INAYATU

13

by @mahmazee

      EMRAN ALIYU BELDO

  Karfe Biyar da Rabi agogon mu na gida Nigeria ya buga, wanda yayi dai dai da saukar jirgin Qatar Airline da ya dauko passengers daga Rome din kasar Italy yayi packing a filin tashi da saukar jirgi na Murtala Mohammed international Airport da ke jihar Lagos.


   "Good evening Passengers this is your captain speaking, welcome to the city of Lagos, The local time is 5:30pm, the captain has parked and the fasten seat belt sign has been turned off, on behalf of the entire crew we wish you a nice stay and wish to see you again" shine sanarwar Captain, wanda hakan ya baiwa passengers damar cire wayoyin su daga Flight mode, kai tsaye calls suka soma shigowa hakanan wasu na kira.

   A cikin wadannan passengers da jirgin ya dauko ya hada da EMRAN BELDO da ke zaune a business class, wanda wayar sa ta dauki ruri kamar dama jiraye ake ta kawo a kira, wayar ta sa ya dago yana kallon screen din domin ganin wa ke mishi wannan kira haka.


 Sunan mahaifin shi da ke yawo kan screen din ya sanya shi yin sliding  ba tare da bata lokaci ba ya daga kiran.

   "Hello" Kakkausar muryar sa mai cike da zati ta fada, daga dayan bangaren aka amsa shi da "Assalamu Alaikum"

   "Waalaiku Salam, "baba Ina yini"

"Lafiya kalau Emran, ya hanya da fatar kun iso lafiya"

"Alhamdulillah the trip was safe"

"Masha Allah" baba doctor ya fada "Ina so ba tare da bata lokaci ba kazo Kano kamar yanda na gaya maka akwai magana mai muhimmanci"

   

    Emran ya nisa yana kallon agogon paco Rabbane da ke daure tsintsiyar hannun sa da ke cike da gargasara tare da sauke yar ajiyar zuciya yace "ban manta ba Baba and insha Allah i will be in kano (zan zo kano) gobe"

  "In da hali ka zo a yau din domin na gaji da wannan shiriritar Emran, Ina so mu kai karshen maganar nan"

   

       Emran ya dan yi shiru tsayin wasu dakiku yana ji a jikin sa a kan zancen nan ne dai kwaya daya da ko yaushe shine topic of discussion din su, sai dai ya dauka sun kai karshen zancen da Baba, ya dauka ya huta tun daga ranar da ya gabatarwa baba da zabin sa, yana da important schedules a abuja da yake son meeting gobe sai dai kiran baban ba wanda ke jira ba ne ba wanda ake jinkirtawa ba ne, saboda haka ya dan yi sighing 

   "It's late Baba but zan duba if there is available flight to kano"

"Yauwa Emran ka kokarta ka zo, Allah ya hutar da gajiya"

 Kafin ya furta ameen baban ya dakile wayar yana barin sa da kurawa wayar ido kamar baban zai bullo ta screen din.


   "Hope all is good" (da fatar ba damuwa) wata kamilalliyar murya ta fada daga gefen shi, wacce ke lure da yanayin sa da ma chanjin yanayin sa tun bayan da ya daga wayar, da ido ya amsa ta kawai ba tare da ya iya furta komai ba, zuwa lokacin tuni passengers sun soma fita, hakan ya sanya shi mikewa yana bude Over head bin din seat din sa domin sauke kayan sa.

   Wani flight attendant ya kama masa sauke karamar suitcase din LV da ke dauke da kayan sa da ba zasu gaza kala hudu ba sai abinda ba za a rasa ba.

    

       Haka suka jero matashiyar na bayan sa janye da Lugagge din ta itama na karamar akwatin Samsonite sai madaidaiciyar Birkin handbag din ta da ke kan akwatin, har suka gama da immigration suka fito.

    Tafe yake da waya makale kunnen sa yana magana da Zahradeen Arik kamar yanda yayi saving number, yaron baba ne da ke musu duk wani harka na Airport

  "I need a flight to kano yanzun nan" abinda ya fada kenan

   Minti biyu zahradeen ya nemi ya bashi zai kira shi back, hakan ya sanya shi dakatawa tun bayan da ya katse wayar wanda ya baiwa budurwar da ke biye da shi tun dazu damar cimmasa kai ba zaka taba cewa tare suke ba saboda tazarar da ya bata.

    Wani irin dogon mutum ne da ke komai cikin zafin nama, tafiya da Emran ba abinda ta ke iyawa ba ne, a duk lokacin da suka jera tare ka'ida ne ya tafi ya bar ta baya domin ita kam ba zata iya wannan saurin ba, idan ya zura kafa daya hakan na dai dai da na ta taku biyu.

   Hakan ya sa ta sanyawa kan ta salama, duk yanda kuwa ta ke so su jero tare haka zata bar shi yayi gaba tana bayan shi.

   Wani irin siririn murmushi ta sakar mishi wanda ya kawata fuskar ta da ta sha simple makeup "honey irin wannan sauri haka" muryar ta ta fada

   Wannan karon ma fuskar agogon hannun sa ya kalla kafin ya dago da kan sa yana sauke manyan idanun sa kan ta, Fara'a ba dabi'ar Emran ba ce, shi ba mutum ba ne da ya cika faran faran, ganin fara'ar sa sai wanda ya dace, wannan karon ma bata chanja zani ba a lokacin da yake amsa ta da "zan je kano yanzu"

   "What kano, yanzu, i thought abuja zamu wuce kawai" ta fada tana gyara vintage scarf din da ke kan ta, kafada kawai ya daga yayin da kiran Zahradeen ya sanya bai bata amsa ba.

    "Akwai direct flight to kano by 8:30pm hakanan akwai connecting flight Abuja to Kano by 7pm" 

  "I think i will go for direct flight din" ( Ina ga zan bi wanda zai je kano kai tsaye) ya fada

 "Okay Toh ba damuwa Ina Aero counter, meet me there"