Part 6
by @chefmuaysh
RAYUWAR MARYAMA*
_*Created by Aisha Hamza(MUAYSHGRAPHICS)*_
*BOOK 📚 1*
Batasan sanda ta sauko daga inda take zaune ba zabar rudewa da tashin hankali me takejin Ammar yana faɗa ne najibu babu shi kenan a duniya ko mene meyake son gaya mata ne yana daya daga cikin mutanen da suka rasa ransu kenan ko me yake nufi
Ah ah bahaka bane tafaɗa tareda kallon Ammar hawaye kawai ke zuba a idonta Ammar ya girgiza kai da nuna tausaya wa a gareta yace gaba ɗaya wanda muka samu raunuka a ɗaki ɗaya aka ajiye mu domin gwamnati ce take kula damu sakamakon duk motar gwamnati ce suka hau
Amma babu najibu a cikinsu hakan ya tabbatar masa da najibu ya rasu kuma da,ace najibu yana
da rai da yadawo gida a lokacin amma yanzu wata takwas kenan
Bayan yagama gaya mata kuma yace gobe da safe taje gidansu akwai abinda zai bata sam hankalin ta ma baya jikinta domin ta daskare a wajen da jin zancen Ammar
Tunani take shikenan tarasa mamanta tarasa yayanta Saduƙu daya zame mata uwa majingina yanzu kuma taƙara wani rashin na dan uwanta wanda shi kadai take tunanin ya rage mata a rayuwa har tanajin saboda shi kaɗai take tunda shi kaɗai ne yake sonta
Ba irin rarrashi da Ammar baiwa Maryama ba amma tagaza yin shuru saidai ta rage sautin kukan nata tanufi gida kamar wadda babu rai a jikinta takeji
A ƙofar gidan ta iske Balaraba a tsaye tana mata kallon daga gidan ubanwa kike Maryama da idanuwanta suka rufe bata lura da Balaraba ba ƙoƙarin ta kawai tashiga gidan tasamu damar yin kukanta yadda Yakamata
Munafuka ta fisgota tareda yimata ƙwanya akai daga ina kike ai Hafizu yazo ya gayamin kin girma kin isa Aure wato har fira kika fara ba tareda sanin kowaba ko
Maryama data fara gani sama sama take neman ƙwatar kanta daga hannun Balaraba saboda abin yayi mata yawa dame zataji
Da jaraba ta tunkuɗa ƙeyarta zuwa cikin gidan ganin yadda yaran makota suka fara tsayawa kallonsu tasan yanzu za,ace kuma takama marainiyar Allah tana duka
Duk unguwar nan munafukai ne daga yaran har iyayen nasu tana jaraba tana Bala,i tashigo gidan tana ingizo Maryama gaba
Faduwar da tayi yasa kanta ya bugu da ƙasa ga tashin hankalin da Ammar ya gama gaya mata ga wani tashin hankalin ta riska a gida kasa tashi tayi domin jikinta ya mutu gaba ɗaya
Kukan da take ma hawayen sun ƙare nunfashi kawai ya rage mata shima tafara tunanin ya kusa daukewa domin tana ganin babu abinda zata rayu yanzu kuma saboda shi
Ba mamanta ba yaya Saduƙu ba yaya najibu mahaifinta da yarage mata ma baya ta,ita kamar bai san tana rayuwa ba yadaina kulawa da,ita akan komai nasa damai zataji da abinda yake damunta ko kuma da wata azabar ta daban da Balaraba ke gallaza mata
Aure kike so yanzu kuma kinfi karfina bari malam ɗin yadawo amfaninki kuma ya ƙare a gidan nan kinfara fin ƙarfin kowa Gara a tattara ki a miƙa ki mu huta kuma kafin kidauko mana abun kunya koh tunda kinfara bin maza fira ba a kofar gidanku ba ma nan gaba bansan me zaki zaman min ba Maryama Gara insan aurar dake nayi ma na huta da jarabarki
Ta inda balaraba take shiga ba tanan take fita ba tayinan tayinan don ko zama takasa yi wai Maryama zata ja mata masifa
