Part 4
by @chefmuaysh
RAYUWAR MARYAMA*
~By MUAYSHGRAPHICS~
_BOOK 📚 1_
*Kuka suke sosai ganin yanda da gaske tafiya zaiyi yabarsu Sadiqu ya dubi najibu yace ka kula da Maryama kaji kanina nima zandawo mu zauna tare kudaina kuka kunji Maryama da ta maƙale masa a jiki tace yaya don Allah katafi dani kaji*
*Banason zama gidan nan maman Hafizu kasheni zatayi idan katafi yaya don Allah kar katafi kabarni nima inaso inje Almajiranta 🥺*
*Wasu hawaye Masu zafi da yake ta ƙoƙarin ɓoyewa ne suka gangaro masa duk yadda ya so ya daure abin ya gagara saeda ƙannen nasa suka karya masa zuciya*
*Tsugunnawa yayi yajawo Maryama itama ta tsugunna yafara goge mata hawa yana kauda kansa domin bayason suga shima yana kuka ya riko hannun najibu yace cikin dauriya bakunaso in zauna tare daku ba*
*Da sauri suka gyaÉ—a kai a tare yace to kudaina kuka kunji idan naje bazan daÉ—e ba zandawo amma idan kuka cigaba da kuka idan natafi ma bazan dawo ba*
*Da sauri suka goge hawayen nasu sukace mun daina yaya amma dukda haka ƙwalla bata daina zubowa a idanuwan Maryama ba*
*Sadiƙu ya kama hannunsu ya haɗa a tare yace kunga yanda muka haɗa hannunmu haka koh sukace eh yaya yace toh zandawo muƙara haɗa hannunmu kamar haka kunji*
*Sukace toh yaya gaba É—aya suka rungume juna Sadiqu baya bari suga hawayen sa sae yayi sauri ya goge kafin sugani*
*Kana ina ɗan jakar uba tun ɗazu malam ya shirya kai yake jira har yanzu baka gama tattara komatsan naka ba ko kuwa wani munafurcin kake ƙulla musu*
*Muryar Balaraba tasa kowa ya kama kanshi yana zare idanuwa nagama maman Hafizu sadiƙu ya faɗa yana mai ɗaukar ɗan ƙaramin buhun daya haɗa kayansa suka fice*
*a hankali suke tafiya har suka isa bakin titi inda zasu hau mashin zuwa tashar da zata kaisu ƙauyen da akace za,a kaishi almajiranta a kano*
*Saeda mashin ya tsaya suka hau Sadiƙu yakasa jurewa nan take yafara hawaye wannan nabin wannan wai da gaske dai almajiranta za,a kaishi kuma a rabashi da ƴan uwansa yanaji yana gani*
*Najibu da Maryama kau saeda Balaraba ta tasa ƙeyarsu gida domin kuka suke kamar ransu zai fita haka suka dawo suka cigaba da rayuwa kamar yanda aka saba saedae yanzu ba mai rarrashin najibu saidai shi ya rarrashi ƙanwarsa Maryama*
*Yau da gobe ba wuya a wajen Ubangiji shekara kamar kwana har an shekara biyu da kai sadiƙu almajiranta amma malam habu ko zancen sa bayayi bare yayi maganar zuwa ya gano shi idan ma najibu yaso tada masa da zancen sai yace karya damu shima zai kaishi can wajen ɗan uwan nasa sai su zauna tare*
*Hakan yasa yake yin shuru domin baya son yayi nesa da Maryama kamar yadda sadiƙu ya bashi amanar mahaifiyarsu*
*Safinatu tayi wayau takai shekara uku da ƴan kai gashi sun shaƙu da Maryama domin bata yarda da kowa idan ba,ita ba*
*Ita kuma Balaraba tana bawa Maryama safinatu badon komai ba saedae don ta huta da raino hakan yabasu damar shaƙuwa wanda a yanzu ta tsani hakan domin ita ba haka taso ba*
*Kamar kullum dai Maryama tariga tasaba tasan aikinta bare yanzu da taqara girma abin ma baya damunta tasan data gama wannan zata kama wannan itada hutawa kuma sai Balaraba ta Kwanta baccin dare*
*Wanke wanke take hankalinta kwance tana rera waƙarta ƙasa ƙasa don kar Balaraba taji ta tafito ta cigaba da dukanta*
*A hankali safinatu take tahowa wajenta tana kiran sunanta Maryama da sauri ta juwo tace kai safinatu jira anan karki karaso nan ki ɓata jikinki kinji yanzu zangama inzo muje muyi wasa ko*
*Safinatu ta taɓe baki tana shirin yin kuka saboda Maryama tace karta ƙaraso inda take ai da sauri Maryama ta wanke hannunta ta,isa inda take tana faɗin kar kiyi kuka ƙanwata kinaso in baki alawa*
*GyaÉ—a kai tayi alamar eh sai Maryama taÉ—auko wata kujera ta ajiye mata tace to zauna anan idan nagama sai inje insiyo miki alawar ko*
