Chapter 1
💋 *GUGUWAR FANSA* 💋
*Romantic*💋
*Love*🌹
*Story*💃
*BOOK 1*📚✍️
*SADAUKAR WA*
*STER LADY*
*GODIYA*
Dukkan godiya su tabbata ga shugaban halitta annabi Muhammad (S.A.W) wan da ya hallaccine ya hallicci dukkan abin dake cikin duniya ,Ina godiya ga Allah suba hanaw wata ala Wanda ya bani baiwa da ikon kawo muku tittattafai dadama ,to ayau ma Nasake samun wata damar da Zan kawo muku kayataccen littafina me suna 💋 GUGUWAR FANSA 💋.
*KIRKIRA*
Littafin 💋 GUGUWAR FANSA 💋 kirkirarene Kuma littafin 💋 GUGUWAR FANSA 💋 yana farune agaske ba hasashe bane Ina fatan ga duk wadda ta sani damar karanta littafin taga yayi shige da rayuwarta toh a rashin sanine,Kuma duk wadda taci Karo dashi ta karanta toh tayi kokari ta Yi amfani da abin da littafin ya fadakar akai.
*NOTE*
Ban amince wani ko wata ya samu damar karanta min book ta hanyar yimin audio batare da neman amincewa ta ba ,dukkan Wanda ya karanta min shi audio batare da yasanar Dani ba zanyi Shari a dashi domin abimin hakkina.
💃MASOYANA NAKUSA DANA KEWA KUNA INA!! KUFITO KU GYRA ZAMA DOMIN KWSAR WANAN LITTAFI MECIKE DA DINBIN ABIN AL AJABI, FADAKARWA,TARE DA NISHADANTU WA DA SHI, KAR KU MANTA TAKU HAR KULLUM ME NISHADANTAR DA KU HAFSAT UMAR DANGORO 💪
GODIYA TA MUSAMMAN. GA YAN UWA DA ABOKAN ARZIKI HARMA DA MALAMAI NA MASU KARAMIN KWARIN GYWA DA MA MANYANA DA WADAN DA SUKA KASANCE SU GARKUWANE AGARENI MAHAIFIYATA INA MIKA GODIYA AGAREKI UMMANA ,AL,UMMA MA ANA MASU BIBIYATA A TELEGRAM, WHAT'S APP, TIKTOK, AREWABOOKS,FECBOOK, AREWAPEN WATTPAD DA MA SAURANEU .
LITTAFIN 💋 GUGUWAR FANSA 💋 ZAI DINGA ZUWA MUKU DAGA KARKASHIN KUNGIYAR 💪JARUMAI 📚WRITAR'S ASSOCIATION✍️
Marubuta masu aiki da fasaha da ilimi domin ilimantar da Al,umma.
*NICE TAKU HAR KULLUM MARUBUCIYAR *✍️
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
GUGUWAR FANSA
_*BY*_
_*HAFSAT UMAR ƊAN GORO*_
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
_*JARUMAI💪🏻WRITER'S ASSOCIATION📚*_
_*Marubuciyar*_
1- Burina Mu'azzam
2- Ba Mahaifiyata bace
3- Babana ne sila
4- Ummu Amani
5- Amatullah
6- Zuciyarta
7- Mace Rayuwa
8- Rayuwar Ƙasƙanci
9- Mar'atussaliha
10-Babbar sakayya
11-Afnan mata Maza
12-salwa
13-rainon yaro
_And now_
🔥🔥GUGUWAR FANSA.🔥🔥
MALLAKIN
HAFSAT UMAR ƊAN GORO A-K-A (H.U.D)
بسم الله الرحمن الرحيم
E_______________1
Gabaɗaya ilahirin family tsaitsaye suke a tsakiyar parlon, kana ganin fuskokinsu zaka san suna cikin tsananin tashin hankali. Dikkansu kallonsu ya ta'allaka ne a kan waje guda, rabi da kwatan mutanen dake cikin parlon sanye suke da sleeping dress, da alamar yanzu suka farka daga barci.
Kana ganin parlon kasan ba gida ne na ƙananan kai ba, dan ya ji komai na more rayuwa, sai dai kuma kaca-kaca yake tamkar an yi yakin duniya na uku a cikinsa, ga wani glass tarwatse a ƙasa saman farin tiles ɗin.
