KOMAI YAYI FARKO...

17

by @rahmakabir13

KOMAI YAYI FARKO...

Na

©®Rahma Kabir MrsMG.

Page 17.

Ƙarshen free pages na book 1.

Sarac Stars R Pen...✍️

Bayan mako biyu, ranar asabar Umar ya dawo na bar shi a gida na tafi makaranta, to lokacin da muka tashi sai na kira shi ko zai zo ya ɗauke ni, sai yace ya fita ya yi nisa amma na ƙarasa gidanmu na jira shi tunda key yana hannunsa, kuma ya kai Amir can gidanmu sai mu dawo tare, nace masa to sai na kashe wayar na samu nqpep na hau ya wuce da ni. Bayan mun isa na shiga muka gaisa da Mamanmu sai na samu guri na zauna a tsakar gidan dan na samu suna aikin ɗaura abincin dare saboda yamma tayi, muna ɗan hira jefi jefi har suka gama sanwa, da aka kira sallar Magriba sai nayi alwala muka shiga ɗaki na yi sallah na zauna zaman jiran Umar, amma shuru har dare yayi, can sai ga shi ya zo bai ma shigo ba ya aiko na fito mu tafi, to gashi sun gama abinci ba mu ci ba, tuwo ne da miyar kuka har da naman kaza a ciki wanda suka ɗauka cikin kajin Mamanmu da take kiwo suka gyara aka saka a cikin miyar, sai na cewa Mamanmu banyi abinci a gida ba ta zuba mini na tafi da shi, ta saka Sakina ta zuba mini a kular tuwo da miya kuma da ɗan yawa wanda zai ishe mu, to bayan na fito mun kama hanya a ƙafa sai Umar ya fara yi mini faɗa da cewa.

Aikin ki kenan ki riƙa tona mini asiri gidana ba abinci. In ba haka ba meye ne na amso tuwo.?

To in ban amso ba meye zamu ci a gida in mun koma.? in kai ba zaka ci ba to ni zan ci tunda ban ci a gidan ba, kuma dan na amso tuwo a gidanmu laifi ne.

Ni tona mina asiri ne, saboda kin nuna cewar na gaza, dan haka in kina son zaman lafiya ki mayar da tuwon nan.

Ban ƙara ce masa komai ba na juya gidanmu, dama ba mu yi nisa ba na mayar da tuwo, Babanmu yaji haushi sosai ya dinga faɗa Mamanmu tana taya shi, ni kuma ba wai tsoro yasa na mayar da tuwon ba kawai dai in nuna musu waye nake aure, mutumin da suke zagina akansa wanda suka so suyi mini baki a dalilinsa, wanda a baya suke gaya min in ban aure shi ba wani irin mutum ne zan samu ya aure ni. Shi yasa na mayar musu su ƙara shan gubar mamakinsa, haka suka ƙaraci faɗansu ni dai na barsu na juyo, na samu Umar yana jirana, haka muka ƙarasa gida baram-baram saboda bakina baya haila sai da nayi masa wankin babban bargo, haka muka ƙarasa gida, ƙarshe sai kayan tea ya siyo da buredi muka ci muka kwanta.

Rayuwa ya cigaba da tafiya da daɗi babu daɗi, zuwa yanzu na riga nasaba da rikicin Umar sam ya daina damuna, sai ya sauya salo ya daina dawowa ranar Juma'a sai ranar Asabar da yamma, washegari kuma ya koma, sai ban nuna masa na damu ba tunda makarantar da yake baƙin ciki da shi ban fasa zuwa ba. Muna rayuwa a haka sai kwatsam babanmu ya sayar da gidansa ga ɗiyar wacce take matsayin uwa a gare shi, domin shi bayi da Uwa da Uba duk sun rasu sai 'yan uwan mahaifinsa ne a nan Kaduna da yake asalinsu mutanen Sokoto ne, to Hajiya Saude ita ce take niman gida wanda in tazo hutu daga Abuja zata riƙa sauka a nan tare da iyalinta, shi ne babanmu ya sayar mata da gidan da muke ciki akan zai siya wani fili ya gina makaranta kamar yadda ya so yi a baya. To bayan sun bashi kuɗin gida ya danƙa musu takardu, shi ne ya yazo har gida ya samu Umar da maganar, ya kuma bawa ɗayar matan da suke haya notice, yace wa Umar.

