006
by @gureenjoh
SAFARA A TAƁO
FATIMA MUHAMMAD GURIN
*GUREENJOH*
*ADABI WRITERS ASSOCIATION*
*PAID BOOK*
*006*
Da ƙarfi ta ji an jijjigata wani hannu kuma ya rufe mata busasssun lips ɗinta, sai ta shiga ji ana kiran sunanta cikin sanyi da kulawa.
"Hibbah! Hibbah Mafarki kike...Babu wani Mahmud a kusa da ke, buɗe idanunki ki ji ni"
Numfashi take saukewa a hankali, kan ta buɗe idanun ganin ɗakin asibiti da kuma fuskan likitan da ba za ta iya tuna sunanshi ba ya sa ta tabbatar da mafarki ne kawai abubuwan da suka haɗe mata da irin kaunar da suka shimfida da Mahmud suka sa shaidan ke mata wasa da hankali, a hankali ta sake lumshe idanu tana ɗan muskutawa, chan ta ce
"Don Allah ƙarfe nawa?"
A ɗan hankali tayi maganan tuna akwai Sallar Magrib da isha a kanta don ta ga garin yayi duhu sossai da shiru alamun dare ya fara nisa.
Wayanshi ya ɗan matsa ya ɗago ya kalleta
"ƙarfe biyu na dare"
Ta ɗan buɗe idanun da har lokacin suke mata nauyi tace cikin Muryar mara ƙarfi
"Ni kaɗai ce ko?"
Numfashi ya sauƙe don kila tana tunanin yadda za ta kai kanta bayi ne tayi alwala kuma a wannan karo da gayya ya hana kowa zama da ita ba don komai ba sai don ta samu natsuwar zuciya da yake tunanin ta gaza samu daga kowa a zuri'arta, wani ko wata za su iya ganin abin da ya sameta da sauƙi amma macen da ta san kanta da mutuncinta kuma ta fita gidan tarbiya dole ta shiga makamancin halin da ta shiga a yanzu.
"Hibbah...!"
Ta kalleshi kaɗan ta kawar da kai don ita kanta kunyar kanta take a wannan yanayi da take ciki na fitar hayyaci.
"Za ki iya cewa ina ruwana ko kuma me ya dameni da damuwar ki amma fa akwai ɗin, ni likitan ki ne kuma zan so miki samun lafiya da fita daga barazanar ciwon dake shirin shigo miki da ƙarfi. Ina so ki ba ni hankalinki na mintuna ki kuma saurari abin da zan fada miki"
Pale eyes ɗinta ta zuba mishi ba tare da ta ce komai ba
"kowa na kuskure amma kar ki kuskura ki bari wannan kuskure ya bi ki har ƙarshen rayuwarki, ba zama nagari ke hana kuskure ba, kuma babu son zuciya a kuskure rayuwa ce ke koyar da darasinta ta wannan hanyar. Hibbah Madaki rashin kuskure baya taɓa gina mutum, darasin dake ciki shi ya kamata ya zama miki tushe da tubalin gina wata rayuwar. Kar ki taɓa tsanar kan ki saboda kuskurenki ki daina hukunta kanki ki ɗauke shi abin da ya wuce sai ki ga kin samu wata babbar damar ta gyara"
Sossai kalaman ke samun matsuguni a ranta tana jin su tamkar wani magani dake watsakar da tarin damuwarta.
Bai tsagaita ba ganin yadda jikinta ke sanyi ya cigaba
"Na tabbatar bayan ahalinki kina fuskantar barazana daga mutanen dake zagaye da rayuwarki especially social media da suka mayar da kalmar "Update" wani abin burgewa suke faɗin abin da alfahari da dariya a kan fuskokin su ba tare da sun san irin makomar da hakan kan zame musu ba saboda Allah bai bamu damar yi wa ƙaddarar wani dariya ba, annabi da ya nuna harshe sai yayi mana gargadi a kanta da Kuffa alaika haza don tabbas harshe na iya kai mutum ga wuta. Ina so ki sani duk irin kyau ko mugun halinki mutane za su yi magana amma wallahi No one owes you an explanation, any irresponsible person can judge by what they see without thinking twice saboda tsadar damar hankali da tunani da suka gaza samu"
Ya isa dab da ita har tana iya shakar kamshin turarenshi cikin taushin murya yace
"Wallahi sau dayawa akuyar da ta hau kan katanga ita duniya ke gani baki san komai ba a kan irin rayuwar da mutane ke yi wasu dayawa suna nan dankare da kashi a karkashinsu amma suna yiwa wani dariya. You have to flight this situation and do what is right for yourself not to please anybody don daga zarar kika yanke hukunci don burge wani ko saisaita wani bayan Allah daga sannan kuma rayuwarki ya gama tabarbarewa."
Murmushi ya saki cike da taushi irin na kwararren likitan da ya san aikinshi, a hankali ta ɗan yi murmushi wanda zata iya cewa rabon ma da tayi irinshi tunda Sagir ya fara mata barazana yana amsar duk wani abin da ta tara don fansar abinda daga karshe bai fansu ba tunda gashinan a duniya.
