14
KOMAI YAYI FARKO...
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Page 14.
Sarac Stars R Pen...✍️
Ko da na isa gidansu Umar na samu sun kwanta saboda ranar an yi ruwa sosai gari yayi sanyi, haka na tura ƙofar gate na shiga na yi sa'a a buɗe yake sai na wuce falonsu na shiga da sallama a bakina, na tadda Babansu yana zaune a falon yana kallon TV, yace mini.
Farida ke ce da daddare nan.?
Nace masa eh, sai na ƙarasa ciki na zauna a kan center carpet muka gaisa, sai na ce masa.
Baban Amir ne ya kore ni.
Eh dama ko be koreki ba ni ina da niyyar nasa a kira ki, saboda wannan yarinya da kike tare da ita ba 'yar arziki bace ki rabu da ita, bana son in ƙara jin labarin an ganki da ita in har kina son ki ceci aurenki, saboda duk wanda ya ganku a tare za ace abunda take aikatawa kema shi kike yi.
Sai na ce masa to kaina a sunkuye da tunanin nan ma Umar yazo ya ɓata ni a gurinsu, sai baban ya kira Jafar ƙanin Umar a waya, da ya zo sai yace masa yaje gidana ya kira Umar su zo tare, yace masa to sai ya fita. Bayan wasu mintuna sai gasu sun shigo falon da sallama duk suka zauna a Cushing, Babansu ya kalli Umar ya ce.
Daga yau karka ƙara gangancin korarta cikin dare, saboda duk wani abun da ya same ta kai za a ɗaurawa laifin, ba za a yi la'akari da laifin da tayi maka ba, duk abunda zaka yi mata sai ka bari sai da safe ido yana ganin ido. Dan haka ku tashi ku koma gida kar na ƙara jin irin haka.
Umar yace to ni kuma na miƙe jiki ba kwari na fita, dan gaskiya nayi mamakin Babansu yadda ya nuna ƙarara nashi yake so, wato shi ba ta korata da Umar yayi yake ba, sai ta kar wani abu ya sameni na shafa masa kashin kaji, a lokacin na tabbatar da na faɗo gidan ƙananan mutane waɗanda kansu kawai suka sani.
Bayan mun shiga gida ina ƙoƙarin cire hijab ɗina sai naji Umar ya fincikoni ya saka mini ƙarfi ya kusanci ni, wanda zance fyaɗe yayi mini ta ƙarfin tsiya tunda ba da son raina yayi hakan ba, kuma cike da ƙasƙanci da mugunta, nayi kuka har na gode Allah na tsinewa Umar na yi masa mugun addu'a akan zaluncin da yake yi mini, har sai da hawayena suka ƙafe na koma kukan zucci, sai bacci ɓarawo ne ya sace ni. Zuwa asubahi na tashi da rashin kwarin jiki da zazzaɓi mai zafi, a daddafe nayi wanka na gasa jikina kafin na fito na gabatar da Sallah, dana idar na shiga ayyukan gida dana saba, ko kayarwa ban tsaya nayi ba na shirya na tafi makaranta. A haka na gama zana jarabawar wannan semester ɗin jiki babu daɗi. Ɓangaren su Fahima kuwa an soke duka jarabawar da suka yi na wannan zangon da sunan sai sun maimaita wannan shekarar, sanadin rabuwata da Fahima kenan, saboda bayan mun koma makaranta mun wuce 300level, ita kuma da wannan yaron da ake zarginsu da malpractice zasu maimaita 200level, sai Allah ya kawo mana hanyar rabuwa cikin sauƙi ba tare da wata damuwa ba. Sai dai a wannan lokacin damuwar da nake ciki yafi matsalar da Umar ya kunna mini na sharri da ya yi mini da Fahima, dan tun fyaɗen da yayi mini ban sake ganin al'adata ba sai zancen ciki ya ɓullo, kuma shima mai baƙin wahalar laulayi, yawan amai da kuma rashin cin abinci, a lokacin Amir yana da shekara huɗu a duniya, aurenmu kuma ya cika shekara