Kowa yai tsuru-tsuru alamar sun sha jinin jikinsu.......... "Hunaish baka son gaskiya kwata-kwata, kome zaka yi sai dai ka yi, amma sai na faɗa maka gaskiya!". A cewa wani kyakkyawan matashi namijin gaske dake tsaye a tsakiyar parlon, wanda da alama fushi a kan fuskansa, dan har wani huci yake yi, kyakkyawan gaske ne ajin farko, kuma cikakken namiji ne.
"Safran bana son gaskiyan okey?". Wani matashin da ya bawa dikkan jama'ar cikin parlon baya ne ya faɗi wannan magana, kuma dikkan jama'ar parlon shi suke kallo, da alamar zafa a cikin muryansa, dik da muryan nasa akwai sanyi da natsuwa, amma akwai kaifi a maganar, dik da cewa ya juya baya ba'a ganin face ɗinsa, lallai tsayayyen namiji ne kuma cikakke, yana sanye da Hoodie launin milk color wanda ya sanya hular kayan a kansa!. Yana kai karshen maganar tasa ya wuce cikin zafa ya haura staircase dake a gabansa.
Kwace kansa daga rikon da aka yi mashi Safran yai, cikin fushi ya ce. "Ko Hunaish zai kasheni sai na cigaba da faɗa mashi gaskiya!". Ya kai karshe tare da nufar in da Hunaish ɗin ya yi. Da sauri wani matashi ya sake rikesa yana faɗin. "Please Yah Safran ka kyalesa haka, dan ALLAH kada ka bisa, zai iya yi maka illah".
Kokarin kwace kansa ya fara yi yana faɗin. "Mahvir ka sakeni, idan ku kuna tsoronsa ni bana tsoronsa, kuma in har bami faɗa mashi gaskiya wannan so sonsa muke yi ba, and yaushe kuke tinanin zai sauya idan bamu ƙoƙarin mai da shi kan hanya?". Cikin faɗa ya faɗa.
Ƙanƙameshi da kyau Mahvir yai yana faɗin. "ALLAH Yah Safran ba zan sake ba, ka rabu da shi sai ya huce sannan ka faɗa mashi bai kyauta ba da ya mari Hajja, tamkar uwa take a garemu, meyasa zai mareta? Da wannan hannun nasa irin na samudawa, ga shi ya sumar da dattijuwa a banza".
A daidai lokacin wata kyakkyawar mace mai zubin dattaku da kamala dake tsaye a gefe ta kariso in da suke, hannun Safran ta rike, cikin sanyin murya ta ce. "Muje ɗaki mu yi magana"...... Tana yin magana kowa dake a cikin parlon ya natsu tsit, dan suna mugun ganin girmanta, suna darajata, Mummy kenan, uwar gidan King Elyan Abdul mutallab, mace mai natsuwa da sanin yakamata, kowa a gidan nata ne, bata da faɗa kuma bata son hayaniya, gata kyakkyawar gaske.
Wai su waye su ne ma? Mu ji a ina muke tukun nan mu cigaba!.
MASARAUTAR DAR AL-MAJD.
Masarauta ce mai ɗinbin tarihi da a yi fice, masarauta ce wacce ta tara tarin tattalin arziki, warriors majiya karfi mara tsoro, basa ja da baya ga yaki dik girmanta, suna da tarin bayi da masu yi masu hidima, masarauta ce dake ɗauke da manyan fadoji har guda biyu, ga ƙanana-ƙananan gidaje da manya na jama'a da sauran wakilan fada.
Tana cike da manyan gine-ginen zamani da na gargajiya a sassan cikinta, dan girman masarautar ta zarce yadda kuke zata. Akwai wadatacce wutar lantarki da dik wasu abubuwa na more rayuwa.
Sannan baya ga fada akwai babban royal square inda ake bikin sarauta ko wani party dai haka. Baya ga haka akwai provinces, ƙananan ne yankuna, kuma kowanne yana da hakiminsa. Akwai gonaki, masana'antu, makarantu, da asibitoci na zamani dik a ciki.
Kowanne yanki yana da salo da al'adarsa ta musamman amma suna biyayya ga masarauta, da umarninta suke komai.
Katafaren fadar sarki tana a tsakiyar masarautar, kofarta launin zinari da farin karfe, an zuba mata kwalliya ta sarauta ga kuma duwatsun lu'ulu'u a jikinta, katan kofa ce mai kauri da girma.
