Kuncin zuci
by @bintuuu
A week Later...
Zuwa sannan yazama saura kwana hudu su Na'ima suyi graduation ceremony na gama Msc dinsu a inda Na'ima zata gama a fannin Data science while Nafisa kuma information management, a wannan ranan suna apartment dinsu sai harhade kayansu sukeyi guri daya wanda zasu koma gida dashi, Na'ima na tsugunne gaban wardrobe tana saka kaya a akwatin nasu Nafisa ta shigo hannunta riqe da wasu books manya, ta dago kai tana kallonta tace "Nafee zo ki zauna muyi magana" da Nafisan ta zauna a bakin gado sai tace "Na miki wani abunne da yasa bakyason fadamin alaqarki da Lamin?" da sauri Nafisa sauqo qasa tana ware Ido tace "Meyasa zakiyi tunanin haka Na'ima?" cikin sanyin murya tace "Toh naga kuna waya kuma kinqi fadamin komai" Nafisa tace "Wallahi ba boye miki komai nake ba, har yanzu muna stage din fahimtan juna ne sis, kuma Ina jira inga step din da zai dauka akan relationship din namu in na koma Nigeria ne" Na'ima ta gyada kai tace "In sha Allah komai zai daidaita a tsakanin ku" sai takai hannunta ta dafa Nafisan tace "Inason inga kina cikin steady relationship sis, I'll give everything to see you happy with the man you love Nafee" sai Nafisa tayi murmushi tace "Kamar ke da Yaya Ahmad" murmushin itama tayi ta kauda kai tana fadin "Ni nace miki muna dating?" Nafisa ta kwashe da dariya tace "Toh wallahi kanki kika rainawa wayo bani ba, Eh lallai" Na'ima bata daina murmushi ba ta cigaba da ciro kayan wardrobe din, sai Nafisa takai hannu ta dauko wani kaya tana kallo tace "Dama har yanzu kayan nan suna nan? dasu kika taho qasar nan daman?" Na'ima na kallon kayan Nurse Aminan itama, ahankali tace "Ina ajiyansu ne har zuwa ranan da Allah zai bani ikon maida mata su tareda kudin da ta aramin" sanyi jikin Nafisa yayi tace "In sha Allah tare zamuje in ga baiwar Allah'n nan, she is truly kind, Allah ya biyata da mafificin Alkhairy" Na'ima ta gyada kai tana jin zuciyarta na karyewa tuna abunda ya faru da ita ranan da aka bata kayan, shiru Nafisa tayi tana kallonta sai takejin kamar ta fada mata yanda sukayi da Ahmad da abunda Bilal ya turo mata a Instagram, amma sai ta fasa, ta miqe zata debo toiletries din Na'ima dake bandaki kiran Husna ya shigo wayanta, a hand free ta saka bayan ta dauka sai Husna tace "Nafisa na barwa duniya ke, na yafe ki kawai" Nafisa na dariya tace "Wallahi baki isa ba, ina maqale dake har duniya ta tashi" sai Na'ima tayi murmushi tana girgiza kai sanin draman mutane biyun nan, Husna ce tace "Dan rashin mutunci har zakuyi graduation amma baki kirani kin fada min ba sai yanzu nakeji a bakin Yaya yana fada wa Mamma akan muzo nida ita da Anty fatima, Bobo yaushe ma yasan kuna karatun da har ze rigani sanin gamawanku" Nafisa tace "Anty Husna ta aminiya ta yau fa nake shirin kiranki" Husna na dariya tace "Karyaaa, sai kace ban sanki ba, yanzu dai ba wannan ba, labari naji gurin Salma wai Laila tabi Yaya har nan qasar" Nafisa ta amsa da "Tazo three weeks dasuka wuce, har dambe munyi amma na mata duka" sai da Na'ima ta bar abunda takeyi tana jin ikon Allah, dariya sukayi dukansu kafin Husna tace "Zamu zo in sha Allahu bakina da maganganu nima, yar banzan wai ance sai rashin lafiya takeh mommyn ta sai sintiri take zuwa gurin Mamma, da safen nan kuma sai gata tazo gidan nan qalau da ita takawo wa Yaya snacks" Jin abunda tace yasa Nafisa kallon Na'ima, ganin ta kauda kai tana zipping box yasa ta cewa "Ke hakura zatayi fa dan Yaya Ahmad ya daidaita da matar da zai aura anan qasar ma" Husna tace "Ke habaaa?..har ina cewa zan miki magana ki san yanda zakiyi ki hadasa da kawarkin nan Na'ima, Allah ya gani tana burgeni sosai" sai Nafisa tayi murmushi tace "In na fada miki wacece sai kinfi kowa farin ciki toh, kedai Allah ya kawoku lafiya" Na'ima yi tayi kamar ba maganan ta suke ba tana cigaba da abun gabanta, amma aranta sai da taji wani zafi najin Laila taje gurin Ahmad din, ranta ne taji yana baci, kawai ta miqe ta fice daga dakin tana nufan kitchen zata tattare musu wasu utensils din...
