BAFULATANA🐄

Chapter 3

by @zmchubado

🐄BAFULATANA🐄

Z.M~CHUBAƊO✍️

         Page: 3

Ta ɗauki lokaci kamin ta kawo ruwan zafin saboda sha'anin itace a lokacin damuna, da kyar ta samu wutar ta kama sannan ta ɗora Ruwan sai minta takeyi ba'a jimaba Ruwan ya tafasa, Cikin wata ƙatuwar ƙwarya ta juye masa ruwan zafin sannan ta ɗauka ta nufi bukkarsa dan ta kai masa ruwan.

Lekawa tayi daga bakin ƙofar ba tareda ta shiga ba har sai da ya yi mata izinin shiga, Ruwan ya karɓa ya Ajiye a gefe sannan ya ɗakko wani farin saki ya jefa a cikin ruwan zafin seda ya fara hucewa sannan ya ɗakko wani garin magani a ɗaure cikin tsumma ya zuba a cikin ruwan, duk  abinda ya keyi ita dai Jaddah kallonsa kawai  takeyi bakinta a cike fal da tarin tambayoyi amma ta rasa ta inda zata fara yin tambayar. 

A hanzarce moddibo ke gabatar da komai saboda matashin ya rasa jini da yawa, ita dai Jaddahar lokacin tana tsaye bata motsa ba tana ganin ikon Allah. A haka  Rabe ta ƙaraso bakin ƙofar ta tsaya ganin Jaddah a gurin, matsa mata Ajdda tayi sannan ta shiga cikin bukkar tana bin ko ina da kallon a ranta tana mamakin abinda ya kawo Jaddah ɗakin Baffah saboda bata saba gani ba tun tasowarta.

Sai a lokacin ta lura da mutumin dake kwance sannan ta kalli Moddibo tace,"Baffah wannan shine mijin daka samo min din?"

Bai kalleta ba ya ce,"A'a Mamana wannan bashi bane amma shima ɗin zaizo nan ba da jimawa ba."

ya ƙare maganar yana saka yatsansa a saitin inda aka cakawa matsin wuƙa don ya shaida zurfin ciwon. 

Cike da damuwa ta kali Baffah ta ce,"Ni kam  ina jin tsoron karmu taimakishi a ƙarshe yazo ya cutar damu tunda bamusan waye shi ba." Rabe ta faɗi haka tana ƙoƙarin leƙa fuskarsa.

Moddibo be damu da ya bata amsa ba sabda shi gaba daya hankalinsa yana kan aikin gabansa,  burinsa a wannan lokacin be wuce yaga ya ceci Rayuwarsa ba.

Kamar za tayi kuka ta ƙara cewa," amma Baffah wannan mutumin ba ɗan nahiyar mu bane ko? Yanayinsa yafi kama dana  baƙo dubi wandon jikinsa ba irin namu bane!" 

Ita dai Jadda har lokaci ta kasa magana saboda mamikin wautar modibbo, duk abinda Rabe ke faɗa tana jinsu amma ba tacw musu ƙala ba har Rabe ta gama surutunta sannan ta jefo tata tambayar ta ce," Modibbo a ina ka samo wannan yaron?"

Shiru ya yi mata ya ƙi bata amsa.

Jadda ta ƙara kallonsa bata damu da shirun da ya yi mata ba ta ce," Kai yanzu ba ka ji tsoron nan gaba yazo ya zame mana masifa?"

Sai a lokacon Moddibo ya kalleta bayan ya kammala ɗinke ciwon ya ce,"Jaddah  mai ya sa kike magana irinta yara ne. a ina kika taɓa ganin inda taimako ya zama masifa?" 

shiru ta yi  tana kallonsa ba tare da ta ƙara managaba, da ya ga bata da niyar magana sai ya cigaba da magana ya ce,"Ni da kyakkyawar niya na ɗakko shi zan taimaka masa, don haka bana zaton alherin da nai masa zai Ubangiji zai bari ya cuceni."

