16
KOMAI YAYI FARKO...
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Page 16.
Sarac Stars R Pen...✍️
Bayan an gama rugu-rugun haihuwa da suna, ranar monday na cigaba da zuwa makaranta saboda muna gabda fara jarabawa. Shi ma Umar ya tafi gurin aikinsa, shi yasa na samu sauƙin lamura ba takura da saka ido, da wuri nake tashi na yi wanka na shirya Humaira sannan Amir shima na shirya shi na saka masa abinci a lunch box ɗinsa sai mu fita tare na aje shi a makaranta, sannan na je wani gida da yake kan layinmu, na bar masa uniform ɗin makarantar islamiya a gurin wata mata Maman Habu da muke mutunci da ita, idan Amir ya dawo daga boko sai ya tsaya a gidan in lokacin Islamiya yayi ya saka uniform ya wuce, sannan in na dawo daga nawa makarantar sai na biya na ɗauke shi mu koma gida. Haka nake gudanar da rayuwata cikin matsi tunda lokaci baya isana bana samun damar hutawa, shi yasa na ƙara ramewa da haske, ga karatu, ga goyon Humaira ga rashin wadataccen abinci, ga kuma rashin kwanciyar hankali a gurin Umar, tunda in ya tafi baya taɓa kirana a waya ban kai wannan matsayin ba har sai ya dawo, in kuma ya dawo faɗa ne da tashin hankali dan bai fasa sakawa a cigaba da kawo masa rahoto a kaina ba.
Ranar Asabar da yamma Umar yana guga a falo yana ta masifa wai ban yi masa gugan kayansa ba, da yake nice nake yi masa wanki da gugan kayansa, to a 'yan kwanakin nan aiki sunyi mini yawa ga shi muna ta shirin fara exam, shiyasa sai dai na wanke kayan na barsu babu guga, shi ne ya riƙa mita da masifa amma ban kula shi ba dan ya saba akan in banyi masa ba sai ya ɗauki gaba dani, kuma nayi wa abincina saboda sai muna magana ne ma zan samu fuskar da zan yi masa maganar abinci, a haka sai ya ɗauki wata yana gaba dani kafin daga bisani ya waiwaye ni, shiyasa jarina ya fara ƙasa duba da nauyin hidimar gidan da nake ɗaukewa a kaina. Yana tsaka da yin gugan sai saƙo ya shigo wayata kuma tana kan TV stand, sai Umar ya miƙa hannu ya ɗauka sai ya ga daga banki ne, saboda ɗazun na saka katin nira ɗari to basu tashi turo da alert ba sai a lokacin, aiko yana ga ni sai ya aje gugan da yake yi ya kwala mini kira, na fito da sauri ina amsawa, ya fara surfa mini masifa.
Akan me zaki je ki buɗe account ba tare da sani na ba.?
Hmmm to massage ɗin daka gani an tura mini kuɗi ne ko kuma kuɗi ka gani mai yawa a cikin account ɗin.?
Farida bazan ɗauka ba dan wlh dole zan ɗauke ki muje banki a yi blocking account ɗin nan, dan ban yarda ba.
Sai ya aje wayar ya koma ya cigaba da guga ni kuma ban sake tanka masa ba na wuce zuwa ciki dan nasan ba zan taba fita zargi a gunsa ba, nasan zai yi tunanin wani namijin zai iya turo mini kuɗi ta account ɗin, shiyasa yace zai yi blocking ɗinsa.
Washegari ban sani ba Umar ya ɗauki wayata yayi mini shige-shige ya yi blocking account ɗina, a ranar da yamma ya koma Zari'a ba tare da ya bar mini abinci ba ya yi tafiyarsa cikin fushi, haka na cigaba da maneji ina ririta abunda ke hannuna. Ranar monday zamu fara exam kuma nasan an hana masu su shigo hol da yara, saboda dokar makaranta ne mai goyo ba zata shiga da shi wajen exam ba, shiyasa nayi tunanin kai Humaira gidanmu saboda jarabawar bai fi muyi awa biyu mu zana mu dawo gida ba, sannan paper ɗaya ne kullum wata rana ma bamu da shi, to inna barta gurin Mamanmu nasan ba lallai tayi rigima ba ƙila ma har naje na dawo bata tashi daga barci ba, saboda tana bacci mai nauyi da safe in na yi mata wanka. Sai na kira Umar da niyyar na shaida masa amma sai da nayi masa kira hudu kafin ya ɗaga, ba bata lokaci na faɗa masa zan aje Humaira a gidanmu saboda ba a shiga exam da goyo, sai yace bai yarda ba sai dai na tafi da ita hakanan na zana. Nace cikin damuwa.
