Chapter -- 03
****Namiji Ƙanin Ajali****
=Page 03
Hhmmmmmm, Nasauke ajiyar zuciya bayan na gama wannan tunanin na juyo na kalleta bayan na rufe marfin tukunyan ɗumamen tuwon dana ɗora a wuta sannan nace..
" Hama ke ba yarinya bace ,bazan ce miki kishiga ko ki fita harkar ta ba, kinsan abun da ya dace da wanda bai dace ba, a duk faɗin unguwar nan ba wanda be san halin hassana ba ko ince ke zaki bada labari tunda kina zauna gida ɗaya da its,bance kuyi gaba ba amma ki kiyaye, zaman majalisa kuwa kada ki fasa bakiga komai bama"
Da ganan naci gaba ayyukan gabana dan damuwata tafi wannan, ina kallon bature ya fita ko kallon inda bayyiba nima na watsar dashi , bayan na koma ɗakin da asuba baccinsa na samu yanayi hankali kwance banyi mamaki ba tunda ni ƙunsa min baƙin ciki dole yayi baccinsa bashi da wata damuwa,yadda ya fitannan kuwa nasan yau ko Naira biyu bazan samu ba balle ɗari biyu irin na jiya,shi da allah, na faɗa a raina dan hakki ne a kanshi dan bazan yafe ba ,tunda baya rasa bane zalinci kawai irin na wasu mazan....
Ehhh wasu mzan dan ba duka aka taru aka zama ɗaya ba ,kuma badan natashi na ga yadda mahaifina keyi da mahaifiyata ba da nayi musu kuɗin goro.....
Ina gama aikin na sa hijabi na fita maƙota gidan maman balki,danna karbo surfen gyaron furan siyarwar da sukeyi ,bayan na karba ina shirin fita naji tana cewa "balki ki tashi kije tambayo ladidi inkawo aikatau ɗin furar ne dan aiki ya min yau bazan samu yi ba". Da sauri na juya ina faɗin
"Maman balki ai har furar sai na miki duka sai haɗa ki biyani"
"Kin iyane?" ta tambaya
"Eh na iya sosai ma" na bata amsa
"To ai shikenan ma kiyi kawai sai faɗa kuɗin gaba ɗaya idan kingama sai a ki kawo ,ki dai yimana akan lokaci"
"To, insha Allah" nace kawai daganan na fita naje na sunkuya aiki ina cikin aikinne masu wanki suka kawo , nan karba na ajiye a gefe dan Ina gamawa zan sauka a kanshi, ina wannan na shiga wacan, aikin kenan kullum ba dare ba rana kullum ba zama an saci Dan barawo, ban ɗauki lokaci ina ba na gama na wanke na shanya na hau wanki,ban daɗe ina wankin ba kasancewar ba yawa sosai kuma ba masu datti bane dan na maza ne , dan bana karbar wankin mata musamman masu ƴaƴa saboda mata sai su kawo miki kayan yaransu da kamar ƙwato a bakin kura tsabar dauɗa ,kuma mata tazo ci mutuncinki wai kayanta bai fita ba ,watama daga zan kawo kudin shikenan baki sake ganinta sai ta fara tunanin kin manta,wata tsabar rainin wayo harda pant da bra ɗin da sunfi sati a jikinta duk zata hada a kayan wanki,kai wata ma harda sauran stain zaka gani a jiki duk a kayan wanki wani bra din sai ƙarnin mama ,ni kuwa na daina karba dan Ina aikin kodago ban zama jaka ba kuma bana juran walaƙanci,shiyasa nakeyin na samari da maza magidanta wani lokaci ma harda guga nakeyi idan bani da aiki da sosai,haka dai na karasa yinin ranar inyi nan-inyi can,da kudin hanuna na hada siya talia leda daya na dafa mana nida su layla, duk da ba wani cin abinci takeyi ba dan saidai Tasha madara ko Lipton Dan bata shan tea da madara ,husna ce mai cin tuwo da kuli-kul itama ba sosai ba ,Dan ban koya musu mugun ci ba,Ina gamawa nasa a kula na rufe na kai daya dakin kujeruna da sauran tarkace na na rufe kofar, dan bazan ba bature ba, da dai nayi amma yanzu bazanyi ba.....Ina sallar magariba ya shigo sai kuma ya fita, nidai ina zaune ina addu'a ko kallonshi banyi, sai gashi ya shigo yana yarfar da ruwa da alama alwala yayi.
