INAYATU

20

by @mahmazee

    THE UNION

 

Tun da lokacin buki ya gabato shikenan shirye shirye ya kan kama babu kama hannun yaro, tuni yan biyu manya manyan kawayen amarya suka iso daga abuja, yayin da Amaryar ke ta zaryar zuwa makaranta domin zana jarabawar ta ta second semester inda zasu samu hutun dogon zango, sai kuma shiga 300level idan an dawo.

    Sannu a hankali su Inaya suka kawo karshen exams na su, suka kuma samu hutu.

   Tun a lokacin aka soma yi mata shiri na musamman, gyaran jiki ake mata da tsimi ba na wasa ba, musamman aka dauko mai gyaran jiki daga Morocco domin gyaran ta wacce ke ta aikin ta tukuru.

   Yan biyu kam sun tare a gidan da su Rabi'a, da wasu daga cikin cousins din su. Yan Port Harcourt da mutanen Lagos tuni suka iso Kano. hakanan a yau yan Uk wato Faisal din Baba Doctor da yayan ta Mas'ud wanda ta ke biwa da ke karatu a  Coventry University England zasu iso.

     Wanka ta fito daure da katon towel baby Pink, wanda ya bayyanar da farar fatar ta da ta sha gyara sai sheki da glowing na musamman ta ke yi, tayi wani irin kyau fiye da wanda ka san ta da shi tana ta zuba kamshin khumrahs da hadin ruwan wankan Yar Morocco.

    Amna ta yi shewa tana fadin "irin wannan kyau haka Inaya kar a rikita yayan mu fa" 

  Ita dai bata ce komai ba face dan murmushin da tayi na yake ta nufi gaban dresser tana murzawa jikin ta body oil din Neutrogena da hadin body mist.

   

     Rabia ke hada mata yan kayan da zata yi amfani da su a yar karamar suitcase saboda gidan baba doctor zasu kwana yau, akwai bridal party na yan mata da zasu yi a can Washegari.

    Dama shirye yanmatan suke, ita kawai su ke jira saboda haka tana gama shirin ta suka fito, sai da suka yiwa su dede sallama kana suka fito, ita dai motar da su Amna suka zo da ita ta bi da wasun su yayin da sauran suka bi motar Abba da Mamman ke ja.


    Kusan lokaci daya suka shigo da motar da ta dauko su Faisal wanda tun da motar ta tsaya ya fito yana rungume Mahma da ta kasa hakuri ta fito tarbar su.

  Gaishe gaishe aka tsaya yi a nan gaban gidan, su ma su twins cikin murna suka rungume yayan su wanda suka jima ba su ga ni.

   Inaya ta zubawa Mas'ud ido, tana mamakin girma da murjewa da ya da da yi kamar ba Mas'ud din ta da suka taso suka yi wasa tare ba.

   Murmushi ya sakar mata yana Jan ta jikin shi, ta rungume shi cikin farin cikin ganin shi.

  

  "Haka yaya Em yayi min kenan, yayi min snatching mata" Faisal ya fada teasingly, sai lokacin kunyar mahma ta kama ta, tun dazu sai murnar zuwan yayan ta ta ke ta manta da gaida mahma.

   Hararen wasa ta yi masa tana sunkuyar da kai tare da isa gaban mahma

  "Kinga tana Harare na ko mahma, na lura duk cikin yayyun ki ba wanda kika Raina sai ni, da anyi auren nan da na shiga uku" Faisal ya sake fada cikin tsokana, dama shi haka ya ke duk inda ya ganta ba zai bar ta da tsokanar shi ba.

 

   Kunyar mahma ta hana ta biye mishi wacce ta yi hugging din ta kamar ba suruka ba, ita kam mahma bata cikin yan sarakutar nan da kunyar da ke wahalar da mutane.

