01
by @oumfatima33
[1/1/29/26/ 8:00pm]
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
KOMAI TSANANI
By
*KANSA'U* BELLO
(OUM FATIMA)
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
PAGE 01
BISMILLAHIRRAHAMANIRRAHEEM
SHIMFIƊA
Rayuwa da ƙaddara abubuwa ne guda biyu da suke tafiya a tare da juna, ko wace rayuwa dole ne akwai ƙalubalen dake kasancewa a cikinta. Dole ne kuma ka karɓe ta a yanda tazo maka saboda haka Ubangiji ya tsara maka, idan kaci karo da faɗuwa a yayinda kake ƙoƙarin cimma wani muradi naka hakan baya nufin cewa ka gaza bane. Ba kuma ya nufin ka haƙura da son cimma muradanka, yunƙuri zaka yi ka ƙara tashi sannan ka jajirce kayi aiki tuƙuru ku kuma miƙa lamarinka ga Allah ka nemi taimako daga gare sa don shine kaɗai mai bayarwa kuma mai hanawa, ko wace nasara bata samuwa sai bayan jure ƙalubalen dake zuwa kafin ta, kar ka taɓa cire rai daga rahamar Ubangiji domin shine masanin abinda ke fili dana ɓoye, yana sane da kowa da komai idan yaso zai iya sauya maka ƙaddararka a lokacin da baka taɓa tsammani ba. Hakan ne ya kasancewa a cikin rayuwar Nana Maryama wacce ta taso cikin matsi, ƙunci da tarin ƙakubalen rayuwa. Abin tambayar a nan shine ya rayuwarta take kasancewa? Zata iya juriya da jajircewa don cimma muradanta? Ko kuma gazawa take yayin da faɗuwa ta same ta?. Labarin KOMAI TSANANI zai taɓa zuciyarka ya faɗa maka cewa KOMAI TSANANI AKWAI FATA....
___________★
Ƙauyen Cigama dake ƙarƙashin Birnin Magaji local government Zamfara state, gidan Alhaji Zubairu Manomi da misalin ƙarfe 6:30 na safiya.
Sassanyar safiya ce mai cike da ni'ima yayin da sassanyar iskar kaka wanda ke nuna alamun ɗaukewar damina da yin ishara da zuwan sanyi ke busawa yana ratsa jikin duk wani wanda yake waje a dai-dai wannan lokacin, garin yayi luf da wani kalar yanayi mai daɗin gaske, duk da cewar iskan sanyi ya ɗan fara kaɗawa kaɗan. Sararin samaniya tayi garai-garai babu alamar gajimare wanda hakan ke kara tabbatar da ɗaukewar ruwa gaba ɗaya, sai alamar rana data fara haskawa wacce ta ƙara dai-daita yanayin, a taƙaice dai yanayine mai daɗi ƙwarai da gaske a dai-dai wannan lokacin a ƙauyen. Babban gidane ginin jar ƙasa da babu ko shafen siminti a jikin bangayen, sai ƙatuwar ƙofar shiga wacce idan ƙyaure za'a saka mata sai ta cinye babban gate. Amma haka take a buɗe hayam kasancewar katangar data kare tsakar gidan bata da wani girma sosai, ɓangaren farko da zaka fara tararwa idan ka wuce ta ƙofar gidan shine ɓangaren da Mazan gidan suke rayuwa, ma'ana samari waɗan da basu da aure. Ƴar ƙaramar katanga ce ta raba su da ainahin cikin gidan wanda ɗakuna uku ne a ɓangaren sai bayi guda biyu da suke amfani da shi, ɗaki na farko ƙananun yara ne ke kwana a cikinsa sai na biyu wanda shine na samarin, sai na ƙarshe na can lungu wanda yake na ƙanen mai gidan ne autan ɗakinsu wanda bai yi aure ba, yaran na kiransa da Baba Manniru.
