INAYATU

21

by @mahmazee

      THE UNION (CONCLUSION)


A tausashe ta dago da idanun ta da suka yi luuu tana sauke su a kan shi, dan examining din ta yayi kadan yana dauke kan shi.

   A mugun gajiye yake har idanun sa na nuna hakan, fitowar sa kenan daga meeting da wasu important clients da suka zo daga Singapore, ya wuce Airport direct ko gida bai koma ba, ba abinda yake bukata a yanzu irin to run a shower ko zai ji jikin shi dai dai.


    Amma haka kawai ya kasa wucewa ya bar ta tun bayan da idanun sa suka yi tozali da ita, at first bai gane ta ba ko don wannan make up din da ke fuskar ta ne oho.

"What are you doing here" ya tambaya a tsanake kuma a natse

  Dan sake kallon sa tayi wannan karon a cikin yanayi na mamaki da wani abu can kasan zuciyar ta da ta kasa bashi suna kwaya daya.


    Idanun ta ta dan lumshe kadan tana sake bude su a kan sa tare da girgiza masa kai alamar aa

  "I hate gestures kiyi min magana" ya fada a gajarce 


Cikin dan rawar murya ta iya fadin "ba komai"

Ba komai ya raya a ransa, ya dan waiwaya gefe da gefen shi ya ga ba wata halitta a gurin bayan ita, haka kawai ta bata ta zo nan ta zauna ita kadai.


   Bai sake cewa komai ba ya dan taba bakin sa yana daga kafada, tare da juyawa kawai ya nufi part din su.

    Kamar daga sama ya juyo yar muryar ta "ya hanya" shine abinda ta tambaya, gana sake kasa sa kan ta.

   dan waiwayowa yayi kadan tare da dakatawa, bai amsa ta ba amma dukkan alamu sun nuna ya ji ta, dan Jim yayi kana ya sake juyawa wannan karon cikin zafin Nama.


    "Inaya Inaya" Rabi'a da ta zo gurin cikin dan sauri ta kiran sunan ta

"Kina nan har yanzu, tun dazu mahma ke neman ki cikin gida" tare da rabi'a suka koma cikin gidan wace ta hana mata sararin reminiscing what just happened.

 

   A cikin gida kuwa suna shigowa mahma ta tarbe ta

"Kina Ina inaya tun dazu muna neman ki"

  A dan sanyaye tayi kasa da kai "muna waje tare da Hanifa"

"Have you eaten" ta tambaya cikin kulawa, dan girgiza kan ta tayi alamar a'a, Rabi'a ta zuba musu ido cikin burgewa at the same time kuma da kyashi, wannan soyayyar da mahma ke nunawa Inaya ya yi yawa ko ya yan ta albarka, don ma ta lura Inayar na kunyar Mahma ai da ba haka ba

"Ina ma ni ce" wani sashi na zuciyar Rabi'a ya daya mata, saurin kawar da tunanin tayi sanin baya da amfani.


    Mahma ta ja ta dinning tayi mata serving Dinner da aka jere table din, Iranian Rice with Saffron sai cikin curry, Mahma da ta Lura da nauyin ta da take ji, ta bar mata dinning section din ganin yanda take ta tsakurar abincin kadan kadan.

   Ba su sake kwana a gidan ba suka koma sharada, inda sauran shagulgulan buki suka cigaba da wakana.

******

     "Sakina, ki same ni daki" Dede da ta leko falon ta fada

"Ina zuwa" Sakina ta mike daga kan kujerar da ta ke kai, tana zaune dama da wasu daga cikin yan uwan su da suka shigo kafin lokacin walima ko sa wani abu da zaayi 

     A daki ta tarar da Dede zaune jugum bakin gado, da dukkanin alamu akwai abinda ke damun ta

  "Dede lafiya" Sakina ta fada tana zama gefen ta

"Akwai abinda yake ta damu na sakina for a while yanzu, a kan inaya ne da Emran, ban ga alamun akwai wata alaka a tsakanin su ba, aure ba abin wasa ba ne, ni dai ko yar wayar nan ta banza ban ga suna yi ba, shine abin yake ta damu na Anya ba wata matsala, kinsan halin yar uwar ki da zurfin ciki, kiyi magana da ita kiji"

    Sakina ta nisa tana sauke ajiyar zuciya

"Nima Dede abin yana damu na, amma kin san zurfin cikin inaya, ba yanda banyi da yarinyar nan ba, nayi mata hauka da wayo, na babba da yaro amma yarinyar nan ta ki bude min cikin ta"


