𝒀𝒂𝒓 𝑵𝒐𝒍𝒍𝒚𝒘𝒐𝒐𝒅

E.P3️⃣⏩4️⃣

by @prettys01

*𝒀𝒂𝒓 𝑵𝒐𝒍𝒍𝒚𝒘𝒐𝒐𝒅*

_TAP THIS LINK TO JOIN MY GROUP👇_
***

_TAP THIS LINK TO JOIN MY CHANNEL👇_
***

_TAP THIS LINK TO JOIN IN AREWAPEN 👇_
https://arewapen.com/u/prettys01





💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

🕊️ *May Allah keep us united, uplift us, and make our pens a means of positive change.*

Much love and respect to each and every one of you. ❤️🔥  
*Keep shining, JAW family!* 🌺


   *JARUMAI WRITER'S TEAM📚✍️*

*BOOK ONE IS FEEE, WHILE BOOK 2 IS ₦500*


*𝒀𝒂𝒓 𝑵𝒐𝒍𝒍𝒚𝒘𝒐𝒐𝒅*

Story and writing✍️
      ```PRETTY SK```
           ~SAKINA ABDULLAHI~
> *PRETTYN JAJIRTATTU 💪✍️



        
       ✽‌»‌≿━༺🌹﷽🌹༻━≾»‌✽
 

_E.P______________3⃣⏩4️⃣._






_ previous_
> Kallona take cikin ido kamar yarda nima nake kallonta cikin ido, har ɗan wani hawa na yi kamar wacce za ta fashe, ba ko tsoro na tsaya gabanta muna kallon juna, har da ɗan ɗaga mata gira na yi dan neman ƙarin bayanin akan abin da ta yi min, A'isha kuwa kallona take kamar da rufeni da duka, sai dai yarda ba za ta iya ba saboda tana mugun sona......................✍️


_Continuotions_


__________________“Inayah, magana zan yi dake.” ta faɗa tana zama kan sopa, ganin ta sake rai nima na sake nawa ina zama a kan dressing mirrow, sai da ta furzar da iska daga bakinta sannan ta ce.

“Sherunki nawa?." Jin tambayar da ta min yasan na ɗan murmushin basawa sannan na ce.


“Shekarun ki a cire 3 kacal, ke 21 ni kuma 17 kinga kusan mate muke.” wani kallo ta watsi min shi yasa na ɗan natsu.

“Hmmm, be serious. I don’t want madness.” sai na gyara zama ina ƙara ware mata dara-daran idanuwana masu haske da ƙyau.

“Me yasa kike son zama ƴar Film?.” sai da na yi fari da manyan idanuna, sannan na ce.

“Coz I love it.” 

“Ke yanzu rayuwar Ƴam matan Hausa Film ne ke burgeki.......” da sauri na katseta.

“Nifa ba kannywood nake so, *NOLLYWOOD* nake so.” Hannu ta ɗaga min alamun na yi shuru.

“Ke fa Musulmace. Dad da Mom ba su da burin da ya wuce ki zama Doctor, amma......” 

“Nifa bance ba zan zama doctor ba, dukka zan haɗa.” da sauri ta miƙe tsaye, sannan ta nufa tvn dake jikin bango ta kunna.

Channel ɗin ɗazu ne in da ake wani film, ɗaga gani zai yi daɗi har na fara murmushi sai na ji ta ce.

“Yanzu wannan kike so? Yanzu irin wannan iskancin kike so ki din ga yi.” ta faɗa a daidai in da aka nuna club, mata da maza suna rawa, mata da wasu tsinannun kaya, yawanci saman ƙirjinsu duk a waje, Mazan dai sun fi shiga mai ƙyau, yawan ci suna jikin juna, suna rawa abun dai ba tsari.

Wani aka hasko wanda ga alamun star ɗin Film ɗin ne, shi da wata budurwa ne suka riƙe da juna, magana ya fara mata tana yin murmushi, sai kuma ta raba jikinsu za ta wuce da saurin saurayin ya juyo da ita tare da haɗe bakinsu waje ɗaya.

Da sauri na kauda kai na daga Tvn.

“Ki kalla mana. Ba irin wannan kike so ba.” cikin ɗaga murya kamar yadda ta yi maganar nima na ce.