"ni dai wllh hankalina bai kwanta da wannan mutumin daka kwaso mana ba, Allah ma yasa ba wani riƙaƙƙen ɗan bashi bane wanda duniya ke nema." cewar Jaddah

"Jaddah ki zama mai yawan firta alheri ba sharri ba, idan ma ɗan fashin ne aini alheri nayi masa ba mugunta ba don haka banga dalilin da zai sa ya cutar damu ba." Baffah ya faɗi hakan yana ƙara barbaɗa magani a kunkumin matashin.

Sai da ya gama saka maganin tsaf sannan ya  ya labartawa Jaddah  komai tin daga Hauwarsa da matashin har zuwa ɗakko shin da ya yi bai ɓoye musu komai ba, 
Nan da nan idon Rabe ya ciko da ƙwalla tausayin matashin ya yi mata bakebake a zuciya, dama ya lafiyar kura balle kuma tayi Zawo.

Ita dai Jaddah ko a jikinta labarin bai wani bata tausayi ba, hasalima wautar modibbo take gani da taga abin nasu ba na ƙare bane sai kawai ta fice da ga bukkar, tana mitar wai moddibo ze jawo musu bala'i da ze fi ƙarfinsu.

Shi dai bai kulata ba ya ci gaba da gogewa matashin busashen jinin dake jikinsa da ruwan maganin daya haɗa.

Cikin muryar kuka Rabe ta ce,"Baffah!"

Ya ɗago a hankali ya kalleta sai dai bece mata komai ba, a hankali ta ce, "dame zan taimaka maka naga yana zubar da jini har yanzu ta kansa?"

Sai a lokaci ya lura da jinin dake zuba ta kanshi, da hanzari ta ya ɗauki sabon almakashin dake cikin ƙwaryarsa ya fara yanke masa kyakkyawan gashin dake kansa, sai da ya aske gurin tas sannan ya lura saran ba mai zurfi bane sosai, wanke gurin yayi sannan ya barbaɗa garin magani a cikin ciwon.

Sai da ya kammala sannan ya kalleta ya yi murmushi  ya ce," ki dage da yi maaa addu'a don ya warke da wuri ya koma garin su."

Jinjina kai tayi sannan ta ce,"to Baffah"

Gurin ya fara gyarawa ya kwashe duk abinda ya yi amfani dashi ya zuba cikin babbar ƙwaryar da Jaddah ta zubo masa ruwan zafi a ciki ya fita dashi, sannan ya kunna wuta ya zuba askar da yayi amfani da ita da almakashi a cikin tukunya ya zuba ruwa ya ɗora a wuta.  sannan ya koma cikin bukkar ya dubi Rabe  ya ce,"kije Rugarsu Bamanga ki Samomin ƙayar ɗinki zanyi amfani da ita yanzun nan."

Da sauri ta juya ta fita da ga ɗakin zuciyarta fal tausayin matashin da ba susan daga wace nahiyar ya fito ba.

Tana zuwa Rugarsu Bamanga Direct ta nufi inda ƙayar take ta fara karyowa, a haka  har ta cira dayawa sannan ta kama hanyar gida, koda suka Haɗu da Bamanga ba irin kiran da beyi mata ba Amma ta shareshi tayi tafiyar ta, ganin yana shirin takura mata sai kawai ta sanya gudu don dole ya ƙyaleta.

Tura ƙofar tayi ta shiga ɗakin Baffah ta zube masa ƙayar a gabansa tana nishi ta ce,"Baffah gashi."

Karɓa yayi cikin mintunan da bazasu gaza 5 ba ya fara haɗa naman kunkumin matashin yana tsirewa da ƙayar har ya gama ɗinke ciwukan dake jikin matashin sannan ya ƙara saka magani a gurin, cikin ikon Allah da hikimarsa kuwa zubar jinin ta tsaya.

Tunda ya fara ɗinkin Rabe ke kuka harya kammala, share mata hawayen yayi da hannunsa sannan yace ta tashi ta wuce ɗakinta ta kwanta, ba musu ta mike ta tafi ɗakin kamar yanda yace mata.

A wannan Ranar dai Rabe batayi wani baccin kirki ba.

