Chapter 2
by @zmchubado
🐄BAFULATANA🐄
Z.M~CHUBAƊO✍️
02
Da haka suka rufe hirar sakamakon Ƙarasowar malam Iro gurin, cike da girmamawa suka gadashi ya amsa tare da sakin fuska ya ce,"An gaida Ƙawayen juna Idan har akaji maganar Rabe to da Ruƙatu ne koda Baffanta Moddibbo." Malam Iro ya faɗi hakan yana murmushi.
murmushin su kayi ba tareda sunyi magana ba Rabe ta sunkuye, Ruƙatu aka fara biyawa Allonta sannan ya biyawa Rabe nata, suna kammala Karatun duk suka miƙe sannan su ka yiwa malam Iro sallama kowa ya kama hanyar gida, a hanyar komawar ne su kayi kacibus da Aliko Wanda ze auri Ruƙatu, Tun kafin su ƙaraso inda yake ya kafesu da idanu kamar ze cinyesu, tura baki Rabe tayi sannan ta zinguri Ruƙatu ta ce,"da alama nan gaba wannan maƙale matan naki har makarantar zai dinga binmu, wannan baƙin nacin nasa idan baki maida hankali kinyi sauka dubu ba watarana sace ki zaiyi a nemeku a rasa saboda maitarsa." Rabe ta faɗi haka yayin da take nuna mata Aliko.
A nitse suke tafiya har su ka ƙarasa inda Aliko ke tsaye, rai a haɗe suka gaisa da Rabe ita kuwa Ruƙatu sai Faman boye fiska take a bayan Rabe wai ita Ala dole kunyarsa takeji.
Ba su jima a tsaye ba Rabe tayi mai sallama ta nufi gida cike da tinanin Abinda zata tarar da ga bala'in Jaddah, tuna haka yasa taita wasa a hanya harta gama cinye sauran lokacin daya rage mata sannan ta kama hanyar gida saboda ta san Baffah duk inda yake a wannan lokacin to ya koma gida, ba ta koma gida ba sai yamma liƙis kasancewar suna da nisa da makarantar sosai, cike da fargaba ta ƙarasa ɗakin da take kwana ta kwanta sai da ta kwanta sannan ta sauke ɓoyayyiyar ajiyar zuciya.
Har cikin ranta take hamdalar rashin haɗuwar da ba suyi da Jaddah ba, Saboda har ga Allah ba tason duk abinda zai ƙara haɗata da ita dan ta san haduwarsu da juna ba alheri bace, ta na cikin wannan tunanin taji Antaɓa Labulan buhun dake jikin Ƙofar bukkar, da sauri ta mike tsaye gabanta na faɗuwa duk zatonta Jaddah ce.
Da sallama ya shiga ɗakin yana kallonta da mamakin kwance a fuskarsa ganin yanda duk ta tsorata, ganin Baffah ne yasa ta nufeshi da gudu ta faɗa jikinsa ta rungume shi lokaci guda ta fashe Masa da kuka tana ƙara ƙanƙameshi.
Shiru ya yi yana sauraron sautin kukan ta wanda ke huda masa zuciya, sai dai beyi yunƙurin hanata ba kukan ba har sai da tayi mai isarta. Sannan ya janyeta da ga jikinsa ya sa hannu ya share mata hawayen da ya ɓata mata fuska cikin sanyin murya ya ce,"kiyi haƙuri Mamana na san Kinada Cikakkiyar hujjar da za kiyi kuka saboda ba kiyi dacen Uwar ruƙon ƙwarai ba, ki Ƙara haƙuri kaɗan In sha Allah wata rana sai kin ba da labarin rayuwarki ga wasu a lokacin da kika fi ƙarfin komai."
Da sauri ta ɗaga kyawawan idanunta ta kalleshi don bata fahimci maganar ba.
Murmushi Baffah ya yi sannan ya kama kafadunta ya zaunar da ita a bakin katifar ciyawar dake ɗakin ya ce "daga yau mamana nayi miki alƙawarin ba zaki sake kukan rashin uwa ba In sha Allahu kinji?"
Bai jira cewarta ba ya miƙe cikin nutsuwa ya nufi ƙofar fita da ga bukkar zuciyarsa nayi maaa zafi akan munanan halin Jaddah.
Ganin zai fita ya barta ne ya sa ta yi saurin ɗa ga kanta ta ce,"Baffah don Allah kayi mini Aure! Ina so nayi nisa da Jaddah, ina so na daina ganinta gabaɗaya....."
