“SANADIN ƘADDARATA”

Page-35

by @zahratulqalam51

*FASAHA WRITER'S ASSOCIATION*
     (*F.W.A)*©✍️
     ⭐⭐⭐

Ƙungiya masu aiki cikin salon hikima da fasaha gurin juya tunanin al-umma, kaifin alƙalumansu ya zarta takobi ©✍
___________________________________________________



بسم الله الرحمن الرحيم.
اللهم صلي وسلم على نبينا محمد. 




❁ 𝐒𝐀𝐍𝐀𝐃𝐈𝐍 Ƙ𝐀𝐃𝐃𝐀𝐑𝐀𝐓𝐀 ❁ 




Free book📓



By: _*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_




Page3️⃣5️⃣





"Ke ce ba kya cikin hankalinki, da ki ka yarda da ni, kuma ki ka amince da zan iya yin rayuwa da ke!!" Cewar S man cikin tsawa fiskarsa babu annuri. Suman tsaye Halima ta yi ta kasa buɗe baki bare wani harafi ya fito daga ciki.

Jikin Halima ya fara rawa shi ko S man ya kafeta da ido na wasu 'yan daƙiƙu, kamar yana jin daɗin kallon yadda jikinta ya ke yi. Bai barta haka ba ya sake ɗaurawa da cewa, "ke wawuya ce da ki ka bari zuciyarki ta amince da ni, Halima Hali! Ni S man na zauna da ke ne domin kawai na cinma wasu burukana akanki wanda ba wani yawa ne da su ba, ban taɓa jin ina sonki ba, amma na ji cewa zan samu wasu abu a tattare da ke, tun a ganin farko ke kin san you're not my type, amma kuma sai ki ka nace".

Sai da ya ba ta baya cikin takun isa ya kuma cewa "to bari in sanar da ke wani abu da ba ki sani ba, kin ga Bassi da na haɗaki da su? To ni ne shugabansu!" Ya faɗi yana juyowa, "na zauna da ke ne kawai don na more sannan kuma na samu 'yan canji. Duk da ba wasu abun azo a gani ba ne amma sun yi min amfani, na gama da ke don haka ki fice daga rayuwata!".

Matsawa baya Halima ta yi har ta kusa faɗi saboda tashin hankali, jikinta ya fara karkarwa, sai kuma ta yi dauriyar zuwa kusa da shi ta sa hannu ta kama na sa hannun ta ce, "my S man wasa ka ke ko? Kamar dai rannan yauma haka ya ke ko?" Shu'umin murmushi ya jefa mata haɗi da sauke hannunta ƙasa ya ce, "bani da lokacin da zan tsaya ina yin wannan wasan da ke, kamar yadda na ce miki, duk zaman da na yi da ke kawai buƙatata ce ba wai don ina sonki da gaske ba".

Maimakon maganar da ya faɗa ya karyar da Halima, amma sai ta samu kuzarin cakumar wuyar rigarsa, idanuwanta da su ka fara fitar da hawaye su ka bushe, a zafafe ta fara cewa. "S man wallahi ka yi kaɗan, S man ba ka isa ka yasar da ni haka banza ba, ba ka isa ka aikata min hakan ba! Yanzun nan ina son ka bani duk kuɗaɗen da ka san ka amsa nawa, ka bani kuɗaɗena S man! Idan ba haka ba kuma wallahi kotu ce za ta raba ni da kai!".

Ta ƙarashe faɗa da sakin ihu tana jijjigashi, shi kuwa dama jira ya ke ta gama duk zubanta. Halima ba ta ankara ba kawai ta ji S man ya hankaɗata da ƙarfi, sai da mazaunanta su ka amsa saboda yadda ta bugu a faɗuwar, bayan ta saki ƙara ta juyo tana kallonsa da tsanin haushi, S man ya tsugunna a gabanta yana cewa, "kina da hujjar tinkarar kotu bisa tuhumana da cin ye miki kuɗi? Ko kuma kina da lauyan da zai tsaya miki gurin fitar da haƙƙinki? Go a head 'yan mata, ko kuma ince 'yar banza! Na baki damar zuwa duk inda za ki je don a ƙwatan miki haƙƙinki, kuɗin na ki ma nawa ya ke?".