    "Na sani amma dai ki fuskance ta da zancen, idan akwai wata damuwa now is the right time da ya kamata ayi tackling na ta ba sai tafiya tayi nisa ba, ni Uwa ce ta yuwu akwai abinda ba zata iya gaya min ba, nima kuma din akwai abinda ba zan iya tambayar ta ba" Dede ta fada da damuwa


Sakina ta gyada kai alamar gamsuwa

"Zanyi magana da ita, duk yanda mukayi i will let you know Dede"

"Yawwa"

   Duk yanda Sakina take tunanin zata iya samun wani abu daga inaya abin yaci tura, Inayar wata irin mutum ce mai zurfin ciki da kokarin bar wa kan ta damuwar ta Komai tsananin abu.

  

   Karfe biyu na rana bayan saukowa daga sallar juma'a dumbin mutane suka shaida daurin auren EMRAN BELDO da Amaryar sa kuma kanwar sa INAYA BELDO akan sada ki dubu dari biyu.

     Adadin jama'ar da suka halarci daurin auren ba su da iyaka, kade kade ke ta tashi na kalangu da maroka da ke ta sanar'ar ta su.

    Ahmadu shine ya zama kamar angon domin adadin murnar da ya ke ba karama ba ce, aljihun babbar rigar sa ya bude ya shiga rabawa maroka kudi, new notes din naira dubu haka ai faisal da Murtala kai har ma da Baba Dr.


  A bangaren ango Emran kuwa, tun bayan da aka gama daurin auren ko gagarumin Reception din da aka hada bai jira ba, kai tsaye ya kwabe babbar rigar sa a lokacin da yake zama bayan Lexus LX600 da ta kawo shi gurin daurin auren.

   Naseer direban sa ne da ke mishi running errands a nan kano or whenever he is around, wannan karon ma shi ne ke jan shi.


   Idanun sa ya sauke kan screen din wayar shi da ta dau ringing, this is like the umpteenth time Hiba ke kiran shi a safiyar yau, bai San me ta ke

So ba, gabakidaya ta ki ta kwantar da hankalin ta, gani ta ke kamar yana chan a gurin Inaya.

    Sai kawai ya sanya wayar a silent mode ya jingina bayan sa har suka iso, kai tsaye bangaren sa ya wuce tare da rufe kan shi domin baya son damuwar kowa. 


   A bangaren Amarya Inaya kuwa karfe uku na ranar Murtala yayi knocking kofar dakin da suke ita da yanmatan ta, shima cikin farar shadda babbar riga da ta matukar karbar sa.

    

      Gaishe shi yanmatan suka shiga yi kana daya bayan daya suka soma watsewa ya rage dakin daga ita sai Amna da ke ta aikin feshe ta da turare tun dazu.

    Tayi kyau sosai cikin wani fitinannen mustard fabric da ya zauna jikin ta das yana fitar da hasken fatar ta, simple make up aka yi mata da ya dace da kayan jikin ta, amaryar ta Emran tayi kyau kamar ba gobe.


      Murtala ya janyo hannun ta yana sanya mata sadakin ta sabbin notes din naira dubu dubu.

"Ga sadakin ki inaya kamar yanda addini ya tanadar, 


      Da kyar ta iya Mika hannun ta da ta ke ji gabakidaya gabban ta  sun sanyaye mata ta karbi kudin da Murtala ke miko mata.

 

   Sunkuyar da kan ta tayi kasa tana jujjuya kudin ba tare da ta iya furta komai ba, wani irin mixed feelings da emotions ta ke ji da bata taba Jin makamancin su ba, kuka zata yi ko murna da yanda auren ya zo mata.


    Ga dai miji ta samu, miji wanda ta jima tana mafarkin samu, miji na kece raini amma sai dai me babu soyayyarta ko dis a zuciyar sa sai itace ke ta fama da dakon soyayyar sa.


Ko Emran bai gaya mata baya son ta ba dukkanin actions din sa sun nuna haka, da yana son ta da ba zai dauki tsayin watanni ba tare da ya ji muryar ta ko sanin halin da take ciki ba a matsayin matar da zai aura, da yana son ta da ko da a message ne ya turo mata sakon Jin dadi ko na murnar kasancewar ta mallakin sa.