Akwai wani gidan abokina da yake saman unguwarmu ya bar mini a hannuna zan zuba masa haya, to akwai safe contain falon ma da tiles, kaga a dubu hamsin ɗin da kake bani kaɗan zaka ƙara akai sai ka biya ku koma can.

To baba in na shirya zan yi maka magana.

Babanmu yace masa to sai ya tafi shi, kuma Umar bai sake ɗauko zancen ba har kwanaki ya haɗu da wani abokinsa, shi ne yake bashi labarin halin da muke ciki, sai mutumin yace masa ai akwai ɗaki a unguwar da na fara zama lokacin ina amarya, mai zai hana ya kama can tunda cikin mutane ne, sannan ma kusa da gidan da abokin yake haya ne, Umar ya je yaga gida yace yayi masa gashi ance kuɗin ɗaki dubu arba'in ne, shi ne yazo ya bani labari ya ce har ya biya kuɗin gida, nace masa to. Washegari da safe na shirya na je gidan dan na gane kwatancensa tunda na zauna a layin, sai dai ban taɓa shiga gidan ba har muka bar unguwa, wlh tun sadda na shiga gidan gabana ya faɗi ganin wani ɗaki dana yi a buɗe, gashi nan ya fita hayyacinsa, matar dake wanki a bakin rijiya ta amsa sallamata tana cewa.

Sannu da zuwa.

Yauwa ina yini.

Lafiya lau sai dai ban waye ki ba.

Na zo ganin ɗaki ne da muka kama, dan Allah ina yake.?

Allah sarki, ai wancen ɗakin ne gashi nan a buɗe ki shiga.

Cewar matar, sai nace mata to na nufi ɗakin na shiga, tsoron Allah ya hanani magana dan ɗakin gabaɗaya sai a hankali, tsohon ginin ƙasan ne wanda uwar ɗaka sai na duƙa kafin zan shiga saboda ina da tsawo, bayi kuwa iya kwano ne ba silin ga huji nan ina gani, wanda in ruwan sama ya sauka sai Allah, daga gani ma anyi masa gyaran sauri ne, sannan kitchen shima kusan yadda bayin yake haka shima aka yi shi, dana buɗe windown uwar ɗaka dake baya da sauri na rufe shi saboda ƙuda da suka fara yi mini sallama, saboda shirgin bola ne a bayan ɗakin mai yawa da mutanen unguwa suke zube bolansu a gurin, da kyar na iya haɗiye damuwata na fito jiki ba kwari, na yi sallama da matar na fita. Koda na koma gida na samu Umar, sai yake ce mini.

Farida kinga gida ko, saiki fara haɗa kaya dan so nake gobe mu tattara mu koma, anjima zan je in shre ɗakuna.

Hummm kawai nace masa dan bani da bakin magana, haka ya zaɓar mana mu koma ƙasƙantaccen guri amma ba komai wata rana sai labari. A lokacin na shiga haɗa kaya ban zauna ba, lokacin dana isa wajen bedside drower dan na cire wasu takarduna da suke ciki, sai kawai na tsinci nama ƙulli huɗu a santana, soyayyen nama ne da aka manta da shi har yayi hunhuna ya danƙare a cikin ledan, nan take masarrafar tunanina ya haske mini wannan naman suna ne da Umar ya ce na bashi na gidansu, sai bai kai ba ya haɗa da nashi ya rarrabasu ya ƙulle yana ci kaɗan-kaɗan har ya manta da su dan mugunta, na kasa haƙuri na fito dan na gaskata zargina, na zo falo riƙe dasu a hannuna na cewa Umar.

Naman sunan nan baka banni naci ba a matsayina na maijego, ba wata kulawa da zance ka bani dan ko tsiren ɗari biyu baka taɓa siya mini ba da sunan ina jego, memakon wannan ka bari ko da a miya muna sakawa muci amma ka ɓoye kana ci, gashi har ka manta dasu sun lalace.