   "Ina yini Mahma, ya gajiyar hidima" Inaya ta fada cikin siririyar muryar ta har ta sa Faisal yana kwaikwayon ta, mahma ta kai masa bugu ya goce yana dariya

  "Kai baka san yayar ka ba ce yanzu, wa ke tsokanar matar yayan shi"

"Mahma ki kyale ni da Inaya kawai saboda tana ganin ki ne, if not ai ta iya ba mutum amsa"


"Ni dai ka shafawa 'ya ta lafiya ah to" 

Dan dagowa tayi kadan daga rungumar da mahma tayi mata tana mishi gwalo

"Kin gani, kin gani ko Mahma" Faisal ya fada yana pouting kamar shi ne Auta.

   "Ni ba abinda na gani" daga haka suka dugunzuma cikin gida, inda aka ba je kan dinning da ke shake da abinci kala kala da drinks, nan suka yi lunch kana kowa ya shige dakin shi.

   Washegari tun da suka tashi suka fice salon, inda aka yiwa amaryar gyaran kai na musamman da spa.

  Tun bayan da suka dawo make up artist din da ta iso tun dazu ta soma aikin ta.

    Tsayawa fadar irin adadin kyaun da make up din yayi mata bata lokaci ne, abin ka da ba dan saban ba.

   turus mai make up din tayi a lokacin da ta kammala aikin ta, ba yau ta Saba yiwa Amare make up ba, amma kyaun da make up din yayi a fuskar wannan amaryar ita kan ta sai da ta dakata tana kare mata kallo.

   Masha Allah Allah ya zuba halitta a nan ta raya a ranta a lokacin da ta ke haske ta da hasken camera.

   

   Cikin wani Velvet Fabric ta shirya kalar burgundy mai sequence sosai a jikin kayan daga gefe daya, dress din ta matukar dauko kalar fatar ta, tana lafewa jikin ta tare da fitar da duk wani curve and shape da Allah yayi mata wadatar sa.

   Ba karamin kyau kayan suka yi mata ba, ita kan ta a lokacin da ta ke zubawa kyakkyawar halittar ta ido a madubin dogon yaro wato standing mirror sai da ta samu kan ta da tambayar kan ta da kan ta Anya ita ce kuwa.


    Karfe uku suka soma gudanar da event din su na Bridal Brunch wanda yayi kyau ya kuma kayatar sosai, an ci an sha an ba za Dj sai rawa yan mata da yayyun Amarya kamar sakina, hanifa, halima da zarar Yah Amadu da suka zo ke kwasa.

   

    Inaya na zaune kan kujerar da aka tanadar mata wacce bayan ta wood Board ne da akayi yiwa rubutu cikin manyan haruffa da FUTURE MRS EMRAN.


   Tayi shiru tana zubawa dance floor din manyan idanun ta da suka sha bakin kwalli da liner, ba don hankalin ta na gurin ba, ba don hankalin ta na ga rawa ko ciye ciyen da ake yi ba, a zahiri ita dai ta samu kanta da zubawa gurin ido yayin da a badini kuma tayi nisa cikin tunani, tunani ire iren wadanda ke hana mata baccin ta tun wani lokaci da ya shude.

   

  "Wannan wane irin aure ne" wani sashi na zuciyar Inaya ke raya mata

Wane irin aure ne wannan da babu Ango babu labarin sa, rabon ta da angon nata tun ranar da ya zo ya gaya mata maganganun da suka hana ta kwana a Daren ranar, daga yan uwan shi har na ta ba wanda ya san ko communicating ba sa yi ko da a waya ne kuwa.

  Lokuta da dama idan abu ya ta so zaka ji su yan biyu ko su sakina na fadar, kira Yaya Em, me yaya Em yace, yaushe angon zai zo, yaya em this yaya em that, a koda yaushe Yake ne amsar ta a gare su domin har yau ta kasa iya gayawa wani halin da suke ciki, gashi yau har suna cikin satin auren su.

   

   Idanun ta suka kawo ruwa a lokacin da wani tunani ya fado mata na wace irin rayuwar aure zasu gudanar, bata ji Yaya Em ya shirya zaman aure da ita kamar ko wadanne ma'aurata.