    Ta kasa dago da kan ta har Murtala ya bar musu dakin, hawayen da ta ke makale wa tun Daren jiya suka samu sararin tunkudo kan su, tana cikin tarabbabi da zullumin abinda zata isko a gidan auren ta.


      A dadin kukan da amarya Inaya ke yi tun 

ana lallashi ana tunanin kukan barin gida ne da sabuwar rayuwar da zata shiga har abin ya koma ba su tsoro, domin kuka ta ke kamar ranta zai fita.


    Har zuwa lokacin da deden ta tayi mata sallama, aka sadar da ita falon Abban ta yayi mata nasiha tare da huduba mai karya jiki, har izuwa Sanda aka zaunar da ita a bayan katuwar 2024 Land Rover Range Rover SUV da ta zo daukar amarya bata daina kukan ba.


    Aunty Amina ta zauna  gefen ta ta janyo ta tana dora kan ta a kafadun ta cikin sigar lallashi, Jamilu direba ya tayar da mota yayi gaba, haka ma sauran convoy din da ke dauke da manyan motoci da yan uwa da abokanan arziki.


     Kai tsaye gidan baba Dr comvoy din ya nufa, yanda motar ke tafiya kan titi kai ba zaka ce tafiya ake yi ba, ba gargada ba komai tsabar lafiya har suka iso katon mansion din Surukan ta.


     Nannade ta ke cikin katuwar laffaya bold blue a lokacin da aunty Amina tayi mata jagora zuwa katon falon mahma na Kasa wanda ya cinye cicciridon matan da suka yi rakiya.


    Hugging din ta mahma tayi a jikin ta a lokacin da suka yi sallama falon, cikin fara'a take dadin "maraba da zuwa, maraba da zuwa 'ya ta" ta fada tana yi mata mazauni a gefen ta. 


    Dan gaishe gaishe aka shiga yi da kuma yan sauran abubuwan da al'ada ta tanadar, basu jima a nan ba aka wuce da amaryar gidan ta.

   Wanda yake 3 duplexes in one compound, daya na yah Amadu, dayan na Emran, sai dayan kuma na Faisal for his future wife.

   Gida ne da mahaifin su ya tanadar musu tun ba yau ba, kowa da apartment din shi sai dai duka a cikin gate daya su ke.

    Da bismillah da addu'o'i a bakin ta ta sanya kafar ta a cikin gidan da yake mallakin ta a halin yanzu, kai tsaye upstairs aka wuce da ita zuwa dakin da yake mallakin ta.


     Yan uwanta suka yi mata sallama aka juyo aka bar ta ita kadai a cikin katon gidan, Zarah ma da ta dan taba zama bayan wucewar yan kai amarya, itama din bata wani jima ba ta koma Apartment din ta.


     Seconds suka zo suka shude suna zama minutes wanda suma sun zo sun shude zuwa awanni, amarya Inaya na zaune a inda aka bar ta, ajiyar zuciya ta ke ta saukewa a jejjere, cikin mutuwar jiki ta sanya hannu tana yaye lullubin laffayar ta, fararen idanun ta fes suka sauka a kan well furnished queen size bedroom din ta, da ya hadu karshen haduwa.

Ido kawai ta shiga rabo a cikin dakin har izuwa lokacin da ta ji motsi alamun an shigo cikin gidan.

   

     Wata faduwar gaba ta riske ta, yan idanun ta na fitowa waje tare da dunkule hannayen ta biyu a guri daya alamar zullumi.


   Bata yi tsammanin shigowar angon dakin ta ba kamar ko wane sabon ango saboda haka bayan shudewar wani dan lokaci da shigowar sa ta mike a sanyaye ta nufi hanyar toilet.


    Gabakidaya kayan jikin ta sun takure ta tun dazu domin ita ba ma'abociyar laffaya ba ce, wanka ta yo ta fito daure da madaidaicin towel.

   Tuni yan jere har kayan ta sun Jere mata a walk in closet din da ke dakin, kowadanne kaya an yi musu mazaunin su, kama daga native wears, English wears, Abayas, underwear zuwa shoes and handbags din ta kowanne da mazaunin sa.


    Routine din ta na ko yaushe tayi idan zata kwanta, ta shirya cikin wata silk nightie mai dogon hannu red da bata nuna jiki, take kamshin ta ya karade dakin gabakidaya.

   Ta kashe wuta ta nemi makwanci ta kwanta, tana jin abin a banbarakwai da bakunta.