*Duk tsoron Maryama kar Balaraba taji safinatu na kuka tazo tahau ta da duka shiyasa taketa ƙoƙarin lallaɓa ta tasamu tayi shiru kota gama aikinta sana su fita*
*Yau da wani irin zazzaɓi da ciwon kai ta tashi ko idonta bata iya ɗagawa sosai tunda balaraba taga yau bata fito ba da wuri tafara masifa*
*Wato yarinya kin girma shine lokaci har yayi wanda sai nazo ina tashinki daga bacci ko haramta kitashi tun kafin nazo na sameki*
*Maryama batasan me yake faruwa ba duk Abinda Balaraba takeyi domin har tafara fita hayyacinta wani irin zazzaɓi ne mai zafi ta tashi dashi*
*Da Balaraba tagaji da magana taji shuru hakan yasa tashiga dakin domin taga ko bata cikine sai taganta a kwance ta ƙarasa tanata magana amma taji ta shuru koda ta taɓata taji jikinta da wani irin zafi anan tagane batada lafiya*
*Amma abinka da wadda rashin tausayi yayi yawa hakan bai dameta kawai tafita ta cigaba da aikace aikacen gidanta tunda tasan ko ta kurɓi Bala,i yau dai yanayin jikin Maryama ba abinda zata iya yiwa kanta bare ma ta tashi tayi aiki*
*tana aikinta tana faɗanta wlh bari malam ɗin yadawo shima ai nagaji da irin wannan rayuwar hakanan yarinya ta lanƙwashe min saboda in zama baiwar su ko*
*Jikin Maryama gaba yake ƙarayi bata fito ba har malam suka dawo shida najibu tunda najibu yaga halinda ƴar uwarsa take ciki hankalin sa ya tashi yaje yana faɗawa mahaifin nasu halinda take ciki*
*Malam habu yace to yaje ya É—ebo tafasar masar ayi mata surace ai kuwa hakan akayi amma jikin Maryama dai sai a hankali gaba É—aya hankalin najibu yaga ma tashi da yanayin jikin nata*
*Fita yayi da ƴan kuɗinsa da yake tarawa a cewarsa zaije yagano ɗan uwansa sadiƙu a ciki ya dauko wasu yafita yaje chemist din dake kusa dasu yasiyo mata magani da awara a leda*
*A ɓoye ya shigo dasu gidan ya nufi dakin nasu domin tunda sadiƙu ya tafi tare suke kwana Shida Maryama a ɗaki ɗaya*
*Da ƙyar yasamu taci awarar bawata ta kirki ba sana ya lallaɓa ta tasha maganin ta kwanta sae bacci yayi awon gaba da,ita*
*Wajen yamma ta tashi tafito tadaura alwala takoma daki domin yin sallolin da tarasa batayi ba nan ta shinfiɗa dan kwalinta a zaune tayi sallah domin jikin nata babu ƙwari*
*Tananan zaune tagama sallah tana addu'ar ta taji sallamar najibu ya shigo bayan tagama ta juya tace masa yaya sannu da dawowa*
*Yauwa Maryama ya faɗa yana zama ya jikin naki yayi sauqi dai koh eh yaya naji sauƙi tafaɗa tana ƙoƙarin cire hijabinta da tayi sallah*
*Abin tausayi yara ƙanana sun zamar ma kansu uwa da uban juna ba wanda yake jin tausayinsu sai su kaɗai suke tausayin kansu mahaifin nasu da suke dashi kwata kwata hankalin sa baya tare dasu dan uwan nasu wanda yazamar musu uwa da uba kuma an nesanta shi dasu*
*Shekara biyu harda wani abu kenan basu ganshi ba ko labarin shi ma basuji ba shima kuma bai waiwayo su ba ko yana ina oho*
*Maryama ta kalli najibu a raunane tace yaya wai yaushe yaya sadiƙu zai dawo saeda yaja numfashi sana ya dubeta yace ki kwantar da hankalinki kinji Maryama nasan shima yana can amma yana tunanin mu*
*Idan ma bai zoba namiki alkawarin da kaina zanje na gano shi sai indawo ƙwalla tafara tarawa tana faɗin amma dani zakaje koh yaya bazaka tafi kabarni anan ba koh kamar yanda yaya Sadiƙu yatafi yace zai dawo amma bai dawo ba*
*Baisan sanda ƙwalla ta taho masa ba saidai yaji tanabin fuskar shi ah ah Maryama ki daina fadin haka kinji yayanki ba tafiya yayi ya barki ba nasan zai dawo zaizo garemu kinji*
*Zaizo muƙara haɗa hannunmu kamar yadda mukayi a baya nima bazan tafi in barki anan ba zan zauna dake kinji ko idan naje ma* *zandawo kawai zan gano mana ya lafiyarsa take a can ɗin*
*Toh kawai Maryama tace amma sam ita bata gamsu da yatafi ɗinnan ya kyaleta ba'' haka dai kawai zata haƙura amma badon taso ba*