Zuciyarsa ce ta buga da matsanancin ƙarfi, mamakin da al'ajabin maganar da tayi ne su ka haɗu suka sabbaba masa sanyin jiki, a sanyaye Baffah ke kallon tsakiyar idanunta don tabbatar da gaskiyar abinda ta firta.
Ajiyar zuciya ya sauke a ɓoye sannan ya sauke idanunsa ƙasa ya ce"Aure kikace mamana?"
Ba tare da tinanin komai ba ta ɗaga kanta alamar Ae.
Jikin sa a mace ya taka har inda take zaune ya dafa Kafaɗunta da kulawa ya ce,"da gaske kike mamana?"
Ba tare da fargaba ko shakkaba ta ce,"Baffah Ina so In dai zan daina ganin Jaddah." ta faɗa tana kallonsa hawaye na zubowa da ga idanunta. har ga Allah ba ta san me ake nufi da Kalmar Auren ba, ita dai kawai tana jin kalmar ne a baki mutane ba tareda ta san nauyin abubuwan dake cikinsa ba, kawai ta fada ne dan ta samu sauƙin a zuciyarta.
Baffah ya yi murmushi ya ce"shike nan ni zan kawo miki mijin da zan Aura miki har cikin gidan nan, tunda dai kince Aure kikeso kin gaji da zama da Baffan ki?"
Da sauri ta washe baki cikin naɗaukakin farin ciki wanda ke baiyanq yarintar ta a fili tace,"to Baffah yaushe zaka kawo Mini shi?"
Sosai naganarta ta bawa Baffah dariya don haka ya kasa cewa komai sai dariyar kawai, ita ma dariyar tayi har sai da haƙoranta suka baiyana.
kumatunta Baffah ya kama ya ce,"nan da 'yana kawanaki kadan zan kawo miki shi Mamana." yana kaiwa nan ya miƙe har lokacin bai daina murmushi ba ya fita daga bukkar ya nufi masallaci,
itama tashi tayi taje tayi alwala tayi sallah sannan ta ta nufi bukkar Baffanta, tana shiga Ɗakin ta sameshi a zaune yana hada maganin Gargajiya, da yake abinda ya keyi kenan bada magani, duk Rugar shi ake kira idan rashin lafiya ya samu wani Kuma cikin ikon Allah ana dacewa da maganin nasa Idan ya bayar.
Zame takalmin ƙafarta tayi ta shiga ɗakin ta zauna da ga gefansa tayi shiru tana kallonsa, hakan ne ya sa Baffah ya gane yunwa take ji. bai ce mata komaiba ya ɗakko kwanon dake gefansa ya mika mata da sauri ta karɓa ta buɗe faifan da aka rufe kwanon dashi, furace da nono wadda ake dama masa duk dare, nan ta kafa kai tafara sha bata sauke kwanon ba sai da ta shanye tasss.
Ganin yanda take shan furar ne abin ya bawa moddibo mamaki, nan zuciyar sa ta fara zargin anya kuwa Rabe taci abinci kuwa?
Tabbas zai Iya ɗaukar komai da Jaddah za tayiwa ƴarsa ɗaya tilo a duniya amma ban da horon yunwa. a fusace ya tashi ya fita daga bukkar ya nufi bukkar Jaddah yana kwaɗa mata kira Sabida yanda Ransa ya ɓaci, har ɗakin ya bita ya Hauta da bala'i akan zai iya jure komai da za tai masa amma banda horon yinwa da dukan da takewa ɗiyarsa.
Tunda ya fara masifar Jadda ke kallonsa cikin tsananin mamaki, saboda tunda ta auri moddibo bai taɓa ɗaga mata murya akan wani abu ba ba balle ya biyota ɗaki yayi mata hargagi Irin wannan ba, "Ashe Dama haka moddibo yake?"
Tabbas ta yarda ransa ya ɓacci sosai shiyasa bata tanka masa ba tunda ya fara fadan, saboda idan tace zatayi magana a wannan gaɓar to tabbas za suyi ɓatacciya kuma ba lallai hakan yayi mata daɗi ba.
Shiru tayi tana sauraronsa har ya zazzaga mata Faɗan sannan ya ja juya ya yi gaba ya barta da fargabarsa.
Ya na fita Bukkarsa ya nufa ya tuta ƙofar ya shiga ya zauna yana sauke numfashi, har ya fita ya dawo Rabe ta na zaune a inda ya bar ta ba ta tashi ba har ta gama shanye Furar tas sannan ta miƙa masa kwanon tace "Baffah na Shanye."