  Bata san a wane matsayi zata dora auren su da ake batun daurawa ba, ta zubawa sarautar Allah ido tana jiran yanda zai yi da lamarin ta, amma idan ta ce bata cikin damuwa tayi karya.

 

   Tana cikin tsananin damuwa da tunani wanda ya dan ramar da ita, da yan uwan ta zasu lura da sun lura da damuwa da kuma yawan tunanin da ta ke ciki, sai dai duka hankalin su ya dauku da shirye shirye hakanan sun danganta hakan da yar ramar da Amare kan yi na zullumin aure da kuma barin gida.


   Larai Shagari kawar ta from secondary school ta karaso inda ta ke zaune da murmushi kan fuskar ta take fadin "Inaya Beldo you make a beautiful bride"

   Dan siririn murmushi ta saki tana kallon Larai da idanun ta da sukayi laushi ta Amsa da "thank you"

 "Come on idan ba zakiyi rawa ba atleast let's take some pictures" larai ta fada tana janyo hannun ta


    Bata da yanda ta iya haka ta mike tana bin bayan Larai har zuwa gaban Photo Booth din da aka kafa ana ta daukar pictures.

  Joining din su tayi ana ta daukar hotuna, duk wanda ya zo dai yayi hoto da amarya tsayin wani lokaci har ta ji zaman ya soma isar ta.

   Karfe Shida na yamma mutane suka soma watsewa, xuwa magbrib suka kammala ya rage su kawai yan gida, da yake tana fashin sallah, sai kawai tayi zaman ta, nan gaban gidan inda aka gudanar da event din ita da Hanifa da ke fama da karamin cikin ta suna dan taba hira.


   Haka kawai ta ji bata son komawa cikin gidan saboda hayaniyar da ake ta yi, har hanifa ta mike tana fadin "da alama nan zan bar ki Inaya ni kam bari in shiga daga ciki i need to pray" dan siririn murmushi kawai ta sakar mata.

   Hanifa ta shige ciki tana barin ta ita kadai nan gurin, zare heels din Mango da ke kafar ta da suka ishe ta tun dazu tayi tana kwantar da kan ta kan table din da ke gaban ta.


    Tun da farar motar Maybach s580 da maigadi ya wangalewa gate ta shigo, a kan ta hasken fitillun motar ya sauka, yana haskewa duk wanda ke cikin motar kyakkyawar fuskar ta, tafin hannun ta ta sanya tana dan kare fuskar ta saboda yanda hasken ya kashe mata ido, har motar ta ratso tsakar gidan zuwa Parking lot tayi parking.


   Direban da ya dauko shi yayi hanzarin fitowa yana bude mishi gidan baya wato owner's corner, ya zuro da dogayen kafafun sa da ke cikin Slip on shoes din Seavees, ya fito sanye cikin wasu fitinannun Brioni Suit grey in color da suka matukar dacewa da shi.

   Blazer din shi ta sama na rataye hannun sa domin tun bayan da jirgin su ya sauka ya zare blazer din yana barin white shirt din ciki.

  

    Jamilu driver ya zo da sauri domin karbar mishi blazer da Briefcase din Montblanc da ke hannun shi, girgiza masa kai kawai yayi alamar ya bar shi kawai, ya taka rike da kayan shi a hannu.


    A hankali ta dauke kallon ta daga kan motar, bugun zuciyar ta na da da tsanan ta tun bayan da tayi tozali da masculine halittar da ke kusanto ta ba tare da lura ko damuwa da wanzuwar ta a gurin ba.

  Tayi kasa da idon ta, tana shakar daddadan kamshin Creed Centaurus da ni'imtaccen iskan gurin ke dauko mata.


   Bata da guts ko karfin halin iya hada ido da shi, ta kasa iya dago da kan ta har sai da ta ji Kakkausar Muryar sa da ke fita cikin wani irin salo tare da ambatar sunan ta in a tone wani dan Adam bai taba ba


   "INAYA" ya fada yana karasowa gaban table din tare da soke dayan hannun sa da baya rike da komai aljihu




       PLEASE DO SHARE IF YOU'RE ENJOYING THIS BOOK 🙏❤️!!