Dana ƙare maganata sai dai yayi mini murmushi kawai amma yaƙi tanka mini saboda rashin gaskiya, na girgiza kai na wuce na cigaba da haɗa kaya amma ina takaicin wannan zalunci irin na Umar. Washegari ƙanwata ta zo ta taya ni muka gama haɗa kaya, zuwa yamma ya kawo mota ta kwashe mini kaya muka koma wannan gida, bamu zauna ba muka shirya kayan sai dai wasu ma basu samu guri ba duba da ɗakunan babu girma, ƙarshe sai dai na haɗa wasu kayan na bawa ƙanwata ta kai mini gidanmu Mamanmu ta aje mini, sannan ƙarin abun takaici ƙusa yaƙi zama balle na saka labule, dan haka sai ɗakin ya zama kamar na tohuwa babu labule, wannan ya tabbatar mini na naci baya ne ba ci gaba ba, domin a gaskiya wannan gidan zamansa sai mai haƙuri ga babu farin ciki a gurin miji sai abun ya haɗe mini baƙin ciki goma da ashirin, haka dai na jure muka fara sabon rayuwa anan gidan. Da farko ina shiri da matar gidanmu amma daga bisani na ganeta tana da gulma da kawo zancen mutane, sai na dai na sake mata ya zamana kullun rayuwa a ɗaki nake yinsa, daɗin dana ji ma bana zama sai yamma inna dawo na yi fafutukan girki, sai ta daina shiga harkata ta soma gaba sani ko gaisuwata bata amsawa na watsar da lamarinta.

Amir kuwa mun sauya masa makaranta an saka shi a wata local private school, tare da wani islamiyya kamar ta allo, to in mun fita da safe sai yamma mu dawo, bayan na biya na ɗauko shi a hannun wata mata da suka taɓa zama layi ɗaya da su Mamanmu, to tana shiri da Mamanmu dan haka sai nake kai Amir can ya zauna in ya dawo boko da lokacin islamiyya yayi sai ya wuce, duk da a yanzu muna kusa da gidan ƙaninsa Jafar amma ban kawo na kai shi can gidan ba, saboda nesa-nesa tafi daɗi saboda bana son wulaƙanci, duk da ina mutunci sosai da matar Jafar dan a hankali muka saba, sannu a hankali ta fihimci danginsu Umar ta dawo daga rakiyarsu sai muke zumunci, na zama nice abokiyar shawararta wacce take kawo mini kukanta akan zamanta da Jafar, shima mugun hali gare shi kamar na ɗan uwansa, saboda bambancin halinsu kaɗan ne, sai dai ni bana ce mata komai dangane da zamanmu domin duk abinda Jafar zai mata shafan mai ne akan wanda Umar yake yi mini, yaronta ɗaya Humaira ma ta girme masa, to da sallah yazo ƙiri-ƙiri Jafar bai yiwa yaron nan kayan sallah ba sai dai yayarta ta siyo masa kaya ta aiko ta basu, shi ne take yi mini ƙorafi ni sai dai na bata haƙuri dan ita kukan daɗi take yi tunda Jafar ya tsare mata abinci, to tunda ta sanar da ni haka da babbar sallah tazo sai na bada yadi aka ɗinkawa Amir tare da yaron Jafar tunda yadi ɗaya zai yi masa, bayan an gama ɗinki na aika mata ta dinga godiya na ce ba komai ai an zama ɗaya.

*****

A haka rayuwa ta miƙa har Humaira ta kai wata sha biyar a duniya sai na yayeta saboda tana cin abinci sosai, dan haka sai na dage mata da abinci tana ci duk da har lokacin ba mu da wadatan abinci sosai, shinkafa ce fara da mai sai in mun samu taliya mu sirka, bazan manta ba akwai ranar dana taɓa zuwa maƙota na samo wa Humaira tuwo saboda ba ni da abunda zan bata, amma ban taɓa faɗawa kowa ba haka na jure wannan ƙuncin ya zo ya wuce.

Ranar Asabar ya kama rana na biyu da aka yi babbar Sallah, da daddare Humaira ta fara zawo har zuwa asubahi tana abu ɗaya, ga Umar baya gari, yarinya ta dinga suma tana sanƙarewa gashi mun kwana ana ruwan sama gari yayi mugun sanyi, a daddafe nayi sallar asubahi, dana idar na rungumota ina shafa mata addu'a, sai da gari ya sha yayi haske kafin na goyata, na ƙullawa Amir Nama a leda na kama masa hannu muka fito, sai na tsallakar da shi titi na rakashi har layin gidansu Babanshi, nace masa yaje gidan ya faɗa musu Humaira ba tada lafiya na kai ta asibiti, ya na zauna a nan sannan su bashi abinci bai karya ba, yace to sai na wuce da Humaira asibitin Dutse, kuma ban da kuɗi sai ɗari biyar da aka bawa Humaira barka da Sallah jiya sabbin 'yan hamsin, a ciki nayi kuɗin mota ya kai ni hamsin saura ɗari huɗu da hamsin muka shiga cikin asibiti, sai dai bayan na samu nurses nayi musu baya ni suka ce sun gama ɗibar masara lafiya da zasu duba saboda corona, dan ba a daɗe da gama cutar corona ba sannan ana kan dokar taƙaita cunkosa a gari. Tunda suka faɗa mini haka hankalina ya tashi ga yarinya sanƙare a bayana kanta ya langaɓe kamar ba tada rai, da wani ma'aikaci ya fito daga wani office ya kalleni sai yake cewa.

