KUNCIN ZUCI

Kuncin zuci

by @bintuuu

Shigan Na'ima gidan bata samu kowa a falo ba ta wuce direct zuwa dakinsu, Nafisa ta samu kwance a gado tana waya cikin qan qan da murya, ganinta yasa Nafisan tayi excusing kanta gurin Lamin tace "Give me a minute please" da haka ta kashe wayan tana kallon Na'iman tace "Bobo na dawo bakyanan, ina kikaje haka?" cikin sanyin murya Na'ima tace "Mun dan fita ne" Nafisa tace "Da Yaya Ahmad?" ta gyada kai batace komai ba, dan bin ta da kallo Nafisan ta rinqa yi like she was trying to figure out something akan fuskan Na'iman, sai kawai Na'ima ta cire gyalen ta, ta tafi edge din gadon ta kwanta, Nafisa na kallonta tace "Wani abu ya faru ne?" girgiza kai tayi tareda cewa "Babu komai kiyi wayanki, zan danyi bacci ne" da haka ta juya wa Nafisan baya tana facing wall din dakin, shiru tayi tana kallon ginin, aranta tana tunanin "Me Bilal yake nufi da rayuwanta this time?" "yana tunanin after all that happened between them zata koma gidansa ne" anan kuma taji zuciyarta ya fara bushewa, anan kuma taji wani takaici na tasowa tun daga qasan zuciyarta, a wannan moment din Na'ima tayi deciding duk lokacin da ya sake bayyana a gabanta bazata gudu ba, she's done running 'from now and ever', ya kamata ta fara tsayawa kanta a abubuwa da dama a rayuwa, a zuciyarta tana jin shirye take ta yafe ahalinta gaba daya indai dan se ta koma cikin rayuwan da ta baro a baya ne, hawaye ne yazo idonta dalilin tunawa da tayi da Alhaji,  be taba uzurrawa rayuwanta ba, ya sa ta makaranta, ya bata roofing under her head a lokacin da take fama da rashin gata, amma kuma har yau tanajin ciwon rashin kulawan sa da maida hankalinsa akan duk wani abu da ya shafi rayuwanta, tanajin ciwon rashin bibiyar rayuwan ta da beyi ba bayan ya aura mata mashayin dansa, tasan zuwa yanzu ya manta da duk abunda ya shafeta ma, haka ta rinqa tariyo abubuwa da dama da suka faru da ita tana share hawaye jefi jefi har sannan bata juya gefen Nafisa ba....
Sai yamma Ahmad ya shigo gidansa, ko parking me kyau be yi ba ya fito daga motan yana jin zuciyarsa babu dadi, ma'aikacin gidan nasa dake gyaran shuka acikin flower garden ya fito da sauri yana masa barka da dawowa, gyada kai kawai yayi ya nufi main door din building din nasa, da fingerprint ya bude giant wooden door din ya shige babban falon nasa, da ya dauko bottle water yana zaune nan falon ba abunda yake sai tunani, dakinsa dake upstairs ya nufa dan yayi wanka simba na biye dashi a baya, yana tsaye under shower ruwa ya zuba a tsakar kansa sai kallon glass wall din yake trying to figure out in da yasan Bilal, he is sure that ya gansa a wani waje, amma a ina?, har ya gama wankan ya fito daure da towel yana goge kansa da wani towel din be tuna komai ba, tsayawa yayi da abunda yake din ya rinqa kallon babban hoton Na'ima dake facing dinsa a dakin, at that moment, it all came back running in to his mind, And he remember ..."Ranar da yaje daukan ta a bakin apartment dinsu yaga fitowar guy din", that's it.. "Guy din ya dan dade a tsaye gefensa lokacin", dan stiff yayi dalilin tuna yanayin da Na'iman ta fito gurinsa ranan, da yanda mood dinta ya koma, ajiye towel din yayi yana kallon dariyan da tayi sosai a hoton, and in that moment, tambayarsa shine "Ya Na'ima tayi rayuwa a baya? who hurts this innocent girl?" ...
