KUNCIN ZUCI

Kuncin zuci

by @bintuuu

Dan dago kai Na'ima tayi jin kaman shigowan mutum falon, sai ta juyo gaba daya tana kallon Ahmad dake nan tsaye bai qaraso cikin falon ba har sannan, ware ido tayi takai hannu daya tsakar kanta tana karewa dayan hannun kuma tana laluban inda dankwalinta yake, dan murmushi Ahmad yayi wanda in ba mutum ya lura ba zai gani ba, sai ya taka cikin sanyin jiki ya qarasa falon, har sannan Na'ima nata laluban dankwalin nata yayin da ya kasa dauke idonsa daga gashin nata, tun da yake bai taba ganin gashin da ya tafi dashi kalan na Na'ima ba, Jafar ne ya miqo mata dankwalin dake qasan sa yana cewa "Anty kin ganshi fa" sai da ta daura sannan ta dago kanta ta hada Ido da Ahmad dake kallon nata har sannan, kallon idanun ta ne ya qara saka masa karyewan zuciya na tuna abunda ya gani a apartment din ta, sai yace "Ina kika ajiye wayanki, I've been calling" ta kauda kai tace "Nima ban sani ba" da haka ta miqe ta nufi kitchen dan kawo masa abun sha, komawa gurin Ahmad jabeer yayi ya bar dan'uwansa da iphad din, sai da ta ajiye masa nan kan table sannan tace "Ina wuni" Ahmad na shafa kan jabeer ya amsa, he wanted to have a talk with her but kids are there, gashi ta kashe wayanta wanda shi baisan dalilin ta na yin hakan ba, Anty Amnah ce ta shigo falon tareda mijinta hannunta riqe da jaka da alamun dawowansu daga asibiti kenan, da gudu twins suka nufesu suka qaraso falon gaba daya, tace "Son yaushe kazo" kafin Ahmad ya amsa jafar yace "Yanzu yazo fa Mummy" sannu Ahmad din ya musu tareda da miqa hannu sukayi musabaha da Abban twins da ya zauna kusa dashi, Anty Amnah na murmushi suka gaisa sannan Na'ima ta gaishesu gaba daya, ganin sun fara magana yasa ta miqewa ta nufi daki, tana shiga ta qarasa gurin wayanta ta dauka amma bata kunna ba ta jawo bedside drawer ta saka a ciki sannan ta fara hada kayan su da zata wanke, da ta sake fita falon hannunta riqe da laundry basket har sannan Ahmad yana nan suna hira hannunsa riqe da plate yana cin abinci, bata kallesa ba ta nufi dakin su twins dan debo nasu kayan, Anty Amnah tace "Na'ima ki bar kayan nasu zan wanke dai" tana murmushi tace "A'a Anty babu yawa ai" da haka ta wuce ciki Ahmad na kallonta ta gefen ido, sai dare Nafisa ta dawo gidan hannun ta riqe da kaya niqi niqi, nan falon suka zauna dukansu yan gidan har da Abban twins, Anty Amnah na ware kayan su Na'ima na kaiwan kowanne mazauninsa agidan, sai da suka gama komai sannan suka tafi dakinsu, suna shiga Nafisa ta daka mata duka a bayan, da sauri takai hannu tace "Auuch, hannunki da zafi dai Nafee" sai Nafisa tace "Yeah right, haka nakeso daman, kinsan haushin dana ji ina ta kiran wayanki a kashe dazu ina mall dinnan" dan dariya tayi tace "Nifa ban san inda wayan take ba" sai Nafisa ta nufi bedside drawer tana cewa "Inaaa, Na'ima ko kyau ma qaryar bata miki ba, don't even start" da haka ta bude drawern ta ciro wayan tana nunawa Na'iman, sai kawai tayi dariya ta zauna a bakin gadon tace "Au dama tana cikin nan wai" nufota Nafisa tayi zata dake ta sai ta dauko pillow ta tare kanta tana dariya, sai Nafisa takai hannu ta daki pillow'n tana murmushi, tace "Ai Yah Ahmad yana ganin ta kansa a hannunki wallahi, bawan Allah haka yayi ta kira nasan baya samunki" shiru Na'ima tayi Nafisan na kallonta sai can ta gyara zamanta a kan gadon, tafara magana a hankali "Nafisa idan na fada masa na gudu daga gidan mu, wane irin kallo kike ganin zai min?" sanyi jikin Nafisa yayi sai ta kamo hannunta tace "Duk wani me hankali in kika fada masa dalilin da yasa kika baro gidan bazeyi judging dinki ba, you made the right decision Na'ima, ki daina barin zuciyar ki tana leading dinki astray, in baki sani ba hakan zai qara masa sonki ne a zuciyarsa" Na'ima tayi shiru tana kallonta sannan ta gyada kai, miqo mata wayan Nafisa tayi sai ta karba ta kunna, ai kuwa nan ta ga messages din Ahmad na shigowa daban daban, jikinta ne yayi sanyi tanajin zuciyarta na sauya bugu akan hakan..... pinging dinsa tayi a WhatsApp nan da nan ya amsa suka fara chatting, amma sai bata ga alamun zai mata magana akan abunda ya faru jiyan ba, har ta masa sallama akan zatayi baccin be tambayeta game da Bilal ba.

