Page-32
*FASAHA WRITER'S ASSOCIATION*
(*F.W.A)*©✍️
⭐⭐⭐
Ƙungiya masu aiki cikin salon hikima da fasaha gurin juya tunanin al-umma, kaifin alƙalumansu ya zarta takobi ©✍
___________________________________________________
بسم الله الرحمن الرحيم.
اللهم صلي وسلم على نبينا محمد.
❁ 𝐒𝐀𝐍𝐀𝐃𝐈𝐍 Ƙ𝐀𝐃𝐃𝐀𝐑𝐀𝐓𝐀 ❁
Free book📓
By: _*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_
Page3️⃣2️⃣
Zuciyarsa na harbawa ya ɗago kai yana kallonsu, a hankali ya buɗe baki zai yi magana, amma kamar mai jin kunya kamar wanda ake ja ya samu dai ya ce, "imm ah Momy... dama so na ke na ce, akan ku je ku ba wani wanda ba ku san ya yake ba, shine na..." "Hajiya Kaka ji min Abba da wani zan ce, to taya za mu ba wanda ba mu sani ba? Ka ga kai dai faɗa mana abun da ka ke nufi kawai, ka sauwaƙe mana jira". Cewar Momy tana sake binsa da ido.
Shiru na ɗan seconds, sannan ya ce, "Momy... ku amince min, ni ni sai in aureta" da sauri Momy ta juya gun Hajiya Kaka, su ka zare ido na jin daɗi sai kuma su ka juyo gunsa, shi dai Abba Shiru ya yi zuciyarsa na harbawa, kada dai Momy ta ƙi amincewa da batunsa. "Da gaske ka ke Abba?" "E... eh Momy" Hajiya Kaka ta ce, "imm imm to amma aurenta ka ke son yi ko kuwa dama kana son na ta?".
Sai à lokacin Abba ya ɗago yana kallonsu, su kuma su ka giɗa masa kai alamar ya basu amsa. 'To yanzu ni me zan ce? Na san dai ba sonta na ke ba, kawai dai ba na son ta auri wani ne, to amma gashi tambayar da aka min. Yanzu ince a ah ba sonta na ke ba, kawai dai ba na son a aurata ga wani ne? To kuma idan Momy ta ƙi yarda saboda na faɗi hakan fa?' Duk a ransa ya ke ta wanna ɓaɓatun tambayoyin.
"A ah, ya ka yi shiru ka zuba mana na mujiya kawai?" Faɗin Hajiya Kaka. Sauke numfashi ya yi, sannan ya ce, "eh eh ina sonta", ya faɗi domin kuwa ƙila hakan shine zai sa su amince. Cikin murna Hajiya Kaka da Momy su ka furta alhamdulillahi, Momy ta ce, "abu ya yi kyau, dama abun da na ke son ji kenan, toh na yi farin ciki, kuma farin cikina zai ƙaru idan na ji itama Nur ta amince da aurenka".
Farin ciki ya kasa ɓoyuwa à fiskar Abba ya tashi ya nufi ɗakinsa, duk da kuwa yana tunani akan maganar Momy, to ya Nuriyyah za ta ɗauki batun? Idan kuma ta ƙi amincewa fa? Ko da ya isa ɗakinsa kwantawa ya yi akan gado, sai faman murmusawa ya ke ta yi ba ƙaƙƙautawa, fiskokin Nuriyyah na ta yi masa gizo cikin ransa....
"Hmm Hajiya Kaka kin ga maganarki ta fito, kai alhamdulillahi" Hajiya Kaka ta ce, "nima na ji daɗi sosai, yanzu abun da za ayi ki samu ki sanarwa Aminun, ki ji me zai ce" da haka Momy ta bar sashin Hajiya Kaka cike da murna. Zuwa dare ta samu Dady da maganar, shima ya ji daɗin lamarin sosai, tuntuni ya ke da burin Abba ya yi aure, amma kuma shi kamar ma ba batun à ransa, sai gashi yau ya sanar da cewa zai auri Nuriyyah, yarinya mai hankali da sanin ya kamata.
Nan ya umurci Momy da ta je ta ji ta bakin Nuriyyahr, saboda amincewar Abba bai wadatar ba, ya kamata aji itama tana sonsa ko kuwa ba ta so?. Da haka Momy ta tashi ta nufi ɗakinmu, ko da ta isa ta samemu muna hira ni da Asma'u. Zama ta yi a gadon da Sadiya ta ke kwana da, wanda yanzu ni ce na ke kwana akai, kallona ta yi sannan ta ce inmatso kusa da ita.