Idan ka ƙara gaba kuma sai ɓangaren mai gidan wato Alhaji Zubairu Manomi wanda yake da matan aure guda huɗu ras, uwar gidansa mai suna Aisha ana kiranta Indo tana da yara tara dashi Maza biyar Mata huɗu. Sai matarsa ta biyu Salamatu wacce ake kira da Salmai itama yaranta bakwai dashi Mata biyar Maza biyu. Sai matarsa ta uku mai suna Baraka ana kiranta da Barai yaransu biyar dashi Maza biyu Mata uku. Sai amaryarsa mai suna Ramatu wacce bai daɗe da aurota ba, don haka bata haihu dashi ba sai ƙaramar ƴarta wacce ta haifa a gidan Mijinta na farko wanda Allah ya masa rasuwa tazo da ita a matsayin agola.
Sai ɓangare na gaba daya kasance na ƙanensa wanda suke uwa ɗaya uba ɗaya da Alhaji Zubairu, daga ɓangaren dama kuma ɓangaren ƴan'uwansa Maza ne guda biyu wanda suke ƴan Uba Mahaifiyarsu Allah ya mata rasuwa bayan mutuwar Mahaifinsu da shekara biyu aka raba gado aka ware musu kason suke zaune da Matansu da iyalansu suma.
Alhaji Zubairu Manomi ne ya fara fitowa daga ɗakinsa wanda yake daga can lungu idan ka wuce ɗakunan matansa huɗu dake jere biyu na kallon biyu sai na Mahaifiyarsa dake can gefe wacce ita kadai ta rage babba a gidan Mahaifinsu ya rasu, daga can bayan ɗakunansu kuma ƙaton store ne da yake ajiyar amfanin gonarsa idan aka kammala noma sai manyan rumbuna guda huɗu suma duk hatsi ne a ciki. Buta ya ɗauka a ƙofar ɗakinsa ya wanke hannunsa daya kammala cin ɗumamen safe wanda matarsa ta tsakiya ta ɗumama ta kai masa kasancewar ita ke da turaka. Bakinsa ya goge ya miƙe tsaye yana sakin gyatsa, kai tsaye ya nufi ɓangaren yaran ɗakin matasan ya fara bugawa kasancewar ƙananan tuni sun fice har sun ƙarya suna wasansu da jiran mai gidan da yayunsu su fito a tafi gona kamar yanda ya kasance al'adar gidan kullum suna zuwa aikin gona rani da kaka don babu abinda basa nomawa a gidan kasancewar garin na noma ne don ita ce abinda suka fi ƙware wa a kai.
"Kai wai me kuka tsaya jira har yanzu baku fito ba har rana ta fara buɗewa kuna nan kuma wannan baccin asarar naku? Maza maza ku fito yanzun nan." Ya ƙare maganar cikin ɗaga murya da hargagi.
Ƙaran buɗe ƙofar ne yasa ya dakata daga bugun ƙofar da yake yi ya kalli sangamemen saurayin daya fito.
"Kai Badamasi wai baccin kuke har yanzu baku yi haramar tafiya gona ba ga rana har ta fara ɗagawa?." Ya faɗa yana kallon Badamasi wanda alamu ke nuna ko sallar asuba bai yiba don ga yawun bacci nan shaɓe shaɓe a gefen bakinsa.
Murza idanu Badamasi yayi yace.
"Yi haƙuri Alhaji yanzu zamu fito makara mukayi ne." Ya faɗa yana komawa cikin ɗakin ya shiga tayar da sauran da basu tashi ba. Tsaki yayi ya juya ya nufi ɗakin Manniru yana ta faɗa da kumfar baki a kan rashin fitowarsa shima har yanzu, shida yake babba kuma kullum shi yake haɗa kan yaran su wuce gonar ko baya nan.
"Kai Manniru... Manniru kai... Me kake yi ne har yanzu baka fito ba?." Ya ƙare maganar yana buga ƙofar langa-langar da aka rufe ɗakin da ita. Kamar sauran shima fitowa yayi babu alamar fuskarsa taga ruwa bare batun sallah don jiya kusan kwana sukayi a wurin dj na bikin abokin Mannirun da akayi sai kusan asuba suka dawo gidan, mai makon ya tsaya yayi sallah shine ya kwanta ya kama bacci don sallar ba damunsa tayi ba.
"Makara nayi Alhaji, amma yanzun nan zamu fito." Ya faɗa yana sosa ƙeya shima.
"Kuyi maza don Allah rana ta fara yi." Alhaji Zubairu ya faɗa kafin ya juya ya koma cikin gida yana ƙananun mita kasancewarsa mutum mai mitar tsiya.....