SAFARA A TAƁO

04

by @gureenjoh

SAFARA A TAƁ


FATIMA MUHAMMAD GURIN 

*GUREENJOH*


*ADABI WRITERS ASSOCIATION*


*PAID BOOK*


*004*


Tun fitowarsu daga gidan take kuka take kuma kwashewa Hibbah Albarka yayinda Alqaseem ke ta ƙoƙarin ganin ya rarrasheta.

"Haba my love! Har yaushe za ki tsaya a kanta kina ɓata precious hawayenki uhmm?"

"Ba Za ka gane bane amma Hibbah ta jima tana kwacemin abin da yake ni ya kamata in same shi, ta jima tana dakile min farin ciki a gidan nan a aurena ma bata bar ni ba?"

Ya riƙo hannunta ɗaya yana ɗan murza wa a hankali 

"A yanzu kam kin mata nisa My love kin manta ke matar aure ce? Matar ma ta Alqaseem Abba? Ko ta ina kin ƙere mata don haka ki kwantar min da hankalinki ki manta da wacce duniya duka suke kan jefa mata maganganu marasa daaɗi, ke fa a yanzu ko a gaban Allah ma kin fi ta daraja"


Numfashi mai nauyi ta sauƙe sai ta tuna yadda hibban ta shiga gida a haukace, ta tuna wai yau Hibbah ce ake zagi a kan idanunta amma bata tanka ba tuni murmushi ya maye gurbin damuwa dake fuskarta ko a haka ta gode Allah, ta tabbatar a yanzu rayuwa sai yayi wa Hibbah kunci ba a gida ba ba kuma a waje ba ko ina zai zama ƙuna a gareta hakan kuma ya haskaka ranta, ta tabbatar duk gidan sai sun yi murna daga ɗakin su har ɗakin Hajiya Zakiya.


Bata sake jinta cikin natsuwa da farin ciki ba sai da ta kalli gidan da Alqaseem ya shigo da ita da sunan nata, kalar motocin da suke jere wasu a rufe, kalar irin tsari da tsaruwar gidan sai taji zuciyarta kal lallai ta yi dace da ta zaɓi Alqaseem dama chan ta tsammaci hakan daga gareshi saboda irin motoci da yake hawa da kuma shigar da yake ta fara kula shi, tana so ko ta wannan ɓangare ta nunawa su Hibbah ita ɗin ta ƙere musu, kyaun nasu na banza ne tunda daga mijin da Hudah ta aura zuwa wanda yake shirin auren Hibban ya fasa duk basu kai nata dukiya ba ko a farce kuwa.


Cike da farin ciki ta taka ƙasan shimfidadden interlocks da yayiwa gidan kawanya hannunta ɗaya cikin na Alqaseem ya taimaka mata ta ƙarasa sauƙa ya rufe gambun motar suka nufi ciki duk haƙorinta waje wane gonar auduga, bata ƙara tabbatar da yana da dukiya ba sai da suka shiga ciki Dukda duk kayan ɗakin mahaifinta ne yayi mata bisa ra'ayin ta sai dai deco da interior Designs na parlorn sun tafi da ita ga wasu chandliers da bata taɓa ganin ma kalar su ba a duniya Dukda nata mahaifinma mai arzikin ne. Har ɗaki ya raka ta 

"Ki shiga kiyi wanka ki samu ki huta ko baby? Ko in zo in yi miki da kaina?"

Ta karya wuya tana cewa 

"uhm uhmm"

Yayi murmushi yana kashe mata ido kan ya juya ya fita ya barta da blushing har da juyi cikin tsananin farin ciki.


****


Su Hudah suna isa gidan da yake mallakin Mu'azzam mai ɗauke da ɓangarori biyu wanda ɗayan ya kasance na mahaifiyarshi ce da suke kira Hajiya sai ƙanwarshi da suke tare falmata, kai tsaye sashensu yayi da ita saboda ta huta don ba karamin sara mata kanta ke yi ba ga damuwa fallll zuciyarta yana tura kofar suka yi ido biyu da Hajiya da falmata da suke zaune cikin parlorn murmushi suka sakarwa juna ya matsa Hudah ta shigo kanta ƙasa ta tafi wurin kafafun hajiyar ta shiga gaisheta.