Har washegarin ranan Na'ima na kallon kiran Ahmad a wayanta amma taqi dauka, gashi dai tanajin zuciyarta wani iri amma batason yarda cewa kishin Ahmad ne yake damun ta, haka ta wuni har yamma zuciyarta babu dadi, gashi Nafisa bata nan ranan sai yamma ta dawo, lokacin suna kitchen itada Anty Amnah Nafisan ta shigo tana musu sannu da aiki, sai da suka gama ta ja hannun Na'iman suka shiga daki tace "Bobo bakisan Ya Ahmad yadawo babu lafiya bane?" sai Na'ima ta tsaya kallon ta takasa magana, ganin hakan Nafisan ta sake cewa "Ashe da rashin lafiya ya tafi last week ma, yanzu ma ya dawo da shi, ina gidansu Lauren, Lamin ya kirani yake fadamin da yazo daukana, har munje na dubasa ma" sai Na'ima ta kauda kai tace "Allah ya bashi lafiya" da haka ta kwanta a gadon, zama Nafisa tayi tace "Me yake damunki ne Na'ima, rashin lafiya yake fa" sai ta dago kai tace "Ayya Nafisa yazanyi toh in ba addu'an zan masa ba" Nafisa tace "Kije ki dubasa, that's it" sanyi jikin Na'ima yayi, ganin haka sai Nafisan tace "Ke ya fara tambaya na da naje dazu Na'ima, and shi yace kar na fada miki amma tun kwanaki ya kulle Bilal a cell sai da zai tafin nan yasa aka sakeshi" kasa magana Na'ima tayi saboda mamaki, sai Nafisan ta shiga Instagram dinta ta kunnawa Na'iman voice note din da Bilal ya tura mata, sai da zuciyar Na'ima ya buga jin Bilal na masifa yana ambato kashe Ahmad acikin maganansa, bata qarasa jin voice note din ba ta kalli Nafisa a dan rikice tace "Bilal ya masa wani abu ne da yake rashin lafiyan?" dariya ma Nafisa taso yi, aranta tana ayyana yanda hakan ma zaizo kan Na'ima amma madadin ta amsa mata sai ta dan gyada kafada tace "A bakinsa zakiji wannan ba ni ba" da haka Nafisan ta miqe tashiga bandaki, shiru Na'ima tayi anan zaunen tana tunanin maganganun Bilal din zuciyarta na qara yin nauyi, cikin sanyin jiki ta miqe ta saka veil akan doguwar rigan jikinta na atamfa me dogon hannu, a jakan Nafisa ta dauki transport money tareda wayanta ta fice daga dakin, sauqinta bata samu Anty Amnah a falon ba sai twins da suke ta wasan ludo, ficewa tayi hankalinsu nakan wasan basu kulata ba..A Uber taje gidan amma da ta isa sai ta tsaya a bakin gate din ta rasa me zatayi ma ganin bata san pin na gate din ba, kiran Nafisa tayi bayan ta dauka sai tace "Nafee bansan pin na gate din ba" kadan ya hana Nafee yin dariya sai ta danne ta fara fado mata, da ta danna ta shiga sai ga ma'aikacin gidan ya fito daga backyard da saurinsa yace "Who are you?" tace "Tell him it's Na'ima" dan kallon attire dinta yayi sai aransa yayi tsammanin yar uwar ogan ce tunda bahaushe ne, sai yace "It's alright come in" da haka ya bata hanya ta nufi entrance din gidan tana tafiya a hankali, tsayawa tayi bakin babban kofan falon bayan ta danna door bell, ana budewa idonta ya fada cikin na Ahmad, da dan mamakin ganinta ya fito daga falon yana murmushi, sai taji damuwan da tazo dashi din yana sauqa a hankali ganin shi cikin kuzari, yana kallonta yace "Muje ciki Babe" da kamar zai kama hannun ta amma sanin da abokansa a falon yasashi beyi hakan ba, yana gaba suka shiga falon sai abokan nasa guda uku suka dago kai suna kallonsu, Lamin dake cikinsu yana murmushi yace "Guys, our princess is here" sai sukayi murmushi gaba dayansu, Ahmad yace "Yau dai bazata kulaka ba" ai kuwa nan Na'ima tace "Ina wuni" sai biyun cikinsu suka fara dariya, Ahmad yana murmushi ya dafa