Da mamaki na matso kusa da ita, sai da na gaisheta da tambayar lafiya ta ke ko? Ta ce da ni ba komai kawai akwai maganar da za ta yi da ni ne. Tashi Asma'u ta yi ta ce bari ta je kitchen ta sha ruwa, wanda kuwa ta yi hakan ne domin ta bamu damar yin magana. A haka Momy ta tarbiyyantar da 'ya'yanta, ba sai ta ce da mutum ya tashi ba, shi da kansa ya san ya kamata ya tafi tun da maganar ƙila tana buƙatar sirri, gwara da ace Momyn cewa ta yi tana son magana da mu duka.
Gaba ɗaya hankalina na ba ta ina tsumayin jin abun da za ta ce, "yata Nur?" "Na'am Momy" "Kin san yau anzo tambayar auren 'yar uwarki ko?" Na ce, "eh Momy na sani" ta sake cewa, "sannan kin san Dadynku bai amsa ba sai nan da sati ɗaya ko?" "Eh" "to ba komai ba ne yasa ya ce hakan sai ke Nur". Da tsananin mamaki na ce, "ni kuma Momy? Akwai laifin da na yiwa Dady ne da ya ƙi ba da damar auren Asmee saboda ni?".
"A ah ko ɗaya 'yata, ba wai wani laifi ba ne ki ka yi, so ya ke ne ya haɗa aurenki da Asma'u tare, shiyasa ya ce sai nan da sati ɗaya zai ba da amsa, kafin nan ya samar miki wanda za ki aura". Ni da na saki baki ina kallonta bayan na ƙolalo idanuna, cikin rawar baki na furta, "aure kuma? Kuma ni Momy? Nan da Sati ɗaya samun miji?".
Cikin kwantar da murya ta ce, "kwantar da hankalinki 'yata, ba wai za a tauye miki haƙƙinki ba ne, sai dai don samar miki da mutunci da ko wace mace ta ke buri, abun da na ke so da ke shine, mu mun samar miki da miji, wanda mu ke da tabbacin zai riƙeki da amana, sai dai fatanmu shine zabin ya yi miki, ko kuma kina da wanda zuciyarki ta amince da shi?".
Ƙasa na yi da kaina, sai da na ja numfashi, ban san me zan ce, kwatsam babu fiskar wanda ya zo min à raina sai fiskar Abba, duk da ban san me yasa shi yazo raina da Momy ta yi wannan tambayar ba, amma sai na ɗaga kai na sakar mata da fiska na ce, "Momy ku iyayena, duk zaɓin da ku ka yi min à rayuwa shine daidai da ni, domin kuwa na san shine mafi alkhairi cikin rayuwata".
Itama cikin jin daɗi ta ce, "na ji daɗi da wannan yarda da kuma mutuntawar da ki ke nuna mana Nur, haƙiƙa ko da ace mu iyyayenki ne iyaka abun da zaki yi mana kenan" "Momy ko sau ɗaya ba na kallonku a matsayin bare a gareni, ina kallonku ne akan ahalina, wa'yanda zan iya komai don na samar musu farin ciki, sannan sai iya inda ƙarfina ya ƙare akan kare martabarku".
Murmushi Momy ta yi wanda ya fitar da haƙoranta sannan ta ce, "ina alfahari da ke Nur, kuma na yarda da ke." Momy ta faɗi tare da ɗaura hannunta gefen fiskata, ta sake cewa, "to yanzu ya kamata ki san waye mu ka zaɓar miki, shi ya ce yana sonki, amma ba mu san ko ke kina sonsa ba. Ina so kisan wani abu Nur, ba na buƙatar ki yi abu don mu muka zaɓar miki, kar ki manta aure ba abun wasa ba ne, ba zai yu ki auri wanda ba kya jinsa a ranki ba, zan so ki auri wanda ki ke so kuma za ki ji daɗin zama da shi kin ji?".
Ɗaga kai na yi alamar toh, har zan yi magana sai na yi shiru jin Momy ta ce, "zaɓin da mu ka yi miki ba kowa ba ne face Abba". Wani irin zaro ido na yi na miƙe zumbur tsaye ƙam ina kallon Momy, zuciyata ta fara wani irin fat faat, wai to ko ni ce ban ji abun da Momy ta ce da kyau ba? Eh zai iya yuwa. Baki na na rawa na ce, "umm Momy... kamar yaya Abba na ji kin ambata? Ko wani yaya Abban ki ke nufi?".