Da karfi ta rufe idanun ta, tana ta juyi kan gadon saboda baccin da ya ki daukar ta wanda ba zai rasa nasaba da bakunta ko rashin sabo ba.

   Ta jima bacci bai iya daukar ta ba hakan ya sanya bata iya tayar da kan ta sallar Asuba ba kamar yanda ta Saba.


      A hankali ya Kai hannun sa ya murda doorknob din dakin ta bayan knocking din da yayi ba a amsa masa ba, turo kofar yayi ya shigo dakin cikin takun sa, tsaye yayi gaban gadon ta hannayen sa duka biyu soke aljihun farar jallabiyar da ke jikin sa yana tunanin ta yanda zai tayar da ita.


 "Inaya Inaya" ya fada cikin wani tone da alama baccin bai Ida sakin sa ba, daddan kamshin sa ta soma shaka kafin ta jiyo muryar sa da ta da da kauri saboda bacci tana kiran sunan ta.

A hankali ta soma bude idanun ta da suka yi laushi kana ta sauke su a kan sa, kamar a mafarki ta ganshi tsaye a gaban ta, cikin wata white haramain jallabiya da ta matukar dauko sa, sai bakaken slide slippers din Nike da ke kafar sa, fuskar sa fayau alamar daga bacci yake shima.

   Saurin mikewa tayi zaune tana janyo quilt din ta rufe jikin takun sosai.

    

    Kamar bai ga abinda tayi ba "it's time for prayer" abinda ya fada kenan ya juya yana bar mata dakin tare da ba mata kamshin sa.

   Yar ajiyar zuciya ta sauke har da dafa kirji, wannan is the closest they have ever been, ita da shi kawai a in a room, a gidan da ba wasu halittu bayan su, shiyasa gabakidaya komai ya kunce mata ta kasa furta komai a lokacin da tayi ido biyu da shi.


    Zuro kafafun ta tayi tana sanya bedroom slippers  din da ke bakin gadon ta ta nufi bandaki.

Dauke da alwala ta fito ta nufi prayer corner da ke dakin.

   Bata koma bacci ba har sai da ta yi Aazkar din ta da karatun qur'ani, har idanun ta ke lumshewa ko da ta isa gado, ba bata lokaci wani irin baccin gajiya ya zo yayi awon gaba da ita, domin ba wani bacci ta samu ba a Daren jiya hakanan rabon ta da samun isashshen bacci tun da aka soma gudanar da shagulgulan buki.


      Ba ita ta tashi ba sai after 11am, kai tsaye ban daki ta fada ta tsalo wanka, ta fito tana ta zuba kamshin warm vanilla body wash din bath and body works.

    Cikin wani tsadadden Swarovski lace mara nauyi ta shirya baki mai adon gold a jiki, kamar hadin baki saukowar ta yayi dai dai da shigowar su Amna da Amal.

    Cikin jin dadi suka yi hugging juna

"Amarya an sha kamshi, ya kwanan bakun ta" Amal ta fada, Amna ta chafe tana fadin "in jin dai angon baya nan, domin in samu damar tsokanar ki da kyau"


    Hararen wasa tayi mata ba tare da ta amsa ta ba, Amal ta ja hannun ta suka nufi daya daga cikin kujerun da ke falon yayin da Amna ta nufi dinning Tana jere abincin da suka zo da shi.

    "Am sure yaya Em baya nan cause banga motar shi ba" Amal ta fada

Da kai ta amsa ta kawai

"Ta ya zai bar muna amaryar mu ita kadai gaskiya ya cancanci query" 

   Waina (masa) da miyar naman kai ta zuba dai dai wanda zata iya ci ta zauna kan dinning tana ci.

  Zuwa zuhr gidan ya soma cika da mutane, wasu su zo su wuce wasu kuma su zauna.


    Sakina ta leko daya daga cikin dakunan da ke kasa a lokacin da ta ke zaune tsakiyar su Amna suna ta hira

"Inaya zo" ta fada tana juyawa kitchen, mikewa tayi ta bi bayan Sakinar, su biyu ne a kitchen din ita da Hanifa suna zuzzuba lunch din da aka shigo da shi a manyan dishes.


    "Yanzu mijin ki ya shigo yayi sama, ki bi shi ki ji ko akwai abinda yake bukata"

   Dan shiru tayi tana zaro idanun ta waje Cikin faduwar gaba ta zubawa hanifa su da ke magana, tana  jujjuya ta yanda zata bi bayan yaya Em kamar wasu normal couples.