YAƊIN MAGE...

Chapter 3

by @ummuaffan

YAƊIN MAGE...

©UMMU AFFAN

🩺 GHT HERBAL SOLUTIONS 🩺

Maganin da ke dawo da lafiya, da izinin Allah!

Muna sayar da ingantattun magunguna na zamani da aka gwada kuma suka shaida aiki.

Duk wannan cutar ana warke wa sosai mutum ya dawo nml

Ga wasu daga cikin cututtuka da muke da magani a kai:

✅ Ulcer

✅ Hawan jini

✅ Ciwon zuciya

✅ Ciwon Suga (Diabetes)

✅ Ciwon daji

✅ Ciwon koda & hanta

✅ Zazzabi mai tsanani

✅ Ciwon gabobi & ciwon jiki

✅ Ciwon ido & kunne

✅ Asma, tarin fuka & mura

✅ HIV

✅ Matsalar rashin haihuwa

✅Gyaran fata

✅Na kurajen fuska

✅Na rage kiban

✅Na Saka kiba

✅Na infection

🟢 Da sauran su...

Me ya bambanta GHT?

🌿 Magungunan mu halal ne kuma an tsaftace su.

🔬 Sun wuce binciken lafiya da gwaji.

🌟 Suna da matukar tasiri – an samu sauki ga dama-dama.

🧕🏽 Muna kula da sirrin marasa lafiya.

🚚 Muna da isar da magani kai tsaye (Delivery available).

Domin ƙarin bayani ***

LITTAFI NA ƊAYA

SHAFI NA UKU

Juyi kawai take yi, domin bacci ya ƙauracewa idanuwanta, mafi akasari daman duk ranaku biyun Hafsatu haka Suwaiba ke kwana juyi, sam ba ta wani wadataccen bacci na azo a gani, saboda mugun abin da ta ƙunsawa zuciyarta. Asubar fari kuwa ta fito da wankin kayan fitsarin yaranta, tana wankewa saboda kawai ta gani ko Salisu zai fito da asubar ta ga ya yi wanka ko alwala kawai zai yi? Domin ganin kwal uwar daka, sai ta ga fitarsa masallaci sannan take samun natsuwar komawa ciki. Daman yana dawowa bakwai ba ta masa a gidan yake fita kasuwa.

Salisu mutum ne mai ƙoƙarin neman na kansa, don tun yana yaro yana da zafin naman yin sana'a, duk da almajiranci yazo, ko kaɗan bai yarda da bara ba, ya gwamma ce ya yi aiko tuƙuru a biya shi ko a ba shi abinci yaci, tabbas ya kasance bango kuma majingina ga iyalansa a yanzu. Hausawa na cewa ba wai ka tara kuɗi mai yawa ba ne arziƙi, indai kana da rufin asiri tare da wadatar zuciya to sai kayi abin da wani mai kuɗin ma ba zai iya yi ba, matansa kuwa suna matuƙar alfahari da kasancewarsa hakan, wannan ne ya saka hatta matan da suke zaune gidan suke mugun sha'awarsu, don kaf gidan ba mai ƙoƙarin kula da matansa kamar shi, sai dai ana cewa daman ɗan adam tara yake bai cika goma ba. Duk da wannan jajircewar ta sa, yana da rauni a ɓangare guda wajen kula da me ke wakana tsakanin iyalinsa baya kula da wannan, duk wata tarbiyyar 'ya'yansa ya mallakata ga iyayensu mata, bai taɓa lura da halin da Maryama take ciki ba, haka watarana ma yana zaune Suwaiba za ta ɗaura mata talla bai taɓa hanawa ba ko ya nuna damuwa akan hakan, sannan a gabansa tana nuna tana matuƙar ƙaunar Maryaman fiye da yarda take ƙaunar 'yarta Asiya, shi dai yasan 'ya'yansa ne amma ba ruwansa da tarbiyyarsu ko saka musu ido, shi dai yana kyautata musu ta hanyar ciyar da su suturarsu da wurin da suke kwana, haka karatu sam bai damu da dole ɗansa ko 'yarsa sai sun yi makaranta ba, kuma abin takaicin duka biyun boko da islamiyya bai taɓa sha'awar saka Maryama ba, haka Suwaiba da za ta fita da kayanta ta sayar ta kawo mata ciniki shi ne damuwarta, sam ba ta taɓa masa maganar a saka yaran a makaranta ba ko da kuwa Islamiyya ce.