Cikin fadar yana da balain girma sosai. Akwai ɗakin karɓar baƙi mai ɗan girma da haske na manyan fitilu chandeliers. A gefe akwai ɗakin shawarwari inda ake tsara dokoki masarauta. Ɗakin zinari, inda ake adana kayan sarauta da dukiya.
A waje gefen fada kaɗan akwai royal garden mai matuƙar girma, ga kuma katan swimming pool a cikinsa, ta ko'ina ka juya a cikinsa kyawawan shuke-shuken furanni ne masu ɗaukar hankali ga ƙamshi mai kwantar da hankali.
Masarautar tana da arzikin na zinari, noma, fasaha da kasuwanci. Akwai Bankin Masarauta wanda yake sarrafa dukiyar ƙasa. Hanyoyin mota da jirgin sama sun haɗa masarautar da sauran ƙasashe.Tana da sojoji na zamani masu kare ƙasar.
Tsarin mulki, akwai Sarki! Majalisar masarauta! ministoci da masu shawara, then akwai kotun masarauta dan hukunci na adalci. Gefe guda majalisa dan jama'a mai ɗauke da wakilai daga yankuna daban-daban dan kawo ra'ayoyin mutane ta yadda za'a samu damar yi masu adalci.
Suna da kayan al'adun da suke sanyawa, kamar ace fulani suna da kayan yarensu, yaroba, kanuri, Hausa da sauransu dik suna da kayan al'adunsu, to haka suma wannan masarauta suke da nasu kayan al'adu. Sarki da sarauniya suna sanya rigunan sarauta masu launin zinari ko fari, suna ɗauke da ƙambun sarauta, sannan suna ɗaura alkyabba da rawani a kan kayan nasu. Dik wanda zai fito daga gidan sarauta shigarsa tana kasancewa ne na tail coat and thobe ga maza, mata abayas, dan suna da haɗi da larabawa. Daga wajen familyn sarki kuma suna shiga ne na wani irin kaya mai zubin A shape ga mata, mazansu kuma thobe.
Suna da bukukuwa na al'ada da suke yi a kowacce sati, akwai irinsu ranar sarauta, ranar ce ta tunawa da kafa masarautar. Sai bikin ranar tunawa da sarakunan da suka gabata. Al'adun suna haɗa zamani da gargajiya, kiɗa, rawa, abinci, tufafi masu kyau.
Sojojin masarauta suna amfani da makamai na zamani da tsarin tsaro mai inganci. Akwai jami'an leken asiri na musamman. Masarautar tana da tsarin sirri da doka da kowa yake binta dole.
Masarautar tana da ofisoshin jakadanci da haɗin gwiwa da sauran ƙasashe. Akwai cibiyar kasuwanci da tattalin arziki a wasu ƙasashe. Ana gudanar da taron kasa da kasa a cikin fadar sarki. Mutanen ƙasar suna rayuwa cikin walwala, lafiya da tsaro. Makarantu suna koyar da fasaha, ilimi da nagarta. Akwai gidajen tarihi da wuraren yawon buɗe ido masu kyau.
Royal Symbols, watau tutarsu takasance launi fari da blue mai bayyana iko da zaman lafiyarsu. Akwai gumakan tarihi sosai, musamman ma gawarwakin tsoffin sarakuna.
KING ELYAN ABDUL MUTALLAB shi ne sarkin wannan katafaren masarautan, sarki mai adalci da son talakawansa, yana da mata uku da yara takwas. Uwar gidansa gimbiya Lailarh tana da ƴa mace ɗaya, wacce kuma ita ce babba a kaf ƴaƴansa, tana da 30 years, tai aure da ƴarta ɗaya budurwa, sai ƴaƴa maza ƙanana da basu fi 15 and 18 years ba su biyu, matarsa ta biyu gimbiya Hoomair, tana da ƴaƴa mata guda biyu wanda ɗaya tana da 28 years, ɗayar kuma 26, dik suna gidan su basu yi aure ba. Sai amaryansa gimbiya Fateema dake da yara uku, ƴan biyu maza da a yanzu zasu kai 28 years a duniya, sai kanwarsu mace dake da 17 years, King Elyan kusan a tare ya auri dikkan matansa ukun nan, amarya da ta biyun a rana ɗaya ya auresu, ta ukun kuma tsakaninsu shekara guda ya aureta.
Sannan King Elyan yana da ƙani namiji ɗaya wanda yake da mata biyu da yara huɗu, uwargidansa yaranta uku, Safran, Mahvir da mace mai suna Farhana, ita kuma amaryan ƴarta mace ɗaya Fateema suna ce mata Bintoo.