Yana kaiwa ƙarshe ya kwashe da dariya haɗi da miƙewa. "Mugu mashayin banza la'ananne, wallahi sai ka gane ni ka yaudara, mutumin banza ɗan iska!" Cewar Halima da ta cika da tsanar S man, duk da kuwa ta san ba za ta iya taɓuka komai akansa ba. Maganar da ta yi ba ƙaramin ɓata masa rai ya yi ba, a fisace ya juyo yana kallonta, wanda hakan ya razanata.

Bai yi wata-wata ba ya sa hannu ya zare belt ɗin wandonsa, kafin Halima ta ce me, S man ya rufeta da duka, duka ya ke yi mata kamar wanda ya samu kayan wanki, ita kuwa sai kururuwa ta ke yi na neman ɗauki. Da ta ga ɗaukin ba zai zo ba, sai ta fara ba shi haƙuri, "wayyo S man za ka kasheni, don Allah ka yi haƙuri na tuba, wayyo Innata za a kashe miki 'yar gudallenki, Innaaaa, ka yi haƙuri".

Haka Halima take ta ihu tana kiran sunan Inna da ba S man haƙuri amma yadda ka san ce masa ake yi ya ƙara. Iya duka Halima tasha shi, wanda za ta iya cewa tsawon rayuwarta ba ta taɓa shan duka irinsa ba. sai da S man ya yi mai isansa sannan ya dakata yana kallonta tare da sauke numfarfashi.

Halima dai kallonsa kawai ta ke yi idanuwan duk sun kumbura, ihun ma ta daina yinsa saboda yadda take jin azaba ta ko ina a jikinta. Da ƙyar ta samu ta buɗe baki ta ce, "S man me yasa za ka min haka? Ni na ɗaukeka da zuciya ɗaya, na ba ka dukkan ragamar rayuwata, na yarda in rasa komai don na zauna da kai, me yasa za ka min haka?" 

Ta faɗi tana sauke zafafan hawaye. Sai da ya ɗan yi dariya kamar ɗazu sannan ya sake sunkuyowa kanta yana cewa, "da gaske kin bani ragamawar rayuwarki? Ita kuma wacche ta haifeki ta yi rainonki fa? Abun da ki ka yi mata shine daidai?" Halima ta ce, "Saboda kai na rabu da Innata, ba saboda kowa ba". "Ƙarya ki ke yi!" Kallonsa kawai take yi domin maganar ta dakar mata zuciya, sai ta tuna da lokacin da ta cewa Inna ƙarya ta ke yi.

S man ya cigaba da cewa, "ƙarya ki ke yi kin rabu da mahaifiyarki ne don son zuciya da jin cewa kin samu jin daɗin rayuwa, ita kuma ki ka yasar da ita a gefe, amma fa Halima! Ba wai ina faɗa miki don na ji tausayin mahaifiyarki ba ne, a ah, ina faɗa miki ne don nima burin da nake da shi akanki ya ƙare!" Wani irin sarawa Halima ta ji kanta ya yi mata, yadda S man ya ke magana kamar yadda ta yiwa Innarta. To shima kenan da ya faɗa mata ta ji zafin maganar, ina ga Inna wacche ta haifeta? Kenan Inna Jummai ta ji fiye da abun da ta ji yanzu?.

