BAFULATANA🐄

Chapter 1

by @zmchubado

🐄BAFULATANA🐄


    Z.M~CHUBAƊO✍️


بسم الله الرحمن الرحيم
 
Wannan littafin tsohon littafine, na rubuta shi tun 2015. It marks the beginning of my journey as a writer😊.


Page: 1

_GYAMBU (TARABA STATE)_

Tafiya suke a cikin daji tare da shanunsu cikin ayari, wata matashiyar yarinya ce wadda ba zata wuce shekaru goma sha hudu ba sai kuma dattijon dake kusa da ita da alama dai mahaifin ta ne.

Cike da damuwa yarinyar ta daga kai ta kalli mahaifinta ta ce,"wllh Baffa nagaji kawai ka tafi Gida idan na huta zan taho tareda sauran shanun." ta Ƙare maganar tana karyar da kanta cikin marairaicewa.

Tunda ta fara magana Baffah ke kallonta sannan Yayi murmushi ya ce,"to mamana amma kar ki bari duhu yayi miki cikin daji ki kula sosai."

A hankali ta ɗaga kanta ta ce,"to Baffah." 

Shafa kanta yayi sannan ya juya ya Kama hanyar gida Ya barta a dajin tareda Dabbobin, ƙura masa idanu tayi tana kallonsa har ya ɓace mata da gani, ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi sannan ta nufi wata Ƙatuwar bishiya dake gefanta ta zauna dan ta huta. 

A nitse ta fara cire takalmin Robar dake Ƙafarta, bayan ta gama cirewa hannu tasa tana jan dogayen yatsun ƙafarta tana yamutsa fuska alamar gajiya, Jingina bayanta tayi da bishiyar bata jima ba wani wahalallen bacci ya samu nasarar ɗauke ta saboda gajiyar dake tareda ita, kallo daya za kayi mata ka fahimci tana jin dadin baccin da takeyi.

A hankali iska mai sanyi da daɗi ta fara kadawa haɗe da ƙamshin ƙasa, cikin ƙanƙanin lokaci hadari mai tsanannin duhu yayiwa sararin samaniya ƙawanya, lokaci guda hasken walƙiya tareda tsawa suka gauraye a guri guda, sosai iska ke kaɗa bishiyun jejin da ƙarfi wanda.

A rikice ta miƙe jin yanda iskar ke ƙoƙarin fusge tufagin dake jikinta, idanunta ta murza lokaci ɗaya ta miƙe sannan ta ɗaga dara-daran idanunta Sama Tana kallon hadarin daya gauraye sararin Samaniya ya koma baƙi ƙirin.

Sai ta sunkuya da sauri ta kwashi takalman robarta ta saka a ƙafa tafara ƙoƙarin kaɗa shanun tana fadin su kama hanyar gida cikin harshen fulatanci, nan da nan shanun suka fara tafiya kamar yanda ta basi Umarni, suna cikin tafiya yayyafi ya fara sauka a hankali can kuma se ruwan sama ya balle kamar da bakin Ƙwarya, A maddin ta nemi maɓoya sai kawai ta dinga tsalle tana murna Ruwan na sauka a jikinta tana dariya, haka nan Ruwan yayiwa Rabe dukan tsiya amma itako ko a jikinta wai an tsikari kakkausa inji 'yana magana.

Cike da annashuwa take tafiya tana tsalle tana kuma shiga cikin ruwan da ya taru a kan hanya Har Ruwan ya ɗauke, Kasancewar kayan jikinta na farin Saƙi ne ya sa duk yayi jajir Saboda jar Ƙasar dake kwance a hanyar, sai data gama tsalle tsallenta a cikin taɓo sannan ta tisa shanun Suka kama hanyar gida.

Ba su jima suna tafiya ba suka iso gida, sai da ta fara kai shanun cikin garken su sannan ta ƙarasa inda bukkokin su suke.

Filine mai girma ko ina a share tsaf babu alamar datti ko ƙazanta, a tsakanin ko wace bukka akwai rumbun dake maƙotaka da ita, sai kuma murahu da tukwanen ƙarfe sai ƙyalli suke tamkar ba'a taɓa ɗorasu a wuta ba.

Wata ƙatuwar bukka ta kalla wadda tafi ko wacce girma, lumshe kyawawan idanunta tayi sannan ta kalli ƙasan farin zanin dake jikinta wanda ya koma ja saboda ruwan taɓon data gama wasa dashi. Hannunta ta ɗora a dedai kunkuminta sannan ta falla da gudun ta Ƙarasa kusa da wannan babbar bukkar, ta gefan bukkar ta raba ta isa Bukkar matar babanta.