*Maryama tasamu sauƙii alhamdulillah domin har ta cigaba da aikace aikacenta kamar yadda tasaba a gida*
*yau malam habu bai *samu zuwa wajen aikinsa ba inda yake gadi saboda zazzaɓi da yake fama dashi a gida ya wuni tunda sukaje kasuwa shi da najibu*
*A ɗaki ta iske yayan nata yana haɗa kayansa domin yace mata yau zai tafi neman ɗan uwan nasu sadiƙu waje tasamu ta zauna domin ta rasa me yake mata daɗi a Rayuwar ta*
*Nan yayi ta bata baki yana lallaɓa ta domin ya lura duk a dame take da tafiyar tasa bataso yatafin saedae itama tanaso taji lafiyar ɗan uwan nata saeda* *yagama shirya kayansa tsaf sana yace ta duba masa idan babu kowa yafita domin ba wanda yasan zaiyi tafiyar sai ita kaɗai*
*Itama yace mata koda an tambaye ta tace batasan inda ya tafi ba domin bayason a hanashi tafiya kuma baya so shima ace za,a kaishi almajiranta a rabashi da Maryama*
*Gashi dama yaji Balaraba tana cewa malam koda za,a kaishi almajiranta baza,a haɗa su waje ɗaya ba shida sadiƙu wai bazasu yi karatu ba idan suna tare*
*Saeda ta duba ta tabbatar da bakowa ta gaya masa sana yafito yayi gaba yace ta iske shi bayan gidan nasu yana jiranta*
*A hankali tasa takalmanta bayan yatafi saÉ—af saÉ—af tana kokarin fita ta bishi ina zakije munafuka kike sanÉ—o ko sata kikamin ne*
*A furgice ta juyo tace ba inda zanje tana in ina'' toh zonan ki wanke kayan safinatu gasu can ki kwaso su duka hada na Hafizu amma naga nashi basuda yawa ma*
*Batasan karyar da zata yimata ba tafita kawai sai ta shige ta tattaro uwayen kayan nasu da suka tara da yawa tili guda ga duk sunƙara yin datti a inda take nake su a ƙasa*
*Jin shurun yayi yawa ne yasa najibu dawowa domin yaga ko lafiya tun kafin ya shigo gidan yake jiyo Muryar Balaraba tana faÉ—in gasunan Allah yasa wasu basu fita ba kiga yanda zanyi dake a cikin gidan nan yau*
*Hakan ya sanya shi laɓewa daga kofar gidan can kuma yaji tana faɗin salan idan nafita kema kisa kafa kifita saboda naga kina wani sanɗo dama bansan ko da ubanwa zaki haɗu ba*
*Da sauri najibu ya ɓuya bayan wani itace domin yaji tahowarta zata fita ai kuwa tana fita ya shiga gidan wankin take tana sharɓar hawaye ya karasa wajenta*
*Yaya baka tafi ba dama tafaÉ—a tana sakin rigar da take wankewa ''eh ban tafi ba Maryama ina can ina jiranki shine nadawo inga mai yahana ki zuwa ashe wanki zakiyi*
*Eh kawai tace masa takasa magana nan yashiga rarrashi a hankali suke magana domin malam yana dakin balaraba yana bacci kaje yaya tafaɗa cikin ƙarfin hali tareda cigaba da wankin tana kuma yi masa addu'a Allah ya tsare*
*Kiyi haquri kinji Maryama ta me kike so in siyo miki idan nagani a hanya ka siyomin kayan wasa yaya da Ć´ar tsana tafaÉ—a tana kakalo murmushi*
*Toh yace ya juya yafita gaba dayansu suna jimamin rashin juna da zasuyi ba kamar* *Maryama domin shima ita kawai yake tausayi*
*Haka sukayi sallama da najibu bata samu damar rakashi ba ta cigaba da aikinta*
*Toh anan zamu tsaya masoyana ❤️ inafatan dai wannan littafi yana saku farin ciki mu haɗu a comment section naji ta bakin ku*
*Na sadaukar da wannan page gareku gaba É—aya masoyana masu bin wannan littafi*
Karki bari karku bari kar mu bari abamu labari top 3 Na A'ishatu Hamza wadda kuka fi sani da Muaysh graphics 🤟 🤗 basai na faɗa muku ba littafaine wanda daga jin sunayen su zaka gane cewa na musamman ne
(UMMU OR SALMA) UMMU kO SALMA
(ORPHANAGE HOME) GIDAN MARAYU
(MARYAM’S LIFE) RAYUWAR MARYAMA
Wannan shine account details din mu 👇
3201868037 A'isha Hamza First bank
Ko kuma 9131096058 A'isha Hamza Opay bank
RAYUWAR MARYAMA akan 400 kacal GIDAN MARAYU akan 400 sai kuma UMMU KO SALMA akan 400 ga wanda yake buqatar duka zai biya 1000 instead of 1200 sana zaka tura receipt after payment a wannan number *** ta whatsapp