Washegari guraren karfe takwas na safe Na'ima na kwance taga shigowan email a wayanta daga supervisor dinta, telling her yanason ganinta a ranan regarding project dinta da tayi submitting, miqewa zaune tayi tana qara karanta mail din sai ta miqe cikin sanyin jikin ta nufi bandaki dan tayi wanka, tana cikin shiryawa Nafisa ta farka, janye mask din dake idonta tayi tana kallon Na'iman idonta cike da bacci tace "Where are you going?" Na'ima tace "School..Dr Kevin yana nemana regarding my dissertation" tsuka Nafisa tayi ta gyara kwanciya tace "Wallahi in na bar England sai nayi shekaru ban dawo ba" Na'ima tayi dariya tana zipping riganta tace "Shine kike dating mazaunin qasar kuma" ai nan Nafisa tafara murmushi tace "And he's the sweetest, ke dan Nigeria ne fa, jiya ma aiki ne ya riqeshi a office wai Ya Ahmad baya nan shiyasa bai rakani shopping mall dinnan ba" Na'ima na murmushi tace "You two look good together, in na dawo zaki bani labarin" sai Nafisa tace "Ina tunanin raka ki ne fa" nan Na'ima ta girgiza kai tace "No kiyi baccin ki, zan bi train ai ba dadewa zanyi ba" Nafisa ta sake cewa "You sure?" ta gyada kai "In sha Allah" da haka Nafisa ta koma baccin ta bar Na'ima na shiryawa, har dakin Anty Amnah taje fada mata , sai bata sameta ba dan tana dakin Abban twins har sannan suma basu tashi daga bacci ba, a waya Na'ima ta tura mata massage sannan ta tafi train station din, sai da suka kusa isa gurin 11am sannan kiran Ahmad ya shigo wayanta ta daga suka gaisa time din shima yana office, jin kamar sautin gudun train yasa shi cewa "Ina zakije haka?" tace "School zanje, supervisor na yana nemana, may be na samu matsala da dissertation dina ne" daga bangaren Ahmad ya gyara zama kan executive chair dinsa yace "In sha Allah babu matsala Babe" ahankali tace "Allah yasa" yace "Zanzo daukan ki, ki jirani please" ta amsa da toh da haka sukayi sallama, Ahmad be kai ga ajiye wayan ba secretary dinsa me suna hanna ta shigo cikin kwalisa, cike da yanga ta ajiye masa files din hannunta anan kan table din tace "Sir, we need your signs on these, and Ox.co reached out again, they really want a meeting with you this afternoon" sai ya dago files din yana budewa, batare da ya kalleta ba yace "Reschedule it for tomorrow" ta gyada kai amma madadin ta tafi sai ta miqo masa wani box ta ajiye kan table din, tana murmushi tace "Sir this is for you" juyawa yayi yana kallon wrapped box din hade da flower a jiki, casually yace "Thank you, you can go now" ta juya bata bar murmushin ba ta fita, aikinsa ya cigaba da yi saida ya shafe awa daya da rabi sannan ya miqe tareda daukan suit dinsa dake rataye a hanger ya saka be yi buttoning ba, ya kai hannu zai dauki wayansa sannan ya ga gift din dake gurin har sannan, dauka yayi ya nufi fita daga office riqe dashi a hannunsa, miqewa hanna tayi ganin ya fito sai ta kalli abunda ke hannun nasa tana murmushi, be kulata ba ya wuce dashi har motansa, sai da ya dauki hanyar Oxford sannan ya bude window ya jefar batareda ya bude ba har sannan....