Da sallama ta shiga Ɗakin jikinta a ɗarare cikin harshen Fulatanci ta ce,"jadda na dawo."

Tunda ta shigo jadda ke kallonta da wata irin tsana baiyananniya, cike da ɓacin rai gamida tarin tsana ta ce," Uwar me zan maki da kike gayamin kin dawo? shegiyar yarinya mai mugun hali, zaki fice mini daga ɗaki ko sai na ƙaraso gurin na sabautaki shegiyar yarinya mai baƙin jinin tsiya har yanzu kinƙi auruwa saboda baƙin jininki, uwarki ma a tsiyace ta Ƙare kuma kema a haka zaki Ƙare tinda kikayo gadon tsiya." Jadda ta ƙare maganar tana hucci kamar macijiya

Tunda ta fara magana Rabe Ke kallonta cikin rashin fahimtar inda magan-ganunta suka dosa, saboda har ga Allah bata fahimci abinda jaddan take nufi ba Sam, kullum tana gaya mata irin haka amma abin bai taɓa damunta Kamar na yau ba, tambaya ɗayace ke mata yawo a zuciya gameda maganganun Jadda "shin mai yasa kullum take Maimaita mata magana ɗaya babu canji?."

Tana cikin duniyar tunanin da takeyi ne taji Saukar murfin kwano a saman goshinta!

Jadda ce ta buga mata tana huci lokaci guda ta ƙara rarumar kwanon dake gabanta cike da Mugunta ta ƙara jefa mata ya sauka a saitin hancinta, nan da nan Jini ya fara fita a goshinta da hancinta, gigicewa tayi ta ƙwalla ƙara sannan ta juya a rikice tana nemam hanyar fita daga bukkar saboda Jinin data gani yana Zuba daga hancinta da goshinta, sosai ta gigice saboda a Rayuwarta bata ƙaunar ganin jini komai ƙanƙantarsa tsoronsa take ji. Da gudu ta nufi hanyar garken shanunsu Tana kuka saboda bata so Baffah ya dawo ya gani, tabbas ba zata taɓa jin daɗin haka ba.

Karo taji tayi da mutum cikin tsoro taja da baya zata faɗi taji an riƙeta gam, Baffah ne Babanta moddibo mai sonta da tauyayinta.

Ganin yanda jini ke zuba ta hancinta ne ya sa zuciyarsa ta buga, yanayinsa ya sauya lokaci guda ya janyota a kiɗime a kiɗime ya ce,"Innanillahiwa'inna'ilaihirraji'un! mamana mai ya sameki haka?"

Ya firta haka yana ƙoƙarin ɗaga kanta sama don ya tsayar da zubar jinin, ganin jinin yaƙi tsayawa ne yasa ya kama hannunta suka nufi wannan babbar Bukkar ta cikin gidan don yasa mata maganin daze tsayar da zubar jinin.

Wata ƙatuwar ƙwarya ya janyo ya buɗe faifan da aka rufe ƙwaryar dashi, ɗaurukan garin magani ne kala'ala a ciki yasa hannu ya ɗakko wani koren magni ya kwance, sai da ya fita ya samo ruwa sannan ya dawo ya zauna kusa da ita, wani farin tsumma ya tsoma cikin ruwan ya sake matsewa sannan ya fara goge mata goshin, sai da ya tsaftace mata fuskar tsaf sannan ya barbaɗa mata maganin.

Cikin ikon Allah kuwa jinin ya tsaya amma sa dai goshin ya kumbura sosai kuma yayi jazir kasancewarta farar fata, a hankali take sauke ajiyar zuciya saboda kukan data sha.

Kallonta kawai Baffa keyi yana jin tausayinta yana ƙara samawa kansa gurbi a cikin zuciyarsa, jikinsa ne yayi sanyi har bai san da ya kai hannu ya shafi gefan fuskarta ba. Shiru ne ya ratsa tsakani na tsahon lokaci sannan Baffa ya fara magana cikin sanyi murya ya ce,"Mamana kiyi haƙuri da rayuwa kamar yanda na jima ina gaya miki, ko wani ɗan'adam baya rasa jarrabawar da ubangiji yake masa, amma da zarar kinyi haƙuri komai zai wuce ya zama labari tankar ba'ayi ba, duk wani abu da zai dinga haɗaki da Jaddah ki yi ƙokari ki kauce masa sboda bata na lura bata da wani burin daya wuce ta illatamin ke! sanin kanki ne mamana bani da wanda ya rage mini a yanzu sai ke kaɗai, tunda na rasa mahaifiyarki nake rayuwa da giɓi a zuciyata.