Bayan ta gama tunanin nan ta ɗaga idanuwanta da su ka sake ciko da ƙwallah ta ce, "kar ka manta yanzu haka ina ɗauke da cikinka a jikina, idan ya salwanta..." kafin ta ƙare kalaman kwanyarta ya girgiza da batun da S man ya katseta da cewa, "da ga ke har cikin ku mutu shine abun da na so! Ba ri ki jii in faɗa miki abun da ba ki sani ba my Hali, idan ba ki manta ba kwana biyu da su ka wuce na baki jus ɗin lemo kinsha, to na zuba miki wani magani mai kama da guba a ciki, wanda zai zubar da cikin da ki ke ɗauke da shi, ko kuma cikin jikin na ki ya zama abun hatsari ga rayuwarki. To amma har yanzu maganin bai yi aikin da ya dace ba, sai dai na san ko yaushe za ki iya jin saƙonsa my Hali".

Kuka sosai Halima ta fashe da shi ashe S man sheɗan ne ba ta sani ba, ta cancanci ya yi mata haka? Ji ta yi kawai S man ya ɗagata, yana janta suna kuma nufan ƙofar fita da ga gida, yana kaiwa nan ya turota da ƙarfin gaske ta yi faɗuwar da ya fi na ɗazu, dama ga jikinta ya sha dukan tsiya. Ciki S man ya koma, ba jimawa sai gashi da akwatinta, hurgo akwatin kayanta ya yi, da sauri Halima ta matsa akwatin ya sauka agefenta, ji ka ke baapp.

Kukan da ta ke yi ta ƙarawa volum, sosai ta ke ba S man haƙuri, shi kuwa hoton Nuriyyahn nan ya gani a ƙasa, wanda ita Halimar ce ta cillar, ɗaga hoton ya yi fiskarsa babu alamar zai yi mata afuwa, ya cillo mata da hoton ya faɗi a kusa da ita, "kada ki sake na ji motsinki a ƙofar nan, idan ba haka ba wallahi sai na yi miki abun da ba za ki taɓa mantawa da shi ba!!" Ya ƙarashe da tsananin tsawa sannan ya rufe ƙofar da ƙarfi.

Rintse ido Halima ta yi saboda yadda bugun ƙofar ya haifar da bugun zuciyarta, ta dakata da kukan a hankali ta buɗe idonta tana bin ƙofar da kallo, sai kuma hankalinta ya dawo kan hoton Nuriyyah da ke kusa da ita, ba ta lura da lokacin da S man ya jefo mata shi ba. Ta ke kamar ana ta-ro mata da memoryn kanta, lokaci ɗaya abubuwan da su ka faru a baya su ka fara dawo mata.

Yadda S man ya ja ta, yadda ya hankaɗota waje, ya yi kama da yadda Inna Jummai ta aikatawa Nuriyyah. Kamar yadda S man ya hurgo mata da akwati, haka ta miƙawa Inna bakkon kayan Nuriyyah, Inna ta amsa ta hurga mata a jiki, S man ya ce kada ta sake ta taɓa ƙofar, kamar yadda Inna ta cewa Nuriyyah. Abubuwan sun zo kusan ɗaya.

'Me yasa hakan ya faru da ni kamar na ta?' Faɗin Halima a cikin ranta, hannunta na karkarwa kamar mai tsoro ta ɗauki hoton, riƙewa ta yi a hannunta sannan ta kama akwatinta ta fara ja tana tafiya ba tare da ta san ina za ta je ba.

Ko wani taku idan ta yi zafi take ji a duk inda S man ya lakaɗa mata duka, amma a haka ta daure tana tafiya kamar wata ɓatacciya, wanda hakan ya yi daidai da yadda Nuriyyah ta bar ƙofar gidan cikin ciwo da raɗaɗi, da kuma rashin sanin makama da mafaka. Halima ta ɗan yi nisa kaɗan, kamar a sama ta tsinkayi maganar wasu mutane manya guda biyu. 