Anya wannan yarinyar ma tana da rai kuwa.?

Naji gabana ya yanke ya faɗi, amma ban iya ce masa komai ba, sai yace ya kamata a duba ni amma cikin nurses ɗin nan babu wanda ya kulani har ya wuce, ina tsaye sai na tuna da wata mata da muke shiri da ita lokacin dana yi yayin kawo Humaira Immunization, Dan haka sai na wuce ɓangaren yara na tambayi matar, aka ce an mayar da ita sashin da ake kwantar da manyan mata, sai na nufi ɓangaren na je na sameta, muka gaisa na kwanto mata Humaira ina cewa.

Wlh yarinya ta ce ba lafiya amma sun ce min sun gama ɗibar marasa lafiyan da zasu duba yau.

Ta amsa Humaira ta soma faɗa tana cewa meyasa ba zasu amshe mu ba ko basu ga halin da yarinyar ke ciki ba, ban ce mata komai ba tace.

Amma yarinya nan ta daɗe ba tada lafiya.?

Wlh a'a jiya ma mun je yawon sallah da ita lafiya ƙalau, cikin dare ne ta fara zawo.

Duk da haka gaskiya ba tada lafiya.

Ta daɗi haka sai ta yi rubutu a paper ta bani na koma ward ɗin yara, na amsa tare da rungume Humaira na tafi can, nurse ɗin dana bawa takardar ta dinga masifa wai bama zuwa asibiti sai ciwo yaci ya cinye kafin zamu zo lokacin abun yafi ƙarfinsu, ban ce mata komai ba ta gama surutunta, suka amshe ta sai suka cire mata rigar jikinta, suka ce in fita da ita mu tsaya cikin ruwan sama da ake yin yayyafi ya taɓata, na je da ita na tsaya ruwan ya fara taɓata sai naji ta fara ajiyar zuciya, sai hakan ya tabbatar mini da sauran ranta, bayan mintuna suka kirani suka yi mata allura sannan suka ce an bamu gado zamu biya dubu goma kuɗin komai da komai, nace to, na koma gefe na saka mata riga ina tunanin yadda zanyi dan ba ni da kuɗi, dan haka na ciro wayata a jaka na soma kiran Umar bai ɗaga ba, sai da nayi masa kira sau goma amma banda arzikin da zai ɗauki kirana, ganin ba sarki sai Allah sai na kira ƙaninsa Jafar na shaida masa Humaira ce ba lafiya sannan na kira Umar ban same shi ba kuma ba kuɗi a hannuna, sai yace wai in ɗaukota in kaita asibitin Barau Dikko saboda can yake aiki, nace masa to kawai dan ba zai yiwu na je ba tunda ga halin da yarinya take ciki, sannan bani da kuɗin motar zuwa, dan haka sai na kira babanmu na shaida masa halin da muke ciki yace mini shi ma baya gari yaje Sokoto, amma bari ya kira Mamanmu ya shaida mata sai ta ranto ko dubu biyar ne ta kawo min, nace masa to tare da godiya muka aje wayar.

Akwai sauran cakwakiya

Humaira tana rayuwa kuwa.?

Ya zaman auren Farida da Umar zai ƙare.?

Farida tana samun nasarar ƙarasa karatunta kuwa.?

Iyayen Farida sune asalin waɗanda suka haife ta kuwa.?

Ya alakar 'yan uwan Umar yake ƙarewa da Farida.?

Iyayen Farida suna dawowa daga rakyar Umar kuwa.? Sannan anya zasu ɗauki mataki akansa kuwa.?

Anya Farida tana farinciki kuwa a rayuwarta.?

Umar kuwa yana girban abunda ya shukawa Farida.?

Akwai tambayoyi da yawa amma amsarsu suna cikin KOMAI YAYI FARKO Book 2.