Chapter 2
by @ummuaffan
YAƊIN MAGE...
©UMMU AFFAN
LITTAFI NA ƊAYA
SHAFI NA BIYU
"Suwaiba, abincin nan fa na Mariya ne ki ka ba Maryama!"
Shuru ba amsa, hakan yasa Hafsatu ta ƙara ƙurɗa kai cikin ɗakin, ganin Suwaiba tayi zaune da yaranta tsakar ɗakin suna cin nasu.
"Ashe kina zaune ina ta magana?"
"Eh ƙwarai, naji tambayar taki ce ba amsa, shi ya sa ba ki samu amsar ba!"
Hafsatu ta taɓe baki, idan masifa ce ai ba a fita ba, ta girgiza kai tare da ƙara furta.
"Amma kin san wancen abincin ya mata kaɗan Suwaiba, don baki haifi Maryama ba bai kama ta kina haka ba."
"Hafsatu ki shiga taitayinki, kin san dai na shiga ban ɗauka ba ba ta fidda ɓarawo, har ɗakina ki ka biyo ni ki ci mini fuska, shin wai me kika mayar da ni ne? Ko zaki nuna mini kin fini ƙaunar Maryama ne? To bari kiji ko Salisu bai isa ya ja mini layi tsakani na da ita ba, ballantana kuma ke karan kaɗa miya."
Hafsatu ta fesar da huci, tare da juyawa tana faɗin.
"Kowa dai ya yi nagari don kan shi, haka duk wanda rai zai yi wa daɗi a baren mai shi ne, duniya ce ga ki ga ta nan."
Ganin Suwaiba zata hayagogo mata da sauri ta fice daga ɗakin don ba ta son ma mutanen gidan suji ballantana su ƙara ƙulla mata sharri wurin Salisu musamman Baaba, duk faɗan da za su yi da Suwaiba to ita ce ake ba rashin gaskiya ko da kuwa ita ce mai gaskiyar.
Suwaiba ta ja tsaki ganin ficewarta a ranta tana cewa.
'Da wasu mazaunanta ɗaya ya yi gabas ɗaya ya yi kudu, to wa zaki nunawa ƙugu?'
Taja kuma jan tsaki a karo na biyu tana ci gaba da cin shinkafarta.
Hafsatu kuwa kai tsaye ƙofar ɗaki ta zauna ta fara ci tana ba Bintu a baki har ta gama, wutar ta iza don tana saukewa ta mayar da tukunyar tuwan dare haka suke kullum da an sauke na rana sai a ɗaura tuwan dare, alwala taje tayi kafin ta shige ciki yin sallah.
Suwaiba.
"Maryama!!"
Ta ƙwala mata kira, da sauri yarinyar ta miƙe jikinta a sanyaye ta ƙarasa cikin ɗakin.
"Ina abincin naki?"
"Na cinye Inna."
Ta faɗa tare da yin ƙasa da kai, Suwaiba ta jawota gabanta ta kama kunnanta taja da ƙarfi, Maryama ta saki 'yar ƙara hawaye suka ɓalle mata.
"Wallahi ki mini kuka na yanka ki yanzu, daman kin san na hanaki idan na dake ki kiyi kuka ko? To wallahi idan ki ka yi sai na da ke ki, shashashar yarinya, na faɗa miki ki zauna anan shi ne gulma ki ka fita ƙofar ɗaki don maƙirar matar can ta gani ko?"
"A'a Innarmu kiyi haƙuri bazan sake ba."
Ta saki kunnan nata.
"Ki ma sake idan ban kashe ki na kashe banza ba.''
Ta ture ta, ai kuwa ta faɗi ƙasa ta bige, amma saboda tsoro ta kasa kuka da ƙarfi sai a hankali don kar Suwaiba wacce ta doshi hanyar fita daga ɗakin ta jita.
"Sannu da shugo Inna!"
"Yauwa Daddawa ce aka aiko daga ƙauye, shi ne na amso wurin wacce taa taho da saƙon, ga ta sabuwa an kawo sai azo a saya."
"Eh Hafsatu ce yau za tayi tuwon idan ta fito zata zo ta saya, duk da naji shekaran jiya wai tana cewa an ɓata daddawar wai ta waƙe zalla ce ba karwa."
"In ji Hafsatun? Ai kuwa daddawar nan ba wani ɓata taa da akayi ba wanda ya ce haka kuwa."
Da yake Inna maganarta akwai sauri, tana da saurin magana haka.
"To sai ita uwar iya, kin san ba a iya mata."