A halin da ake ciki yanzu Hunaish shi ne babban ɗan King Elyan, wanda ya kasance mutum mai kafiya, taurin kai, taurin rai, zafin zuciya, fushi, izza da isa, baya da hayaniya, kuma baya son a shiga gonansa, dik gidan tsoronsa ake ji, harta iyayensa suna shakkar shiga gonansa, amma a baya ba haka yake ba, lokaci guda ya canza, a yanzu Safran ne kawai yake iya shiga harkansa idan yana magana, saboda Safran ɗin babban amininsa ne, a tare suka taso, suka yi karatu, suka yi komai, akwai shakuwa mai karfin gaske a tsakaninsu.
Mu koma cikin labarin........
Babu wanda ya motsa, sai shessheƙar kuka daga gefen parlon inda samha take zaune, tana sharar hawaye cikin sanyin murya, fuskar TA kallo Daya zakai mata kasan Tana cikin damuwa. “Wallahi ni bana gane Yah Hunaish ɗin da muka sani... wannan ba shi ba ne, kamar wani ne ba shi ba, lokaci guda yah hunaish ya canza why?.”
Kowa ya juyo gareta, amma babu wanda ya iya cewa uffan, domin kowa ya san maganarta gaskiya ce. Hunaish ya zama wani iri, yana yin abubuwan da basu dace da sunan ɗan sarauta ba gaba daya fishi da zafin Rai zai hauka tashi.
Mummy ta janye hannun Safran zuwa sama da ƙaton hallway ɗin gidan. Fitilu masu sanyi suna haskawa, bangon yana sheƙi da duwatsu masu launin blue da fari, ƙamshin lavender yana tashi daga ƙananan furanni da aka jera a cikin gilashi.
A lokacin da suka shiga cikin wani ɗaki mai nutsuwa wan da ya dauki shiru ga kanshi ko taina tashi yake, Mummy ta ja numfashi a hankali kafin ta zaunar da Safran. “Safran,” ta fad'a cikin muryar dattaku da nutsuwa, “ban hana ka faɗa masa gaskiya ba, amma ina son ka koyi lokacin da ya dace ka faɗa. Yanzu zuciyarsa tana cikin rikicewa, kana kallo sai ya sumar da hajja daga mari guda Daya kawai, shin meyasa zaka tun kareshi a wannan lokacin so kake ya illata ka?" "Uhm am..."ya isah haka safran, kada kace min komai" tayi maganar tare da Dora hannunta na dama a kan keykewan labbansa, alamar yayi shiru..
Ba tare da Safran ya sake yun kurin cewa wani a buba ya juyar da kansa gefe guda hadi da furzar da iska daga bakin sa ya dafe kansa, idonsa cike da hawaye masu zafi. “Mummy, kin gani da idonki yadda ya mari Hajja, har ta faɗi! Wallahi ko ya zama sarki, An ya hunaish zai iya adalci Kuwa?. Na tsani ganin yadda yake wulakanta mutane kamar baI San muhimmancin d'an Adam ba, shi komai zafin zuciya da takama haba mummy, na San cewar Ammi a yanzu zuciyarta kamar ta fashe sabi da bakincikin abin da hunaish yake, da mai za muji da ciwan haukan da yasamu Huzair ko Kuma da fitinar Hunaish?.”ya Kai karshen maganar tare da hade girar sama da kasa a Lamar ransa ya baci.
Mummy ta dafa kafadarsa. “Ka yi haƙuri ɗana. Ina da tabbacin akwai wani abu da ke damunsa. Hunaish ba irin wannan yaro bane da na raina ,ni kaina nasan cewar hunaish ya canza ba haka yake ba, yanzu ina son ka tashi ka huce part din ku zuwa anjima kafin Nan ya sakko daga dokin zuciyar da yake Kai, in yazo daga baya sai ka dawo, Dan nasan a yanzu ko mai Marta ba bai da karfin guywar karasawa Inda Hunaish yake , idan ka koma part din ku ka gyda min da mamma" Kai kawai Safran ya gyda yayi mata sallama ya fice batare da ya sake cewa komai ba.
Bayan fitar sa mummy tayi shiru kana ta runtse idonta tana tunanin yadda komai ya sauya lokaci guda, a hankula a kasan zuciyarta ta furta"innalillahi wa Inna ilaihirraju'un, Allahumma ajirni Fi musibati".