Hafsatu..

Sallamar Goggo ne ya saka Hafsatu da ke tsakar gida miƙewa da hanzari.

"Maraba lale, sannu da zuwa Goggo."

Zumbur Baaba ta hankaɗo labule.

"Ah sannu da zuwa Goggon Hafsatu yau ku ne a gidan?"

"Ai kuwa mu ne, sannunmu dai."

Goggo ta amsa, nan suka gaisa. Haka matan gidan da ke tsakar gida duk suka gaisa. Suka shiga ɗakin Hafsatu wacce bakinta ya kasa rufuwa tsabar farin ciki.

Ruwa ta kawo mata da ragowar abinci. Goggo ta sha ruwan suka ƙara gaisawa.

"Hafsatu zuwa nayi na tafi da Bintu, ina fatan Salisu ya faɗa miki?"

Da sauri ta dafe ƙirji.

"Tafiya da Bintu kuma Goggo, wani abin ne ya faru?"

"Babu abin da ya faru Hafsatu. Salisu ne da ya kai kayan miya kasuwa can Mahuta bayan ya tashi kasuwa yazo muka gaisa, shi ne ya ce Baaba ta ce ya kamata a ɗaukar miki Bintu ko kema kya huta ga ciki ga yarinyar nan tun da aka mata yayen dole sai lalacewa take. To shine na faɗawa Babanku yau ya ce nazo na tafi da ita kawai."

Hafsatu ta sauke numfashi da cewa.

"Ai kuwa bai faɗa mini ba, sannann kin san Baaba ba ƙaunata take ba, wallahi ba haka nan banza zata ce ya ce azo a ɗauki Bintu ba, shi kuma haka yake mata biyayya kamar tsohuwarsa."

Goggo ta girgiza kai,

"Ban ce kiyi ƙorafi da kowa ba, kowa ya yi daidai ko akasin hakan ai kansa, ni kaina daman na daɗe ina cewa zan zo na ɗauketa Allah ne dai bai nufa ba."

Shugowar Suwaiba yasa suka dakata da maganar, har ƙasa ta gaishe da Goggo don tana ganin girmanta saboda Goggo akwai kwarjini ko maƙiyanta shakkarta suke, ko kishiyoyi da suka sakata gaba. Haka suka barta don ita ce uwargida tayi zama da kishiyoyi kusan shidda don Baba mutum ne mai ajiye mata har huɗu, kuma ya binne biyu duk sun rasu bayansu kuma ya cikishe yanzu haka mata huɗu cif ne Baban su Hafsatu ke aure, shi ya sa yawa gare su yaransa kusan su hamsin manya da ƙananu, ko ɗakinsu su tara ne biyu sun rasu masu rai su bakwai ne. Autarsu ce kawai ba tayi aure ba, maza uku mata huɗu su uku mata suna da aure sai autarsu Zaliha wacce kakar bana za a yi aurenta.

Bayan Suwaiba ta fita, Hafsatu duk ta haɗa kayan Bintu a cikin Riyon kayanta, sannan Goggo ta fito suka yi sallama da matan gidan ta wuce.

Bintu ta buɗe ledar magungunan dauri da tazo mata da su, sai tsarabar masara da waken suya da ta kawo musu, kasancewar mahaifin Hafsatu babban manomi ne, ya yi shura kuma mai kuɗi ne na ƙauye sosai.

Kaduna State.

Malali Area

Cikin shigar alfarma ta sakko daga matattakalar benen tana tafiya tamkar wata sarauniya. Hajiya Sa'a kenan, amarya a gidan Alhaji Barau, kuma uwargida a yanzu, domin shekararta biyu a gidan ta fatattaki uwar gidansa Hajiya Zulaihatu kuma uwar manyan yaransa huɗu, mata uku sai namiji ɗaya, amma haka maƙirci irin na Hajiya Sa'a sai da ta raba sa da matarsa ta farko wacce ta zauna da shi tun kafin arziƙinsa ya kai wanda yake kai a yanzu, haka ita ma ta haifa masa yara har biyar babban ne namiji sai ƙannansa mata huɗu reras! Duk da ba haka aka so ba, wai gurguwa da auren nesa, domin a son samun Hajiyar ace duka 'ya'ya maza ta haifawa Alhajin saboda ta mallake sa, sai dai Allah ya nuna mata ikonsa inda ta haifi namijin a farko sannan mata huɗu suka biyo bayansa. Sai dai duk da hakan tana kallon kanta a sarautar mata, ba ta bari kanta ya kulle ba domin nuna mulki da isa take kai ka ce 'yar wani babban basaraken ce, saboda yadda take nuna mulki idan ba ka sani ba kai tsaye zaka furta 'yar sarauta ce.