Abin indo tafara jin yayi yawa yasa ta shigo gidan sallama tayi Balaraba bata amsa mata itama kuma bata damu da amsawar tata ba saboda inda sabo tasan halinta
Haba Balaraba wallahi kiji tsoron Allah abinda kikeyiwa yarinyar nan yayi yawa kullum ke bakida magana sae Maryama tayi miki laifi kodan maraicinta ai kin tausaya mata ko
Dakata munafuka dama abinda ya kawoki kenan Balaraba ta faɗa cikin tsawa tana kallon indo da tayi shuru jin tsawar da Balaraba ta aika mata da,ita
Inda Maryama take tanufa tana ƙoƙarin ɗagata daƙyar ta kamata tamike numfashi kawai take tana shesshekar kuka
Kutafi munafuka idan kinje karki barta tadawo gida ai haka rayuwar ku zata ƙare a munafurci Indo bata bi takanta ba tayi waje rike da hannun Maryama a hannunta cikin gidansu tawuce da,ita
Maryama da tashin hankalin da yayi mata yawa hakan yasa bakomai ma take ganewa ba a wannan lokacin
Saida aka idar da Sallah isha,i sana ta tashi zaune daga inda take kwance a gidansu indo idanuwanta gaba ɗaya sun kumbura tsabar kukan da tasha daƙyar ta iya mikewa tashiga ban daki tafito tayi alwala
A zaune tayi sallah domin bazata iya tsayuwar ba bayan tagama nan tazauna tayi addu,ointa sana ta jingina da bango
Indo ta dubeta tace Maryama kiyi haquri kinji komai yayi farko a rayuwa yanada ƙarshe sana ba shuru akeyi ba idan masifa ta sameka sai kayi ta karanta innalillahi wa,inna ilaihirrajiun
Ai kuwa shi ta cigaba dayi domin dama tarasa mema zatayi tasamu sauƙin a rayuwarta tananan zaune har wajen tara na dare ta tabbatar da lokacin mahaifinta ya isa dawowa
Tacewa indo tanason tawuce gida tasan babanta yadawo nan dai indo tayi mata nasiha sana tabata adduoi tace tadinga yi inshaa Allah komai zaizo mata da sauƙi
Taɗanji daɗin yanda Indo ta kula da,ita domin a rayuwarta babu wanda yake damuwa da,ita bare yabata shawara ko kuma ya mata nasiha bare yanzun data rasa gaba ɗaya ƴan uwanta
Ɗakinsu ta nufa ta shige ta kwanta kawai domin bawanda ma yaji dawowarta ranar kuwa bacci sai ɓarawo domin ko abincin darenta ma bata samu taci ba na ranar ma saboda ɗokin jin labarin yayanta yasa bata cinye duka ba
Ko Indo saida tayi tayi da,ita akan taci abinci amma tace ita ta ƙoshi ba abinda take so yanzu face kadaici addu,o,in da indo tabata su suka taimaka mata har ta ɗan samu bacci kaɗan dukda bamai yawa bane
Idan ta farka saita cigaba da karanta innalillahi wa inna ilaihirrajiun la,ilaha illa antas subhanaka inni kuntu minazzalimin a haka ta kwana tanayi har gari ya waye
Ana kiran sallah Asuba ta farka taje taɗauro alwala domin tayi sallah bayan ta,idar ta cigaba da karanta addu,o,in data ɗan sassani har gari ya soma haske
Bata jira komai ba ta mike ta ɗauki bokiti ta nufi inda take ɗebo ruwa taje ta ɗebo dukda ciwon da kanta yake mata kuwa
Haka tagama tayi shara tayi wanke wankenta duk a lokacin da safen tun kafin kowa ma ya tashi tagama aikinta domin batason fitinar Balaraba yau tanason kadaici sosai
Da hamma ta fito daga ɗakin nata ko rufe baki batayi tana zare idanuwa tace yau kuma baƙin aljanu mukayi tunda safe haka domin ita bata ɗauka ma a gida Maryama ta kwana ba
Ta nufi wajen ruwa taga komai a cike ta hangi kayan wanke wanke komai an wanke har ta ɗan fara tsorata ta hangi takalmin Maryama a kofar ɗakinsu da lemar ruwa a jiki