A parlor kuma, Mahvir ya dawo kan kujera yana kifa kai a gwiwa , Inda samha take zaune Tana rera kuka, a hankula ya furta a kasan zuciyarsa “Ya Allah ka shiryashi,” ya furta cikin rauni. Farhana ta ƙaraso kusa da shi tana cewa. “yah Mahvir, ka tuna lokacin da yake dariya da mu a baya? Yanzu idan ya shiga parlon, kowa yana tsoron motsawa. Me ya same shi?”
Mahvir bai amsa ba, sai kawai ya ce, “Tun ranar da ya dawo daga tafiyar nan da sukai tare da Yah Safran , komai ya canza. Yana dawowa, sai abubuwa suka fara ɓaci a gidan nan.”
Dukkansu suka kalli juna, idonsu cike da tambayoyi da tsoro.
A saman bene, Hunaish ya tsaya a gaban mudubi yana kallon kansa. Idonsa yakumbura, fuskarsa cike da gajiya da baƙin ciki. Hannunsa da ya mari Hajja yana rawa, kamar yana jin zafin abin da ya aikata.
Ya rintse idonsa, numfashinsa yana nauyi. A hankula Rai a matukar 'bace ya dunkule hannun a fusace, ya kaiwa bango duka Yana huce, hadi da sakin wata razananniyar kara wadda ta kara tada hankalin su samha dake zaune a parlorn kasa suna jimami, lokaci guda karar ta daki dodon kunnen su, can Kuma sukaji shiru.
Mikewa samha tayi da sauri zata nufi saman Mahvir yayi saurin rukota "why! yah Mahvir ka sakeni kada d'an uwana yayi wa kansa illah" girgiza mata Kai yayi Sannan ya soma mata magana cikin nutsuwa "samha!" Kada ki manta mumafa muna son yah Hunaish okay, Try your best to control yourself, because if you react out of anger, it will become a fault in his eyes, ki saurareni" ya karasa maganar Yana zaunar da ita a kan kujerar hadi da bubbuga bayanta "“That’s enough now.”
Dai dai lokacin Ammi da gimbiya Hoomair wadda aka Fi sani da Mahmy, lokaci guda suka karaso gurin a tare, Rai a matukar 'bade Ammi ta daga kanta sama hadi da furzar da iska daga bakin ta Tana mai tauna labban ta,A Lamar ranta idan yayi dubu ya baci, gaba ki daya bakin ciki da takaicin abin da Hunaish ya aikata ya isheta, kan tane ya soma juyawa bakin ta ya soma matsawa da ker ta iya kallon mahvir wan da yake zaune ina nazarin halin da Ammi ke ciki ,kamar daga sama yaji Ammi tayi maganar "Mahvir!..... Ina shi yayan naku yake?".......... Tayi maganar a takaice fuskarta dauke da alamar bacin Rai.
"Yah Hunaish Yana dakin sa...." Abin da ya fada kenan a takaice, Sannan ya Yi kasa da kansa Yana jiran tambayar da Ammi zata sake jefo masa.
"Mai ne abin da ya hada shi da hajja har ya mare ta?" Sosai TA zubawa Mahvir ida nunta masu kyau Tana nazarin sa, da Kuma jiran amsar da zai bata.
"Allah ya kara miki lafiya da nisan kwana!..... Ku karaso ku zauna maganar baza ta yuwu kuna tsaye ba, ya kamata ace kune a zaune ni Kuma adur kushe a gaban ku" ba tare da Ammi tace kala ba ta samu guri TA zauna, haka itama gimbiya Hoomair ta karasa Inda samha take cikin takun kasaita da Isa Tana Dan wani basarwa ,Sannan ta samu guri TA zauna.
"Ina sauraron ka"
Ammi ta fada a takaice Dan ita har TA matsu taji irin girman laifin da wannan dattijuwar ta aikatawa Hunaish har ya mareta da wannan basamuden hannun nasa.
"Ranki shi dade kin San dai shi yah Hunaish ba sai an masa wani babban laifi ba ma fusata yake ,kawai fa akan yace ta kawo mashi Cappocino ta kawo mashi Americano saboda bata ji me ya ce da kyau ba, baya buɗe baki ya yi magana da karfi, kuma idan ya yi ko baka ji ba ya maimaitawa, So tasan ko ta tambayesa ba zai sake maimaitawa bane, shi ne ta haɗo mashi Americano, ransa ya ɓaci ya bugi cup ɗin ya zube, ta tashi tana ƙoƙarin bashi hakuri ya maketa saboda tsabar masifa irin nasa".