Sai dai 'yar ƙauye ce, wacce ba ta da ilmin komi duka ɓangarori biyun, sai tarin jahilci da jin cewa ita wata tsiya ce. Aurenta da Alhaji Barau ne har ya sakata yaƙi da jahilci, da kuma haɗuwa da manyan mutane wayayyu yasa ta iya turanci, amma kan nan nata ba komi sai izzar.

Duka yaran mijin nata huɗu a hannunta suka ta so, sun ga izaya da maƙirci, a haka har Allah ya saka babbar da ta biyun aka musu aure kuma sai da ta samu talakawa sannan ta ce su za a aura musu. Na ukun ne namiji sai ƙaramarsu ma mace budurwa su ne yanzu suke hannunta, amma ba su da maraba da boyi-boyin gidanta. Namijin ma a ɗakin waje wajen mai gadin gidan yake kwana, itakam macen ba ta samu zarrar samun ɗaki a gidan mahaifin nata ba duk kuwa da akwai ɗakunan amma ba a bata ikon shiga ko ɗaya a ciki ba, sai dai ta kwana a parlour, kuma duk aikin gidan da wahalar 'ya'yanta Salima ita ce ke yi, ita za ta dafa abinci, amma sai dai taci a ɓoye ba a gani ba domin duk da ta dafa sai ta ba ta uwarni lokacin da taga dama sannan zata ci.

Hajiya Sa'a da Alhaji Barau sun haɗu da juna ne lokacin da Alhajin ya kai ziyara wajen Baffansa a garin Mahuta wanda Yaya ne a wurin mahaifiyarsa, a wancen lokscin shi kaɗai ya rage masa a dangin mahaifiyar tasa, shi ya sa duk bayan wata shidda yake zuwa ya gaishe shi da kawo masa abubuwan buƙatunsa. Ita kuma Sa'a ɗiya ce ga maƙocin Baffan nasa Alhaji Iro Alhajin ƙauye manomi da ake ganin girmansa da ƙimarsa a cikin garin. Tun da yaga Sa'a yaji yana son yarinyar lokacin shekarunta goma sha biyar har anyi baikonta da wani saurayin, amma tunda Alhaji Barau ya ce yana sonta ta amince kuma ta cewa Babansu ita shi zata aura don ta ganshi da kuɗi da mota, daman tun a lokacin burinta ne ta auri nai kuɗi kuma ɗan birni tana son rayuwar birni sosai.

To haka fa aka ɗaura aurenm Sa'a da Barau, Sa'a yaya ce a wurin Hafsatu mamar Bintu, kuma uwarsu ɗaya ubansu ɗaya. Sai dai an samu banbanci na ɗabi'u wanda ko da 'yan biyu ne ku ba lallai halinku yazo daidai ba. Duka suna da faɗa sosai amma na Hajiya Sa'a har da rashin imani da ɗaukar duniya da faɗi, sannan tunda ta zamo wata, sai ta fara janye jiki ga danginta hatta garinsu sai tayi shekara biyu ko uku ba ta je ba, idan akayi sa'a taje kuma ba ta wuce kwana biyu jal take tafiya. Mijinta mai alkhairi ne, domin duk shekara bai mancewa da iyayen matarsa yana ba su zakka, haka kuma duk da Baffansa ya rasu, yakan tako lokaci zuwa lokaci yana gaishe su tare da alkhairi. Itakam sosai ta janye jikinta ga dangi tayi sabbin wasu dangin ƙawayenta masu kuɗi su ne ta mayar danginta.

Tana ƙarasowa cikin parlourn ta ƙwalawa Salima kira.

Da gudu ta karo tare da durƙusawa gabanta sai ka rantse mai aikinta ce.

