TATSUNIYOYI

Epi-four

by @zahratulqalam51

*TATSUNIYA*




By: _*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_



🌑🔥 KOGIN ASIRI
Episode 4: Zaɓin Duniya Biyu.



Daga nan Junaidu ya mutu. Ba mutuwa na ƙalau ba. Mutuwa na rushewar rai. 

Sai mutane suka ɓoye gaskiya, domin kare yaranshi.

Kogin ya dawo yanzu ne. Domin Mustapha da Sumayyah sun girma. Jinin rantsuwar ya farka. Lokacin zaɓi ya cika.

Jinin da ya ke gudana ajikinsu yanzu. 

Ba na cikakkun mutane ba.
Ba na cikakken kogin ba.

“WANNAN SHINE LABARIN”

Zarawu ta ce.

Mustapha ya yi shiru. Zuciyarsa na rawa. Tsoro na shigansa. Ya ce.

“To yanzu ya zan yi, in tsayar da kogin Asiri?”

A wannan lokaci, ruwa ya fara zubowa daga bango.

Sai kuma ga Sumayyah ta fito. Amma ba Sumayyah ɗin da ya sani ba.

Idonta fari tsaf. Muryarta sanyi sosai ta ce.

“Yaya… Lokaci ya yi.”

Mustapha ya ja da baya ya ce.

“Me ya same ki haka?!”

Sai Sumayyah ta ɗaga hannu. Ruwa ya zagaye ta kamar rawani ta ce.

“Kogin Asiri yana so ya dawo cikakke. Ɗaya daga cikinmu zai zauna da shi.”

Mustapha ya girgiza kai.

“Ni zan zauna! Ku bar ta!”

Sai kogin ya yi magana daga ko’ina.

“Ba zaɓinka ba ne kaɗai... Dole jinin ya amince.”

Ƙasa ta fara tsagewa. Iska ta yi ihu.

Zarawu ta ce da rawar murya.

“Mustapha ba zan iya taimakonka ba.”

Sai ta ɗaga sandarta tana shirin bugawa ƙasa. Sai kuma ta ga Mustapha ya ɓace. 

“Kogin Asiri!”

Ta faɗi da ƙara.

Mustapha ya farka a kan wani dutse mai sanyi.

Ba da rana ba ne.
Ba da dare ba ne.


A gabansa KOGIN ASIRI. Amma yanzu ba kogi kaɗai ba ne… ƙofa ce.

Sumayyah tana tsaye a ɗaya gefen ruwan.
Jikinta ya zama gida biyu. Sama mutum, ƙasa ruwa.

Idonta fari tsaf kamar ɗazu. 

“Yaya… Ina jin sanyi… Amma ban jin zafi.”

Mustapha ya fashe da kuka. Saboda muryarta cikin rauni ya ke.

“Zan fitar da ke! Ko da raina zan bayar!”.

Sai Hajiya Zarawu ta bayyana a bayansa ta ce.

“Ka saurare ni yanzu, Mustapha.
Ba kowa ne ke samun wannan damar ba.”

Ta ɗaga sandarta, ruwan da ke motsi ya tsaya cak ta sake cewa.

“Kogin ya buɗe Zaɓin Duniya Biyu.”

Mustapha ya juya.

“Wane zaɓi?”

Zarawu ta yi numfashi mai nauyi ta ce.

“Ɗaya daga cikinku zai zama mai tsaron kogin. Ɗaya kuma zai koma rayuwarsa amma ba tare da ya tuna da ɗayan ba.”

Mustapha ya ɗaga kai da tsoro.

“To idan ban zaɓa ba?”

Sai kogin ya yi dariya ya ce.

“To zan ɗauke ku duka!.”

Sai ruwa ya fara hawa ƙasa, yana girgiza fiye da kima. Yana rugugi kamar tsawa.

Sumayyah ta kalli Mustapha da hawaye na zuba daga idonta, amma hawayen ya zama ruwa sosai ya ke zuba kamar bakin fanfo.

“Yaya… ka rayu. Ka manta da ni.”

Mustapha ya girgiza kai. Ya ce.

“A’a! Ba zan iya ba! Ke za ki rayu, mahaifiyarmu tana can tana kuka, tana jiran dawowarki”

Zarawu ta ce a hankali.

“Idan kai ka zauna… Zuciyarta za ta tsira.”

Mustapha ya kalli kogin. Ya kalli Sumayyah. Ya kalli hannunsa, har yanzu sai ya ga yana ɗauke da jinin rantsuwar mahaifinsa.

Sai kogin ya yi magana da ƙarfi:
“KA ZAƁA, MUSTAPHA!!.”


_Shin wani zaɓi Mustapha zai yi?_
_Zai tsira da Sumayyah ko mutum ɗaya zai tsira?_