“Ni sam ba haka ba, ba zan yi irin wannan ba, kuma Ni a maid nake so na fito, a ban kaya ne mutumci zuwa ƙasan gwiwa kamar dai wannan uniform ɗin nawa.” shiru ta yi tana girgiza kai tare da min wani irin kallo. 

“Fita...... Fita.” ganin yadda ta haɗe fuska yasa na fita da sauri, dan Ni ko a jikina, ko tsoron ta faɗa masu Dad ban yi saboda nasan tana sona ba za ta so ta ga ina kuka, kuma Ni Ko sun sani babu mai hanani film ɗin NOLLYWOOD 🔥.


 
   ********** ********** ******

    *GIƊAƊO MANSION*
    
_______Babban gida ne wanda yake da get guda huɗu, cikin gidan kuwa kai ka ce gari ne guda, dan kuwa Mansion ɗin ba ƙarami bane, gida ne mai hawa huɗu. Masu gadi kuwa a ƙalla sun kai 40 kowanne suna riƙe da bindigu, sannan duk wanda zai shiga sai an yi bincike kuma sai wani daga gidan ya tabbatar da wajensa zai je.


Parking lot kuwa motoci ne ajere kala-kala masu tsaɗa. 

Masu gadi ne suka buɗe get ɗaya sannan wata mota ta kunno kai zuwa cikin gidan, a hankali motar ta faka a jerin motocin dake wajen, sannan aka buɗe, wata budurwar falullata ce ta fito tana kulle motar, farace masha Allah, a ƙalla ba za ta wuce 21yrs ba, cikin gidan ta nufa tana taunar chewing gum a natse.

Ƙofar mai aiki da nunfashi ne, ya jin an matso yake buɗe wa, shiga ta yi wani tanƙameman falo mai ɗauke da kujeru ba iyaka, ga dukkan alamu gidan Family House.

“Sarah." Da sauri ta juya dan jin muryan mahaifiyarta. Ilai itace murmushi ta yi tana nufan ɓangaren da take.

“Ya makarantar." Mahaifiyar ta faɗa cike da kulawa.

Ko ba'a faɗa ba ana ganinsu anga jini ɗaya, dan suna kama da macen dake zaune, Babbar mace mai jiki masha Allah, ga haske ga ƙyau, kana ganinta kasan jinin Fulani ne tsantsa. 

“Alhamdullah.” budurwar ta faɗa cikin sanyin hali.

“To masha Allah, je ki huta.” sai ta miƙe har ta fara tafiya sai ta ji muryan wani saurayi daga stairs na uku.

“Darling.....Darling.” tsayawa ta yi cak sannan ta ja ƙaramin tsaki ta na ɗaga kanta, da fuskarsa ta fara cin karo yana mata ɗan iskan murmushi. 

“Ki jira ni ina zuwa." Ya faɗa yana fara saukowa, daga in da yake zuwa wajenta akwai nisa sosai, amma tsayawa ta yi cak har sai da ya sauko.

Saurayi ne wanda a kallo ɗaya za ka gane ɗan Allah ya shirya ne, dan kuwa shigarsa ma ya bayya haka, riga da wando ne jikinsa ƙananan kaya, sai wasu sarƙoƙi a wiyarsa kusan guda uku, haka hannunsa ma akwai su banda sosai, harda ɗankunne yake da shi a kunnuwan biyu. yana da ƙyau sosai, gashi dogo mai cika ƙirji, Babban star ne na fina-finan NOLLYWOOD, kuma tantairin mara jin magana dan kuwa kaf gidan shine babban ɗan Allah ya shirya, har zanen tattoo yana da shi a gefen wiyarsa ɓarin dama har ƙasa, ina da ka mai wani lafiyayyen zanen wata dabba.

“Darling ya kike?.” ya faɗa da zazzaƙar muryarsa kuma cikin ɗan taushi.

Saurayine ƙyaƙƙyawa dogo mai hasken fata sosai, sai dai shigarsa yana rage masa ƙyau sosai.

“Lafiya." Ta faɗa da ɗan rawar murya.