Ta yatsina baki fuskar nan tata sam ba annuri, mace ce mai ƙiba sosai kuma guntuwa ce ba ta da tsayi sosai, duk da ada tana da ɗan tsayi, sai dai ƙibar da ta shirga ne yasa tsayin nata ya shige, haka kuma tana da faɗi sosai, fara ce a launin fata kuma tana da kyawun fuska sosai irin na fulani. Sai dai rashin fara'arta ke sa ake gani munin halinta kuma ba ta da kwarjini irin na mahaifiyarsu daman mafi akasari masu irin halinta kana samunsu a haka, suna da ban tsoro kuma zaka ji kana shakkarsu.

"Kin gama abinci ne?"

Ta faɗa da isa da jin kai.

"Ban gama ba Mummy, ina gyara ɗakinsu Saimah ne."

"Hmmm!"

Ta faɗa ba tare da ta kuma magana ba, ta ƙarasa gaban wayar tarfo, ko ince tafi da gidanka kasancewar a lokacin waya ba ta wadata ba. Ba wai don babu kuɗin sayen ba sai dai ba ta gama shugowa da yawa ba, sai dai irin wannan ta parlourn da ake ajiyewa tafi da gidanka. Ta daddana kafin ta kara a kunnenta minti biyu ta fara magana.

"Eh Hajiya daman akan angon nan ne, kin san dai bikin nan ba na wasa ba ne, bikin ɗan aminiya sai mun biki ƙirji.!"

Shuru da alamar ta cikin wayar ce ke magana, zuwa can ta kuma cewa.

"To ki taho mana da su duka, nawa da kuma na uwar bikin har da goggoron."

Ajiye wayar tayi ta kuma kallon Salima a yatsine.

"Ki yi sauri ki kammala girkin nan, ki kira ni idan kin ƙara sa zan ba Salim ya kai wa yara school, idan kuma lokaci ya ja uhmnmm!"

Ta nuna ta da yatsa tare da komawa sama.

Salima ta bi ta da kallo, fuskarta da damuwa har ta ɓacewa ganinta, duk sonsu da boko haka suka haƙura. Yayunsu biyu Sabila, Samira, duk ba wacce tayi karatun islamiyya ballantana boko har aka aurar da su, ga shi ita da ɗan'uwanta ma Salim haka zasu ƙare rayuwar ta su.

Yaranta kam duk suna makarantar boko don anan aka fi ƙarfi babu arabi, Shahid shi ne babba, Shahida ke binsa sai Saliha sannan Saimah sai autarsu Shuhaidah ita ce mai shekaru uku ita ce ke rainonta, suma duk sauran ita ta raine su kafin su shiga makaranta, duk da har yanzu idan sun dawo ita ce komi nasu Shahid shekarunsa goma sha uku, Shahida goma sha ɗaya Saliha tara Saimah bakwai sai auta Shuhaidah me shekaru uku.

Sauri-sauri ta kammala gyaran ɗakin nasu sannan ta koma kitchen, tana yi tana duba lokaci Allah-Allah take ta ƙara kar sha biyu tayi ba ta ƙarasa ba, domin sha biyu ake kai musu abinci kasancewar ƙarfe ɗaya suke cin abinci a makarantar tasu.

Hamdala tayi da ta ga ta kammala domin idan ta mata kure duka take sha, tun tana ƙarama har yanzu kuma da take da shekaru sha takwas a duniya ba ta daina bugunta ba, hatta Salim da ke da ashirin da ɗaya dukansa take, don ma yanzu ya fara fin ƙarfinta don ranar ta kai masa duka yana miƙewa da ya hamɓarata taa kusa faɗuwa tun daga lokacin ta rage, sai dai fa ranar har koransa sai da Alhaji ya yi a gidan da ta faɗa masa ƙarya da gaskiya. Sai daga baya ya dawo ga shi kullum cikin aibata shi da tsine masa Alhaji yake, wataran sai dai Salima ta dunga kuka don ita kanta zagi da tsinuwa tana shansu a wurin mahaifin nasu.

Da sauri taje ta sanar da ita ta kammala, sannan ta fito wajen gidan, ɗakin mai gadi ta nufa da sauri don kiran Salim ya yi hanzarin zuwa kafin ta kammala sakkowa ta haɗa masa kar ya jawowa kansa laifi wurin mahaifin nasu. Sai dai turus tayi daidai lokacin da ta ga abin da magananta suka gane mata a ɗakin....