KOMAI YAYI FARKO...

15

by @rahmakabir13

KOMAI YAYI FARKO...

Na

©®Rahma Kabir MrsMG.

Page 15.

Sarac Stars R Pen...✍️

Tunda 'yan uwan Umar suka samu labarin sunan Mamanmu yasa wa baby sai ƙura ya tashi, nace can musu, saboda na ɗaura ɗamara akansu, idona ya bushe akan duk ɗan iska daya zo mini da maganar banza a shirye nake na basu amsa, dan kan mage ya waye. Sai dai shuru babu wanda yazo dan haka na watsar da batunsu na cigaba da shirin suna duk da ba wani abun arziki Umar yake shiryawa ba, domin bai yi mini kayan fitar suna ba kamar dai haihuwar farko, shiyasa na ɗauki turmi biyu cikin waɗanda na adana ina ta ɓoyesu, ɗaya na akwati ne da ya rage ban ɗinka ba, ɗayan kuma na sunan Amir ne, sai na aika ƙanwata ta kai mini ɗinki, aka ce kuɗin ɗinki dubu biyar da ɗari biyar ne, sai na bayar da dubu uku saura dubu biyu da ɗari biyar ciko. Ranar Asabar ana gobe suna banda cikon kuɗin ɗinki gashi mai ɗinki harta kira ni ta gama, sai kawai na kira Khalifa ƙanin Umar a wayata, da ya ɗauka muka gaisa sai nake sanar da shi ina buƙatar cikon kuɗin ɗinki, ya tambaye ni nawa ne na faɗa masa sai yace na tura masa account number ɗina, nayi masa godiya muka aje wayar, ba jimawa sai naji alert kuɗi dubu huɗu sun shiga, na kalli ƙanwata Jidda wacce bata wuce shekara sha uku ba, dama itace Mamanmu ta turo ta riƙa taya ni aikin jego, nace mata.

Jidda gashi ya turo da kuɗin kije ki ciresu, sai ki kaiwa mai ɗinki dubu biyu da ɗari biyar, sai ki dawo mini da sauran kuɗin.

Tace mini to ta amsa ATM ɗina ta fita ba jimawa sai gata ta dawo da canjin dubu ɗaya da ɗari biyar, to dama Sakina tana nan kuma ba aikin da take yi mini sai danna waya, tuntuni na fahimci babu abinda yake kawo ta gidana sai ɗaukar rahoto, dan ta samu labarin faɗa taje ta fesawa Mamanmu, sai naga ta miƙe tana ce mini ta tafi.

Ya zaki tafi kuma, ki tsaya ki goge mini kayan nan mana.

Gaskiya Anty bana son magariba tayi mini a hanya.

Hmmm shikenan na faɗa sai ta fice, Jidda kuma ta ɗauki kayan ta goge mini, na samu na yiwa yarinya wanka na shiryata nima nayi nawa. Zuwa dare wajen ƙarfe takwas sai ga Sakina ta dawo tana ce mini.

Mamanmu ce ta aiko ni tace wai in akwai kuɗi a hannunki ki bata koda dubu ɗaya ne.

