KUNCIN ZUCI

Kuncin zuci

by @bintuuu

Cikin jeep din da Ahmad ya basu kwanaki Nafisa taje gidan nasa, wanda gudun da tayi yasa ta isa cikin 30 minutes, bayan tayi parking sai ta fito tana kallon sleek rides dinsa dake nan parking lot, yau ko kwadayin daukan motan ma taji bata yi, so take taji menene dalilin wannan kira da Yayan nasu ya mata, dan a saninta ba ya kira haka sai da dalili, da dan saurinta ta nufi falon gidan sai ta kusa cin karo da ma'aikacin dake kula da gidan, shiya fada mata Ahmad din na gurin pool din gidan sai ta juya da sauri ta nufi backyard din, tsaye ta hangosa a bakin pool din hannunsa duka cikin aljihun wandonsa yana kallon ruwan pool din kamar me tunani, da sanyin jiki ta qarasa sai ya dago kai, a nutse yace "Kinzo" ta gyada kai tace "Eh Yaya Ina wuni" casually yace "Lafiya" sai ya nuna mata resting chair dake gurin yace "Seat" zama tayi tana kallonsa, ganin yanayin sa yasa duk ta sha jinin jikinta, dan juyowa yayi yace "Tell me everything Nafisa, ina nufin komai da ya faru da ita tun daga farkon rayuwanta" sai tace "Yaya nima farkon haduwa na da ita a BUK ne, daga nan ne friendship din mu yayi qarfi har na san me yake faruwa da ita" yace "Is she married even before then?" ta girgiza kai tace "A'a, haduwana da ita baifi da wata ba aka mata auren ala dole, Yaya tun farko Na'ima bata so amma familyn nata suka mata dole" yana kallon Nafisan yace "Who are they?" sai Nafisa ta miqe ta qaraso bakin pool ta tsaya itama, nan ta fara bashi labarin asalin Na'ima yana sauraronta attentively, jefi jefi yake dago kai yana kallon Nafisan da fuskansa da ta fara ja, da ta iso gurin da ta fara haduwa da Bilal sai ta kalli Yayan nata tace "Yaya har cikin gidan auren nasu ya kawo mata karuwarsa suna rayuwa akan idanun Na'ima, this is the extreme of how Na'ima keda hakuri" yana kallonta yace "Da sanin iyayen nasa?" tace "Da sanin mamansa, komai da ya faru da Na'ima a gidan Bilal da sanin ta duka, the first time da nayi convincing dinta akan ta fadawa mahaifin sa, uwar hana Na'ima fada tayi and the worse part is, that same day Bilal beat Na'ima to the point that bata iya tafiya" sai Ahmad ya dunqule hannu yakai bakinsa, shiru yayi ganin haka Nafisa ta cigaba da bashi labarin tana hawaye, Ahmad sai kallon pool din yake ransa na zafi, da ta fada masa kisan da Stella taso yiwa Na'iman sai da ya rufe fuskansa da tafin hannunsa, aransa ya dinga fadin duk addu'an da tazo bakinsa, kafin Nafisa takai masa qarshen labarin sai da duk wata jijiya ta tashi a fuskan Ahmad, abunka da farin mutum sai fuskan tayi jaaa, Nafisa na kuka tace "Komawa tayi kamar me ciwon kwakwalwa Yaya, she was depressed to the point that neman mutuwa take a lokacin, karfe biyun dare ta iso Abuja ranan fa, cikin bodin Daf Yaya, babu inda babu ciwo a fuskanta, ko gani batayi da ido daya, wallahi kasheta ya so yi Allah beyi ba dan tabon da suka yiwa Na'ima tun daga bayanta har kafanta bazasu qirgu ba" sai sannan Ahmad ya bude baki a hankali yace "He's an animal, ko me nayi masa bazan huce ba Nafisa, ko me na musu dukansu bazan taba jin dadi ba" itama tace "Sun cuci Na'ima a rayuwa, har