"Sannu Hudah"

Hajiya ta amsa da shi yayinda falmata ma ta yi mata sannu.

"Ki isa ciki ki huta bari zan yi magana da Mu'azzam din"

Miƙewa tayi ta nufi corridor da ta gani Dukda bata san ma kan gidan ba, ɗakuna biyu ta gani sai dai duk wanda ta taɓa a rufe Juyowa tayi da niyyar dawowa cikin parlorn ta faɗawa Mu'azzam din kila ya bata makulli sai ta tsinkayi Muryar hajiyar tana cewa 


"Ni dai Allah ya gani ba don kaddara da ya riga fata ba da baka amshi wannan yarinya ba, tabbas ba don sai da aka ɗaura wannan abin ashhan ya faru da biyunta ba da na hana, ina dalili? Haɗa zuri'a da gurbatattu? Kaima ka san abokin ɓarawo baya rasa zama ɓarawo ka san ko tare suke yi na wanchan ɗin ne ya fito fili?"


Maganganun ba ƙaramin duka suka kai mata ba a zuciya, jiri ya nemi ɗaukarta saboda tashin hankali tuni idanunta sun rine sun sauya hawaye na sintiri bisa saman fuskarta, kallon da aka juye yi musu kenan? Ashe ana judging wani da laifin wani? Innalillahi wainna ilaihi rajiun..! Take ta nanatawa ta juya da sauri ta bi wani karamin hanya da ta gani sai ya kaita zuwa ga kitchen ta ga wani kofa ta buɗe ta fita haraba ce mai faɗi yana dauke da bishiyar almond wanda muka fi sani da umbrella ƙasan bishiyar an zagaye da interlocks kai taje ta zauna tana kuka sossai, ta jima cikin wannan yanayi kan ta ji motsi sai tayi hanzarin share fuskarta Dukda idanunta basu ɓoye yanayinta ba ta yi yunkurin daidaita fuskarta ta miƙe tsaye daidai lokacin da Mu'azzam ya tura kofan ya fito.


"Hudah! Ashe kofofin rufe suke shine kika zo nan?"

Ta gyaɗa kai murya a sanyaye ta amsa

"Na duba ganin a rufe shiyasa na tsaya kallon gidan kan ku gama magana da Hajiya"

Ya matso ya riƙe hannayenta 

"Fatan yayi miki ɗari bisa ɗari? Ko akwai abubuwan da kike so a chanza?"

Ta ɗan yi murmushi da bai kai ciki ba tace 

"Komai yayi masha Allah"

Janta yayi suka koma ciki ya kaita har ɗakinta ya tafi toilet ya tare mata ruwan zafi daga heater a bucket ya surka a jikin pampo ya kai wurin wankan ya ajiye kan ya dawo ɗakin 

"Ki shiga ki yi wanka bari na duba ko falmata ta kawo abinci sai ki ci ki sha magani ki samu ki huta ko? Na tabbatar kan nan ba zai rasa ciwo ba ga hidimar biki ga kuka"


Murmushi ta ƙaƙaro again 

"Na gode sossai"

Fita yayi ta miƙe ta zame kayan jikinta tana karewa ɗakin kallo daidai misali komai yana nan a tsare kuma kayan da Daddyn nasu yayi musu na ji ne da gani, gidan ba zata kira shi cikin na manyan kusoshi ba sai dai masha Allah yana da kyaunshi kuma a tsare yake, harabar bashi da girma don ba zai ɗauki motoci biyu ba sai dai ɗaya, an zagaye gidan da wasu koraye da jajayen furanni masu tsari babu mai gadi don haka ta ciki suke rufewa da jamlock idan ka kira sai a je a buɗe maka, mai gidan kan fita da key idan ya dawo ya kan buɗe ya shigar da motar shi ciki kan ya koma ya rufe, parlornta na da ɗan girma madaidaici dashi da ya ɗauke kujerunta da dining table ɗinta mai six chairs ba tare da ya takure ko ya matse chan chan ba, kitchen ɗinta ma madaidaici ne da aka shirya mishi carbinates farare masu kyau sai kayan kitchen da iyayenta mata suka yi matuƙar kokari a kai sun zuba abubuwan zamani da yaaayi kusan babu abin da zata nema ta rasa na aiki idan ta ga dama ma ba sai ta yanka komai da wuka ba don komai na gayu ne Aunty kubrah ta sayo su birjik daga Lagos nata da na Hibbah.