To nace mata kawai dan ban isa in ce babu ba saboda tasan ina da canjin kuɗin ɗinki da na amso, sai kawai na bata dubu ɗaya da ɗari ɗari biyar ɗin ta amsa, sai take ce mini wai Mamanmu ta na can tana aikin donot wanda za a bawa mutane, nace tayi mata sannu da aiki sai ta wuce, na so ace na riƙe kuɗin saboda tsaron lalura in ya taso mini, musamman yadda naga Umar yana jan jiki da hidimar, na san ba komai ne zai siya ba, sannan a zatona wannan donot ɗin gudun mawa ce Mamanmu take yi mini zata aiko da shi. Ranar Suna da safe sai gashi ta aiko da donot a ƙulle a fararen leda an saka shi bibbiyu a ciki, a wata farar roban fenti babba, na amsa ina godiya sai na koma na fara tunanin yadda zan yi wanka dan ba a kawo wutar nepa ba tun jiya, dan haka sauran ruwan da ya rage a flasks ɗina kaɗan shi ne na juye na yi amfani dashi na gogewa yarinya jiki, ni kuma sai dai na sauya pad, gashi anyi mini ɗinki ina son na yi tsarki amma ba ruwan zafi, sauran ruwan da ya rage dana gogewa baby jiki kaɗan ne, sai na wanke fuska da shi na fito na shirya cikin ɗaya daga kayan dana ɗinka ba tare dana yi wanka ba ni da yarinya, Amir shi ma daka tsamin aka yi masa, Jidda ta shirya shi cikin kayan sallar bara, na shafa mai na goga power da kwalli Na fesa turare sai na fito fes babu mai cewa ban yi wanka ba, yarinya ma na saka mata wani riga cikin kayan da Mamanmu ta bani. Ɓangaren abinci kuma Umar ya kawo shinkafa loka goma da kayan miya da mai da sauran kayan haɗi, sannan ya siya wani rago ɗan ƙarami, dan wannan sai dai ayi amfani dashi da haƙuri, da yake ni ba mai rainuwa ba ce ban damu ba dan zance ta wannan fanni yayi ƙoƙari, to da sassafe Umar yasa aka yanka aka cire kayan ciki, aka rataye ragon kamar yadda ake yi, sai ya fice daga gidan ban sake ganinsa ba, kuma yasan ba wuta ina buƙatar ruwan wanka ni da baby na kira shi bai ɗauka ba shi yasa daga ƙarshe na haƙura nayi daka tsami. Maƙotanmu sunyi mini kara sun shigo sun taya aikin abinci, to da suka ɗaura girki sai suka tafi saboda gari ya haɗa hadari dan muna cikin watan August ne, cikin ikon Allah sai ga ruwan sama ya sauka da ƙarfinsa, to ƙanwata Sakina tana nan tare da Ƙanwarsa Mamanmu mai suna Amina, suna nan zaune a ɗakina amma cikinsu aka rasa wacce zata je gurin abincin nan ta kwashe sauran itacen tare da kare murhun da abinci ke kai gudun kar ruwa ya kashe wutar, gashi an riga an zuba shinkafa a cikin tukunyar, ƙarshe ni ce na fita cikin ruwan da ɗanyan jego, na yi kaye-kayen da zanyi na kwashe sauran itace na duba shinkafa har ruwa ya tsotse kuma shinkafar bata gama nuna ba saboda sun yi mata ƙauron ruwa, haka na rufe tukunyar na koma ɗaki, ruwa duk ya jiƙani sai na sauya kaya zuwa ɗayan atamfar na shanya wanda na cire a ƙofa na koma na zauna ina jin zuciyata tana yi mini zafi, saboda banga amfanin zamansu a gidan ba sannan nayi magana cibi ya zama ƙari, amma duk da haka sai da na yi wa Sakina ƙorafi, sai ta nima yi mini rashin kunya na biye mata muna musayar magana, Inna Amina ta shigar mata wai ba dole sai Sakina tayi mini aiki ba, sai kawai nayi shuru na rabu da ita. Bayan an ɗauke ruwa suka sauke shinkafa tayi cikin shege, wani ɓangare ya nuna wani kuma bai yi ba, tayi gatse-gatse da an saka a baki sai mutum yaji tana gari-gari, a taƙaice dai shinkafa ta lalace sai dai mutum ya yi mata cin yunwa. Na fito zan je kitchen sai na hango ƙanina Usman ya fito daga ciki riƙe da kwano mai murfi ya wuce gida, a zatona abinci ne ya ɗiba ya tafi amma dana shiga kitchen ɗin sai na samu an kwashe rabin kayan ciki ɗanye, kuma na san shi ne ya ɗiba, sai dai kawai nayi shuru ban ce komai ba dan kar in ɗaga murya na jawa kaina magana, na ɗauki abunda zan ɗauka na koma ɗaki, sai a lokacin ne Inna Amina ta fito ta ƙara haɗa wuta ta gyara sauran kayan cikin, tayi masa wani banzan suya bai nuna sosai ba, dan in mutum ya saka a baki sai dai ya taune zaƙin magi ya yarda, itama ta kwashe rabi ta ƙulle a leda ta ɓoye, a taƙaice kayan cikin da aka kawo mini bai fi cikin tafin hannu ba gabaɗaya shi ne wanda ya rage, ta saka mini a ƙarƙashin gado tana cewa.