goshinsa alamun Kash, sai ya juya yana kallonta bai daina murmushin ba, tsayawa tayi nan gefensa duk a taqure sai ya kalli abokanan nasa yace "Na'eemah meet my Gee's, Lamin kinsan shi, sai Mus'ab and Jason" tana kallonsu a kunyace tace "Ina wuni" suka amsa banda baturen da baya jin hausa, Mus'ab ne ya fara miqewa yana cewa "Muma lokacin tafiyar mu yayi daman" da haka suka miqe gaba daya Ahmad ya rakasu can wajen inda anan suka tsaya suna wani maganan kuma, zama Na'ima tayi a kujera tana jiransa sai ta hango Simba yana sauqowa daga stairs, da saurinta ta nufeshi ta tsugunna a gabansa tana shafa gashinsa, Ahmad bai dade ba ya sake turo kofan falon ya shigo, ganinta tsugunna gaban muzurun yayi murmushi yace "Babe bakya tsoronsa?" ta dago kai tana murmushi tareda girgiza kai, kitchen ya nufa bai dade ba ya fito hannunsa riqe da drink ya zuba mata a cup sannan ya taho gareta riqe dashi ahannu, miqewa tayi ta karba sai ya duqa ya daukin Simba yace "Kina sonsa har haka" tayi murmushi tace "Yana da kyau sosai, adopting kayi?" ya girgiza kai yace "Stray cat ce ta haifa a forest din gefena dinnan na dauka" ta gyada kai suka nufi kujera, bayan ta zauna sai ya zauna agefenta ya bar gap a tsakaninsu, sai da ta aje cup din hannunta bayan ta kurba sannan tace "Ya jikin naka?" yana kallonta yace "Me ya faru baki dauki wayana ba Babe" taqi kallon idonsa tace "Ban san inda na ajiye ta ba" sai yayi murmushi yace "Bari dai kiga zan fara kiran Anty ta rinqa hadani dake kawai" adan shagwabe tace "Uhm uhm nikam" sai ya rinqa kallonta, kauda kai tayi tana murmushi, cikin sanyin murya tace "Ka daina min irin kallon nan" sai taga ya duqo kansa ahankali yace "Wane irin kallo nake miki?" nan Na'ima taji iskan falon ya fara mata kadan, she know it's risky zaman ta guri daya ita kadai da Ahmad amma batasan me yazo kanta ba ma tazo din, Ahmad na kallon yanda take wuri wuri da ido yana murmushi, ji yake he can do alot to her at that moment amma sai yafara kokarin danne abunda yakeji din because ba irin wannan son yake mata ba, he purely wants her in a pious way, dan gyaran murya Na'ima tayi tace "Nafisa ta fadamin ka kullesa" sanin me take nufi ya sashi gyara zama yace "I'm not even done with him, it's just a start" sai tace "I don't want you to get involved with him, he is so evil Ahmad" yana kallonta yace "He is only evil akan mace, he's a fool Na'eemah, and i will give him what he deserves soon enough" cikin kwantar da murya tace "Komai ya wuce fa" sai ya kamo hannunta yana juyo da tafin yace "Abunda sukayi bazai taba wuce wa ba Na'eemah, look here" yana nuna mata tafin hannun ya sake cewa "Wannan yayi kama da abun da zai wuce" ta girgiza kai cikin karyewan murya tace "Banaso ya cutar da kai" sai ya tallafo fuskanta yace "Sai dai kiji tausayinsa Na'ima, Billahi i'm going after him so hard that sai ya yi choosing mutuwarsa" hawaye ne ya fara zuba a idonta tace "What if na yafe" sai ya kauda kai rai adan bace yace "Ni ban yafe ba" shiru sukayi babu wanda ya sake cewa komai acikinsu, ganin kamar ransa ya baci ya sa ta kwantar da murya tace "I'm sorry" sai ya juyo yana kallonta yace "I hate him Na'eemah, i hate everything about him, inajin zafin saninsa da kikayi kafin ni, inajin zafin abunda ya miki a rayuwa" ahankali ta sake cewa "I'm sorry" sai kuma zuciyarsa ta karye ganin yanayinta, riqo hannunta yayi yace "It's alright