A kwana a tashi ba wuya a gurin Allah yau matshinnan ya cika sati biyu Cif a gidansu Rabe amma ba alamar farkawa a taredashi sai dai kawai numfashi, tun suna sa ran farkawarsa har suka cire rai da farkawar sa a nan kusa.

Rabe ce ke kula dashi ita ce ke saka masa magani har zuwa kan abin da zaici, kunu ne kawai ke iya shiga cikinsa saboda yanda haƙoransa suka datse.

Kullum ita ke zuba masa kunun a baki da ludayi tin baya shiga bakin har yazo yana shiga kaɗan-kaɗan, 
Kallo ɗaya zaka yiwa matashin ka fahimci ya rame sosai akan ranar da moddibo yazo dashi Gidan, tun ranar da aka kawoshi gdan Jaddah bata ƙara leƙawa dakin ba.

A cewar ta idan masifar ta zo to ta afkawa moddibo shi da ɗiyarsa😂.

Wasa-wsa Rabe ta shafe kwanaki bata zuwa makaranta Haka kuma ko kiwo bata zuwa, amma sam hakan ba ya damunta sabda damuwar da tasa a ranta, Abinda tasa a ranta kawai shine taimakon mutum yana daya daga cikin dabi'u masu kyau A Rayuwa. Dole ta san wata rana zasuci ribar abinda abinda sukayi na taimakon wannan bawan Allah.

Mlm iro yazo gidan  yafi a Ƙirga kan Rabe ta dawo makarantar ankawo sabon karatu amma fir taki yarda ta koma dan a ganin ta idan ta fita koda Ƙofar gida Ne to waye ze Kula da baƙon Baffah?

Moddibo ne ya shigo Ɗakin hannunsa riƙe da wata saiwa ya mika mata ya ce," maza jeki tafasa Min ita ki kawo min."

Da sauri ta karɓa taje ta haɗo Ƙirare ta Kunna wutar ta Dora maganin, ba'a dau lokaci me tsayiba ruwan ya fara dahuwa tareda saiwar bata sauke ba har sai da Wutar ta mutu gaba ɗaya sannan ta juye maganin a kwarya ta kawo masa, da murmushi a kan fuskarsa ya karba yana sa mata albarka, sai da maganin ya fara hucewa moddibo ya dago kan matashin ya shiga zubawa Masa abaki.

Ana zubawa wani na zubewa a jikinsa ansamu wani ya shiga cikinsa, bayan ya gama ne ya shiga goge masa jiki da sauran maganin, tundaga ranar
Kullum Se'an masa haka har aka shafe Tsahon wata Guda anayi amma still babu wani ci gaba. Ita ko Rabe bata da aiki sai dai ta zauna ta ƙura masa idanu tana kallonsa, ta wani ɓangaren kuma ga Bala'in Jadda yana ƙara tsananta, nan da nan duk tabi ta rame sai dogon hanci da idanu Kamar ba ita ba.

Sosai ramar da takeyi yake ƙara ɗagawa moddibo hankali amma bashi da yanda zeyi illa kawai yayta addu'a, Jadda ce ta shigo ɗakin ya Baffah ya ɗaga kai ya kalleta ba yabo ba fallasa.

A dakile tace," yame jikin?"

Modibo ya ce"Da sauƙi Alhamdulillah"

Sai kawai ya yi murmushi a karo na biyu ya ce,"hala fita zakiyi naga kin shigo min ɗaki?" 

Basarwa tayi kamar bata jishi ba ta ce,"Ae Fita zanyi."

dama ta rasa ta Inda zata fara tambayar sa cewar zata fita, a takice ya ce,"Sai kin dawo ki gaida   Iro da Gwaggoji." 

Bata amsa Shi ba tayi gaba. 

hamisu Ne Ya shigo gidan hankalinsa a matiƙar tashe ya dubi Baffah yace" don Allah  modibbo kazo muje ka duba Baban jikin nasa ne ya tashi." 

moddibo bai ɓata lokaciba ya fito suka wuce Gidansu Hamisu, har sun fita ya dawo yace Rabe ta koma dakinsa sabda maralafiyan,
Da sauri ta mike tare da yi masa Allah Ya kiyaye ta koma dakin ta zauna, zubawa matashin ido tayi tana kallonsa kamar yanda ta saba, kyakkyawar fuskar wadda rama ta baiyana ƙarara ta kai hannu a hankali zata taɓa sai kuma ta fasa.