Yana nan tsaye yaji dayan wayansa tayi qara anan kan gadon sai ya juya tareda qarasawa ya dauko yana kallon number'n dake kan screen din, daukan kiran yayi sai yaji muryan Laila cikin sanyi, kamar zatayi kuka tace "Haba Yaya, ko ba komai ni qanwarka ce fa, I've been back for days amma bazaka kira kaji ya na iso gida ba" sai Ahmad yakai yatsunsa biyu ya danne idanunsa dasu sannan ya sauke numfashi, can ya sauke hannun nasa yace "How have you been?" cike da shagwaba tace "Yaushe zaka dawo Yaya, banida lafiya ma" sai ya juya yana kallon hoton Na'iman sannan yace "Ya jikin naki?" ganin yayi ignoring question dinta yasa ta sake cewa "Haba Yaya na, you've stayed in London for so long this time" coldly yace "Laila" ta amsa da "Uhm" yace "Ki gaida su Daddy" da haka ya kashe wayan bai jira me zata ce ba, kiran Adam yayi be yi ringing uku ba ya dauka, casually yace "Meyasa zaka bata personal line dina?" ta daya bangaren Adam yace "She asked for it, kuma meyasa zakayi blocking dinta toh" Ahmad da yaji ransa ya fara baci yace "Ra'ayina ne hakan, and i'm blocking her on this one too, in ka ga dama ka qara bata wani line dina, har kai zanyi blocking" murmushi Adam yayi yace "I dare you wallahi, wai meyasa zakayi blocking dinta ne, ko ba komai tsakaninku ai qanwar ka ce, she loves you Man hatta iyayenmu sun san haka" coldly Ahmad yace "Na fika sanin hakan, and i mean what i said about blocking you" dariya kawai Adam yayi sai yace "Anyway, yakamata dawo nan fa, the works are piling up sosai, Man i can't handle them alone, nayi sending permit renewals and still no replies on them, these people only respond to your emails Ahmad, and you know that" dan sauqe numfashi Ahmad yayi sannan yace "I can't come back now, inada abunda zanyi anan din" Adam yace "Something like what? Kayi appointing masu kula da London branch har mutum hudu fa Ahmad, and they're doing a great job, sannan ka fadamin duk wani personal deals dinka na Apps ka gama su a italy saura kayi developing wasu" sai Ahmad ya shafa kansa bai bar kallon hoton Na'iman ba yace "Something came up, zan dawo when i'm done" da haka ya kashe wayan tareda ajiyeta a gadon ya nufi closet dinsa dan shiryawa.....
Sai kusan Magreb Na'ima ta tashi dan bacci me nauyi ne ya dauketa bayan ta gama kukan, bayan tayi wanka ta saka kaya mara nauyi sai taji wayanta na ringing, Faruk tagani ke kiran nata, ta dauka suka gaisa, sai yace "Habibtin Mami in ban kiraki ba, ke bazaki kira yayan ki ba ko" cikin sanyin murya tace "Kayi hakuri Yah Faruk ba haka bane" yana dan dariya yace "Na hakura, Nafisa tace nan da two weeks zakuyi graduation ceremony din naku ko" ta gyada kai tace "Eh in sha Allah" sai ya kwantar da murya yace "Tell me, me kikeso for your graduation gift" murmushi tayi tace "Komai ma Yaya" yace "Shikenan Habibti..oh Habibtin Mami ce kadai ashe" bata bar murmushin ba tace "Kai Yaya" da haka ta tambayesa lafiyan mutanen gidan ya amsa sannan ta bashi gaisuwa ya isar wa lantana sannan sukayi sallama, dan su Abu tana waya dasu sosai. Wannan wayan da sukayi ba qaramin debe mata damuwanta yayi ba, da ta fito falon ta qarasa kitchen sai ta samu Nafisan da Anty Amnah suna girki, nan ta sa hannu suka cigaba Anty Amnah tace "Na leqaki dazu ai kinata bacci ai, hope lafiya" ta amsa da "Eh Anty kai na ne ke dan ciwo" tace "Sannu kinsha magani?" Ta gyada kai Nafisa na kallonta, dan itadai ba ta yarda ciwon kai ne ke damun Na'iman ba, da dare har suka yi shirin bacci Ahmad bai kirata ba, Nafisa tace "Ya kan naki Bobo, yayi sauqi kuwa" ta gyada kai, sai Nafisa ta sake cewa "You can't expect me to believe kan ki ne yake ciwo Na'ima, meya faru dake yau din" Na'ima tasan definitely in ta fadawa Nafisa abunda ya faru zata kira Mami, ita kuma a yanzu ta fara sakawa a ranta Bilal bazai rinqa zama damuwanta a kowanne lokaci ba gaskiya, balle har ta tada hankalin su Mami akan hakan, kawai sai tace "Babu abunda ke damuna" tsayawa kallonta Nafisan tayi sai ta kamo hannunta tace "Dagaske nake sis" ganin har sannan Nafisan batace komai ba yasa ta cewa "Bani labarin Lamin, naga abu nata kankama a tsakaninku" ture hannunta Nafisan tayi like she was not buying that, tace "Zan baki labarin gobe, nima kaina na ciwo yanzu" da haka ta juya tana gyara kwanciya Na'iman na bin ta da kallo, itama gyara kwanciya tayi tana jin zuciyarta babu dadi, sai da tayi switching off na wayanta sannan tayi baccin ma....