Kofar dakin ta nufa ta leƙa au Ashe kece kika dawo ai naɗauka kin canja gidan uba, Maryama ta sunkuyar da kanta tace ina kwana maman Hafizu
Bata amsa ta ba itama kuma dama tasan dawuya ta amsata ɗin tariga ma tasaba shiyasa rashin amsawar nata baya damunta
Ba neman gaisuwarki nazo ba tawuce tabar ƙofar ɗakin tanata maganganunta irin wanda tasaba tawuce tayi abinda zatayi takoma ɗaki
Sai wajen tara Hafizu ya leƙo yace Maryama kizo inji baba Saida gabanta ya faɗi domin daga kiran babanta har na Balaraba tasan da wuya Alkhairi yasa su kirata
Tafara tunanin ko wani laifin kuma za,ace tayi ko kuma abinda yafaru jiya ne Balaraba ta gayawa babanta shine yake kiranta ai kuwa tana tafiya tana addu'a domin batason ta ƙara shiga wata masifar yanzu kuma
A hankali tayi sallama tasamu waje daga gefe ta zauna tace baba Ina kwana lafiya lau Maryama ya amsa ta ba yanda tayi tunani ba hakan yasa taɗan kara sakin jiki kaɗan
Shuru ɗakin yadauka nawasu ƴan lokuta kafin malam habu yayi gyaran murya yafara magana a hankali Maryama yanzu kin girma ma kinyi hankali zaki iya yiwa kanki komai
A hankali cikin zuciyarta tace Ni tun ba yanzu ba nake yiwa kaina komai harma inyiwa wani indai shine girma wannan na daɗe da yinsa
Malam ya cigaba da cewa saboda haka dama akwai alƙawarin da nayiwa Balaraba akan ki idan har lokacin yayi kuma gashi yanzu lokacin gab yake da yi
Kasancewar kema kinada hakƙi kisani yasa zan gaya miki cikin hanzari tace haƙƙi kuma malam kenan baka isa da,ita ba dazaka iya yanke mata hukunci nan take
Bahaka nake nufi ba Balaraba ina nufin ya kamata ace tasani itama saboda abin akanta ne koh Balaraba ta kuma ya mutse fuska tace kaidai malam kawai kace sai abinda ƴarka tace za,ayi shine kawai amma Ni banga ma abin neman shawarar ta ba
Maryama da take sunkuye da kanta takasa gane me suke nufi shuru kawai tayi tanata sauraren taji abinda mahaifin nata zaice
Tashi kitafi Maryama yafaɗa yana kishingiɗa da alamar yafasa gaya mata abinda ya kirata akanshi a hankali ta mike duk jikinta ba daɗi takeji tanufi ɗakinsu da tunanin me mahaifin nata yake son sanar da,ita mai muhimmanci haka
Amma Balaraba ta hana ya sanar da,ita din saboda ya nuna tanada haƙkin dazata sani akai ita kuma take ganin ko isa ne baiyi da,ita ba daza,a nemi shawarar ta
Haka ta dinga tunanin me ake shirin yimata a gidan ne da ake ganin ko ba lallai sai tasani ba
Kullum da yamma Maryama takan samu dama taje wajen indo domin takan bata shawarwari da nasiha da kuma koya mata wasu abubuwan na rayuwa masu muhimmanci
Yau tazo gobe tazo kullum da ƙarin ƙalubalen da take fuskanta har tafara sakewa da rashin yayyen nata domin Indo takan ɗebe mata wasu kewar da yake Indo itama bata taɓa haihuwa ba
Kuma Allah ya haɗa jininsu da Maryama hakanan takejin tausayin Maryama har takejin dama ƴarta ce ma
Kullum da yamma haka zata samu hanya domin zuwa wajen Indo tasaba da,ita sosai har wasu abubuwan na damuwarta takan gayawa indo tafaɗa mata abinda ya kamata yayi
Tunda safe ta tashi da ciwon ciki matsananci haka tadinga murgine murgine a cikin dakin su tana kuka