Ɗaki ɗaya aka bata don haka ɗaki ɗayan mahaifinta yayiwa kaya don na Mu'azzam da kanshi yayi kayanshi saɓanin wanda aka yiwa Hibbah na dakuna biyu da parlor biyu, inda na Amal dakuna har uku. Ko ɗarr bata ji ba don mahaifinsu kaya uku yake yiwa kowacce idan ɗakin naki uku ne a zube miki idan ɗaya ne a saka ɗaya a baki full kudin biyun ki nemi abin yi ko sana'a ko wani abin haka yayi musu, Dukda an yi ta cecekuce akan yanayin gidan na Mu'azzam ta nuna musu yana da rufin asiri kuma tana son shi a haka don shi mai zuciyar yi ne, don haka hankali kwance ta auri kayanta sai dai bata taɓa tsammatar irin kalaman hajiyar shi a kanta ko gidansu ba, har ta gama wanka ta fito ta shirya bata daina sake-saƙe ba tana gama sanya doguwar rigar ya shigo ɗakin.


Ta isa ta miƙa hannu da niyyar ta karbi tray da ya riƙo da kular abinci a kai ya zagayeta ya wuce yana furta

"wa ya gayamiki amarya na aiki a ranar farkonta gidan miji?"

Murmushi ta ɗan yi ya ajiye a gaban rug carpet ya zauna yana nuna mata gefenshi, a hankali ta taka taje ta zauna, da kanshi yayi serving ta karɓa ta fara ci a hankali tana juya kalaman mahaifiyarshi na ɗazu ta zura mishi idanu tana son jin ra'ayinshi a kan hakan sai kuma taji da ma bata tafi ba a dazu ta tsaya ta ji shi me yake tunani? Hure mata idanu yayi ta ɗan yi murmushi tana sauƙe idanun ƙasa har lokacin ita kaɗai ta san me ke wakana cikin zuciyarta.


*****


"Hibbah! Ki tashi ki sanya wani abu a cikin ki, zama da yunwa ko azabtar da kai ba shi zai sauya abin da ya riga ya faru ba, don Allah ki cire duk wani damuwa ki fuskanci Allah ki nemi yafiyarshi ki nuna nadama ki kuma nemi gafarar iyayenmu shine babba ba kuka da damuwa ba"

Ta ƙarasa tana janye mayafin, fuskar hibban da ya zama jajazir ya kumbura sossai ya bayyana idanunta a rufe, bandegi da aka zagaye kanta daga goshin ya ɓaci da jini saboda yanayin motsin fuskarta na buɗe ɗinkin dake a wurin ba tare da ta sani ba Dukda tana jin zafi da raɗaɗi daga wurin amma bata damu ba don na zuciyarta ya ninka hakan sau dubu.


A hankali tace 

"Yaya Zaitoon ba na jin yunwa"

"Dole ki ji yunwa Hibbah yaushe rabon da ki ci abinci? Kin san Hudah ce ta kira ni ta sa na mata alkawarin za ki sa wani abu a cikin ki? Don Allah ki tashi ko tea ne ki sha gashinan kinji?"

Hawaye ne yake gangara daga gefe da gefen idanunta zuwa cikin kunnuwanta har lokacin bata buɗe idanu ba ta san kowa ya tsane ta dama, kowa kyamarta yake ji a yanzu kila har Hudah ɗin ma a ƙasan zuciyarta nadamar zamansu ciki ɗaya take, ina ma za ta iya mayar da lokaci baya? Ina ma ana iya hasaso gaba kan bawa yayi wani kuskuren da zai sauya komai har ya kai ga buɗuwar baabin wani sabon ƙaddarar ba tare da shiri ko tsammani ba? 