Mamakin tsayinsa da murɗewar jikinsa takeyi ita dai kaf nahiyarsu babu mai irin wannan jikin, hannunta ta kai ta ɗan taba tudun ƙijinsa sai kuma ta matsa baya ta ƙyalƙyale da dariya ta ce,"Aradu Kaɗo har nono gareshi."

Haka ta dinga danna masa ƙirji tana dariya har ta gaji tayi bacci a gurin, sai da tayi baccinta ta farka sannan ta miƙe ta zauna ta ƙara ƙura masa idanu nan da nan hawaye Ya fara wanke mata Fusaka ta fara magana cikin sanyin murya mai cike da wauta ta ce,"wai kai yaushe zaka tashi ne? kasan yanda mukeji a ran mu duk sanda muka ganka a kwance? don Allah kaɗo ka tashi hakanan in dai ba mutuwa kayi ba!"

Ta jima tana surutanta kamar wadda ta zare sannan tayi shiru ta cigaba da kukanta fukarta dik tayi ja idanuntaduk sun kumbura abin ka da farar mace....

Ta jima tana kukan sannan bacci ya ƙara daukar ta a gurin, 
A hankali matashin ya fara motsa hannunsa wqnda ya yi masa nauyi tamkar an ɗora masa dutse, da ƙar ya Iya daga hannun ya maidashi Ƙirjinsa Saboda tsamin da jikinsa ya yi ko ina ciwo yake masa a jikinsa.

A hankali ta buɗe idanunta saboda motsin data ji idanunta ta sauke a kansa tana  ƙare masa kallo, miƙe tayi ta zauna sannan ta zaro manyan idanunta cikin tsananin  mamakin yanda akai hannunsa ya koma Ƙirjinsa?

A nitse ta maida kallonta ga fiskarsa ta ƙura masa idanu kamar wadda ke son gano wani abu a taredashi, ta jima tana kallon sa kamar ba zata daina ba kamar a mafarki taga ya motsa idanun sa, Ƙara zaro idanu tayi sai kawai ta miƙe tsaye still idanunta akansa.

A hankali ya fara bude Idanunsa har ya gama buɗesu gaba ɗaya Yana me ƙarewa ɗakin kallo, cikin nutsuwa yake kallon komai na ɗakin har ya sauke manyan idanunsa a kan fuskarta.

A firgice ya fara ƙoƙarin tashi amma ya kasa saboda tsamin azabar da jikinsa ya yi, Ƙara Ya saki ba shiri ya koma ya kwanta yana maida numfashi.

Da sauri Rabe ta matsa kusa dashi har tana naniƙarsa wai zata leka fuskarsa, rintse idanunsa ya yi saboda wani ƙarni da yaji tana yi wanda bai gane masa ba. kusa dashi ta ƙara matsawa sosai sannan ta fara magana cikin harshen fulatanci ta ce,"yi a hankali kaɗo har yanzu  jikin ka akwai rauni Sosai!" 

Tunda ta fara magana yake kallon Yanda take motsa bakinta har ta kai Ƙarshen maganar. dikda  bai fahimci abinda take faɗa ba hakan be hanashi Ƙare mata kallo ba.

ta na gama maganar ta sakar masa murmushi sai kawar ya juyar da kansa gefe, fita tayi daga dakin cikin maɗaukakin farin cikin farkawarsa,
ta na fita bukkarta ta nufaa ta Ɗakko wani rufaffen kwano Wanda Moddibo ya bata kafin ya fita sannan ta dawo ta sake zama dab dashi Tana murmushi a karo na biyu  ta ce,"Tashi kaɗo, tashi ka zauna kaji?"