biyar, sannan a lokacin Umar ya samu aiki a wani College dake Zari'a, idan ya tafi tun ranar Lahadi da yamma ba zai dawo ba sai ranar Juma'a da yamma, to shinkafa lokaci ɗaya yake siya da taliya guda ɗaya, sai ya bani ɗari biyu ko ɗari uku shi ne kuɗin cefane da siyan gawayi har ya dawo, sannan wannan abincin zan janjana muna ci har tsawon wannan kwanakin, wanda yasan ba isarmu zai yi ba ga ni ga Amir ka ciki duk da ba wani abinci nake ci sosai ba, kuma a ciki zan dafa ranar da ya dawo mu ci da shi, dana yi masa ƙorafi, sai cewa yayi ina yin almubazzaranci da abincin, amma in ba haka ba ya san abunda yake ba mu yana isarmu, daga haka ban ƙara magana ba sai nake ɗauka cikin kuɗin dana ke sana'a ina siyan wasu abubuwan na ƙara, saboda zuwa yanzu ya san ina siyar da gyaluluwa, amma da yake ya san ina amfani da kuɗin a gidansa sai bai nima ba'asin ina na samu jari ba, ni kuma ganin inna biyewa lamarin gidan to fa zan ƙarar da ribata ne da uwar kuɗin, dan haka sai na buɗe account a GT bank na fara saving kuɗi dubu ɗaya, ɗari biyar duk in na samu, kuma cikin ikon Allah a haka na tara kuɗi, wanda lokacin bikin ƙaninsa Jafar na ɗauki kuɗin na ɗinka wata atamfa roba, dan ko anko bai yi mini ba nima naƙi ɗinka nasu saboda ba su saka ni cikin bikin ba, sun mayar da ni saniyar ware kamar wata mujiya, sai dai na shiga cikin 'yan uwansu na ƙauye muyi hira, suma dan basu da masaniyar takun saƙar dake tsakanin da 'yan gidan ne, haka aka yi biki aka gama ango ya samu gida anan Arean gidansu amarya ta tare.
Ni kuma na cigaba da zuwa makaranta tare da kula da cikin jikina, sai dai har lokacin ina yawan amai ga babu abinci kamar baya. Akwai ƙanin Umar mai suna Khalifa, shi ne ƙaninsa na biyu dan Jafar shi ke bin Umar, to gaskiya Khalifa yana da kirki sosai duk cikin ƙannansa shi ne mai kirki, ba ruwansa da shiga cikin gulmace gulmacen da ake ƙullawa, dan baya saka baki, sannan tamu ta zo ɗaya saboda yana matuƙar tausaya mini halin da nake ciki, ya sha siyawa Amir kaya da sallah English wears, ko yace naje na zaɓar masa a wani shagon abokinsa dake nan cikin kasuwar bacci, haka zan je na zaɓar wa Amir kaya masu kyau har da takalmi kuma duk khalifan ne zai biya kuɗin. To yau na tashi jikin babu daɗi sai amai nake yi ko ruwa masha sai ya dawo mini, ko kuma ina jin yunwa sai amai ya taso mini, sai ga Khalifa ya shigo gidan da sallama na amsa, ya ƙaraso yana kallona.
Sannu Anty Farida ya jikin,
Da sauƙi Alhamdulillahi.
Allah ya ƙara sauki, ɗazun nake jin labari wai ba kida lafiya. Shi ne na zo duba ki, yanzu me kike so kici na siyo miki.?
Ka siyo mini Coke ko Indomie sune nake so, dan in naci su bana amai.
Yace to sai ya fita da kanshi ya siyo mini Indomie da ɗan yawa, sannan ya haɗo da coke ɗin ya kawo mini, na amsa nayi masa godiya sai ya tafi ni kuma na dafa Indomie ɗin fara ƙal ko magginsa ban saka ba, haka naci shi tsurar taliyar na kora da coke, to Alhamdulillahi na samu ya zauna ban yi aman ba, dan dama muddun na samu abunda rai na ke so to bana amai, na dinga yiwa Khalifa addu'ar alkairi, dan wlh ba ƙaramin ganin girmansa nake yi ba, saboda yana sona tsakani da Allah dan ya fiye mini 'yan uwansu gabaɗaya.
