Rudin Zamani

chapter 2

by @rularnt

Ciro wayan Anisha tayi daga jaka. Nadiya tace:

 “Wanene?”

Anisha ta duba screen din, da murmushi a fuskarta tace:

 “Daddy yo ne.”



Da sauri Nadiya tace:

 “Pick it dan Allah, ki sa mun a speaker, tunda kema baza ki iya tashi ba.”

Dan gyara zama Anisha tayi, ta yi picking call din ta sa a speaker. Samha dai kallon Nadiya take, zuciyarta cike da takaici da mamaki game da irin rayuwar da take yi.

Daga cikin wayar suka ji kakkausar murya, mai nuni da cewan the caller is around his late 50’s:

 “Baby na, ya kike?”


Kakalo shagwaba Nadiya tayi tace:

“Haba Sugar, kasan bana iya baccin dare ba tare da mun yi proper sallama ba. Shine baka sake kirana as you promised ba last night.”


Alhaji Bala, wanda aka fi sani da Barrister,  ya dan murmusa har a na jin shi daga wayan sannan yace:

“Dadi na dake baby akwai shagwaba, gashi nan har kin sa Big D yana motsi a cikin wando.”


Dariya ne ya kusa kwace wa Saudat da Anisha. Samha kuwa mamaki ya cika ta—surprised by what she just heard.

Murmushi Nadiya tayi tace:

 “Toh idan ban maka shagwaba ba, wa zan mawa?”


Alhaji yace:

“Ai babu wanda ya isa ki mashi shagwaba sai ni. Daman kiran ki nayi ne in fada maki ina gari, anjima zan aiko driver ya dauko ki. And guess what? Your iPhone 17 is here with me.”

Ihu Nadiya ta saka a mota dan murna. Duk da takuran kayan dake jikinta, sai da ta juya ta fizge wayan daga hannun Anisha, wacce ta sa hannu ta toshe bakinta don kar a ji ihun ta da Saudat suna taya kawar su murna.

“Sugar! Fada min me kake so a fadin duniyar nan yau n maka!”

Dariya sosai Alhaji yayi yace:

“Ke dai ki zo da shirin ki yau, dan ba ni kadai bane. Get ready for threesome…”


Da sauri Nadiya ta kashe handsfree, ta sa wayan a kunnenta. Samha ta fahimci dalili—ba ta so ta ji abin da zai biyo baya.

Bayan wayar ta katse, jiki babu kwari Samha ta tada motar. Babu wacce ta ce kala a motar har suka kai apartment din da su Nadiya ke zama. Wanda ba gidan iyayen su bane musamman suka karba hayan gidan suna zama su su uku… Nadiya, Anisha da saudat.

Da suka sauka, Saudat da Anisha suka ce:

“Thank you Samha, you saved our asses from humiliation din rashin mota yau. Na kosa a kammala gyaran motan Nadiya….”


Nadiya ma ta juya ta kalli Samha tace:

“Think over what I told you. In as much as you want to gain your crush’s attention, you need to wise up, my friend. Domin Dr. Tariq looks like a highly civilized man wanda daga ke har ma da wasu mata da dama na mararin shi.”


Kallon banza Samha ta yi mata—kamar yadda Nadiya tayi expecting—sannan fuska a hade, cike da takaici tace:

“Idan har duk wannan,”
(ta nuna kayan jikin Nadiya)

“da wannan,”
(ta nuna wayan hannunta)

“da kuma irin maganganun da na ji daga bakin wannan katon banzan over the phone—idan duk su ne wayewa ko trend that I have to follow…”


Ta tsaya kadan, idonta na nuna tsantsan bacin rai sannan tace:

“Toh ki sani babu komai tattare da shi face RUDIN ZAMANI, kuma babu inda yake kai mutum sai HALAKA.”


Ta cigaba:

 “Ni da kike gani dinnan kin fi kowa sanin da gata na da kuma galihu na gida da waje ma kuwa, sannan kuma da sana’a ta. Ko ina da sha’awar wannan so-called trend din, ba a wahale zan yi shi ba—amma ba shi ne a gaba na ba.”

Ta ja numfashi:

 “Now please, can you excuse me? Ina bukatar tafiya. Ana jiran dawowa na a gida.”

Sauke ajiyan zuciya Saudat da Anisha suka yi, suka ce mata sai da safe. Nadiya bata ce uffan ba—da kyar ta fita daga motar, hannu daya rike da waya, dayan kuma na rike da gown dinta dake jan kasa.

Samha ta bita da kallo, zuciyarta cike da takaici— a ranta she is wondering how she has been able to cope friendship with girls like these. Duk da ta san basu jin magana, tayi iya kokarin ganar da su, But today she regrets ever knowing them not after all she heard over the phone…

Daidai Nadiya ta kai gaban gate din gidan, ta juyo suka yi ido hudu. Girgiza kai Samha tayi, hawayen tausayi na taruwa a idanun ta, kawai ta ja motarta ta bar wajen.