"Hibbah!!"

Zaitoon ta ƙira tana jijjiga mata kafada, a hankali ta buɗe idanunta dake a suntume ta yunkura Zaitoon ta taimake ta ta kai zaune, tea ɗin ta shiga bata da kanta tana sha a hankali duk yadda tayi ma da ta ci cake slice ɗin ko samosa da ta haɗo da su ta ƙi iya tea din ta sha rabin kofi kan ta furta a hankali

"Na gode"

Ta koma da baya ta kwanta.


Yinin ranar gabaɗaya Zaitoon a ɗakin tayi shi Dukda daga ita har Hibbah ba magana suke yi ba amma bata bar hibban cikin kaɗaici ba kuma wanzuwarta ya hana kukan da hibban take yi akai akai, babu abin da ke ɗaga su sai sallah yayinda Hibbah ke kwance kawai zuciyarta blank ita Zaitoon tana operating waya ne, Dukda irin abin da take cin karo dasu a Twitter da tiktok na cin mutuncin Hibbah da zuri'arsu zuciyarta a kuntace cikin ƙuna da damuwa shikenan kuma mutane abin da suke jira kenan, babu mai tunanin wani hali wacce abin ya sama take ciki, babu tunanin ta yaya hakan ya kasance an haɗa da ita da iyayenta da basu ji ba basu gani ba ana zagi ba tare da an hango laifin shi saurayin da ya fitar da komai ba, akwai laifinta tabbas tunda Its willingly amma kalaman sun yi mata muni har bata sanin hawaye na gangaro mata chan ta ji Muryar hibban 


"A kaina ne ko?"

Ta Yi saurin share fuskarta 

"A'a Hibbah wani abin tausayi ne na gani anan"

Murmushi mai cike da ciwo ta ɗan yi wanda ko Bakinta bai buɗe ba tace 

"Uhmm Yaya Zaitoon ba sai kin ɓoyemin ba, na san halin mutanenmu na yanzu Jira suke, kaman adu'a ma suke abu ya faru da mutum mai muni da za'a yi ta yaɗawa, ko ban hau media ba zuciyata da kwakwalwata sun gama karanto min irin munanan kalamansu gareni ba ga mace ba, ba namiji ba, ba babba ba ba yaro ba duk zasu mance tasu matsalolin su rufu akan wannan."

Zaitoon ta share fuska tace 

"Abin nan yana min ciwo Hibbah, ba tun yau ba na kan ji tsoron yadda mutane kan haɗu a kafar sadarwa da gayya a tasa mutum musamman mace a gaba da kalar zagi da cin mutunci wanda ko kusa addininmu bata koyar da hakan ba, wani abin ma sirrinka ne amma wani na chan yana neman bankaɗowa duk don ya samu mabiyar da idan zai mutu a yau da wuya ɗaya daga cikinsu yayi mishi Adu'a bare ya bishi har kabari ya taya shi zama, irin wannan cin zarafi ya tura mutane dayawa cikin halin tashin hankali da damuwa haɗe da ciwo mai tsanani, wani fa za ki samu shima da nashi zunuban amma na wani chan yake hange, wata uwar ma da nata lalatacciyar gabanta take zagin wata uwar daban da bata iya ba yarta tarbiya ba wlh media na iya kai mutum wuta idan ba mu yi hankali ba"

Ta ƙarasa da tsananin damuwa.


Shiru kawai Hibbah tayi don a zancen ta fahimci abinda ya saka Zaitoon kuka iyayenta ake tuhuma da rashin bata cikakken tarbiya alhali basu Gaza mata ba, kaiconta a matsayin 'yar da ta janyowa iyayenta tozarta, wani irin turiri take ji yana huruwa daga cikin zuciyarta me amfaninta a duniyar? Bata chanchanci cigaba da rayuwa ba bare tsammanin farin ciki, ta gama taɓewa. Me soyayya ya ja ta ta aikata? Ina alkawarin da Sagir yayi? Ina rantsuwarshi na cewa iya idanunshi hotunan za su tsaya? Me yasa yayi mata hakan? Wani irin masifaffen kuka ne ya kwace mata ta shiga dukan kanta da ƙarfin gaske tana ihu da gunji.


