a ciki.

Na basu amsa cikin rashin sanin me nayi da za a rufe ni da faɗa, dan na gaza fahimtar in da suka dosa, sai dai na gane Umar yazo ya faɗa musu an kore ni a makaranta nayi satar amsa, amma duk bayanin dana yi musu basu yarda ba sai Babanmu yace cikin haɗe fuska.

Wlh Farida idan kina sona to ki so mijinki, in Kuma kina ɓata wa Umar rai to babu ni babu ke har abada, kuma duk in da nake kar ki ƙara zuwa. Kai kuma idan kuka koma gida tayi maka wani iskanci ka kirani ka faɗa mini zan zo har gidan naci ubanta.

Umar yace masa to daga haka muka fito ya kama gabansa ni kuma na gangara gida a ƙafa zuciya ta a cunkushe kamar zata faso ƙirjina ta faɗo tsabar tashin hankalin da nake ciki. A ranar Umar bai dawo ba sai wajen ƙarfe sha ɗaya na dare, buɗar bakinsa yace mini.

Farida ki shirya ki bar mini gidana yanzun nan dan bazan zauna da ke ba, saboda kina bin ƙaruwa kuma 'yar lasbians, dan nasha ganin Fahima Ango da Tatue a jikin ta.

Wlh ba Tatue bane jar lalle ne ake yi mata, saboda lokaci zuwa lokaci yake gogewa ta sake yi kuma zanen fulawa ne.

Ƙarya kike yi, kawai ki shirya ki bar mini gidana.

A lokacin yasan ba zan iya dosan gidanmu ba, duba da irin abunda Babanmu ya faɗa ɗazun, sai kawai na shirya na wuce gidansu Umar a cikin daren.

Gaskiya a labari ban taɓa cin karo da tsinannen namiji irin Umar ba. Yau na ƙara tabbatar da Labarin nan karatu ne da mata za su gane cewar zaman aure akwai tarin ƙalubale a ciki, sai dai ko wacce mace da irin nata. Dole 'yan mata ku aje hasashen mijin novel ku kama hanyar gaskiya, domin wlh babu irin mazan da wasu writer ɗin suke rubutawa a wannan duniyar namu, sai dai akwai na kwarai masu hali nagari da suke kyautata wa matansu, amma ba wanda zai ɗauke ki ya yi miki wanka ba ya baki abinci a baki ba a tafi wata ƙasar honeymoon, bance ba a yi ba amma da kamar wuya gurguwa da auren nesa. Sai mu dage da addu'a akan zaɓin Allah da niman nagari, Allah yasa mu dace.

Rahma Kabir...