Chapter 10
by @mrsalkali01
💫 ƘAUNA DA KADDARAH💫
✍️Mrs Alkali
Page 1️⃣0️⃣
VIP SECTION – CLUB
Ramlart zaune kusa da Al’ameen da Zuly, suna dariya suna shan drink (non-alcoholic mocktail) fiskar su cikin nishaɗi. Ramlart tana tura hotunanta a Snapchat da Instagram story –nata, ta rubuta, “living my best life” caption, d'in ta.
ZULY ce ta leƙa wayar Ramlart tace.
"Yauwa ta waje na sai dake haka nake so, kiyi komai ba komai , wlh, a duniya muke ,aljannah ta mai rabo ce."
Cike da Nishad'i RAMLART tace .
"Zan koya masa rayuwa! Naga yanzu shi da soyayyarsa suna son su dawo mini jidali, ya kamata ace kowa ya ji da kansa, wannan lokaci nane."
Takara sa maganar tare da juya wayarta, tana kallon hoton AA Turaki a profile picture dinsa, ta ɗan langwabar da kai tace.
"In har ni Ramlart ce, sai na mallake zuciyar ka, babu wata ya' mace da zan bawa damar mallakar zuciyar ka, i promise u that, ta ƙarasa maganar tare da juya manyan idanun ta."
Muryar DJ ya ne ya ɗaga wajen da sauti, nan take suka sake shiga cikin nishaɗi. Sannan Ramlart ta miƙe da ƙarfi ta fara rawa a dance floor, tana janyo hankulan mutane, zuwa kanta.
Zuly ce tayi dariya tare da kallon al'ameen dake manne a jikin ta, cikin narke wa tace masa baby.
"Yau dole club ɗin nan ya ƙonu da sunan mu!" Sabida babbar yarinya ta baiyana, murmurmushi al'ameen yamata tare da ci gaba da shafa jikin ta.
Hasken disco lights na ta yawo, music mai ratsa jiki yana tashi. Dancers sun cika dance floor, ana rawa da annashuwa. Ramlart na tsakiya cikin masu rawa, tana juya jiki da salon rawa mai jawo hankalin mai kallon ta, Hannunta a sama, idonta a rufe, tana jin music din har cikin zuciyar ta.
Wani gaye, kyakyawa, cikin kaya masu tsada yana zaune a VIP table yana shan drink. Daga can yana hango Ramlart, a hankali ya tsaya kallon ta yana murmushi, a lokaci guda yana kai drink bakin sa yace.
“Wannan cikar ba zata kubuta ba a daren nan dole ne na kasan ce yare da ita.”
Cike da boomcing Ya mike ya nufo dance floor kai tsaye, yana tafiya yana bubbudawa, kamar wani sarki, sai Da ya ƙarasa kusa da Ramlart sai ya ɗan tabo hannunta a hankali Ramlart ta buɗe ido ta kalle shi, sai ya ɗan yi mata murmurmushi tare da rage sautin Muryar shi kamar mai rada yace.
“Ni da ke sai mun karya wannan dance floor tare in ba damuwa ina son muyi dancing tare.”
Ramlart ta yi murmushi, sai ta bashi hannun ta, Suka fara rawa tare, jikin ta a jikin sa. Music yana ta Kara karfin sauti, A hankali sai ya sanya bakin sa a kunnenta yana cewa.
“Na shirya baki daren da bazaki taba mantawa da shi ba in kin shirya let's go…”
A haka ya rika janta zuwa VIP section, inda aka kawata shi da curtains masu haske da d'aukar hankali ,nan fa ya shiga romancing din ta cike da kwarewa, a haka ramlart ta fita daga cikin haiyacin ta, har ya samu nasara ya biya bukatar sa, da ita, Bayan mintuna kadan, ramlart ta fito daga wajen gashinta sun dan bazu, murmushi take cike da gamsuwa.
Ramlart tana shirye-shiryen tafiya, tana gyara dan kwalin ta da d'an lullubin veil din ta, Gayen yana tsaye yana kallon ta da murmushi, yana da confidence irin na wanda yasan ta kan bariki, Wurin shiru ne, fitilar lounge din na launin ruwan hoda da blue suna ba da haske na musamman , wanda yake kara musu shauqi.