Kura mata ido yayi saboda rashin fahimtar abinda take faɗa. da taga bai gane me take nufi ba sai tai masa nuni Da hannu alamar ya tashi, A hankali ya Fara yunƙurin tashi a karo nabiyu amma kuma seya kasa dole yasa ya koma ya kwanta, alama tayi masa da hannunta kan cewar ya sake  ƙoƙartawa Amma sai taga bashi da niyar yin hakan. 

mikewa tayi sannan ta koma bayan sa faa fara ƙoƙarin dagoshi da ƙarfin tsiya, ihun Azaba ya saki amma yarinyar nan taƙi ƙyaleshi sai ma ƙara cakumarsa da takeyi. 

Har lokacin Ihu yake amma har cikin ransa yake Girmama Ƙarfin halinta, gata 'yar ƙarama a gabansa wai ita ala dole Ɗagashi za tayi. "lallaima yarinya nan ta gama raina masa Hankali" ya faɗi hakan a zuciyayarsa, ba zato yaji ta ƙara cakume shi da dukkan ƙarfinta ta fara giji-gijin ɗagashii, Wata uwar Ƙara Ya saki saboda ciwon dake kunkumin sa, bata damu da ihun da yeke ba har seda ta zaunar dashi,
da ƙar Sannan ta zube ƙasa tana maida numfashi.

A wahalce ya ɗago idon sa da suka canza kalah saboda azabar data gana masa ya kalleta, a dedai  lokacin itama ta dago nata idon.

gabanta ne ya Yanke ya fadi da sauri tayi Ƙasa da da nata idon, a nitse ta kai hannunta kan kwanon data ɗakko a bukkarta ta ta buɗe, fura ce da nono Wadda aka dama da lafiyayyen nono ta saka ludayi a ciki ta ɗiba ta kai msa Bakinsa alamar yasha.

Sa rai ya gane nufinta amma sai ya kawar da fuskarsa gefe alamar ba zai sha ba, harara ta ɓalla masa sannan ta kai hannu ta juyo da fuskarsa ta danna masa ludayin a baki don dole ya buɗe bakin ya sha.

Ƙara ɗebo furar tayi ta sake kaiwa bakinsa amma  yaƙi karɓa, ya jima yana kallon ludayin sannan ya maida kallonsa kanta Batareda ya karɓa ba.

Da ga can cikin ransa ya ce,"Where am I? And who is this girl?"

"Who did he ask, and who answered his questions?" 

Da ta ga bashi da niyar bude bakin a karo na biyu sai ta ƙara manna luɗayin da leɓabsa sai a sannan ya dawo daga duniyar tinanin da ya afka, a nitse ya buɗe bakin ya fara seeping Furar a hankali, sai kuma ya kauda kansa da sauri kamar wanda ya tina wani abu.

Da ƙar ta samu ta tilasta shi ya sha furar sosai.

Bayan ya gama sha ta ɗakko masa maganin sa shima ta bashi yasha, tunda ta Fara bashi maganin yake mamakin yarinyar ba dan komai ba sai yanda take da zafin nama a komai nata, ƙoƙarinta ya zarta  shekarunta duba da yanda taketa ɗawainiya dashi, har cikin ransa yaji ya yaɓa da ƙwazonta sannan ya jinjinawa jarumtar ta matiƙa.

tana gama shafa mai maganin ta taimaka masa ya kwanta, yana kwanciya bacci ya ɗaukeshi bai jima ba moddibo ya shigo Ɗakin, da gudu Rabe ta nufeshi ta rungumeshi ta ce,"Baffah ya tashi, wllh kaɗo ya tashi har na bashi  fura da magani ya sha." tayi maganar tana dariya 
Kana kallonta zaka fahimci tana cikin Farin ciki ba kaɗan ba.

Tunda ta fara magana moddibo yake kallonta da murmushi ya ce"Shikenan kuka ya ƙare ko mamana?"

Da sauri ta rufe fuskarta da zarazarn hannayenta tana dariya.

Tun shigowar moddibo matashin ya farka saboda hayaniyar surutunta, cikin nutsuwa yake kallon su har zuwa sanda Rabe ta ƙara rungumeshi, sai kallon su yake ba bu ƙiftawa "da alama mahaifin tane" ya fada a zuciyar sa saboda ganin yanda suke bala'in kama da juna........

Z.M.C💋