Washegari
Cike conference room din yake da ma'aikatan company din wanda suka kasance turawa hade da baqaqen fata, duk sun hallara kowa da laptop da bottle water a gabansa suna zaman jiran Ahmad ya jagoranci meeting din kuma har sannan bai iso ba, daga gefen kujeran Head din Lamin ne zaune a nashi mazaunin damuwa bayyane a fuskansa, daya daga cikin manyan ma'aikatan company'n dake gefen Lamin din ya dan matso kusada kunnensa yana masa rada "Whats taking him this long?" sai Lamin yace "He's on his way" da haka ya miqe ya fita daga conference hall din ya danna kira a line din Ahmad,
Daga dayan bangaren Ahmad yana driving ya miqa hannu ya dauko wayan dake gefensa, yana dagawa Lamin yace "Ahmad tun dazu fa kai muke jira" sai sannan Ahmad ya tuna da meeting din da yake jiransa a office ranan, yana kallon titi yace "I'm sorry Man, reschedule it" Lamin ya dan ware ido yace "What? This late? where are you Ahmad?" Yace "My way to Oxford" Lamin yace "Da safen nan kuma, what happened?" Ahmad yace "Something came up, talk to you later" da haka ya kashe wayan, sai ya ga message din Nafisa ya shigo, na door pin dinsu da ya tambayeta, a take ya dauke numbers din a idonsa ya ajiye wayan, sai ya qara gudun motan, yana ji ajikinsa wasu daga cikin answers dinsa suna can Oxford...
Nafisa dake tsaye jikin mirror bayan ta tura message din ta juya tana kallon Na'iman dake zaune kan gado tana danne danne cikin iphad dinta bata dago ba, aranta tasan dama za'ayi haka, something is definitely wrong with Na'ima yesterday, aikuwa tananan zata jira dawowan Ahmad, dole ne tayi breaking promise din da tayiwa Na'iman tun ita ta kasa samun courage din fada masa abubuwan da suka faru da itan, qarasawa tayi gaban wardrobe dinsu ta bude tana bincikawa, sai ta juyo tace da Na'iman "Sis ina kika ajiye min veil dinda kika wanke tun shekaran jiya" Na'ima ta dago kanta tace "Ki duba dayan bangaren, fita zakiyi ne" tace "Eh, Anty Amnah ta aikeni" Na'ima ta gyada kai tana kallonta, sai bayan Nafisan ta fice daga dakin sannan ta juya gefenta tana kallon wayan ta dake kashe har sannan akan bedside drawer...