Inda ɗayan ya ke cewa, "ai ni na taabbatar da Allah ba ya ya fe haƙƙin wani da wani, na faɗa maka yadda mutanen nan su ka gallazawa bawon Allahn nan, sai ga shi a ƙarshe rayuwarsu ta taɓarɓare" ɗayan ma ya ce, "dama duk wanda ya ce wulaƙanta ɗan adam ne burinsa, to kuwa ba zai taɓa yin nasara ko jin daɗi a rayuwa ba, ai haƙƙi babban abu ne wallahi".  

Wanda ya fara maganar ya sake cewa, "wannan gaskiya ne, ai sai ga shi da su ka gane gaskiya kuma su ke son neman yafiyarsa, shi kuma alokacin ya koma ga ubangijinsa, su ka rasa ya zasu yi ga duniya ta yi musu zafi, suna tunanin yadda za su yi idan suma su ka mutu kuma haƙƙinsa na kansu".
 
Da sauri Halima ta sake datse idonta saboda wani irin abu da ya shigeta, ji ta yi kamar mutanen nan da ita su ke yi, buɗe ido ta yi ta juya tana cigaba da tafiya. A wani dutse ta samu ta zauna ga dare ya yi sosai gari ya yi tsit sai sautin ƙwari kawai ke tashi, take ta ji rugugin iskar hadari a saman kanta, da sauri ta kai idonta sama hakan ya yi daidai da fara sauko da yayyafi. Wato dai wasu daga cikin tarihin abun da ya faru da Nuriyyah shj ne ya ke maimaituwa akan Halima yanzu, ko kuma ince foye da haka.

Tunanin baya ya fara dawowa Halima cikin ƙwaƙwalwa shafi-shafi, tun bayan da Innarta ta auri ABBAN NURIYYAH, abubuwan da take yiwa Nuriyyah, a yi mata sharri ta sa Inna ta jibgeta abanza, abubuwa da dama da ta sha yi mata na musgunawa, amma kuma Nuriyyah ko uppan ba ta ce mata, har bayan rasuwar mahaifiinta izuwa abun da ta yi mata na ƙarshe, ta sa Inna ta koreta. A lokacin ta ji daɗin barin Nuriyyah gidansu, har wani farin ciki ya ke shigarta sosai cikin ranta.

Sulalewa ta yi daga kan dutsen da take zaune zuwa ƙasa, "tabbas haƙƙinta ne, haƙƙin Nuriyyah ne ya kamani!" Ta yi maganar da ƙarfi sannan ta fasa kuka sosai, kuka take yi na nadama, kuka ta ke yi na dana sani, babu jira babu jinkiri tabbas ta gane gaskiya, "me yasa? me yasa na yi hakan?" Abun da ta ke cewa kenan ta sanya hannunta akan wuyanta tana cigaba da kuka.

Kawai kuma sai maganar ɗaya daga cikin mutanen can ya dawo mata, 'ai sai ga shi da su ka gane gaskiya kuma su ke son neman yafiyarsa, shi kuma alokacin ya koma ga ubangijinsa, su ka rasa ya zasu yi ga duniya ta yi musu zafi, suna tunanin yadda za su yi idan suma su ka mutu kuma haƙƙinsa na kansu'.

Girgiza kai Halima ta hau yi kamar taɓaɓɓiya tana cewa, "a ah Nuriyyah ba ta mutu ba, ba za ta mutu ba, ba ta mutu ba, sai na ganta, sai na roƙeta ta yafe min, zan je in nemeta", ta faɗi sannan ta miƙe ta yi saurin ɗago hoton Nuriyyah tana kallo, "kiyafe min, na san na zalumceki, gashi duk abin da na yi miki ya dawo kaina" ta sake ɗaurawa da cewa, "sannan zan je innemi yafiyar Innata, na san wancan ranar na raunana mata zuciya, wai ni mahaifiyata na aikatawa hakan, kaico, kaico duniya, Inna mai sona wacche ta ke kula da ni ta ke ba ni duk abun da na ke so, ita ni na yi wa haka, ki yafe min Inna don Allah".