Mahaifiyarki ita ce duniyata da duk wani farin cikina, tun da tabar duniya nake ji a raina cewar na rasa wani ɓangare na rayuwata. shi kuma dan Uwana da muka fita ciki ɗaya tuna kina jaririya aka nemashi aka rasa sai daga baya aka samu gawarsa a bakin hanya mota ta bigeshi, A kwai cuwuka sosai a cikin Rayuwata wanda banaso ma na dinga tunasu saboda yanda zuciyata ke zafi." shiru ya yi sannan ya janye hannunsa daga kan kumatunta ya matsa baya ya jingina bayansa da karan bukkar.

Murmushi ya yi mai ciwo sannan yaci gaba da cewa,"Na rasa abubuwa da yawa a rayuwata wannan yasa bana so na ƙara yin wani sabon rashin, sanadin mutuwar ɗan Uwana muka daina bin titi da dabbobin mu har lokacin da mahaifiyarki ta haifeki, tunda na rasa iyaye na ban Ƙara samun farin ciki ba sai da na aureta. Ahaifiyarki ta ƙaunace ƙaunar mai tarin yawa, ta ririta ni irin riritawar da sai da nayiwa mazan nahiyar mu zarra, sannan ta sadaukar da farin cikinta don nawa farin cikin. A cikin kaso ɗari na soyayyar da nake mata ne duk suka dawo kanki bayan mutuwarta, ta rasu ta barmin ke, tun kina shan nono ni na raineki da hannayena sannan na shayar dake da madarar dabbobin mu, saboda ba zan iya ba dake ruƙo ga wasu ba har kika fara girma ina kula dake ban taɓa gajiyawa ba.

Bayan rasuwar Maryamu da shekara 2 malm iro yazomin da shawarar na Ƙara aure saboda kina buƙatar kulawar Uwa a tareda ke, ta hakane ka ɗai za ki samu rayuwa mai in ganci.

A wannan lokacin sai na ɗaga kai na kalleshi da matsananciyar damuwa na ce,"Banƙi shawararka ba Iro amma wllhi ba zan iya haɗa soyayyar Maryamu da wata ɗiya mace a duniya ba, ina matiƙar ƙaunarta sosai ta yanda ko bayan ranta ba zan iya yi mata kishiya a soyayya ba, sannan wacce mace zan Aura wadda zata iya riƙemin amanar Rabe bisa gaskiya da tsoron Allah?"

A wannan lokacin kallon dana gani a idanun Iro kallon tausayine tsantsa, don haka nayi murmushi nace,"shawararka mai kyau ce a gareni Iro, amma wllh bana so Rabe ta rayu da gurbin maraicin wani abu a Rayuwarta Ko kaɗan."

da kulawa malm Iro ke kallon Aminin nasa sannan yayi murmushi ya ce,"indai wannan ne matsalarka to ka kwantar da hankalinka Moddibo, ni zan baka ƙanwata Jaddah ka aura nasan zata riƙe maka ƴarka tsakaninta da Allah, kai dai kawai ka Amince da maganar Auren Jaddah ik sha Allahu hakan zai zame muku alheri."

Ba dan zuciyata taso ba na Amince Da maganar Auren Jaddah, kallo ɗaya Iro yayi mini ya fahimci maganar auren bata kwanta mini a rai sai kawai yayi murmushi a karo na biyu ya ce,"in dai ka amince ka auri Jadda ni kuma nayi maka alƙawarin zan zama me koyar da Ƴarka Rabe ɗan karatun da nake dashi akan alƙur'ani, ta yanda zata zama daban a cikin sauran yaran dake maƙotaka da Rugar mu." Ya ƙare maganar yana faɗaɗa murmushinsa

Ba tare da tinanin komai ba na amince zan auri Jaddah. Ashe abinda ban sani ba shine sanadin tarwatsewar rayuwar gidana da farin cikin Ƴata na Auro."

Baffah ya Ƙare maganar Yana Kuka sosai.

A nitse Rabe ta rarrafo kusa da shi tana kallonsa zuciyarta na mata zafi, ba ta san abinda ya kamata tayi ba sai kawai ta matsa baya ta takure kamar mai jin sanyi. sosai ta rungume hannunta a ƙirjinta ta fara kuka sosai kamar yanda ta ga yanayi, 

sai da moddibo ya yi kuka mai isarsa sannan yayi shiru, ganin har lokacin ita bata daina kukan bane ya sa ya matsa kusa da ita ya ɓanɓare hannun da tai folding a ƙirjinta ya ce,"Bar kuka mamana, yi shiru kinji." ya firta hakan yana share mata hawaye da tafin hannunsa.