Murmushi ya ƙirƙiro ya yi sannan ya shafa kanta Ya ce,"Allah ya yi miki albarka Mamana."
Cikin harshen fulatanci ta ce,"Amin Baffah"
Hira ta fara yi masa jefi-jefi tana tayashi tankaɗe maganin dake gabansa har suka gama sannan ta kwashe ta zuba masa a cikin Boronsa (jaka) da yake zuba magungunan a ciki, sun jima tana yi masa shirmen hirarta har ya gaji yace taje tayi bacci Dare ya yi, nanfa Rabe ta Tubure ita fir ba zata tafi ba sai ya rakata Bukkarta.
har bukkarta Moddibo ya Rakata bai fito ba sai da ya tabbatar da ta fara bacci sannan sannan ya fita ya Rufe mata ƙofar ɗakin da ƙofar karan dake gefe.
Wshe gari da zanyi safiya Rabe ta fito cikin shirinta na tafiya kiwo, sanye take farin Saƙi kanta babu ɗankwali ƙafarta sanye cikin rufaffen takalmin roba Yalo.
Kai tsaye Bukkar moddibo ta nufa ta tura kai ciki ta zauna nesa dashi ganin yana Karin kumallo.
da fara'a ya dubeta cikin harshen fulatanci ya ce" Matso kusa dani mamana."
Sai a lokacin tayi murmushi ta matsa kusa dashi tana kallonsa, hannunta ya kama ya saka cikin kwanan abincin, tare su kayi Karin kumallo cikin ƙauna da tsantsar tausayin juna, bayan sun gama tare suka fito yana riƙe da hannunta. Nan su ka tarar da Jaddah tana ƙoƙarin sauke ruwan zafin dake kan murhu.
Haɗe rai ta yi tamkar taga mutuwar ta Sannan ta ɗauke kai daga barin kallonsu.
A dan tsorace Rabe ta gaisheta sai da ta faki idon moddibo sannan ta watsawa mata wani ɗan iskan kallo wanda ya sa da sauri Rabe ta koma bayan moddibo ta Ƙanƙameshi.
Bai ce komai ba ya kama hannunta suka bar gurin ko waiwayen Jadda baiyi ba, su na fita garken Shanu suka nufa dan su fita kiwo.
A nitse ta kalli Moddibbo ta ce,"Baffah yau ni kaɗai zan tafi kawai ka raba mana shanun kai kayi gabas ni kuma inyi yamma, idan muka dawo se'a ga Shanun waye sukafi Ƙoshi."
Ƴar dariya ya yi sannan yaja hancinta ya ce,"yau kin tuna baya kenan idan hakane sai dai ki raba ki bani nawa."
Da sauri wuce gaba cikin zumuɗin yau zata kiwo ita kaɗai, ba su wani ɓata lokaci ba ya raba Musu shanun gida biyu ya tisa nasa yay gaba itama tayi gaba da nata, amma sai da ya yi mata kashedin ta kula da kanta kuma kar tayi nisa da gida sosai sannan ya kama hanya.
Tafiya take Hankalinta a kwance kallo ɗaya za kayi mata ka fahimci tana cikin farin ciki mara misali, a haka taita karaɗe dajin ba salla ba salati har ta shafe Awanni masu yawa a cikin Dajin.
Sai da suka ɗauki lokaci mai tsayi sannan Rabe ta lura Da lokacin zuwa makarantar ta Yayi, haka ta kora shanun suka kama hanyar gida ba dan ta gaji da kiwon ba.
Lokacin data iso gida sai ta fahimci Baffanta bai dawo ba al'amarin da ya jefa tsoro a cikin zuciyarta kenam, saboda duk lokacin da su ka raba kiwo yana rigata dawowa gida, ganin bai dawo ba yasa duk ta rasa kwanciyat hankali.
tambaya ɗaya ke mata yawo a zuciya,"Ina Baffah ya je har yanzu bai dawo Gida ba?"
*** **** ***
A can ɓangaren moddibo kuwa Tafiya ya ke tareda shanun Amma gabaɗaya hankalinsa yana kan ɗiyarsa wadda ya tura daji da shanu ba tareda kulawar kowa ba, addu'a ya keyi Allah ya tsare mas ita da ikonsa, a dai-dai kan kwanar da zai yanka ya ɗauki hanyar gida ya hangi mutum kwance a ƙasan wata ƙatuwar bishiyar Marke, Bai kawo komai a ransa ba har ya isa jikin bishiyar kasancewar ta gefanta ze Ratsa ya kama hanyar gida Sai ya yi zaton ko gajiya ce ta sabbabawa mutumin zama a bakin bishiyar don ya huta.