Momy kuwa da ta ke bina da ido ganin yadda na dire ƙasa daga kan gado, sai ta ji razani kaɗan a cikin zuciyarta, na kar dai ni ba son Abban na ke ba, amma kuma sai ta kawar da tunanin tana cewa, "a ah kwantar da hankalinki, shi ya ce yana sonki, amma in ke ba kya sonsa ba wata matsala ba ne, sai ki fito da wanda ki ke so, shi kuma inbashi wata 'yar ƙawat..." "a ah à ah Momy...".
Na yi gaggawar faɗin hakan ba tare da sani ba, domin kuwa wani irin zafi na ji da ta fara maganar wai za ta bashi 'yar ƙawarta. A hankali na zauna Momy ta kuma cewa, "to ya a ah Nur? Kar ki damu ke kam idan ma bakya so" kaina a ƙasa na ce, "am Momy shi yaya Abban ya ce yana sona?" Sai da ta sauke 'yar numfashi sannan ta ce, "eh haka ya ce min, amma kamar ke ba kya son..." "no Momy ba wai hakan na ke nufi ba".
Momy da ta fara fahimtar wani abu, alamu sun fara nuna kamar itama Nur ɗin tana ciki fa, sai ta ce, "to me ki ke nufi 'yata?" Shiru na yi na kasa magana sai murmushi da na ke yi, kaina a ƙasa cikin jin kunya, domin kuwa wani irin abu ne ya shige raina jin wai Abba ya ce yana sona. "Toh in ba za ki yi magana ba zan je in janye abun da ya faɗi, ni dai kawai farin cikinki na ke so." Cewar Momy ta miƙe tana son fita à ɗakin.
Da sauri na dakatar da ita na ce, "imm Momy kada ki... na amince!" Na ƙarashe da sauri ina rintse ido. Sai kula na buɗe à sannu, juyowa ta yi cike da murna sai kuma ta ga kaina a ƙasa, ta ce, "Ban gane kin amince ba, kina sonsa kema Nur?" Cikin eii'ina na ce, "eh Momy" nan ma na kuma ƙarasawa da sauri. dawowa Momy ta yi ta rungumeni cike da farin ciki matuƙa, "na yi farin ciki sosai da sosai, Allah ya yi muku albarka" ta faɗi sannan ta wuce bayan ta min sai da safe.
Ni dai sai da ta fice a ɗakin na ɗago kaina, saboda tsabar kunya da kuma wani yanayi da ke shigata, a hankali na rintse idona domin insaurari zuciyata, saboda motsawar da ta ke ta yi min wanda ban san na menene ba, 'Nuriyyah kin amince da kina son Abba, shin da gaske ne ko kuwa saboda Momy ne?' Cewar zuciyata, sai kuma ɗayan na ji ta ce, "a ah da gaske kina son Abba ba saboda kowa ki ka amince ba, kina sonshi'.
Nan ɓangarorin su ka hau cecekuce akaina, suna tambayata in basu amsa, da sauri na buɗe idona, shiru na 'yan seconds, ''shi ya ce yana sonki" na tuna da maganar Momy, "kenan dama yana sona? Ni ina son sa?" Na faɗi sannan na rufe fiskata ina dariya, "tooh wannan baiwar Allahn lafiyanta kuwa?" Na ji muryar Asma'u da ta shigo yanzu, da sauri na buɗe idanuna, sai kuma na juya na kwanta ina cigaba da dariyar........
Dady bai yi sanya ba ko da jin cewa ita ma Nuriyyah ta amince, washe gari ya sake neman magabatan Sanusi, aka sa rana nan da watanni uku masu zuwa za ayi auren Asma'u da Sunusi da kuma Abba da Nuriyyah. Farin ciki a gurin Abba ba a faɗa domin kuwa irin yanayin da ya shiga ya tabbatar da cewa ba ƙarya ya kamu da soyayyar Gajera.
Nima à nawa ɓangaren na yi murna sosai da wannan al'amari, amma kuma sai kunyar Abban ya kamani, ko kaɗan yanzu ba na bari na haɗu da shi. Su Wasila sun yi ta tsokanata akan ashe dama faɗa ya dawo soyayya ba su sani ba, ni dai sai dai inyi musu murmushi kawai idan suna faɗin haka......
Hmm Mama kuwa yadda ka san ɗanta aka ce zan aura, domin kuwa sam maganar farin ciki ma babu à cikin ranta, amma ba yadda za ta iya, domin kuwa ba ta da damar cewa a fasa auren, na ɗaya Abba ba ɗanta ba ne, kuma shima ance yana son Nuriyyah, sannan kuma daga su Momyn har Hjiya Kaka suna ƙaunar Nuriyyah. Don haka kuwa ba ta da wani zaɓi sai ta zuba musu ido kawai.