Babe, ba laifin ki bane kinji" ta gyada kai sai ya kwanto da kanta a kafadansa bata daina hawayen ba, cikin lallami ya kwantar da murya yace "I Love You Na'eemah, Billahi ina sonki, inason in rayu dake" sai ya dago kanta tana kallonsa yakai hannu ya share mata hawayen yace "Zan iya yin komai akan wanda ya tabaki" sai tayi murmushi hawayen bai daina zuba a idonta ba tace "Nima haka Ahmad, Nima haka" yana murmushi yace "Ranan da na ganki a karo na biyu a falon Mami, you know what i felt?" sai ta girgiza kai tana kallonsa, yace "Naji ajikina Allah ne ya sake bani wani daman a karo na biyu, shiyasa banyi wasa da ita ba Na'eemah" sai tayi murmushi tana duqar da kanta, ji take komai na duniyan na mata sanyi a rai, haka So din yake daman, haka akeji in ana So, indai haka ne toh 'tanason Ahmad' kuma zata sake fada da babban murya tana sonsa, shiru sukayi kowannensu da abunda yake saqawa arai, Ahmad sai kallonta yake baya ko kifta ido, ganin taqi dago kan nata sai ya duqar da kanshi suka hada Ido, kawai ta fara dariya kadan kadan tana kare bakinta da hannu, bai bar kallonta ba shima yana murmushin yace "You're a Fulani right?" ta gyada kai ahankali tace "Duka fannin iyayena" sai yace "You're beautiful Na'eemah, idanunki sunada kyau sosai" ganin yana kallonta dayawa yasata yin gyaran murya tace "I have to go, it's getting late" sai yace "So soon Babe" idon ta ne yakai kan abunda ke cikin laptop dinsa dake kan glass table sai tace "Wannan ma App dinka ne?" sai ya kalli laptop din yace "Yes, ina encrypting dinsa ne, to tighten the security" ta dan duqo tana kallo tace "It looks unique, menene sunan" yace "Bizgo" gyada kai tayi tace "Sounds nice, what does it do?" sai ya dauko laptop din ya daura mata akan laps dinta yana nuna mata ciki, yana briefing nata yadda sales platform da freelancing features ke aiki acikin App din, sai da ya gama yace "Do you like it?" ta gyada kai tana murmushi tace "Ta yaya kake iya creating App irin haka?" sai yayi murmushi yace "App din ya miki kyau?" tace "Sosai fa" sai yace "Then, it's yours" ware ido tayi tace "What? A'a bazan karba ba" yace "Zan miki transfer din komai anjima, as a Data scientist nasan kinada developer account ba" Na'ima dake cikin mamaki har sannan ta kasa cewa komai, ganin haka sai ya kamo hannunta yace "It's your graduation gift Babe" karbe hannunta tayi cikin sanyin jiki ta miqe dan tasan kome zatace bazai fasa bata din ba, ahankali tace "Zan tafi" sai ya miqe shima tareda daukan car key dinsa dake nan kan glass table din yace "Bari na kai ki" ta gyada kai kawai ta nufi kofa yana tafe abayanta, ahanya ya tsaya a wani babban supermarket ya lodo mata kayan ciye ciye kamar bai san ciwon kudinsa ba, sai kallon kayan da suka cika back seat din take ta kasa magana, sai da yayi settling a driver's seat sannan ya bare wani chocolate ya miqa mata yana cewa "Ci kiji, it's my favorite" sai da ya jira ta gutsura sannan ya karba daga hannun ta ya cigaba da ci tareda miqa mata wani sabo, sai taqi karba tace "Nidai kabani wanda nafara ci gaskiya" ya sake kaiwa baki yana danne dariya, ta shagwabe fuska tace "Kana cinyewa fa" sai da ya rage dan kadan sannan ya miqa mata, aikuwa ganin shi dan mitsitsi tace "Nafasa ci" dariyan da yake dannewa ce ta fito fili sai ta juya kai tana murmushi, dakyar ya lallabata ta karbi wani sabon chocolate din sannan ya kunna motan suka tafi....