“Nasan kin gaji, je ki huta zuwa an jima zamu haɗu .” ɗaga mai kai ta yi sannan ta fara tafiya har da gudu-gudu ta hau stairs.


A hawa na biyu ta yi kwana room 25 nan ta buɗe ta shiga. Tana shiga ta kulle da murza key.


Hijab ɗin jikinta ta cire tana zama a ƙasa, ɗabas, ita har ga Allah ta tsana rayuwar *GIƊAƊO MANSION,* domin kuwa irin matsalolin dake cikin gidan, ji take dama Allah ya sa an haifota a talaka masu rayuwar kunci da ya fi mata akan rayuwar gidan *GIƊAƊO MANSION* 


Gida mai yawar al'umma, mai mabanbanta mutane da halaye, family ɗaya ne dukka amma yadda kasan gidan haya ko gidan yari, haka ake rayuwa a wahale babu damar rabuwa saboda wata *WASIYYA* guda ɗaya da ya zama silar zamansu a gidan, wato *WASSIYAR GIƊAƊO* wasiyyar da ya zama suka zama tsintsiya wanda bai da madauri kwata-kwata.



Sai da ta jima sannan ta miƙe ta shiga bayi, wanka ta yi sannan ta sauya kaya, ba ta fita har sai da ƙarfe 8:00pm ta buga wanda lokacin cin abincin dare ya yi, ko ba ka jin yunwa dole ka hallaci cin abinci safe da dare, wannan dole ne, da safe ƙarfe 7:30am dole kowa ya fito ko da ba za ci komai ba, sai ka fito.


Doguwar riga ne jikinta sai ta yafa vail sannan ta fita. A hankali take tafiya kamar wanda ƙwai ya fashe nawa, dama ita haka take da sanyi.

Ji ta yi an bangajeta da sauri ta riƙe ƙarfen stairs ɗin da sauri, tana bin wacce ta buge ta da kallo. Girgiza kai ta yi tana ƙarasa sauka, sun saba da irin rayuwar nan a cikin gidan, balle ƴan ɗakinsu.


Daga ko wani ɓangare sauka ake yi zuwa wajen cin abinci, ita ma nan ta nufa. Babban Dining area ne wanda yake da kujeru 50, kowa zama yake a nasa, gaba ɗayansu su 47 suka halarta wajen, babu mutum ɗaya, dan gaba ɗaya ƴan gidan su 46 ne yara da manya. 


Manya da yara duk suna zaune, amma babu wanda ya fara cin komai.


Sarah tana saukowa ta zauna gefan mahaifiyarta tana ɗan yaƙe kamar yadda ta saba.

“Ina Ayan? Shi kullum sai ya ɓa ta lokaci, salon ayi ta zaginsa” Bafullatanar dake gefen Sarah ta faɗa tana haɗe fuska.

“Ummee ku mai uzuri, zai fito yanzu." Sarah ta faɗa tana mai kallon wanda ke zama a gefan ta, Ahmad ne wanda aka kira da A.G. murmushi yake sakin mata har da kashe mata ido.

“Ummee Barka da dare." Ya faɗa yana kallon mahaifiyar Sarah. 

“Yauwa." Ta faɗa tana kauda kanta da kuma jin tsanar Ahmad a cikin ranta, kaf gidan shine ɗan Allah ya shirya, kuma aka rasa duk cikin samarin gidan wa za'a Sarah da shi sai shi.


Manya maza guda huɗu uwaye 6 kowanne matansa biyu, amma biyu sun rasu, sannan kowa suna da yara mata da maza. 

*GIƊAƊO* shine kakan wannan dangin wanda yaransa biyu ne kacal Yusuf da Yunus sai yaran ƙannin sa wanda ya mai da su na shi, Adam da Musa, gaba ɗayansu ya raina cike da so da ƙauna.

*GIƊAƊO* mutum ne mai tsatstsaurar ra'ayi, sai Allah ya bashi yara masu matukar biyayya. Shi ya gida wannan tangamemen gidan kuma anan ya yi rayuwa har mutuwarsa. 