Balaraba ta leƙo tace mata tafito ta ɗebo ruwa tunda yau saita tuna mata abinda ya kamata tayi Maman Hafizu cikina ciwo yakeyi tun ɗazu nakeson infito amma bani iya miƙewa dakyau tana gaya mata tana hawaye
Toh me kikeso yanzu ayi intafi dakaina in debo ruwan ko me kike nufi Maryama tayi shuru domin ita kaɗanta tasan irin azabar ciwon ciki da takeji
Da ƙyar tamike domin ko tsayuwa bata iyawa saedae a duƙe riƙe da ciki take iya tafiya bokiti taɗauka tanufi hanyar fita
Idan kinje ki zauna acan karki dawo da wuri kiga yanda zanyi dake Balaraba tafaɗa tana shigewa ɗakin ta
Tana fita tawuce gidan Indo domin tasan ba yanda zatayi ta,iya zuwa ɗebo ruwan saboda bazata iya ɗaukowa ba
Tana shiga ta zube a tsakar gidan Indo tana numfashi sama sama tana kiran cikinta Indo tayo kanta tana fadin subhanallah Maryama me yake damunki
Cikina ne yake ciwo sosai tun da safen nan toh ko kinci wani abin ne daya juya miki ciki ba abinda naci wlh Anty da yake haka take kiranta
Toh muje chemist ɗin can saeya dubaki sai Maryama tace maman Hafizu ta aikeni in ɗebo mata ruwa kuma tace idan banyi sauri ba zata dakeni
Kaini Balaraba bazata daina halinnan nata ba dai bakida lafiyar ma bazata barki ba toh shikenan bari Almajiri na yadawo na aikeshi sae yakai miki ruwan ko
Tashi muje chemist din toh tace sana taɗauki buta tashiga bandaki a guje Maryama tafito hankali tashe tana faɗin na shiga uku na Anty jini
Indo tayi sarara tana kallon Maryama data bi duk ta gigice ganin jini a wandonta Anty baki gani ba jini nagani wlh nashiga uku tanayi tana yarfa hannu
Indo ta tsaya gefe tarasa mema zatace ma Maryama domin abin nata har yafara bata dariya wato batasan jinin haila ba ma kenan ko da yake ba zuwa makaranta take ba da tuni tun kafin tafara zata sanshi da kuma yadda zata kula da kanta idan tafara
Indo tace ke nutsu mana Maryama zonan ki zauna yanayin yadda Indo tayi mata magana hakan yasa ta fahimci magana mai muhimmanci take so tayi da, ita
Maryama bakisan jinin haila ba koh daga kai kawai tayi alamar eh Indo ta cigaba da cewa alamu ne na mace ta girma kuma zata iya ɗaukar ciki ma zata iya haihuwa kuma ta,isa har Aure ma
Zare idanuwa kawai take tana jinta wato yanzu shikenan ta,isa Aure yanzu tabani aurar da,ita ma tasan babanta zaiyi da yaji idanuwanta suka fara tara ƙwalla domin gani take shikenan Aure za'a yimata
Ina fatan dai kuna nishaɗantuwa da wannan littafin nawa na rayuwar Maryama muje zuwa masoyana ❤️ don jin me zai biyo baya ga Maryama dai yanzu ta girma😆 ina ƴan team ɗin Balaraba toh inga comments kamar zasu fasa wayar sai insan kuna nishaɗantuwa
Karki bari karku bari kar mu bari abamu labari top 3 Na A'ishatu Hamza wadda kuka fi sani da Muaysh graphics 🤟 🤗 basai na faɗa muku ba littafaine wanda daga jin sunayen su zaka gane cewa na musamman ne
(UMMU OR SALMA) UMMU kO SALMA
(ORPHANAGE HOME) GIDAN MARAYU
(MARYAM’S LIFE) RAYUWAR MARYAMA
Wannan shine account details din mu 👇
3201868037 A'isha Hamza First bank
Ko kuma 9131096058 A'isha Hamza Opay bank
RAYUWAR MARYAMA akan 400 kacal GIDAN MARAYU akan 400 sai kuma UMMU KO SALMA akan 400 ga wanda yake buqatar duka zai biya 1000 instead of 1200 sana zaka tura receipt after payment a wannan number *** ta whatsapp