Suwaiba ta faɗa tana taɓe baki tare da jefa guga rijiya zata ja ruwa. Inna kai ɗakinta ta wuce tana juya maganar Suwaiba domin duk gidan Inna ce kawai ke ƙaunar Hafsatu, ita ma a ɓoye take don da Baaba zata gani sai sunyi faɗa sai ka rantse Baaba ce masu gidan ba Innar ba.
Suwaiba kuwa taja ruwanta a bokiti ta kai ƙofar ɗakinta, sannan ta ɗauki buta ta zuba tare da shigewa makewayi.
Kamar kullum Salisu ƙarfe taran dare yake dawowa gida daga kasuwa. Hafsatu ta masa sannu da zuwa, ya amsa tare da zama saman kujerarta.
"Bintu tayi bacci ne?"
"Ai kuwa ba ta daɗe da bacci ba, yau babu rigima sosai, sai dai zawon da take ya dawo."
"Ayya, maganinta ya ƙare ne?"
"Eh na asibitin da ka saya ya ƙare, wanda Gwoggo ta aiko mini na gargajiyar nan dai da saura."
Tana faɗa tare da ajiye masa farantin silba wanda aka ɗaura kwanon tuwo da na miya da kofin ruwa dukansu na silba ne.
Bayan ya wanke hannun ya fara cin tuwon, bai kuma magana ba har ya kammala, sannan yaa dube ta.
"Na manta fa ledar can kajin ruwa ne guda biyu da na saya a kasuwa daman duk sati mutumin ke zuwa, yau ya kawo ki gyara su ki sulala aci."
"To bari na kira Suwaiba sai muga yadda za ayi."
"To ya bata amsa, tana fita ya zauna a ƙasa ya baje kuɗin da ya dawo kasuwa da su domin ware 'yan dubu-dubu da ɗari biyar, ɗari biyu da 'yan ɗari hamsin ashirin da goms a haka yake kullum, sana'arsa kayan miya ne wato kayan gwari, kuma alhamdulillah yana samu a ciki sosai, da ita yake ci da iyalansa haka taimakon maƙota da abinda bai fi ƙarfinsa ba.
Salisu mutumin ƙauyen Jargaɓa ne ƙaramar hukumar Bakori ta jihar Katsina, fari ne amma ba sosai ba kasancewar mahaifinsa bafulatani ne na usul, wani rikici ne da akayi tsakanin makiyaya da manoma aka kashe iyayensu daga shi sai ƙanwarsa Hindatu ne suka rayu, hakaan ya saka wani malami anan Jargaɓa ya dauke su, suka dawo hannunsa da zama, ya yi karatu a hannun malamin sosai, ƙanwarsa da ta shekara goma sha shidda malamin nan ya aurar da ita a ƙauyen, sannan shima Saminu, mahaifin Salisu yaci gaba da karatunsa har shima ya zama malamin, ya auri ɗiyar malam, har suka haifafa, ya haɗu da Indo mahaifiyar Salisu ne tana kawo masa tallar nono ita ma bafulatana ce, haka Allah ya ɗaurawa Saminu ƙaunar Indo, ko da ya sanar da malam bai musa masa ba sai ma fatan alkhairi da ya yi masa, ya auri Indo shekara ɗaya ta haifi Salisu, ta samu ciki na biyu wajen haihuwa ta rasu daga ita har abin da ta haifa ɗin. Lokacin Salisu yana da shekaru huɗu a duniya. Baraka ba ta ƙaunar Salisu kamar yadda ba ta ƙaunar Indo, ko da ta rasu ba ta ragawa Salisu ba, wannan dalilin ne ya saka Salisu na shiga shekaru shidda a duniya mahaifinsa ya kawo shi almajiranci a Ɗandume, matar Babansa Baraka tana da 'ya'ya maza huɗu sai macce ta biyar don haka su shidda ne wurin mahaifinsu. A garin Ɗandume ya yi girmansa, tun farkon zuwansa ya haɗu da Baaba wacce yake ɗauko mata ruwa tana ba shi abinci, sun sami shaƙuwa sosai saboda ko 'yar sana'arsa yaje ita yake kawowa kuɗinsa ajiya tana tara masa. Lokacin da ya koma ganin gida ya kusan shekara ashirin, Babansa ya ce ba zai dawo ba sai da matarsa, a gida aka ɗaura musu aure da Fatima Bintu, da farko a gida ya barta, ganin yana daɗewa bai je ba, malam ya ce ya taho da ita inda yake zaune, sun haifi yara uku biyu sun rasu sai ɗaya Maryama wacce da cikinta ya ƙara aure ya auri Suwaiba, wacce silar Baaba ya aureta don ita ce ta fara kwaɗaita masa ya aureta duk da Suwaiban ba su haɗa komi da Baaba ba, sai zaman gida ɗaya da suka taɓayi a baya da iyayen Suwaiban, tunda tazo gidan zaman lafiya ya ƙaura tsakanin Uwar Maryama da Salisu, duk da gidan haya suke daman amma sai uwarɗakinsa Baaba ta ce Uwar Maryama ce mara gaskiya, don tun bayan zuwansa da ita taji ba ta mata ba, kuma ada komi ya samu Baaba ce amma zuwanta sai ya tare a kanta wannan abu ya mata zafi ta ƙara tsanar Fatima a zuciyarta, lokacin shekarun Maryama huɗu ya sake uwarta, ta shirya ta koma gida, shikam yaƙi zuwa don yana tsoran yaje ya tarar da malam don yasan bai kyauta ba, sai ya zamana Maryama ta zauna hannun Suwaiba daman lokacin ita ma ta haifi 'yarta Asiya tana da shekara biyu haka ta haɗa su ta riƙe.