Amma daya Ƙaraso sai yaga sabanin tunanin sa,
Yaro ne matashi sanye Cikin kyakkyawar shadda light blue an masa dinkin Muhammed, kallo ɗaya za kaiwa kayan jikinsa ka fahimci daga gidan masu wadata ya fito, kan sa babu hula wannan ya bawa Modibbo damar kallon tarin sumar dake kansa, wadda take a nannaɗe sai ƙyalli take alamar mamallakinta yana wahaltawa mata da gyara.
Abin mamaki jinine ke kwaranyowa ta cikin tarin sumar dake kansa, a tsorace moddibo ya matsa kusa sosai nan ya lura da ƙaton Saran da akai masa da ga gefan kansa ta hagu, hakama ƙirjin sa da kunkuminsa na gefan dama, sai kuma gefan cikinsa wanda Alamace ta sukar wuƙa.
Dik da uban saran dake jikin sa hakan ba zai hanaka ganin kyau da tsarin Halittar da Ubangiji ya yiwa wannan matashin ba, cikin sauri moddibo ya Ƙarasa kusa dashi ya dago shi Lokaci guda kuma ya ɗora yatsunsa a saitin Wuyansa dedai babbar jijiyar dake kai saƙo ga ƙwaƙwalwa, a nan ya fahimci da sauran numfashi a taredashi.
Saboda tsabar Rikicewa yama rasa ta Inda ya kamata ya fara bashi Emergency treatment,
Can wata dabara ta faɗo masa, nan da nan Moddibo ya ɗaga matashin da ƙarfin tsiya ya ɗorashi a bayan ɗaya da ga cikin shanunsa ya ɗaure shi tamau a jikinta ta yanda baze faɗi ba Sannan ya nufi hanyar gida dashi.
Sun jima Suna tafiya sannan su ka isa gida.
A bakin garken shanu su ka haɗu da Rabe wadda tun dawowarta taƙi yarda ta tafi gidan ta kafa ta tsare A waje tana jiran dawowarsa.
Da sauri moddibo yace ta shiga da shanun cikin garke ta ɗauresu ba tare da ta kula da mutumin dake ɗaure a bayan saniyar ba tayi gaba, da ƙar moddibo ya kwanto shi daga jinkin saniyar Yayi hanyar sannan ya fara kici-kicin jansa a turɓayar gurin don ba zai iya ɗaukar sa yayi masa nauyi.
Jansa ya dinga yi har ya isa babbar bukkarsa dashi, shimfiɗa ya yi masa sannan ya jashi ya kwantar a kai, Sannan ya mike ya ɗakko Boronsa da yake saka magani a ciki ya ajiyeta daga gefe Sannan ya janyokatuwar Ƙaryarsa ya ajiye Wadda ke ɗauke da Ƙaho da kuma Aska a ciki sai wani garin magani da kuma wasu manyam ganye masu girma kamar ganyen gamji duk ya ajiye a ƙasa.
take moddibo ya ɗauki wannan Askar ya shiga yanka rigar dake jikin matashin," ya subahanallah." Shine kawai abinda Moddibo ya iya firtawa saboda yanda yaga jini ya taru a gefan Ƙirjinsa Da kuma irin saran Rashin Imanin da akayi masa, da alama sai da aka dake shi sosai sannan aka sareshi wanda hakan ya bada tabbacin Kashe matashin akai ƙoƙarin yi.
A nitse ya dauki Askar ya dai-daici gurin da bakin jinin ya taru sannan ya yanka nan da nan Mataccen jini da ya taru a gurin ya fara fita, a hankali ya shiga goge mai Jinin har seda ya gama gaba ɗaya sannan ya shiga shafa masa garin magani a jikin raunukan dake jikinsa.
bayan ya gama sa masa maganin ne ya fito yana kwaɗama Jadda kira,
jikinta na rawa ta fito da ga bukkarta ta ce,"gani Lafiya dai ko?"
Bai ƙara kallonta ba ya ce "maza ki kawo min ruwan zafi Yanzu."
jiki na rawa ta tashi ta hada wuta ta Dora Masa ruwan zafin......
Z.M.C💋
***