Gashi kayan cikin nan ki ɓoye dan kar mutane su gani suce zasu ci tunda ba yawa.

To kawai nace mata dan nasan ta riga ta ɗiba rabonta, kuma bawai an saka a tire bane an raba kamar yadda aka saba. Haka mutane suka dinga shigowa ana zubawa musu abinci amma basa iya ci, sai dai in sun tashi tafiya ne sai a basu ƙullin donot, ganin ya kusa ƙarewa sai na ɗiba donot ɗin na saka a babban leda mai zane, na ƙulle saboda 'yan yawan Umar koda sun zo na basu su raba dan kar su yi ƙorafin ba a basu ba duk da ba shi ne yayi mini donot ɗin ba, na ɓoye musu akan in zasu tafi na basu, amma abun mamaki lokacin dana zo ɗaukar donot ɗin sai yace ɗauke ni, dan sama da ƙasa ban ganshi ba an ɗauke shi gashi zasu tafi har suna tambayar ina nasu, na tsaya ina nazari sai na tuna ɗazun naga leda irin wannan mai zanen dana ɓoye donot ɗin a hannun Inna Amina, wanda nan take na fahimci ita ce ta kwashe donot ɗin ta yi tafiyarta gida, dan bata tsaya ba tana gama suyar kayan ciki ta wuce, haka 'yan uwan Umar suka tafi dani a baki akan nayi donot ban basu ba, wanda suma ɗin haka suka zo taron sunan hannu sakayau ba sabulu balle omo, shiyasa nima ban damu ba da ban basu donot ɗin ba tunda basu da kara.

Zuwa dare mutane kowa ya watse an yi wanke-wanke an gyara gida, ina zaune a ɗaki na fito kenan daga wanka saboda nepa sun kawo wuta na dafa ruwa, Humaira ce kaɗai ban yi mata wanka ba dan ance ba a wanka da yamman ranar suna. Sai ga Umar ya dawo fuskarsa a haɗe ya zauna ya fara yi mini mita akan meyasa ban bawa 'yan uwansa donot ba, na kalle shi sheƙeƙe nace.

Ka bani kuɗin yin donot ne? Nima Mamanmu ce tayi mini, sannan lokacin da 'yan uwanka suka zo da yamma ne, ya riga ya ƙare tunda dama ba yawa.

Wannan ai wulaƙanci ne.

Babu batun wulaƙanci tunda babu sisinka a ciki.

Sai ya miƙe a fusace ya soma masifa, ban kuma tanka masa ba yayi ya gama ya fice fuuuu kamar guguwa, sai na bishi da guntun tsaki da harara dan nasan a dake dai bazan duku ba, sai a naji daɗi da ban basu ba tunda basu da mutunci.

Washegari da safe sai ga Inna Shafa ƙanwar Mamanmu ta zo ta kawo mini kuɗin meeting da ake yi a family ɗin su Mamanmu duk wata dubu ɗaya mutum zai bada, to wanda yake da hidima shi ake haɗamawa, sannan kuma za a haɗawa mutum kuɗin tallafi ɗari biyar-biyar, shi ne ta bani dubu goma na meeting dubu biyar kuma na tallafi da aka haɗa mini, na amsa ina godiya cike da murna tare da lissafin yadda zan juya kuɗin na cigaba da sana'ata da shi saboda na samu jari, sai muka yi sallama ta tafi ta bar ni cikin farin ciki tare da ganin alfanun yin meeting ɗin, dan ba ƙaramin ƙuƙutawa nake yi ba wajen bayar da dubu ɗaya na meeting ɗin duk ƙarshen wata, wani lokacin daga cikin kuɗin motar da Babanku yake bani na makaranta nake tarawa na bayar, ko kuma ribar sana'ata na haɗa na bada, sai gashi yau naga ranar haka. Ina tsaka da tunanin yadda zanyi da kuɗin sai ga Mamanmu ta kirani a waya, na ɗaga muka gaisa sai take ce mini.