A gaban kowa Suwaiba na nuna tana ƙaunar Maryama fiye da 'yarta Asiya, amma a zahirin gaskiya ba haka ba ne, ta tsani Maryama tsana mai muni, duk wasu azaba tana gana mata, haka tun daga shekara huɗun ta fara aza mata talla, duk da daidau gwargwado Salisu yana da ƙoƙarin ciyar da matansa, yana da kyau Salisu ga shi da ɗan hasken fata, bai cika tsayi ba haka ba gajere ba ne, yana da faɗi kaɗan kuma bai cika ƙiba ba. Maryama kam tana kama da Salisu sosai har ta fishi haske sannan ɗan jiki ƙarami gare ta irin na mahaifiyarta. Asiya kuma sai ta biyo tsawon mahaifiyarta da kuma duhun fatarta amma akwai hanci da ido irin na Babanta. An haifi Khamis da shekara ɗaya Salisu ya fara neman auren Hafsatu wacce jinin fulani ce.
Duk wani ƙoƙari da tuggu da maƙyirci Suwaiba tayi don ganin auren Salisu da Hafsatu bai ɗauru ba, amma sai da alƙawarin Allah ya ɗauru, haka tana ji tana gani aka wanko Hafsatu daga garin Mahuta da ke ƙaramar hukumar Funtua aka kawo ta gidan Salisu a Ɗandume, ko in ce gidan da yake haya ( Ƙarfin hali na malam bahaushe ba gidan kai an girke mata biyu a na haya)
Suwaiba ta amshi Hafsatu a matsayin abokiyar zama ba yabo ba fallasa, da taga Hafsatu tela ce kuma tun zuwanta garin mutane ke kawo mata ɗinki sai abin ya ƙona ranta don ita ba ta da wata ƙwaƙƙwarar sana'ar da ta wce ta ƙulle-ƙuullen da ta ke, haka zaman ya kaya tsakaninsu suke da ƙyashi da hassada, wata tara kuwa Hafsatu ta haifi 'yarta Fatima Bintu, sunan kakar Hafsatu kenan kuma uwargidan Salisu da suka rabu shi ne ake ce mata Bintu. Anyi suna na bajinta ganin Bintu ce 'yar Hafsatu ta fari, kuma iyayen Hafsatun ma sun yi rawar gani ta fannin gara domin mahaifinta babban manomi ne duk da shiɗin bafulatani ne amma yana zaune ne a Mahuta shima matansa huɗu kuma mahaifiyar Hafsatu ce uwargida. Buhun masara, buhun gero bugun dawa, buhun alkama haka aka girkewa Hafsatu a haihuwar Bintu, watan Bintu bakwai Hafsatu ta fara wani laulayin wato dai ciki ta samu gunne zatai, nan fa ran Suwaiba ya kuma ɓaci hankalinta kuma ya tashi da ganin ita ma ta samu cikin duk da kusan a tare suka haihu daman.