Haka na cigaba da goyon ciki yana ta tsufa, kuma a haka nake lallaɓawa naje makaranta, sannan shi ma Amir an saka shi yana zuwa wata makaranta private ta yaku bayi bai matsakaici kuɗi, Sai islamiyya kuma irin ta allo da aka zamanantar da shi, tunda suna saka uniform sai dai karatun ne sai haƙuri saboda yawan yaran tunda makaranta ce mai sauƙi, da yawan 'ya'yan talakawan arean nan suke zuwa, ban damu ba domin shi ilimi kogi ne wata rana zai tsinci abunda zai amfane shi, sannan ina da burin in Allah ya buɗa mini da kaina zan sauya masa makaranta, domin na san ilimi shi ne gishiri zaman duniya, kamar yadda mahaifina ya dage mini da karatu to suma yarana zanyi wannan jajircewar su samu ilimi mai inganci.
Cikina ya kai wata takwas amma ban taɓa zuwa awo ba, sannan ma babu wani kaya da muka siya dan zuwan baby, sai kayan Amir ne dana adana su na wanke su, sannan a lokacin mamanmu tana goyon Maimuna wacce bata wuce wata shida ba, dan haka sai ta tsinto mini wasu kayan da basu yi amfani dasu ba, sabbi na jarirai wanda mace dana miji za a iya yi musu amfani dasu, ta bani na adana, sai kuma wani zuwa da Umar yayi ya bani dubu biyu akan naje na tsinto kayan gwanjo na baby, ban yi ƙasa a guiwa ba naje kasuwar bacci na tsinto over roll da baby suit na adana su, saboda a lokacin kayan gwanjo suna da sauƙi shi yasa na samo kaya da ɗan dama na wanke na goge na aje so, to wannan kayan da na siyo na dubu biyu sune kaɗai kayan da Umar na san ya bani kuɗi na siya.
....
Lokacin haihuwa ya gabato ina lissafe da shi duk da ba zuwa awo nake yi ba, ranar Lahadi cikin dare na fara naƙuda gashi ana ta ruwan sama dan muna cikin damuwa ne, haka na dinga naƙuda cikin azaba da wahala, idan bacci ya bige ni can kuma ciwon mara ya mintsile ni na farka, haka dai na dinga ja har gari ya waye, to a haka a daddafe nayi ayyukan da zanyi dan nasan motsa jikin zai taimaka mini, bayan na gama ina mayar da numfashi na fito na yiwa matar gidanmu magana ta tsammani ruwan zafi, ta amsa kofin ta zubo mini sai na koma na jiƙa Lipton da sugar na fara sha, bayan wasu mintuna sai naji kamar wani abu yana son fitowa daga ƙasa na, sai na duka na fara nishi ina kwalawa matar gidanmu kira, gashi itama yarinya ce dan haihuwarta guda ɗaya nima kuma haka balle ta taimaka mini na haihu, da ta zo na roƙeta ta bani wayarta na kira Umar dan ni babu kuɗi a nawa wayar, ta ɗauko na saka number ɗinsa na kira, daya ɗauka na sanar da shi ina naƙuda zan haihu, yace to gashi nan zuwa. Ba a jima ba yazo muka tafi wani primary health care da aka buɗe sabo anan unguwarmu, da kyar nurses ɗin suka amshe ni suna ta faɗa akan meyasa bana zuwa awo, daga ni har shi mun kasa magana, wata nurse tace ina kayan haihuwa.? sai Umar ya koma gida ya ɗauko kayan dana haɗa a kit, zannuwa ne biyu da over roll tare da body suit sai ya siya pampers guda biyu ya kawo kayan. Zuwa wani lokaci na haihu 'ya mace Allah ya sauke ni lafiya, ba jimawa suka sallame ni na dawo gida Umar ya biya kuɗin asibiti. Haka muka dawo ba gawayi ba itacen wanka, sannan ma babu abinci, mutane suna ta shigowa barka ina zaune a gado sai hamma nake bugawa dan ban ci komai ba tun wannan ruwan lipton ɗin dana sha, sai zuwa dare ne matar gidanmu tayi tuwo ta bani naci, da aka kawo wuta muka saka ruwa a kettle matar Babansu ta yiwa yarinya wanka ta tafi, ni kuma na tara ruwan zafin in ya tausa na juye, har ya kai yadda nake so, sai na shiga nayi wankan towel na gasa jikina, sannan nayi tsarki da ruwan ɗumi na zauna a ciki kafin naji daɗin jikina na samu bacci. Washe gari haka 'yan barka suka dinga zuwa daga ɓangarensa zuwa nawa, sannan fa babu batun wanka sai in an kawo wuta shiyasa da asubahi nake tashi nake tara ruwan wanka na yiwa baby nima nayi, ranar da ko babu wuta haka zamu yini da tsatstsamar jiki, tunda nayi maganar ice ko gawayi yace bayi da kuɗi, abinci ma ƙarma ƙarma muƙe yi.