Sai dai ya mutum ya bar *WASIYYA, kan cewa, so yake duk su aura mata biyu, su haihaifa, kuma su dinga haɗa aure a tsakanin su, ko da wasa kar wani nasu ya auro bare, ya zamana jininsa shine a cikin zuri'arsa.* 

Da haka yaransa suka ɗau wannan wasiyyar da muhimmanci, kuma ba su yi wasa da shi ba, ƴan dangi suka auro dukka, suka haifafa kuma suke haɗa aure, ko mutum ya so ko bai so ba haka nan yake yarda, a wasa-wasa, an yi aure 8 na yaran gidan. Yaron Musa ya aura yarinyar Yusuf, sannan yaron Yusuf ya aura yarinyar Adam, sai yaron Yunus ya kuma auren yarinyar Adam. 


Haka suke haɗa wa, kuma a gidan kowa ke rayuwa, yanzu mata huɗu suka rage da maza biyar, sai kuma yara masu tasowa. 

“Ina Ayan?." Faɗin Baba Adam wanda shine mahaifin Ayan da Sarah da wasu biyu.

“Kunsan halinsa ai, sai ya gama ɓa ta mana rai zai fito." Matar Yusuf ta faɗa wacce ita ce mahaifiyar Adam (Ammee), kuma ƴan ɗakinta sun fi kowa rashin mutumci da iskanci, duk dan Ammee tana ganin ai dukiyar GIƊAƊO ta su ce, ba ta su Adam ba, dan su yaran ƙaninsa ne.


Abubuwa dai a gidan babu daɗi sam, ga uban dokoki mara sa tsari. Sai dai babu wanda yake da ikon furta komai idan Iyaye maza huɗun nan suka yanke.

 Gaba ɗayansu ƙyawawane sai dai wasu sun fi wasu haske, amma gaba ɗaya jini ɗaya ne a jikinsu na cikakkun Fulani.

Cike da izza da kamala yake takowa, tafiya yake kaman wani basarake ko yarima, ƙyakykywan saurayi ajin farko, dogo mai cikar haiba da kalama, wanda a kallo ɗaya za ka fahimci tarin ni'ima da Allah ya yi mai, yana cikin faɗin ƙirji, ƙyawawan idanuwa masu rikata mata, Ayan kenan, gagara kowa a gidan sai mahaifansa.


Shine mutum ɗaya, wanda yake faɗa da tsarin gidan, be da wasa ko kaɗan, abu idan ba ya zama dole ba, ba ya magana, sam be da surutu haka yake, gashi shine duk yafi mai da hankali akan GIƊAƊO'S INDUSTRIES duk da ba kullum yake zuwa ba dan Lectural ne na Islamic studies anan Kad-poly. Sai dai duk da haka yake da mahassada a gidan.


Amma shi sam be damuba ko ta kansu baya bi dan rayuwarsa kawai yake yi, yana da tsare-tsaren sa ba irin da gidan ba duk da wasu lokutan iyayensa na taka mai burki, da yake mutum ne ma mai biyayya sai yake musu biyayya kamar yarda suke so, badan yana so ba...................✍️
END.

> Kunfa ji Jama'a. AYAN, AHMAD DA SARAH, da alamun kuna cikin taurarin labarin🥺.

> GIƊAƊO MENTION 😬😬


> WASIYYA 🙆

> Mu haɗu dan yi wa Inayah karatun natsuwa🤣, ga duk kan alamu a buɗe take.


*PRETTY SK* Marubuciyar Littattafan👇:  

📘 *DAGA INA TAKE* free book
📗 *RASH ƁOYAYYEN MASHEƘI* free book
📙 *BARRISTER* Paid book₦300
📕 *THE SLAVE* free book
📒 *ZAMU HAƊU* Free book
📓 *KWANA HUƊU* Paid book₦300 
📔 *GOLD DIGGER'S* Paid book₦300 
📚 *HASASHE KO BURI Book ONE* Paid book ₦500  
📝 *ISLAND OF WITCHES 👹* Free book
📘 *DARE ƊAYA ALLAH KANYI BATURE* _Paid Book ₦500_
📔 *YAUDARA ZALLA ❤️* 
      HIKAYOYI kuma sune :
*SARAUNIYA HIDAYA 😬🔥*
*SARKIN MU🤣*
*MOHINA DA MATSAFIYA💀*
*RAMUWA💀🔥*