Cikin 1 hour 30 minutes Ahmad ya isa Oxford saboda gudun da ya buga a hanya, shiganshi apartment din ya fara cin karo da dustbin dinsu dake bakin kofan a kwance, abubuwan dattin cikin ya zube sanadin hankada Na'iman da Bilal din yayi ranan, cikin sanyin jiki ya qarasa cikin falon ya duqa ya dauki hair band din Na'iman guda daya da ya cire shima garin fusgo gashinta da Bilal din yayi, kallon band din ya rinqa yi sai ya fara bin falon da kallo, gurin is neat, juyawa yayi ya tura kofan dakin dake gefensa sai akayi sa'a na Na'iman ne, sai da ya dan yi stiff ganin glasses everywhere a tsakar dakin, sauqinta har sannan bai cire sneakers din kafanshi ba yasa shi takawa cikin dakin ya tsugunna yana kallon gurbin jini akan tiles din, duk yanda ya kai da juriya saida yaji zuciyarsa na karyewa ganin diddigen jinin Na'iman, sai ya miqe cikin qunan rai ya ciro wayansa daga aljihu yayi kira, ana dagawa yafara magana da zafi zafi cikin turanci kamar haka "Na chanja shawara Micheal, qara sati daya su zama biyu, kar ya bar cikin cell dinnan sai bayan kwana sha hudu" daga daga daya bangaren Micheal ya daga kai yana hango Bilal dake zaune cikin cell din police station din duk yayi zuru zuru a kwana daya, sai ya danyi qasa da murya ya amsa Ahmad din cikin harshen turanci "Zanyi hakan, amma ka dan qaramin kudin" Ahmad yace "Done..I'll double it, just do what you must to keep him there" da haka ya kashe wayan sai ya juya ya fita daga dakin, bai dade ba ya dawo hannunsa riqe da tsintsiya da parker ya tsugunna ya fara kwashe glass din zuciyar sa na quna, da ya gama kwashewan yakai dustbin sai ya hado ruwan mopping daga toilet yayi ta neman mopper bai samu ba sai kawai ya dauko wani tsumma da suke aiki dashi a gidan, tattare hannun rigansa yayi ya tsugunna yana goge duk gurin da jinin Na'iman ya zuba har ya bushe, dirzan gurin ya rinqa yi har sai da ya fita tas sannan ya miqe ya shiga bandaki da ruwa da tsumman ya dauraye, da ya gama ya dawo dakin sai ya qarasa gurin gadon Na'iman ya zauna a bakin sa tareda kai hannu ya dafa filon da take kwanciya akai, wani zafi ya rinqa ji a zuciyar sa a wannan lokacin, babban baqin cikinsa ma shine rashin shigowan da yayi ranan, 'maybe ranan yana bakin building din lokacin da incident din ya faru', sake miqa hannun yayi kan bedside drawern ta ya dauko wani text book dinta na data analysis ya bude yana ganin short notes din Na'iman dake first page, fara lissafo kwanakin da suka rage na graduation din nasu yayi, indai abun da yagani da idonsa yau yana daya daga cikin abunda guy din yayi wa Na'ima a rayuwa, then it's going to be a war between them, sai ya tabbatar da ya maida masa fiye da abunda yayi mata but not in England, saboda baya son abu da law wani lokacin, abu daya yafi ganewa a rayuwansa "An Eye, for an Eye" (rama cuta daidai da daidai).....
Daya fito daga apartment din sai da ya sake kiran line din Na'iman yaji har sannan a kashe, yana so yaji daga gareta tun jiyan amma wayan a kashe, da haka ya shiga motansa ya sake daukan hanyar komawa London, nan ma cikin 1 hour 40 minutes ya isa, ganin kiran da Lamin ke masa babu qaqqautawa yasashi deciding zuwa office din amma yana cikin tafiyan sai ya samu kansa da juya akalar motarsa ya dauki hanyan zuwa gidan Anty Amnah.
Bayan ya isa direct ya tura kofan falon ya shiga hade da sallama ciki ciki, Na'ima ce zaune kan kujera kafanta a tankwashe, ga twins nan sun haye mata jiki har dankwalinta sai da suka zame mata, gashinta me santsi ya sauqo mata har baya, hankalinsu duk ya tafi ga wani abu da suke kallo a iphad dinta suna dan dariya dukansu...Kawai tsayawa kallonta Ahmad yayi yanajin duk wasu gabobi na jikinsa na mutuwa, and in that moment he knew, he is ready to wage that war for her....ze iya duk wani yaqi akan Na'ima......