yau nakasa kwatanto rumuwan da zeyi daidai da abunda suka aikata mata Yaya" sai sannan ya kalleta amma bece komai ba, aransa yana ayyana how little she knows about the world, acikin maganganunta yaji cewan Bilal yana yi wa Na'ima alluran bacci awasu daren, does that means raping Na'ima yakeyi in her sleep kenan, Hasbunallah, sai ya daga kai yana kallon sama zuciyarsa na dacii, , a zuciya yace 'Ya Allah, give me strength' dan wani irin ciwo yakeji a zuciyarsa, irin wannan abubuwan suna ta faruwa da Na'ima a lokacin da ita da shi suke mabanbantan guri a duniyar, then his biggest regret in life shine rashin kulata da yayi ranar da ya fara ganinta a Kano, rashin bibiyar rayuwarta da yayi a wannan lokacin shi yafi komai yi masa ciwo yanzu, bai dena kallon sky din ba ya sake wani maganan zucin 'Ya Allah kabani juriya akan lamarin Na'eemah', sai Nafisa ta sake cewa "I was meaning to tell you everything amma Na'ima taqi bari inyi hakan, har nan qasar ya sake biyota, and he beat her again a ranan da kaje daukan mu a school, she was afraid in kasan asalinta ko kasan ta bar gida alaqanku zai chanja" yana kallon Nafisan yace "Ni nake tsoron ta chanja min saboda abunda namiji ya mata a rayuwa Nafisa" tace "Tana sonka Yaya,i know her and i see it in her eyes, nasan at first she was reluctant about it but not now, not now wallahi, Bilal was all in the past" sai yace "Not for me Nafisa, i only know him now so he is my present" sai ya sauqe numfashi ya sake cewa "He is in cell right now, and don't even speak of it to her" sai sannan Nafisa tayi murmushi tace "Toh Yaya, dan Allah ka barshi yayi rotten a cell dinnan" sai yace "Cell is a good place Nafisa, i won't mind letting him go free now, dan komai yanada lokacinsa" ya juya yana kallon pool din sannan ya sake cewa "Komaii"..
Da Nafisa ta tashi tafiya sai da ta biya kitchen din sa ta dauki coke mai sanyi a fridge, tana kurba ta nufi parking lot wani nutsuwa na shiganta, tasan lokacin da Bilal zeyi kuka in return ya kusa, dan a iya sanin da suka yiwa Ahmad a familyn su, gwara yabi abu cikin gaggawa akan yace zai bisa a sannu, tashin nakiya yake yiwa abun a lokacin da ba'a yi tsammani ba...Har motan Nafisan ya fita daga gidan Ahmad yana nan zaune a bakin pool din, cikin sanyin jiki ya miqe tareda nufan cikin gidan nasa, alwala yayo ya fara sallah anan falon, da ya idar sai ya nufi stairs da nufin ya je yayi wanka a dakinsa amma beep din wayansa da ke kujeran falon ya katse sa, dawowa yayi ya dauka sai ya ga hotunan Bilal din ne Micheal ya turo masa, hotunane gasunan kala kala wani Bilal din yana zaune wani kuma gashinan kwance kan dandaran qasa acikin cell din, ahankali yakai hannu yana zooming fuskan Bilal din abubuwa dayawa na zuwa masa arai, tuna wannan mahaukacin, wannan mashayin yayi sharing same bed da Na'ima yasashi juyawa yayi wurgi da wayan, da karfin gaske ta daki gini sannan ta tarwatse anan falon, cikin huci ya zauna a kujera ya kama kanshi da duka hannunwansa yana jin komai nasa na masa ciwo, wani radadi yake ji a zuciyar sa me dacin gaske...And he know har ya mutu bazai dena jin tsanan Bilal a zuciya ba....