To yanzu waye zai riƙa riƙe mini ita da zan samu na yi jarabawar.?
Oho miki, sai ki san yadda za ki yi amma ban yarda ki aje yarinya a gida ba.
Nace masa to sai na kashe wayar ina jin takaicinsa. Washegari Monday sai na je gidanmu da safe na samu Mamanmu akan maganar, sai tace tunda ga ƙanwata Husna to mu tafi tare sai ta riƙe mini ita na zana exam ɗin, duk da itama ta na zuwa makaranta amma sai ta kashe mata nata tunda ba kullun bane exam ɗin, nayi mata godiya dan naji daɗin wannan maslaha dana samu, sai muka tafi makaranta tare da Husna na bar mata Humaira na shiga ajin jarabawa. To bayan mun fito sai matan ajinmu suke cewa ai Husna tayi ƙarama da raino saboda sun ga Humaira ƙatuwa saboda tayi ƙiba sosai kasantuwar haka goyona yake, kafin muyi arba'in yaro yake cika baya, ita kuma Husna bata wuce shekara takwas ba, sai dai nayi murmushi kawai dan ba yadda zanyi hakan ne kaɗai mafita na. Haka muka cigaba da jarabawa ina zuwa tare da Husna, in mun dawo sai na fara rakata gida kafin na wuce gidana.
Ranar Laraba da yamma na dawo daga gidanmu dan jarabawar rana muka yi, to da muka dawo na raka Husna kamar yadda na saba sai na tsaya na ci abinci zuwa bayan sallar la'asar na dawo gida, sai kwatsam na tadda Umar shima ya dawo, shi da nake tsammanin sai ranar juma'a zai dawo sai gashi a yau laraba, na same shi zaune akan dadduma a tsakar gida, da yake kafin na fita nayi wanki na shanya kaya a igiya kuma har da dadduma a ciki, shi ne ya ɗauka ya shimfiɗa ya zauna saboda ba key ɗin ɗaki a hannunsa. Sai na ƙarasa da ɗan sarkin fuska ina cewa.
Ikon Allah kaine ka dawo yau, to sannu da zuwa.
Bai kula ni ba sai ya sha kunu fuskarsa a haɗe, ni kuma sai na wuce ɗaki na buɗe na shiga na aje jakata, sai shima ya biyo ni ya tsaya ya fara masifa ta in da yake shiga ba tanan yake fita ba, yana cewa.
Yau an gaya mini baki tafi da Humaira makaranta ba, ina kika aje mini yarinya.?
Gaskiya ban gane me kake magana akai ba. Ga Jakata nan ɗauke yake da kayan Humaira da komai dana saba fita dasu saboda hidimarta a makaranta, taya zaka ce ban je da ita ba.
Ƙarya kike yi ba da ita kika je ba.
Ya faɗa a fusace, sai naji na kawo wuya, sai kawai na biye masa muka yi cacar baki, da ya gaji sai ya fice daga gidan, na zauna ina mayar da numfashin takaici saboda na tabbatar wannan aikin class rep ɗinmu ne daya ke guntsar gulma ya fesa wa Umar, na sauke numfashi tare da jan guntun tsaki na miƙe na shiga yin aikin girki. Zuwa dare mun gama cin abinci da Amir har na yi masa shirin bacci ya kwanta, Humaira ma tayi bacci, ina shirin duba littafi sai ga Umar ya shigo ko sallama babu, ya nima guri ya zauna yana cewa cikin haɗe fuska.