A ranar da muka kai kwana huɗu da haihuwa cikin dare Umar ya dawo, ya same ni a uwar ɗaka kwance a gado sai ya zauna a gefen gadon, sai yake tambayata.
Farida batun suna, 'yan uwana sun tambaye ni wani suna zan saka wa yarinya.
To kai me kace.?
Nace musu ban yanke shawara ba.
To kai wani suna kaga ya dace a saka mata.?
Eh da zan saka mata sunan Mamanmu Sadiya data rasu '.
Aiko wannan ne baka isa ba.
To akan me zaki daɗi haka.?
Ya yi maganar yana haɗe fuska, na tashi daga kwancen da nake na bashi amsa nima ina ɗaure fuska.
Na farko ka saka sunan Babanku sannan na biyu ka saka sunan Mamanka sai kace kai ne kayi mini naƙuda, to wannan ne baku isa ba wlh.
Amma 'yan uwa na suka buƙaci a saka sunan Mamanmu saboda a yi mata takwara.
To ai duk cikinsu babu wanda bai da kwan haihuwa, su bari idan sun haifa sai su saka tunda ga matar Jafar nan da ciki inta haifi mace ya sa tunda kai ka saka Babanku. Dan haka ni sunan tawa uwar zan saka, sannan dana haife ta meka siya mata.? kuma ina ce cikin ma by mistake aka same shi ƙaddara ya sa na haife ta, tunda dukanmu bamu shirya samun ciki a lokacin nan ba.
Ni kike faɗawa wannan magarar.?
Umar na faɗa! Na faɗa ɗin!! tunda nake haihuwa akwai abunda 'yan uwanka suka tsinana mini ne, dana yi haihuwar farko ko sabulu ƙannanka basu kawo mini ba, sannan dana yi jinyar wancen cikin daya fita babu wanda ya tako ƙafarsa yazo gaishe ni, sai yanzu ne zasu zo su yi mini mulkin mallaka, to ba zai yuwu ba wlh.
Farida ni kike faɗawa magana haka ko.?
Na faɗa ayi yadda za a yi dani, nan ɗan uwanka ya kirani da matsiyaciya, to matsiyaciyar ce ta haihu har ake so a yi mata mulkin mallaka da 'yarta, to ba za a saka sunan Maman naka ba sunan uwata za a saka.
Muna cikin sa'insan, sai mutumin dake haya a gidanmu yayi sallama a ƙofar ɗakinmu, nan Umar ya amsa ya fita, ina jin mutumin ya yi masa wankin babban bargo yace masa.
Ya za a yi mace ta haihu tasha zafin naƙuda madadin ka zauna da ita kayi shawarar sunan da zaku saka wa yarinya, sai kajewa 'yan uwanka su zasu zaɓa sunan da za a saka, sannan ba ganin ta suke da mutunci ba, to baka nima zaman lafiya ba, karka bari ranar da idon yarinyar nan zai buɗe wlh, dan zaka kwashi 'yan kwallo da ita.
Ina ji yayi masa tas, kafin suka yi sallama ya shigo ɗaki bai tanka mini ba, sai ya amsa yarinya yayi mata huɗuba da Aisha sunan Mamanmu.
Lamarin auren nan naku akwai sauran ƙura..
Zaku iya fara biyan kuɗin cigaban wannan littafin KOMAI YAYI FARKO book 2... Domin saura pages kaɗan mu gama book 1 mu tsunduma a zango na biyu wanda sai kun biya kuɗinsa kafin zaku samu cigaban wannan labarin ɗoɗar har zuwa ƙarshensa In Sha Allah. ₦500 ne kuɗin. Sannan kuna da garaɓasan samun littafin ALHAKI kyauta a cikin paid group ɗin komai yayi farko.
Pay ₦500 to 9034940106
RAMATU KABIR
MONIEPOINT.
Sai a tura shaidar biya a WhatsApp ta number nan ***.
Rahma Kabir ce Matar MG.