Har dare Na'ima ta kasa bacci dalilin rashin ganin kiran Ahmad, ta juya tana kallon Nafisa dake bacci a gefenta hankali kwance, sai taji kamar ta tasheta ta fada mata abunda ya faru tsakaninta da Ahmad a Oxford ranan, gashi kuma har sannan bai kirata ba, tana nan zaune jingine da gadon tana tunani sai ta kasa jurewa kawai ta dauko wayanta ta danna masa kira, cikin ringing na ukun ya dauka sai yayi shiru, ahankali Na'ima tace "Are you there?" sai taji muryansa ahankali shima yace "Babe i'm sorry ban kiraki ba" tace "No it's okay, I'm just checking on you" yace "Uzuri ne ya riqeni, but I'll come tomorrow kinji" tayi saurin cewa "No it's fine, good night" ahankali yace "Good night" ta gyada kai tana gyara kwanciya zatayi bacci, da haka Ahmad ya kashe wayan, sai ya juya yana kallon likitan da ke tsaye kansa yana hada allura ga Lamin zaune shima a gefen gadon yana kallonsa, Lamin bai ce komai ba sai da likitan ya gama yiwa Ahmad alluran sukayi sallama ya fice sannan ya kalli Ahmad yace "Does this has to do with her?" shiru Ahmad yayi bai amsa ba ya kai yatsunsa yana danne audugan hannunsa dake gurbin alluran, da dan bacin rai Lamin ya sake cewa "Ahmad what is wrong with you these days?, you're not yourself" Ahmad dake jin zazzabin jikinsa na tsumashi ya dago kai rai a bace yace "Just leave me be Al'amin, dan Allah kabarni da abunda nakeji, just go please" miqewa Lamin yayi ganin yanayin abokin nasa, sai yace "Sorry Man, Allah ya baka lafiya" Ahmad ya jawo white duvet a jikinsa sai ya rufe idanunsa ya jingina kansa da fuskan gadon baice komai ba, juyawa Al'ameen yayi zai fita sai ya dan tsaya kallon hoton Na'ima dake dakin yaqara juyowa yana kallon Ahmad din da har sannan be bude idanunsa ba, ahankali yace "Saida safe" da haka ya fice daga dakin abubuwa dayawa suna zuwa ransa..Sai karfe ukun dare bacci ya dauki Ahmad ranan, bayan yayi sallahn asuba yana kwance kira ya shigo dayan wayansa dake kusada bedside lamp, sunan Mahaifinsa ya gani akan wayan sai yayi saurin dauka tareda sallama, daga daya bangaren kamilin mahaifin nasan yace "Wa'alaikumussalam babban mutum" duk yanda Ahmad ke jin yanayinsa sai da yayi murmushi yace "Ina kwana Baba" yace "Ka tashi lafiya?" Ya amsa da Alhamdulillah sannan Baba yace "Ya ayyukan kuma?, London ta riqeka dayawa" Ahmad bai bar murmushin ba ya sake cewa "Alhamdulillah" a nutse Baban ya fara magana "Adam ya samoni da maganan ayyukan jiya, you have to be there tomorrow for the shareholders meeting, they'll be expecting you there as their Head, kana da pending meetings da ayyuka har haka kuma kake zaune a London har yanzu Babana" cikin ladabi Ahmad yace "In sha Allah za'a gyara" sai Baban yace "Yauwa dai, I'll be there tomorrow nima" da haka sukayi sallama Ahmad ya sake danna kira a line din mahaifiyarsa, yana shiga ta dauka da sallama, bayan sun gaisa sai yaji kaman tana kitchen dalilin sounds din da yake jiyowa, sai yace "Kina aiki ne?" fita Mamma tayi daga kitchen cikin kwantar da murya tace "Baka da lafiya ne naji muryanka haka?" yace "I'm fine Mamma, it's just headache" ta sauqe numfashi tace "Ka rinqa sararawa kanka da aikin nan da Allah, dazu mahaifinka ya fadamin zakuyi maganan zuwan ka Lagos, in ka gama ka dawo nan gida ka dan huta tukunna" murmushi Ahmad yayi yace "In sha Allah zanyi yanda kika ce din" tace "Allah ya baka Lafiya, Allah yayi albarka" ya amsa da Amin sukayi sallama, nan ya hau neman available flight na safiyar ranan, economy class ticket ya samu ya siya saboda late booking din, miqewa yayi jikin sa babu qarfi ya nufi toilet kansa na juya masa, da ya gama shirin cikin riga da wando masu tsadan gaske sai ya dauko farin jacket ya dora akai tareda saka farin facing cap sannan ya dauki jakansa ya fice yana texting me kula da gidan nasa wanda ya kasance drivernsa shima anan basement din gidan yake zama..