Farida bari kiji sai dai ki haƙura da makarantar nan har zuwa lokacin da kika gama yin rainon mini yarinya, sai ki koma makarantar ki cigaba da yi, dan ban yarda ki aje mini yarinya a gida ba kina tafiya makaranta.
To wai kai waye ne ya gaya maka ban je da ita ba.?
Sai yayi banza da ni bai amsa ni ba, ya cigaba da sababi, da naga fitinar tayi yawa ga dare yayi, sai kawai na ɗauki wayata na kira Mamanmu na shaida mata abunda ke faruwa, tace tana zuwa sai ta kashe wayar. Ba jimawa sai ga Mamanmu tare da Babanmu sun zo a wannan daren wajen ƙarfe sha ɗaya, suka shigo tsakar gida suka tsaya, Mamanmu ta ƙaraso ƙofar ɗakina tayi sallama, na amsa na miƙe na fito shima Umar ya biyo bayana, nan muka ƙarasa inda Babanmu ya tsaya, muka gaishesu, sai Babanmu yace.
Umar naji abunda ka faɗa, amma kasan mu ba zamu yi maka ƙarya, Farida bata bar yarinyar nan a gida ba, da ita ta tafi tare da Husna ta riƙe mata ita.
To ba komai, ai da baku taso cikin daren nan ba, ita ce bata yi mini bayani yadda zan gamsu ba shiyasa ban yarda ba. Mun gode.
Cewar Umar cikin borin kunya, nan su baba suka yi mana sai da safe suka tafi, sai muka koma cikin ɗakin yana surutun meyasa na faɗawa mama, ai ban yi masa bayanin yadda zai fahimta ba ne.
Hmmm bayani wanne kake so nayi maka.? Ko so kake sai na rantse na dafa al-Qur'ani kafin zaka yarda.
Na ƙare maganar cikin ɓacin rai, bai sake magana ba ya nima guri na kwanta. Tun daga wannan abun ɗaya faru sai na samu sassauci daga saka mini ido da yake yi har muka gama jarabawa muka shiga hutu, na cigaba da juya kuɗin hannuna ina manejin rayuwa duba da bana zuwa makaranta babanmu baya aiko mini da kuɗin mota, dan haka sai na fara cin uwar kuɗi ya zama saura kaɗan, ba zai ma isa na cigaba da sana'ata ba, ga account ɗina Umar ya rufe mini dan haka dole na shirya na je can banki suka buɗe mini account ɗina, sai na kwashe kuɗin ciki dubu ɗaya da ɗari biyar na bar naira ɗari a ciki, na dawo gida na fara tunanin sana'ar da zan fara, sai dai na rasa wanne zanyi wanda a haka kuɗin ya dulmiye na cinyesu a ciki na koma gidan jiya.
Har muka koma makaranta zaman bai sauya zani ba dan babu abincin kirki, ga shi cikina ya buɗe saboda goyo, sannan a lokacin Humaira ta fara cin abinci, wani lokacin dole sai na dafa mata wani abu nake tafiya da shi makaranta na bata, saboda ba ni da ruwan nono sosai tunda ni ban ci na ƙoshi ba, shi yasa kullun gani nan a rame a lalace kamar ana ɗibana ana miya. Dan haka wannan zuwan da Umar ya yi sai nayi masa ƙorafin abincin baya isarmu, amma buɗar bakinsa sai cewa yayi.
Ni abunda yake bani mamaki ina kike kai abincin nan.? Dan na san ina wadataku da abincin da zaku ci har naje na dawo.
Takaici yasa na yi masa banza har ya gama maganarsa ya fice, raina ya ƙara ɓaci sai kawai na saka hijab naje gidanmu na samu Mamanmu na kai mata ƙarar Umar, wanda wannan shi ne karo na farko dana taɓa kai ƙorafinsa tun aurenmu zuwa yanzu, na zauna a falonta muka gaisa sai na ke ce mata cikin matsar kwalla.
Mamanmu wlh na gaji, duk abunda zanyi mutumin nan bana burge shi, yana zargina da bin maza, yana zargin ina yi masa ɓarna da abinci wanda kuma bai wadatamu da shi ba, kullun cikin zargi nake a gurinsa kwata-kwata babu farin ciki a zamanmu.