Kai Mahmy Hoomair ta dafe fuskarta cike da bacin Rai tace "oh good...! Why Hunaish?" ta Dan ja tsaki, hadi da turbine fuska .
"Have you people checked on Huzair’s health today? Or is it that the storm has reached Hunaish’s side too?" Tayi maganar Tana kallon su gaba daya .
" No, my dear, honestly no one has gone yet, kowa Yana tunanin halin da yah ya jefa hajja" Mahvir ya bata Amsa a takai ce, fuskar sa tana nuna alamun damuwa.
"Let me go and check on that Hunaish myself okay".
Mahmy Hoomair ta mike ta nufi stapdin da zai sadata da dakin Hunaish..
Da sauri samha tace "Mahmy Noor Tana dakin" ta fada hadi da tsare Mahmy da idanunta "Noor Kuma... Toh mai taje yi ,ko sotake itama ya mata irin marin da yayiwa hajja?"...
Kai ta dago alamar tsorata da maganar Mahmy tadan rausayar da Kai "Dad ke nemansa" ta fada a takaice.
“Dad again, but why did your father suddenly get up and even say she should call him? Mahmy ta daga ido Tana tunani cike da mamaki bayyane a kan fuskarta.
"Well… that’s what she told us anyway, Amma mu haka ta fada mana " TA karasa maganar Tana kallon su farhana dake zaune a gurin alamar ,ai haka ne koh....
Kai kawai Mahmy ta daga ta cigaba da taka stapdin benan "bari na je na duba okay"..
Ita Kuwa Ammi tagumi ta Yi hadi da tallafar kumatunta masu laushi da sheki, ta tsurawa wani door ido ko kiftawa bata Yi, idanunta sun ciko fal da wata a zababbiyar kwalla mai dauke da zafi da yaji.
A hankula jiki a sanyaye babu kwari samha Ta dawo kusa da mahaifiyar tata hadi da dafa kafadar ta da hannu ,Tana Dan bubbuga bayanta a Lamar rarrashi "Am so sorry!..... Bana son ki cigaba da saka damuwa a ranki.... in fact kinga kina da hawan jini, so duk awannan abin bai ka mata ya cigaba da damun kiba ,please Ammi "I was just crying — did you hear?" Samha ta kara tallafo kafadar mahaifiyar ta tana sake rarrashin ta cike da damuwa fal a fuskarta , Kai kana kallon yanayin yadda launin idonta ya sauya kasan cewar samha na cikin damuwa.
Kwallar dake kwance a idonta Ammi ce ta karasa sakkowa ,ba tare da ta iya ce mata komai ba ta saka hannu TA share hawayeta , bayan minti 1 TA dago ta kalli samha wadda ga ba daya ilahirin jikinta yagama sanyi, babu abin da take jiran sauraro daga bakin mahaifiyar TA irin abin da zata fada a yanzu, bata karasa tunanin ba ta tsinkayo muryar ta mai taushi da dadi cikin nutsuwa
“Get up, let’s go and check on Huzair.” Ammi TA mike ta soma ta kawa,duk da cewar hankalin ta ba a kwance yake ba, tafiyar nan dai ta kasai ta ba a fasa yin ta ba ,domin ita sarauta a jini take, Dan haka take takawa cikin Isa da nutsuwa kamar baza taka kasa ba.
Ita ma samha da farhana and Mahvir,bin ta sukayi a baya har zuwa bakin wannan 'kofar da dazu ta zuba mata ido....
Mahmy Kuwa Tana 'kara sawa bakin kofar ta jiyo muryar Hunaish cikin masifa "get out!......"
"Yah Hunaish, it’s Dad who asked me to call you…
Wani gigitaccen Mari da ya zuba mata, sai da yayi sana diyyar han tsilawar ta, tsabar furgicin da tayi ,tama rasa hanyar fita sabi da zugin da fuskar TA take mata,mikewa tayi da ker ta watsa a guje ,sai jitai tayi Karo da mutum ,ai da sauri ta kankane Mahmy jikinta narawa TA saki wani azababben kuka na azaba, Tana kara rike Mahmy....
"Are you mad at me? I was just joking — why are you sending me out of the room? Get out? Get out Noor okay"
Share & comments fisabilillahi