Wannan kuɗin da aka baki na meeting da tallafi nake so ki bani, saboda dama na aro kuɗin ne na haɗa miki donot ɗin nan, gashi kusan dubu sha biyar aka kashe.

To kawai na iya ce mata na kashe wayar, jikina yayi sanyi kamar an watsawa kaza gishiri, saboda tsoron Allah yasa na kasa kwakkwaran motsi, duk a zatona Mamanmu tayi mini wannan donot ɗin ne a matsayin Sadaƙatul Jariya ko kuma tayi ne saboda a bawa mutanenta, ashe ba haka bane, amma kuma wlh a ƙiyasin dana yi bai fi dubu shida zuwa bakwai ta kashe ba na nefanen donot ɗin, domin abinci yana da sauƙi sosai a lokacin. Ba a jimaba sai ga Ƙanwata ta zo ta amsa kuɗin na bata dubu sha biyar ɗin, ni dai ban amfana da komai ba sai donot da aka ce anyi, wanda da ta yi shawara dani ta faɗa mini niyyarta akai, wlh da ba zan amince ta yi ba duba da ni ce na cutu dan sosai na saka rai da wannan kuɗin.

Umar ya shigo ya ce na kawo robar da za a zuba nama dan yana so a gyara da wuri, nace to na fita zuwa kitchen na ɗauko wani bokotin fenti babba na ba shi, sai ya koma gurin me gyara a nan cikin tsakar gidan nima nabi bayansa, sai naga Umar ya yanke cinyar baya guda ɗaya ya saka a leda, yana cewa zai kai gidansu ne a gyarawa Babansu saboda baya cin soyayyen nama, ban ce ƙala ba ya fice zuwa gidansu, ko kafin ya dawo mai gyara ya gama fasa mana naman ya tafi, Umar ya dawo ya tsaya a gurin yana duba naman wanda yake ɗan kaɗan ne dan ko rabin bokitin bai kai ba, sai ya ce mini.

Ko da an gyara an soya, kar a sake a raba har sai na dawo.

Nace masa to, haka ya fice ya bar ni ina aikin nama ni da Ƙanwata Jidda saboda babu wanda ya zo taya ni aikin kamar yadda ake yi a al'ada. Haka na ɗaura tafashe a wuta, da ya yi na soya shi duka sai na samu wani kwano na ɗiba na ɓoye a kitchen, dan na tabbatar idan Umar ya dawo ba lallai na samu abun arziki ba, kuma nice da haihuwa amma sai abunda aka bani, gashi nayi ƙan baki ba zan ji daɗin naman ba sai bayan kwana biyu. Zuwa rana Umar ya dawo ya tadda an gama suya, sai muka zauna a falo aka kawo tire yace na kasa nama gida huɗu, nan take na kasa shi huɗu, sai yace na ɗauki kashi ɗaya, nashi kashi ɗaya, sannan gidanmu kashi ɗaya, haka gidansu ma kashi ɗaya, shuru nayi bance masa komai ba dan inna yi magana rai ne zai ɓaci, amma banda son kai ya ɗauki ɗanyen nama ya kai gidansu me zai sa a yi rabo dasu yanzu, haka na zuba na gidanmu a ƙaramar baƙar leda na ƙulle, na gidansu ma na ƙulle sai na kwashe masa nashi, ya saka na gidansu a cikin nasa ya amsa ya adana da kanshi sai ya fita, nawa kuma na ƙullawa maƙota na aika musu, na cirewa Ƙanwata mai taya ni aiki, sannan na cirewa Amir na shi, nan take nawa kason ya ƙare ko tsoka ban samu ba, kuma saboda takaicin abunda yayi mini yasa na rabar da shi kawai, sai wanda na ɗiba na ɓoye ya zama shi ne kaɗai rabo na dana ci.

... Wannan uwa ce ko uƙuba