Zaune Na'ima take a gaban Dr Kevin yana mata bayani akan matsalan da ta samu gurin analysis da references dinta, shiru tayi tana sauraron bayanin nashi, dama ta san za'ayi haka tun lokacin da Bilal ya sake reappearing a rayuwanta, daga wannan lokacin ne hankalinta ya fara rabuwa biyu, rabi akan dissertation dinta, rabi kuma akan rayuwanta na baya da take yawan tunani akai akai yanzu, qarshen project din nata daman ita kanta wani lokacin bata san me take rubutawa ba, a hakan dai ta qarasa komai tana addu'an kar ta samu matsala, Shirun da Dr din yaga tayi ne yasa shi cewa "Are you really okay Ne'ima?" tayi saurin gyada kai tace "I'm fine Sir, i'll make the corrections thoroughly, I'm sorry please" Yace "No problem, I'll give you a week to amend the mistakes, by then.. you're good to go" ya qarasa maganan yana ma ta murmushi, miqewa tayi cikin ladabi tace "Thank you sir, I'll ensure it meets the required standard" yana murmushi ya gyada kai ta juya ta fice, sai da ta samu zama a wani rest bench cikin school premises din sannan ta kira line din Ahmad, yana dauka yace "Are you done?" Tace "Eh" sai yace "I'm almost there, where are you exactly?" sai da ta fada masa sukayi sallama ta ajiye wayan tana qara duba iphad din nata ganin sai lokacin take lura da mistakes din ma, kiran zarah tayi zasuyi maganan....
Tananan zaune ta hango Ahmad yana tahowa hannunsa riqe da bag na takeout me tambarin McDonald, yana murmushi ya qaraso gurinta sannan ya zauna a gefenta, gaishesa tayi ya amsa, ahankali ta sake cewa "Daga office ko?" sai ya kalli suit din jikinsa sannan ya gyada kai yace "Here, ci abinci tukunna dan nasan bakiyi breakfast ba" ya qarasa maganan yana bude takeout din ya miqa mata ta karba tana dan murmushi tace "Thank you" da ta ciro sandwiches guda biyun sai ta miqa masa daya ta fara cin dayan, suna cikin ci Ahmad ya kalleta yace "Me ya faru da work din naki Babe" dauko iphad din dake gefenta tayi ta fara nuna masa yana kallo tareda sauraronta attentively, sai da tazo kan codings din yace "Just mail everything to me kinji" ta kallesa tace "Bazan taquraka ba?" kallonta ya tsaya yi da kamar zai riqo hannunta sai ya fasa, cikin kwantar da murya yace "Kinason in miki sabon project din?" tayi saurin girgiza kai tace "No, corrections din is okay" sai ya gyada kafada baice komai ba ya juya yana kallon mutanen dake shawagi acikin school premises din, kallonsa Na'ima ta rinqa yi ganin yana cin abincinsa hankali kwance, tasan yanason sanin abubuwa da dama daga gareta, tasan yana son jin maganganu daga bakinta, amma he's patiently waiting for her ta fada masa a duk sanda ta shirya, hakuri da kamalansa sun tafi da tunanin ta, mutum ne mara gaggawa a almarinsa, sai ta fara tunanin may be ta hakan ne ya samu nasara sosai a rayuwarsa tun yana matashinsa...
Juyowa yayi ya kalleta sai tayi sauri dauke kai takai sandwich din bakinta tana gutsira, daga gefensa ya miqa mata bottle water ta karba babu wanda ya sake cewa komai a cikinsu, bayan sun gama suka nufi motan Ahmad din dake can parking space na wajen makarantan, da ya tada motan suka dau hanya sai Na'ima taga ya dau hanyan zuwa apartment dinsu madadin su dau hanyar barin garin, kasa magana tayi ta dan juya ta kallesa ganin idonsa na kan titi ko kallonta beyi ba, da suka isa sai ya kamo hannunta suka qarasa har apartment din su, mamaki ta rinqa yi ganin ya saka door pin din nasu, da haka ya sake janta suka shiga ciki har saida ya je bakin room din nasu ya bude Na'ima taga babu glasses din sai ta fusge hannunta tace "You were here before?" shiga dakin yayi ransa a dan bace ya nuna mata fasasshen mirro'n yace "Ina buqatan amsoshi na yanzu Na'ima, tell me everything, who da Hell is that guy Bilal, me ya miki kike boyemin?" tana tsaye bakin qofar dakin taqi shiga, sai ta sunkuyar da kanta tace "Ba son boye maka abunda yamin nake ba" rai abace ya dan daga murya yace "Then