Sai da ya tabbatar da ta samu nutsuwa sannan ya ƙara dubanta da kulawa ya ce,"Mamana kinci abinci Kuwa?"

Da sauri ta Ɗaga masa kai alamar taci, amma kuma a zahiri ba wani abinci data ci kawai ta amsa masa ne dan kar ya ɗaga hankalisa.

Moddibo ya yi sannan ya kai hannunsa saman tulun gashin kanta ya ce "to maza tashi ki tafi daukar karatu kar lokaci ya ƙure miki, banda wasa a hanya kinji Mamana? Allah ya albarkaci rayuwar ki Rabe na."

Da kyakkyawan murmushi ta amsa da "amin Baffah" sannan ta tashi ta nufi makarantar Allon malm iro inda take daukar karatu can gaba da rugar su kaɗan.

Dik da kasancewar su fulanin daji hakan be zama tawayar da zai hanasu neman sani akan karatun salla ba, dukda shima malam iron dake koyar dasu ba wani ilimin ƙwarai gareshi ba, hasalima budunbidimarsa kawai yake koya masu da sunan karatun addini.

duk cikin sa'o'in Rabe babu wacce ba'ai mata aure ba sai ita kaɗai ta rage tareda Ƙawarta Ruƙatu, sune kawai suka rage a yaran da basuyi auren ba.

Rabe kyakkyawar yarinya ce Ajin farko kallo Ɗaya za kai mata ka fahimci haka, sai dai bata da dirin budurci irin na sauran mata, saboda tsamurarren jiki gareta ba ƙiba sai tsaho, idan tana tafiya sai ka rantse karyewa za tayi saboda rashin guzari.

tana da dara-daran idanu masu ɗaukar ha kalin mai kallonta, don wannan dalilin yasa Jadda ke kishi da tsarin halittar da Ubangiji ya bawa Rabi'adu moddibo Arɗo.

Ta nada yalwar gashin kai mai tsananin laushi da cika Irin na Fulanin Usuli ƴan gado, Rabe miskilace ta ajin Ƙarshe ta wata fuskar, amma kuma idan ta samu guri akwai surutu da wauta ta ban mamaki.

Rabe yarinya mai kaifin basira don haka cikin ƙanƙanin lokaci a ƙure ilimin Malam Iro, dama shima Fatiha kaɗai ya iya sai wani karatu da yake musu wai karatun sallah wanda har yau bai fara biya musu shi ba.

Ƙoƙarinta na saurin hadda ya sa malm iron ke Ƙaunarta sosai, wannan ya sa bata sakewa da samarin Rugar saboda malam yace mata duk jahilai ne basa gane karatu.

Mutum ɗaya rak take kulawa shima saboda baƙin nacinsa Ana kiransa da Suna BAMANGA, shima ba ɗan Rugarsu bane ɗan Rugar dake maƙotaka da tasu ne wannan ya sa take biye masa, a nitse ta ƙarasa makarantar Abin mamaki babu wanda yazo sai ita ka dai, Ajiye Allon ta tayi sannan ta dauki tsintsiya ta share gurin Tass ta shimfiɗa tabarmar kabar Dake jingine a gefe zauna ta fara bitan karatunta dan a ranar zata ƙawa wankewa.

Tana cikin karatun ne Ruƙatu ta Ƙara so gurin, Rabe tana ganinta tayi murmushi ta ajiye allon
Ruƙatu tayi dariya tace," ko ki biyo min ko? to ai gashi nazo nima kuma na san dan ki rigani wanke Allo ne yasa kika tawo kika barni to."
*_(duk wannan maganar cikin harshen fulatanci suke yinta)_*

Rabe tayi dariya ta ce "Ruƙatu kenan keda za kiyi aure kwanan nan ai kin ma kusa ki dena zuwa makarantar Gabaɗaya, gashi kuma malam yace zai kawo sabon karatu."

Haɗe rai Ruƙatu tayi Sannan ta ce,"to ai sai munyi sauka dubu sannan Auren ya halatta a kanmu saboda malam yace idan aka fara sauka sai anyi dubu kafin ayi zaman aure idan aka fara. 

"ƙwarai kuwa haka malam ya gaya mana, shiyasa na dage yanzu nayi sauka casa'in saura ta ɗari da ɗoriya."

Idan littafin ya birgeku kuyi comment da kuna so sai muci ba❤ idan bai muku ba sai na ajiye alƙalamina.

ZMC💋

Comment
Nd
Share
***