Sai da Ahmad ya zauna a cikin jirgin sannan ya turawa Na'ima text na tafiyan nashi, daga daya bangaren Na'ima na kitchen tana hada breakfast dan Anty Amnah zasu fita da wuri ranan, daukan wayan tayi ta karanto saqon nashi.
'Babe i'm sorry i can't come today, I'm heading to Lagos right now but I'll call you the moment we land Okay, take care'
Jikinta ne yayi sanyi bayan ta gama karantawa, sai ta tura masa da saqon Addu'an isa lafiya sannan ta cigaba da abunda takeyi...

Da safiyar ranan Bilal ya fito daga cikin police station din a jikkace yayi wani wujiga wujiga dashi, jacket dinsa dake hannunsa ya saka sannan ya ciro wayansa da aka bashi yau din daga aljihu ya kunna, sai yayi sa'a akwai sauran chargy aciki, nan messages din Hajiya da Alhaji suka rinqa shigowa amma na Hajiya sunkai talatin, sharesu yayi sannan ya danna kira a wani abokinsa me suna Anas da ya sauqa gurinsa a qasar, har ta gama ringing ba'a dauka ba, qarasa wa bakin street din yayi ya tari uber yanajin ransa na suya, lallai daga Na'ima har wanda suke zaman iskancin tare a qasar zasu gane shi suka kulle, wato riqanta har ya kai ta saka abokin zaman dadiron nata ya masa wannan wulaqancin, da ya isa gidan abokin nasa dake Dulwich, kansa tsaye ya shiga gidan, aikuwa nan kan kujeran falon ya samu Anas yana badalarsa da karuwarsa jikinsu duk babu kaya, sai ya miqe yana kare gabansa yace "Shit man, ya zaka shigo wa mutane babu sallama Bilal" dauke kai Bilal din yayi ko kulasa beyi ba ya nufi dakin da ya sauqa, shi bata su yake ba, abunda ke cin zuciyarsa yafi gaban wannan, da ya shiga dakin sai ga kiran Hajiya ya shigo wayansa yana cire kayansa, da kamar baze dauka ba sai yayi qaramin tsuka ya dauka, daga daya bangaren Hajiya kamar zatayi kuka tace "Ayya Babana so kake in mutu kawai ka huta kenan, Ina ka shiga cikin satikan nan dan Allah?" Yace "Ina London fa" tace "Me ya kaika can kaida ga aikinka ya dawo kano kuma" cikin karyewan zuciya yace "Naganta, Naga Na'ima Hajiya" ai daga can miqewa Hajiya tayi tace "A London ta ke barikin kuma, Bilal in kana yiwa Allah ka rabu da yarinyar nan, me zaka cewa Alhajin in ka dawo da ita, ta ina zaka fara kare kanka akan abubuwan da kayi" zuciyar sa na quna yace "Sai na dawo da ita Hajiya, Na'ima mata ta ce ni kadai, babu wanda zai aureta ina raye, har wanda tasa ya kullenin bazan barshi ba" Hajiya da ta hangame baki tana shirin magana Bilal ya kashe wayan, yana gani tana sake kira amma bai dauka ba, message notification yagani a saman wayansa da baquwar number sai ya shiga ya karanta content din..

'This is my first warning to you, don't let me see you near her again'

Bilal ji yayi kamar yayi ta dukan gini ko zaiji dadi a wannan lokacin, ransa in yayi dubu ya lalace, yau shine wani banza zai kullesa sannan ya bashi warning akan Na'ima, lallai sai ya nuna masa shima qwaro ne...sai da yayi wanka ya cire kayan jikinsa da suke wari sannan ya sake dauko wayansa yayi sliding Dm din Nafisa dake Instagram....