"bani sallaya" ya fada yana gyara tsayuwa da alama sallah zaiyi,
Na dauke kai batare da na nuna naji mai yace ba....Dan abu ɗaya daya ke daɗa cimun rai da bature shine rashin sallah a jam'i ,musamman asuba , magariba da isha'i, baya jam'i sam, ya gwammaci ya dawo
gida yayi wani lokaci ma har azahar, kamar dai yanzu gashi ana sallah a masallaci kuma daga waje yake amma ya dawo gida zaiyi ,tun farkon auren mu har yanzu , nayi nasiha , nayi borin ,nayi fadan amma abanza ko a jikin shi wai an tsikari kakkausa da har azahar da asr yake dawowa sai da nayi da gasken gaske.....
"Wai ba magana nake miki ba kinyi banza dani ga ɗan iska ko?", Maganarshi ta katseni, Takaici ya hanani ce mishi komai kuma na hana sallayar na cigaba da jan carbi na....
"Ina miki magana kin min banza ko , wai halima me kika ɗauki kanki ne", ganin ba zai barni nayi damuwan gaba na yasa na tura mishi daddumar batare na ko kalle shi ba ,
"Wato ga ɗan banza mara aikin yi shine ina miki magana sai sanda kika ga dama kafin zaki kula ni" nan ya hau faɗa yana ta magan ganu iri-iri,ta inda yake shiga bata nan yake fita ba,ganin zai soma minkwakwazo kuma mutane zasu iya jinmu yasa nace ,
"Dan allah kayi sallahr ka lokaci yana wucewa" haba kamar na ƙarawa wuta fetur , ya hau cewa nace mishi jahili mara addini... Nikam zuwa yanzu ai nadena mamaki juya magana irin nashi , ganin abin nashi bana naƙare bane yasa na miƙe, dan mamakin haƙurin da bansan ta ina na koyo shi ba nakeyi dan bana barin sai ta kwana amma yanzu tunda bature ya tsiro wannan halayen nake haƙuri bazan ce ga sanda haƙuri ya shige ni ba , ko dan yanzu na haihu ne na zama uwa ohooo, amma zuwa yanxu ya kaini bango dan bzan iya dauke kai ba cikin hassala nace..
"Bature amma idan manta ba daddumar nan nawane ko? ", ban jira amsar shi ba na cigaba dan ba amsar nake buƙata ba nace,
"kuma ni bance maka jahili ba , amma kuma inka kira kanka da hakan bazan hanaka ba, sannan da kake wani dagiya akan dadduma ai mazan kirki mazan ƙwarai a irin wannan lokacin suna masllaci suna sallah , ba wai suna ɗaki suna a maƙale kamar amaren jego ba,suna masifa akan dadduma,ai duk namijin kwarai ba abinda zai haɗashi da daddumar matarshi sai nafila ko juma'a,kaima kaje can inda maza suke ,bawai kazo nan kana wani buɗe hanci kana wani kana kwa-kwazo akan aikin banza " Ina gama faɗan hakan nayi waje dan ba ja-in-ja nake nema ba ɗayan ɗakin na shiga ,ina jiyo shi yana tayi ni dai ban bi ta kanshi na kulle ƙofar dan nasan zai iya biyoni dan ba damuwarsa bane mu kwana muna mahawara, ba sake fitowa zanyi ba sai gobe kuma ,na riga shigar da abinci na ina da alwala sallar isha'i ya rage min kawai, su husna kuma ɗakin inna lami , dama watarana a can suke kwana dan ita ta yaye su ma, hakan yasa bani da damuwar da zai fito dani ba idan ba fitsari ba, shikuma bai zama lallai ba haka tunani suka taru suka min yawa har na rasa Wanda zanyi ma, dana sanin auren bature kuwa nayi shi yafi cikin tirela,koda yake tun ba yau ba nakeyi kuma ina kai , da haka nayi sallar Isha nadora daga inda na tsaya,dan ko abincinma banci ba, haka tunani suka cika min kaina, ina wannan ban gama wannan ya shigo, addu'ar allah ya min mafita mafi alkhairi kawai nakeyi a zuciyata ta da fatan Allah ya amsa addu'ata , haka na tasa tunani a gaba har shugaban barayi na duniya International yayi gaba dani ba tare da na shirya ba........
Masu karatu ayi min afuwa zamu dakata sai mun haɗu a page na gaba ina godiya ga duk masu karatu allah ya barni daku , much❤💓💕💖💗💙💛💜🖤💝💟💚 ƙauna to you , your own har kullum da ko yaushhe (Amdeey Tejj) I love u na gaban kawatance....
Pls comment and share dan bani ƙwarin gwiwa na gode 🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻 sai kun jini .....
Good Bye👋👋🏻👋🏼👋🏽👋🏾👋🏿👋🏿
See 👀👁👁👁 U next time