A hankali yake matsowa kusa da ita, yana kallon ta cike da shauki , yace.
"Kin cancanci fiye da haka, Ramlart… amma na bar miki wani abu a matsayin tunawa da wannan daren."
Ya ciro wata bundle na kudin kasashen waje – euro da dollars – ya saka a hannunta, sannan yace .
"Ga wannan… just for your time and your shine."
Ramlart ta karba, tana murmushi tana kallon sa da murmushin da ta saba amfani da shi wajen nuna farin ciki da yaudara.
Cikin d'an basarwa ramlart tace.
"Wannan fa ?."
Ya dauko wata karamar card mai sheki, ya mika mata. Akan card din: sunansa, lambar waya, da adireshin email ne.
Kallon ramlart yayi yace.
"Sunana Majeed Ibrahim Jatau, kuma mahaifina shine Honourable Senator Ibrahim Jatau – sanannen dan siyasa a kasar nan."
Ramlart ta zaro ido waje, sai kuma ta saki murmushi cike da farin ciki da burin sabuwar hanyar daukaka da ta zo mata a cikin sauki.
Tace.
"Oh wow… nice to meet you, Majeed."
MAJEED ne ya Dan matso kusa da ita.
"Kuma wannan – card ɗin nan – ya bude miki kowanne kofa idan kina bukatar wani abu let me know."
Yana gama fada'r haka Ya lumshe ido yana sumbatar goshin kafin yace.
"Let’s say this is not goodbye… it’s just the beginning."
Ya juya cikin class, na yara marassa jin magana, ya bud'e mota ya shiga. Ramlart ta tsaya tana kallon bayan motar na barin wajen, tana lumshe ido cike da tunani da wani sabon tunani a cikin ranta.
Zuly na jiran ta a gefe tana mata dariya.
“Na faɗa miki... wannan shine maganin ciwon tunani, amma kinbi zaki kashe kanki a banza akan wani da namiji.”
RAMLART ce ta busa iska a bakin ta tare da cewa .
“Hmmm, ai yanzu naji sauƙi. Let’s go... kafin wancan mutumin ya tashi ya san bana cikin gidan.”
Haka al'ameen ya yi driving d'in su, Suna isa bakin gate na gidan, Ramlart Ta gyara shigar ta, ta feshe jikin ta da turare sannan ta ɗan dafa hannun ta a jikin k'ofar motan.
ZULY ce ta sheke da Wani irin dariya tace.
“Ki tabbatar baki bar wani alamar da zata nuna cewa kin fita, club.”
RAMLART ce ta juyo tana kallon Zuly tace.
“Don’t worry. Nasan gidan nan fiye da yadda su ke tunani. Allah ya saka da alheri Zuly.”
ZULY ce ta daga gira tana dariya tace.
“Alherin club ko? Hahaha... Mun kusa cin nasara, bestie.”
Ramlart ta yi sallama da su, ta rufe kofar mota sannan ta ratsa ta bayan wani bangon ginin gidan inda take da wata sirrin hanya ta musamman da take shiga daga baya ba tare da an lura da ita ba, ta yi wuff ta shige ciki, A hankali, ta shiga gidan cikin nutsuwa tana duba gefe da gefen ta domin tabbatar da cewa kowa yana bacci, babu wanda ya ganta.
A dai-dai lokacin, ake kiran sallan asuba ya fara tashi daga masallacin anguwa dana cikin gidan AA Turaki, Gidan na cikin shiru, haka Ramlart ta kutsa kanta zuwa part ɗinta tana mai sauke ajiyar zuciya, dayiwa Allah godiya, naganin babu wani mahluqi da ya ganta.
Bayan shigan ramlart Cikin dakin ta, ta cire veil da takalman ta high heels dinta sannan ta zauna akan gado tana kallon kyautar kudaden da Majeed ya bata da card ɗinsa.
Wani murmushin jin dadi ne ya subuce a saman fiskarta a hankali ta furta.
“Senator’s son… hmm. Ramlart, kin soma samun hanyar da zata sa ki mallaki duniya, yadda kike so.”
Batare da ta gabatar da sallan asuba ba ta kwanta. Ba da jimawa ba, barci mai nauyi ya dauke ta.