Hafsatu tana fita ta iske Suwaiba zaune akan kujera 'yar tsugunnau, tsakanin ƙofar ɗakinsu tana zaune, daman duk ranar da Salisu ke ɗakin Hafsatu haka take wannan zama ko ta tara matan gidan suna hira, ko ta ce Amarya tayi wa yaran gidan tatsuniya, yau ma ba ta sauya zani ba, Hafsatu kam ba ta kawo komi a ranta, yarinta ce ko har da wauta oho, don idan taga an fara zaman nan ko da Salisu na ɗaki sai ta fito ayi zaman da ita. Duk da cewa Suwaiba idan ranar nata girkin ne ba ta fitowa tana ɗaki ƙunshe da miji, har an fara ganewa ranar da ba ta fito ba kowa sai ya yi zamansa ɗaki yasha baccinsa.
"Suwaiba, daman Salisu ne ya kawo kazar ruwa ya kike ganin za a yi?"
(Haka suke kiran junansu gatsal ko miji sunansa suke kira)
Suwaiba ta kauda fuska, zuciyarta cike da baƙinciki, mafi yawan lokuta sai yana ɗakin Hafsatu ne yake zuwa da abin daɗi ya ce tayi, ita kuma uwar iya sai tazo ta faɗa mata. Ta juyo da fuska.
"Tao kije ki tada wutar naga kamar ma da sauran rushi, icce zaki zuba da tayi hayaƙi zaki ga ta kama."
"To."
Ta ba ta amsa tare da juyawa ta nufi inda suke girkin, Suwaiba taja tsaki ƙasa-ƙasa. Haka ta fara aikinta duk da tana da ciki amma Suwaiba ko da iza wuta ba ta tayata ba har ta kammala, sannan ta ɗauko kwanon da take zubawa Salisu miya ta wanke ta zuba masa nashi ta raba har da mutanen gida ta ce Suwaiba tazo ta gani ko ya yi.
"Eh ya yi."
Ta faɗa tare da kwasar nata da 'ya'yanta, ita ma Hafsatu ta haɗe nata da na Bintu sannan ta miƙawa mutanen gida kowa a babban farantin silba da ta kakkasa.
Tana shiga ɗaki ta iske ya gama ware kuɗin, ta ajiye masa gabansa.
"Sannu da aiki amarya sarautar gida."
Murmushi tayi,
"Yawwa Angona sarautar zuciyata."
"Lallai kam sai ango."
"Eh mana, ai ni kai ango ne a gare ni."
Duka suka saka dariya, ya nuna mata yagaggun kuɗi wasu da 'yan'uwa wasu kuma babu ya ce,
"Gobe ki duba, masu 'yan uwa ki gyara waɗanda ba 'yan uwa ki ajiye idan aka samu wasu da suka yi daidai sai a haɗa."
"To godiya nake."
Daman haka yake duk wacce yake ɗakinta to ita yake ba. Salisu mutum ne mai tsananin kula da iyalansa, yana ƙoƙarin sauke haƙƙin da Allah ya ɗaura masa har da wanda yake ƙarawa saboda kyautatawa.
Hafsatu fita tayi a daren tayi wanka saboda aikin da ta wuni tana yi na girki. Suwaiba da ke leƙe taja wani dogon tsaki, tare da kaiwa bango naushi tana furta.
"Fitinannu aikin kenan, duk tsiyarku dai sai an sauke wannan cikin za a sami wani."
Ta kwanta saman gadonta zuciyarta na tafarfasa kamar zata faso ƙirjinta ta fito...
***
🩺 GHT HERBAL SOLUTIONS 🩺
Maganin da ke dawo da lafiya, da izinin Allah!
Muna sayar da ingantattun magunguna na zamani da aka gwada kuma suka shaida aiki.
Duk wannan cutar ana warke wa sosai mutum ya dawo nml
Ga wasu daga cikin cututtuka da muke da magani a kai:
✅ Ulcer
✅ Hawan jini
✅ Ciwon zuciya
✅ Ciwon Suga (Diabetes)
✅ Ciwon daji
✅ Ciwon koda & hanta
✅ Zazzabi mai tsanani
✅ Ciwon gabobi & ciwon jiki
✅ Ciwon ido & kunne
✅ Asma, tarin fuka & mura
✅ HIV
✅ Matsalar rashin haihuwa
✅Gyaran fata
✅Na kurajen fuska
✅Na rage kiban
✅Na Saka kiba
✅Na infection
🟢 Da sauran su...
Me ya bambanta GHT?
🌿 Magungunan mu halal ne kuma an tsaftace su.
🔬 Sun wuce binciken lafiya da gwaji.
🌟 Suna da matukar tasiri – an samu sauki ga dama-dama.
🧕🏽 Muna kula da sirrin marasa lafiya.
🚚 Muna da isar da magani kai tsaye (Delivery available).
Domin ƙarin bayani ***