Ruwan da ta ga ya ɗiga akan hoton ne yasa da sauri tasa hannu ta goge tana kuka, tana cewa ba abun da ya samu Nuriyyah, buɗe ƙaramin zip ɗin akwatin ta yi, ta fito da leda baƙi, ta sanya hoton a ciki ta ƙulle ba tare da ta tsaya da kukan ba, kawai ta ji saukar ruwan samma mai ƙarfi akanta, gashi ba inda za ta fake, a haka dai ta cigaba da tafiya tana cewa sai ta gano Nuriyyah ta ba ta haƙuri, sannan za ta je gurin Inna ta nemi yafiyarta.

Ko ɗaukar akwatinta ma ba ta yi ba, ga zafin dukan da S man ya yi mata, ga ruwan sama da ke sake jibgarta, sannan ga abubuwan da ke yawo a ƙwaƙwalwarta, sai kuma wani yanayi da ta fara jin cikinta na yi mata, a ƙarshe dai jiri ya fara ɗibanta ta zube ƙasa a sume........

S MAN.

Babu abun da ya dameshi don ya kori Halima, dama ƙaramin abu ne a wurinsa. Yana zaune ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, ya ji wayarsa ta fara ruri, ba tare da ya sauya daga zaman da ya yi ba ya ɗaga wayar.

"Helo Bassi ya aka yi ne?" Cewar S man, Bassi ya ce, "oga ka gama aiwatar da ƙaramar furen nan ne?" "Na gama da ita, ya kayan nan ne na ji ku shiru ba ku tafi ba ne?" Bassi ya ce, "oga matsala aka samu, wasu matsiyata sun kame mana kayan". Sai da S man ya ja tsaki sannan ya ce, "gobe zan shirya inje, in ta kama har Lagos ɗin ma zan je to zani, abun da na ke so da kai ka maida hankali akan wa'yan da ke gabanka kana ji na?", "to oga S man angama" cewar Bassi, daga haka S man ya ijje wayar yana kuma jan tsaki.

WASHE GARI ASABAR.

NURIYYAH.

Tafiya nake yi zuwa sashin Hajiya Kaka, saboda ance min tana kirana, amma fa sai da na ga fitar Abba sannan, domin har yanzu ba na bari mu haɗu da shi, ko ya kirani a waya bana amsawa, wai ni kunyarsa nake ji har yanzu.

"Buum!" Aka yi min ƙarar ta baya, hakan yasa na ji tsoro, sakin ihu na yi ina faɗin, "Inna lillillahi, Momy!' Na faɗi haɗi da rintse idona. Dariya da Abba ya fara yi ne yasa ni a hankali na buɗe ɗayar idona cike da mamaki, ko da ganin shi ɗin ne sai na ƙarasa buɗe ɗayan ma a hankali. Zuba masa na mujiya na yi ganin yadda yake dariya sosai, lokaci ɗaya na haɗe rai da fiska, saboda abun da ya min ya ɓata min rai sosai, taya zai tsoratar da ni har yanzu zuciyata ba ta lafa ba, sannan kuma ya yi ta min dariya haka saboda mugunta?.

"Nuriyyah...." Abba ya faɗa à hankali dariyar fiskarsa na gushewa, ya tsaya yana kallona.


Last page
___________________________________________________


Toh ga dai Halima nan, wuya ya ci ta ta gane gaskiya, shin kun ji tausayinta? Ga ta ta suma, Shin maganin da S man ya ba ta ne? Ko kuwa wani abun? Shin sumewar tashi ne? Ko na ƙarshen rayuwa?

Ga Nuriyyah da Abba, anya ba shi yasa akirata asufa Hajiya Kaka ba? To ranta dai ya ɓaci, me zai faru a tsakaninsu?.

Mu kasance a next page don jin me zai faru gaba?




_*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_