"Thank you"
Ta faɗa chan ƙasa, ya gyaɗa kai sai ya juya ya fita.
Ba'a jima da fitanshi ba sai ga wata Nurse mace ta shigo ta taimaketa zuwa bayi bayan tayi tsarki tayi alwala ta fito ita ta kawo mata hijabi da sallaya ta zauna a zaune ta rama sallolinta tana idarwa ya shigo hannunshi riƙe da mug ya miƙa mata, ba musu ta karɓa harda cake da ya haɗa kuma ta shiga ci a hankali har ta ji ya isheta ta sake mishi godiya don yana zaune ne yana azkar rike da counter, sai da ya ga ta kwanta kan yayi mata sai da safe ya fice, bata tsaya dogon tunani ba bacci yayi awon gaba da ita.
Ko da ta tashi da safe misalin ƙarfe bakwai bayan ta koma da tayi sallah jikin sossai ya sake ta, nauyin da zuciyarta yayi mata ainun ya rage haka take jinta kaman bata da wani damuwa saboda ta riga ta karɓi kuskurenta kuma ta shirya gyarawa, da kanta ta shiga toilet ɗin ta ɗan wanke bakinta da fuskarta ta fito, tana fitowa ana turo kofan ɗakin Dr Najeeb ne bayanshi wata babbar macece sai wata budurwa da zasu iya yin sa'anni suka shigo.
Fuska a sake ta gaishe shi
"Ina kwana Dr.?"
Yana murmushi ya furta
"Masha Allah! Jiki yayi kyau Hibbatu. Kin tashi lafiya?"
Ta gyaɗa kai kan ta dubi matar tana ɗan duƙawa tace
"Ina kwana?"
"Lafiya ƙalau Hibbah ya jikin dai?"
Tace
"Alhamdulillah da sauƙi. Ga wurin zama"
Tayi maganan tana nunawa matar mai cike da fara'a kujera ta kuwa zauna, yarinyar da suka shigo da ita ma tayi mata sannu ta amsa.
"Ummana ce, dama dai ana ji da ni da duk na kwana a asibiti kuma zan kai rana sai an turo min abin kari da nace ta haɗa da ke shine tace bari ta zo da kanta ta samu ladar duba marar lafiya"
Murmushi kuwa tayi
"Sannu Umma mun gode sossai Allah ya ba da lada"
Murmushi Umman tayi
"Ameen ɗiyata. Nihla saka mata abinci ta samu ta ci ko zata ƙara jin karfin jikin"
Yarinyar da ta kira da Nihla ta shiga zuba mata kuwa, farar shinkafa ce da kidney sauce sai kunun gyaɗa babu musu ta amsa ta shiga ci a hankali daidai sallamar su Aunty Kubra, Zaitoon, Ya Nasir da Momma.
Sai da ta nemi ƙwarewa ganin Momma a asibitin, a hankali ta ajiye spoon ɗin kanta ƙasa Aunty Kubra ke furta
"Masha Allah! Barkanmu jiki ya fara kyau sannu Hibbah"
Kai ta gyaɗa tana furta
"Ina kwana?"
"Lafiya ƙalau Alhamdulillah, baki ganmu da wuri ba sai da muka ajiye su Asiya a airport ne ya karfin jikin?"
Ta amsa da Alhamdulillah.
Ta ɗan dubi Momma kan ta gaisheta da mamakin ta kuma ta ji ta amsa har tana karawa da ya jiki ta amsa da sauƙi a hankali.
Duk zama suka yi suka shiga gaisawa da Umman Dr. Najeeb har godiya suka yi mata kan ta miƙe tana yi musu sai anjima ta fice.
Zaitoon ta zauna a gefen ta tana ƙara sakata cin abincin da ta koma ci a hankali ganin mommansu a ɗakin sai taji kaman wata bakuwar ce ta daban ba mahaifiyarta ba, Sun jima sossai har ta gama cin abincin suna hira Dukda daga Nasir, Zaitoon da Aunty Kubra ne ke involving ɗinta shima sama sama take amsawa.
Bayan fitansu daga ɗakin Nihla ta kalli Dr. najeeb tana furta
"Ya Njeeb ba wannan ce yarinyar da media ta ɗauki magana..."
Kallon da yayi mata ya sa tayi shiru Umma da tun suka fara zancen a gida da sauran ƙannenta biyu mata ta kwaɓe su kuma tausayin iyaye da ita kanta Hibbahn ne ya rufeta don har cikin sallah ta saka ta a Adu'a, ta harareta
"Wallahi ku kiyaye yamaɗiɗi da kuma dariya da ƙaddarar wani ba fata ba amma babu wanda ya san inda rana zata faɗi..."
"Umma ki yi haƙuri"
Ta girgiza kai tana cigaba da yi mata nasiha har ya raka su mota ya koma office.
