7
by @mahmazee
Karfe bakwai da rabi suka doko sallama main falon gidan sai dai ba kowa a falon, hakan ya sanya kai tsaye suka nufi uwar ďakar Dede, wacce ke zaune kan sallaya da alama tun da ta sallame sallar magrib bata daga daga gurin ba, da qur'ani hannun ta pieces tana dubawa..
Shigowar su ya sanya ta kai aya tana amsa sallamar su tare da zare farin gilashin da ke idon ta na Karin karfin gani
Kan center carpet din da ke dakin duka suka zube da yake itama kan carpet din tayi shinfidar ta, fara'ar fuskar ta ta fadada a lokacin da take fadin "yan ukun baba Dr"
Murmushi suka saki dukan su, ba yau Dede ta Saba addressing na su da yan uku ba, a duk lokacin da zata gan su haka a tare su uku zaka ji ta kira su da yan ukun baba Dr.
Gaishe ta suka yi Amal na fadin "mun shigo muyi muku sallama Dede inshaAllah this week zamu koma school"
Dede tace "za'ayi muna halin bakunta kenan, toh Allah ya tsare hanya ya kuma dawo muna daku lafiya" duka suka amsa da ameen
"Shin aji nawa ake yanzu" Dede ta tambaya
Amna ta amsa da "300 level muke yanzu Dede"
Dede ta kalli inaya da mamaki kan fuskar ta take fadin "ya akayi haka, na dauka duka tare kuke ai"
Inaya ta murmusa tana yiwa Amna hararen wasa take fadin "perks of private universities kenan Dede, tare fa muke amma strike ya sa yanzu suna gaba da mu, amma fa da semester daya ne kawai"
"Ai wallahi ko semester daya ne na gaba yayi gaba" Amal ta amsa cikin dariyar mugunta, Dede ta kalle su cikin burgewa a lokacin da inaya ke kai wa Amna duka tana goce wa, a ire iren wadannan lokutan ta kan ji ta a yanayi na fulfillment, ta kan yi alfahari da tarbiyar da suka yiwa yaran su, ta yadda suka ta so cikin so da kaunar juna ba nuna banbanci.
"Hakanan wanda ya girme ka ko da hour daya ne ai yana gaba da kai Yawwa" Inaya ta amsa itama domin tana gaba da twins din da wata uku, idan gardama ta surnuqe tsakanin su wadannan watanni ukun inaya jin su ta ke kamar shekara uku yayin da yan biyun har Ila yau sun ki yarda da tana gaba da su, domin in ta wayo ne, wayon su ya girmi na inaya nesa ba kusa ba.
Da haka dai suka yiwa su deden Sallama suna da da jaddada gaisuwar su ga uncle Ubaidu idan ya dawo da yake baya gidan, har harabar gidan suka raka su cikin kewar juna da suke ji tun basu yi nisa da juna ba.
Washegari Karfe takwas saura a jami'ar Bayero tayi mata wato BUK, direban Abba ya sauke ta kamar yanda ya Saba, shi ke ajiye ta kuma ya zo daukar ta unless suna tare da abba ko wani uzuri ya ta so gida ta kan shiga adaidaita.
INAYA UBAIDU BELDO shine cikakken sunan, matashiyar budurwa yar kimanin shekara goma sha takwas a haife, dalibar BUK university Kano da ke karantar telecommunication Engineering .
A duk fadin duniyar nan bata da kawayen da suka wuce Amal da Amna, hakanan bata da shaqiqan da take sharing damuwar ta ko sirrinta da su da ya wuce wadannan biyun da shaqiqiyar ta sakina.
Sai dai wannansabon al'amarin da ta ke ji a tattare da ita, wani abu ne da bata taba experiencing ba, wani abu ne da ita kanta bata san da wane suna zata kira sa ba, wani abu da koma meye abu daya ta ke da tabbaci a kan sa shine it has to do with yayan ta EMRAN ALIYU BELDO.
Babban damuwar inaya a halin yanzu bai wuce yawan tunanin da take samun kan ta a ciki ba, tunani ba na kowa ba face na Emran Beldo da ya addabe ta, ya cika ta, ya Hana ta sukunin kan ta, Kamshin shi, Muryar sa da amon ta, kwalisar sa da yanda yake komai kamar ana yi mishi dole su suka taru suka yiwa Inaya tsaye a rai, har duk wanda ke tare da ita zai fahimci akwai abinda ke damun ta a kwanakin.
Babban tashin hankalin ta bai wuce Daren da ta tashi da mafarkin sa ba, ranar har da hawayen ta domin dai ta rasa abinda ke damun ta, tana so ta kira Amna ko Amal ko yaya ne ta ji wani abu dangane da yayan su, haka kawai ta ji tana son sanin wani abu about him, amma ta san halin sharri irin na su, nan da nan zasu yi mata wata ma'ana, yayan su Faisal ma da ta ke shiri da shi sosai don yana da son wasa da tsokana haka nan ta su ta zo daya cewa suke son ta yake yi, haka ma Sakina ke fada wai kila yar gida zasu yi bare da ta kawo kan ta da kanta, sai kawai tayi shiru abin na cin ta ita kadai.
Hankalin ta ya rabu gida biyu daya yana tare da karatun ta yayin da Dayan ya ke a gurin Emran Beldo.