Rumaisa ce zaune akan kujera tana waya da Hajiya, zumbur ta miƙe tsaye ko da jin abun da Hajiya Kaka ta ce, yadda ta miƙe zai tabbatar maka da ko kaɗan abun da Hajiya Kakar ta faɗi ba ta ji daɗinsa ba, da sauri ta katseta da cewa, "haba Hajiya Kaka ya za amin haka kuma? Bayan mun gama maganan nan da ke Abba Aisha zai aura, amma sai yanzu kuma ace min wai wannan tsintacciyar zai aura? Haba don Allah Hajiya Kaka, sai da na gama sakan-kancewa? Yanzu anyi min adalci kenan?".
"Rumaisa komai da ki ka ga ya faru a rayuwar nan muƙaddari ne daga Allah, Allah bai nufa Aisha Abba zai aura ba, kuma maganar nan dama can ke ki ka faɗeta, ni na ma manta da ita sai yanzu da ki ka kawo zancen, sannan Abba ya shaida cewa yana son Nuriyyah, kuma itama tana sonsa, dama ba abun da ake buƙata kenan ba? Aisha ai ƙanwa ce a wurinsa, tun da ubangiji ya tsara hakan addu'a za mu yi" cewar Hajiya Kaka.
Sannan ta ɗaura da cewa, "dama ina son tambayarki Aishar ma, tana lafiya dai ko? Yaushe ne dawowarta ta daɗe sosai va ta ƙasar nan" Kamar Rumaisa ba za ta yi magana ba, domin kuwa idan ranta ya yi dubu to fa ya ɓaci yanzu, "ta kusa dawowa, dama saura mata wata ɗaya kacal ta dawo, har ina shirin idan ta dawo mu ɗaura daga inda aka tsaya amma kuma yanzu na ji wani batu daban". Faɗin Rumaisa tana sake haɗe rai kamar tana gaban Hajiya Kaka.
Ita kuwa cewa ta yi, "kamar yadda na faɗa miki haka Allah ya nufa, Allah ya ba Aisha miji na gari, wanda ya fi Abban, don haka ki bar maganar nan, dama daga ni sai ke mu ka yi ta, yanzu kuma komai ya canza", cike da takaici Rumaisa ta ce, "ameen shikenan Hajiya Kaka sai anjima a gaida mutan gidan" da haka ta kashe wayar.
Komawa ta yi ta zauna akan kujera, ta damƙe wayar da ke hannunta da ƙarfi kamar za ta fasa shi. Ta ya hakan zai faru, tun tuni ta ke wa Aisha fatan auren Abba, ta yi tanadi lokaci kawai ta ke jira daga zarar Aisha ta dawo daga ƙasar waje shikenan za ta je ta samu Hajiya Kaka akan maganar, amma ta ya mahaifiyarta Hajiya Kaka za tai mata haka? Sai ka ce ita bare ce? Dama ko da yaushe ita ba aganin darajarta.
Babu wanda Abba ya dace sai Aisha 'yarta, idan Abba bai auri Aisha ba to ba zai taɓa auren Nuriyyah ba. Yarinyar da ta tsana à ganin farko? Yarinyar da ko kallonta ba ta son yi? Tsintacciya mara gata? Ace ita za ta auri Abba ɗan ɗan uwanta? Inaaa ai ba za ta saɓu ba, dole ta san hanyar da za ta bi.
Sauka daga kan kujerar ta yi ta ɗago wayarta, nan ta fara duba number sai kuma ta dannan kira, kira biyu amma ba a ɗaga ba, tsaki ta ja tana faɗin, "sai a yi ta kiran mutum amma ya jefar da wayarsa" a kira na uku aka ɗaga, da alama ma mai maganar daga barci ta tashi, ba tare da dogon magana ba Rumaisa ta ce, "keh nan da kwana biyu ina buƙatarki ki dawo ƙasar nan, ba dama kun kammala komai ba? To ina da buƙatarki tabbas!" Tana faɗi ta sauke wayar tana sauke huci, ta haɗe idanuwanta alamar samun mafita.
Last page
___________________________________________________
Lallai, to abu fa ya yi abu😃 gashi dai Abbah da Nuriyyah sun amince kuma ansa ranar aure. Gefe ɗaya kuma ga Rumaisa ashe dama so ta ke Abba ya auri 'yarta, to me ku ke tunani anan gaba? Wa ta kira? Wani mafita ta samu? Hmmmm mu je dai zuwa
Alƙalamin 👇🏼
_*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_