Daren ranan suna kwance Na'ima na game a iphad dinta taji qarar shigowan notification a wayanta, dago wayan tayi sai taga daga App store dinta ne, Ahmad ya mata transfer din komai related to App din nashi, da mamaki ta rinqa duban App din, da tazo kan CPM na Ad's revenue saida takai hannu baki, bata gama shan mamaki ba sai da taga monthly income na App din, magana ake ta hundred of millions ne zasu rinqa shigo wa Na'ima duk wata, App din nada over four million users and CPM din ta yana zuwa daga kasashen turawa ne wanda sune 80% users din, Na'ima batasan lokacin da takai duka a bayan Nafisa dake gefenta ba, agigice tace "Na shiga uku Nafisa ina zan kai kudin nan" da sauri Nafisa ta miqe tareda leqo kanta suna ganin wayan tare, sai ta ware ido tace "Wooo, Na'ima what is this?" sai Na'ima ta kalleta tace "Nafisa bazan karba ba, maida masa ownership dinsa zanyi" Nafisa tace "Ya Ahmad ne ya baki?" ta gyada kai sai Nafisan ta sake cewa "Wallahi bazaki maida masa ba Na'ima, Allah ne ya baki, and you deserve more than this" cikin sanyin murya Na'ima tace "Toh muyi sharing, be a patner, kudin is too much for me Nafisa" ganin yanda Na'iman ta gigice yasa ta kamo kafadan ta tace "Rabon ki ne Na'ima, wannan shine son ai, yana sonki ne shiyasa ya baki, ki karba ki gode Allah kinji" sai Na'ima tayi shiru ta sake juyawa tana kallon App din akan wayanta....Da Ahmad ya kirata da daren suna cikin magana tace "Me zance wa su Abba akan App din" cikin kwantar da murya yace "Zan fada musu Babe, karki damu kinji" tayi shiru sai yace "Baki fadamin yanda kukayi da supervisor din ki ba" ahankali tace "Yace i'm good to go, Nagode sosai" yace "Ma Sha Allah, Allah yasa ku gama a sa'a" ta amsa da Amin....
Washegarin ranan su Mami suka diro qasar itada dasu Abu, su Na'ima ne sukaje daukansu tareda da twins, da babban sign dinsu sukaje Airport din sukayi rubutu ajiki 'We Love You Mamii' Nafisa har da siyan balloon sukayi decorations a jikin, anan waiting area suka tsaya tareda da dagawa suna jiran fitowansu, aikuwa suna fitowa suka hangosu, suna daga sign din Nafisa na cewa "Oyoyo..Mami, Oyoyo... Mami" juya kai Mami tayi tana dariya tace "Ji shiririta" Abu ya daga hannuwa ya taho yana cewa "We love you tooooo" da gudu Nafisa ta nufi Mami, Na'ima ta bita abaya riqe da twins, sai da ta kai kusa da Mamin kawai ta sake twins din ta nufeta da sauri itama, rungumesu duka Mami tayi tace "My babies" sai da ta cika su Al'ameen dake gefe yace "Ni komawa zanyi, har wani we love you Mami kadai ajikin sign din, to mu din duwatsu ne?" sai Nafisa ta talli qeyarsa ya kai hannu gurin yana dariya, Abu ya matso kusada Na'iman yace "Anty this time zaku koma nikuma zan tafi, guess qasar da zan tafi karatun" kafin Na'ima ta amsa Mami tace "Muje sai mun huta tukunna ayi maganganun" sai Nafisa tace "Mami Ina Yaya Faruk fa" Na'ima ma sai kallon bayan su take tana duban inda zata ga bullowarsa...