INAYATUFree

ArewaPen original

RomanceFreeOngoing

INAYATU

  • 1views
  • 24chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

Sample · Shinfida

  BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM.     This is my first novel, I hope you enjoy reading it as much as I enjoy writing it!!!!!!!         "Allah idan baki fito ba INAYA wallahi zan tafi in bar ki, sai dai ki samu adaidaita ya ajiye ki wannan wane irin shiririta ne"       Wata matashiyar muryar ta fada tana ratsa dodon kunnen INAYA wacce ke zaune gaban madubi ta zurawa farar fuskar ta ido, ba don zata yi kwalliya ko wani kyale kyale na yan mata ba, aa sai don tufafin ta da ta fitar zata saka da ta manta bata yiwa turaren da ta Saba ba.      Kwalliya ba dabi'ar ta bace hakanan kyale kyale ba damun ta yayi ba idan ba wanda ya zama dole ba, amma a rayuwar ta bata wasa da turare  idan akwai abinda take so har kasan ranta na gyara to turare ne ko wane irin ne kuwa, be it na fesawa na gogawa na turarawa, deodorant ne, oils ne Sam bata wasa da shi.    Toh wannan Karon ma bata chanja zani ba lace din da ta fitar yana kan kabbasa yana tsima da turaren bakhoor na kajiji da farce     da ba don da mantuwa ba da tun safe zata zauna tayi turaren kayan ta a natse yanda ya kamata ba yanzu da Sakina ta sanya ta gaba da takura ba.     Sakina da ke jinini tun dazu ta kalli mahaifiyar su tace "kin gani ko, kin gani ko Dede INAYA tana saka mu latti bayan wanda muka yi"     Murmushi Deden ta su tayi ba tare da tace komai ba, halin INAYA na sanyi da shiririta tuni ta Saba dashi kuma tuni ya daina bata mata rai,              Sakinan ma tana tunanin yan shekaru biyun da tayi ba tare da su ba ne ya sanya ta manta halin INAYA wanda tun tana karama, fada duka da kwankwami bai saka ta chanza ba.      A azurce ta dauki kayan ta ta soma kiciniyar sakawa duk da turaren bai gama kone wa ba, duk da ba haka ta so ba amma ya zata yi da kwankwamin Sakina.      Dama tun tuni ta shirya, ta kuma gyara kan ta wanda shi kadai ta ke iya tsayawa bata lokacin ta ta gyara, doguwar straight gown din ta sanya tana zuge zip din rigar sama, da ta zauna das a kan dan jikin ta zaka iya sanya ta a cikin jerin siraran mata domin bata da kiba Sam       dan lafaffen cikin ta ya bi rigar ya kwanta, sauri sauri ta daura dankwali ta sake feshe jikin ta da daddadan turaren ta black opium na yves saint laurent, ita kan ta ta sani Allah yayi mata jaraba da kamshi.      A lokuta ire irin wadannan deden ta kan gaya mata yanda ko sanda take karama idan akayi mata wanka aka manta da turare to ta dinga fitina kenan har sai an fesa mata.       Mayafi ta Dora kan kayan wanda ya tafi ta kalar suturta sosai kalar dark blue mai cizawa wato bold blue, ta kawo takalman ta masu saukin dundu...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters24
premium0

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play