what?..me kike boyemin Na'eemah? Menene?" Kallonsa tayi tana hawaye tace "Ahmad guduwa nayi daga gidan mu, a ranan da ya sakeni ban koma gida ba na gudu Abuja" daskarewa yayi yana kallonta cikin ido, itama tana kallonsa ta cigaba "Ya dakeni, ya kuma dukana, babu daren da baya dukana, budurwarsa da ya kawomin har cikin gida ta dauko wuqa zata kasheni a gabansa Ahmad, and he did nothing, ya sakeni agadon asibiti sanadin dukan da ya min aranan da amininsa yazo har gida zeyi rapping dina, kuma babu wanda ya tsaya min kaf cikin family na," sai ta fashe da kuka me qarfi tace "And i run away Ahmad, i run away the moment Bilal ya furta min sakin da nayi shekaru ina addu'an samu daga gareshi" Ahmad was in shock har sannan, sai kawai taga ya taho gareta da sauri ya rungumeta, qanqameta yayi a jikinsa itama tayi wrapping hannunta a bayansa tana sake fashewa da wani kukan me qarfi, rufe idonsa da suka kada yayi yana jin wani zafi da tausayinta na ratsa duk jikinsa, sunfi minti biyar a haka kafin ya saketa yana kallon ta yakai hannu yana share mata hawayen, ahankali yace "I'll kill him, sai na batar dashi" ta girgiza kai tana kallonsa tace "Don't please, karka masa komai, it's all in the past now" sai ya tallafo kumatunta yace "Sai na rama Na'ima, ko ba yau ba sai na rama abunda suka miki sannan zanji sauqin abunda nakeji a zuciyata" batace komai ba tana hawayen har sannan, ahankali ta sakeshi sai ya kamo hannunta suka zauna kan kujera anan falon, ahankali yace "Ina kika hadu dashi har kukayi auren?" tace "Dan'uwana ne, a gidansu na girma" ganin yana kallonta sai ta cigaba da maganan sanin cewa so yake ta cigaban, Anan zaunen ta fara bashi labarin nata amma da tazo daidai ranar da Bilal ya mata dukan mutuwa lokacin da suka dawo daga gidan Alhaji kuka yaci qarfinta, sai Ahmad ya bar kan kujeran ya tsugunna a gabanta tareda da dago habanta da yatsansa, cikin ido suke kallon juna yace "Wallahi sai na wulqantashi Na'eemah" nan ma tayi saurin girgiza kai tace "You're not like him Ahmad, banason ka zamo kamarsa" ta sake cewa "Banaso" ganin yanda ta rikice ya sashi cewa "It's Okay, it's Okay Babe, you don't have to tell me everything now, banason kukan nan kinji" sai ta gyada kai tareda sauqe idonta qasa, Ahmad ya kamo hannun ta duka biyun be tashi ba sannan be daina kallonta ba, aransa yana ayyana "Kuncin da tasha a rayuwa saboda sanyin ta" a dan labarin da ta basa yasan ta azabtu a hannun mashayin mijin nata a baya, sai ya juya hannunta yana kallon tabon cikin tafin yace "Bazan taba ganin laifin decision dinda kikayi making ba, thank you Na'eemah, for having this courage in life, it brought you to me" sai ya shafa gefen fuskanta yace "And i'm never letting you go" .....A hanyarsu ta komawa ya kwantar mata da seat din, nan bacci ya dauketa, yana driving din yana kallonta jefi jefi, wani irin tausayinta ne yake shigansa gashi wani irin bugu yakejin zuciyarsa nayi akanta wanda bai taba yi ba sai ranan, yasani daga ranan da ya fara ganinta fuskanta ya zauna a idanunsa, amma zuwa yanzu...zuwa yanzu what he feels about her is something else, something big, something that was rising like a fire in him, and he won't mind if it burns him alive....

Da yammacin ranan Na'ima na zaune a gado tana typing cikin laptop dinta, tana duba inda zatayi correcting mistakes din da tayi a project din nata, gefenta littattafai ne kusan biyar tana aiki dasu, shigowa Nafisa tayi tana cin biscuit tace "Kema dai da wahalar da kai Na'ima, kinada kwana shida a agaba fa" Na'ima bata kalleta ba tace "Sai yanzu nake ganin tarin mistakes din Nafisa, kamar a makance nayi wasu rubutun fa" kafin Nafisa tayi magana messege din Ahmad ya shigo wayanta, sai taga yace "Kizo ki sameni a gidana yanzu" tayi masa reply da "Toh Yaya, ganinan zuwa" da haka ta nufi wardrobe ta dau mayafi, har ta fita daga dakin hankalin Na'ima na kan aikin ta bata kulata ba....