"Hibbah! Hibbah!! Hibbah keeee!!"

Ihun kiranta da kokarin natsar da ita da Zaitoon take ne ya janyo hankalin Aunty Kubra da ta zo wucewa ta kofar ɗakin da sauri ta shigo, halin da ta iske Hibbahn ya sakata a cikin damuwa ya kuma karya mata zuciya da sauri ta ƙarasa ta rungumeta tayi luub jikinta tana kuka sossai da sossai, a hankali Aunty Kubra ke shafa bayanta

"Na yi kuskure Aunty amma wallahi na yi nadama, wallahi nayi nadama... Zuciyata rabewa zata yi gida biyu mutuwa zan yi! Me yasa mutane za su zargi iyayena da laifin da na aikata? Me yasa na zama 'yar kuka mai janyowa iyayenta jifa? Me yasa Sagir yayi min haka bayan duk alkawarurrukanshi gareni? Na zaci Mahmud zai zama yana da bambanci da shi sai dai kashhhh shima ya kasa sauraron uzurina ya tsinewa ranar da ya sanni, ya saka kafa ya shure duk soyayyar da yake ikirarin yana yi min. Kuskure ɗaya takk ashe yana iya kashe mutum? Aunty ko ban mutu ba ba zan moru ba, ba zan iya sake farin ciki ba, tarihi zai rubuta cewa Hibbah ta gama wanzuwa cikin mutane masu walwala cikin shekaru sha tara kachal a duniya..."

"Shhhhhhh! Shhhh Hibbah ki yi shiru ki daina wannan sambatun babu wanda ya fi karfin jarabawar ubangiji ke kuma naki da haka ya zo..."

"Babu ruwan ubangiji ni na ɗora wa kaina Aunty... Duk komai laifina ne Allah...! Allah....Allah na tuba"

Yadda take yi kaman zata mutu ya sa Aunty Kubra dake zub da hawaye duban zaitoon

"Zaitoon dubo Abdallah da Nasir suna ƙasa maza maza su zo su ɗaukar min ita zuwa mota mu koma asibiti"

Duk sai ta ruɗe ta shiga damuwa, da sauri yaran nata samarin waenda su ne Zaitoon ke bi ma a haihuwa suka shigo bata bari ma sun yi magana ba tace

"Maza..! Maza ku taimakamin da ita zuwa ƙasa bari na ɗauko mayafi ku hanzarta Abdallah"

Nasir shi kaɗai ma ya ɗaga ta chak don bata da wani kumari suka yi waje numfashi take ja da kyar hawaye kuwa wane pampo hannunta dafe da zuciyarta da take jin ya kusa fashewa a haka suka zo suka wuce Momma dake zaune a parlorn ƙasa da kallo kawai ta bi su har suka fice, Fitowar Aunty Kubra da mayafi bayanta Zaitoon ne ya sa ta sake mayar da hankali kansu har suka fita bata ce musu komai ba kuma bata motsa ba.


A waje Nasir ya sanyata cikin motar da Abdallah ya karɓa na Momma tun zuwansu auren kasancewar Hotel ne suka sauƙa saboda su rage saukin zirga-zirga sai suka karbi motan, Daddy da ke tsaye suna magana da Uncle zubair dake tabbatar mishi a yanzu an yi kokari an sauke duka hotunan sai waenda suka yi saving suma idan har za su ɗora to automatically zai goge kanshi ko ya ja musu shafewar shafinsu gabaɗaya, ganin yadda suka fito ya sa dole suka mayar da hankali kansu.


Zuciyar Daddy ne ya karye, ya ɗan cije lips yana kallonsu ba tare da ya motsa ba har suka bar gidan, numfashi ya sauƙe ya mayar da kanshi ƙasa a hankali ya furta

"Jarrabawa ne! Allah ya ba mu ikon cinyewa duka. Zubair ka bi su please a san menene problem ɗin kuma ku yi magana da likitan"

Kai ya gyaɗa kan Daddy ya juya ya nufi sashenshi shi kuma uncle zubair ya fice daga gidan cikin tashi motar.