Na ƙare maganar ina kuka sosai dan ji nayi zuciyata ta karye ba zan iya daurewa ba, gwara nayi kukan ko hakan zai rage mini raɗaɗin dana ke ji a zuciyata. Mamanmu ta nisa tace.
Kiyi haƙuri Farida ko wani aure da akwai ƙalubale, ke irin naki kenan, sannan ko wace mace haƙuri take yi a gidanta, dan haka ki dage ki jure saboda bana fatan auren nan ya mutu ko dan saboda yaranki.
Haka ta dinga bani baki har na ji zuciyata tayi sanyi dan banyi zaton ma zata karɓi maganar haka ba, tasa ƙanwata ta zubo mini abinci na ci ni da yarana, daga bisani nayi musu sallama na tafi gida. Zuwa dare muna zaune a falo Umar ma yana nan sai ga ƙanwata Jidda Babanmu ya aikota da garin tuwo mai yawa fari ƙal da shi, tace Babanmu ne ya bayar da nikan rabin buhun masara shi ne aka ɗiba mini saboda yayi musu yawa, dan yaran gidanmu zaɓan abinci suke yi basu ciki cin tuwo sosai ba, shiyasa mama y'ta faɗawa Babanmu a ɗibar mini kar su aje ya saki ya lalace, na amsa cikin farinciki ina zuba godiya, dan ba ƙaramin daɗi naji ba, ko ba komai zamu riƙa sauya abinci tunda mu bama tuwo kullun sai dai na sarrafa shinkafa ko taliya. Sai naji Umar yaja tsaki ya kalle ni yana cin magani.
Farida ki bata ta mayar da wannan garin ba zamu yi amfani da shi ba.
Kamar ya ba zamu yi amfani da shi.? kyauta fa iyayena suka bamu. Sannan ka kawo mana irin shi ne ko ka kawo mana makancin wannan da zai maye gurbi wannan? aiko ba za a fita da garin nan ba tunda ba mu da shi.
Wlh sai an fitar da shi daga gidan nan, kin ji na faɗa miki.
Ya faɗa a fusace yana miƙewa tsaye, nima sai na miƙe muka fara cacar baki, nan take Jidda ta fara kuka da yake tana da sauri kuka musamman akan abunda ya shafe ni, sai Umar ya ɗauki garin ya fita da shi nace.
Jidda tashi ki bishi ki amsa kar ya je ya wulaƙantar da shi, gwara ki mayar da shi gida ku yi amfani da shi tunda ya hana na amsa.
Sai ta miƙe da sauri tana share hawaye ta fita tabi bayansa ta amsa ta wuce gida, shi kuma ya dawo ya zauna yana fizge-fizge ban kula shi ba amma kuma ya kawo ni wuya dan ba ƙaramin haushi ya bani ba. Muna zaune sai ga Babanmu ya dawo da garin, ya yi sallama a ƙofar gida, Umar ya fita nima na bi bayansa muka gaisa, sai baba yake cewa.
Umar nine na baku garin nan ba wai roƙonmu Farida tayi ba. Kayi haƙuri ka karɓa garin nan, in banda abun ka mun taimakawa bare ma balle ita da take 'yata.
Gaskiya baba bazan amsa garin nan ba kayi haƙuri.
Cewar Umar yana cuzgune fuska, Babanmu ya kaɗa ya raya amma Umar ya shafawa idona toka shi ba zai amsa ba, ya watsawa Babanmu ƙasa a ido, cike da ciwon abun nan Babanmu ya hau mashin ɗinsa ya juya da garin nan, zuciyarsa ba daɗi dan ko bai furta ba fuskarsa ta nuna haka, muma muka koma gida zuciyata ba daɗi, sai dai ni naji daɗin abunda Umar ɗin yayi masa, domin gwara ya fara nuna musu asalin halinsa ta yadda su da kansu zasu fahimci waye shi, ƙila hakan zai sa su sarara mini akan in ya kai ƙarata gurinsu su gane bani da laifi.
.... Umar dai kwallon ɗan hau ne...