****
Kaman yadda kowasu Amare ke tafiyar da dararensu na farko gidan miji haka ta ɓangaren Amal da Hudah ya tafi don sun sha soyayya da kauna ba ƙarya tare da alkawarurrukan da babu wanda zai san da tabbatar cikinsu ko akasin hakan bayan Mahalicci.
Ko da gari ya waye Mu'azzam shi ya taimakawa Hudah ta sake kintsa gidan, bayan sun gama suka nufi sashen Hajiya don kai mata gaisuwa suka sameta zaune da falmata suna shan ruwan bunu ganinsu ya sa hajiyar ta gyara zama suka duƙa ƙasa suka shiga gaisheta cikin girmamawa
"Muna ta zuba idon abin kari kuma shiru?"
Ta jefa tambayar ga Mu'azzam, ba shi kadai ba har Hudah sai da ta ɗago ta kalleta ganin sun hada ido ya sa tayi ƙasa da kai.
"Ban gane kuna kallona ba? Yanzu a tunaninka da tsufana da komai kana da mata sai na shiga kicin na yi girki? Idan ma bata zo da babban tukunya bane to ta zo na bata aron shi don girki dai yanzu ba za mu sake yi a wannan sashe ba"
Ya ɗan sosa kai yana furta
"Wai na ce Hajiya ko za'a dan bari ta kwana biyu kan ta fara? Ga falmata ba sai tana yi ba idan ma ta fara ɗin sai su haɗu suna yin bibbiyu"
"ita ta ce maka falmata na zaman banza? Yanzu da ka gantan nan makaranta zata shiyasa take shan wannan bunu, kuma dai wannan aiki ai na me ɗakinka ne tunda itama gidan wani zata ta samu nata ladar"
Ganin zai sake magana Hudah ta ɗan ja gefen riganshi tana ɗan murmushi
"Ki yi haƙuri Hajiya in shaa Allah yanzu zan je sai in yi in kawo"
Bata amsa ba sai taɓe baki da tayi ita kuwa ta miƙe zai bi bayanta hajiyan ta tsayar da shi, tana zuwa kuwa ta shiga kitchen ta hau girki don komai tana da shi na gararta cike a karamar store ɗin nasu, sam zuciyarta ɗaya ta gama ta zube a warmers masu kyau ta kai musu, bata yi mata tayin zama ba itama kuma bata nemi zaman ba don tana so ta sake watsa ruwa ta fice, a takaice bata ga idanun Mu'azzam din ba sai wurin sha biyu da arba'in shima alwalar azahar ya shigo zai wuce masallaci.
**
Ita dai Amal ƴar gata ce saboda komai Alqaseem ne yayi mata a ranar yana cika ta da soyayya yana riritata wane kwai, komai daga kan gado ake mata sai ta ji kanta na sake yin girma, ƙauna da tarin soyayyar Alqaseem ɗin na ƙara mamaye mata zuciya da bargo tana jin ta fi kowace mace sa'a.
***
Kwanan Hibbah biyu a asibitin wannan karo kuma Alhamdulillah har Daddy da kanshi ya zo sau ɗaya, sossai Dr. Najeeb ya tsaya mata kuma yayi mata ƙoƙari wurin ganin ta samu lafiya, haka mahaifiyarshi kan kira a waya ya haɗa su ta gaisheta da jiki mace mai kirki da sanin darajar dan Adam, bai sallame ta ba sai da suka yi alkawarin duk sati biyu za ta ke zuwa asibitin ana duba lafiyarta.
Dukda ba za'a ce ta manta komai ba amma sossai damuwar ya ragu mata kuma idanunta zuwa yanzu suka bushe da zubar da hawaye, ko da ta koma a Washegari Zaitoon dake debe mata kewa suka tarkata suka koma legos abin su, ya saura su ya su a gidan.
A koyaushe tana ɗaki a kwance bata sakewa da ƙannenta bare a kawo zancen ma Fitowar ta zuwa harabar gidan ko hulda da wani ko wata daga waje, tsakaninta da Aina'u gaisuwa tunda ɗaki ɗaya suke haka Momma da Daddy duk za ta sauƙa ta gaida su kan ta dawo ɗaki sai kuma Washegari da safe, ta zube sossai kuma ta yi duhu kaman ba Hibbah sarauniyar gayu ba, kasancewar cimanta ba kaman da ba ya sa ramar ma bai ɓuya ba tana kewan 'yar uwar ta sossai tana so ko muryarta ne ta ji amma tana tsoron karbar aron wayan wani ta kirata.
Yau ya kama Asabar a sashen Daddy ake karyawa don haka Momma da ke da girki da masu aikinta chan suka jere duk wani abu da za'a bukata wanda zai ishe duk ahalin kan ta dawo ta shirya cikin atampharta doguwar riga da ya ji ɗinki tayi ɗaurinta daidai da shekarunta su sarka da abin hannu duk bata bari ba ta fita fess da ita a buzuwarta, sai da ta haɗa kan yaran ta tura su kan ta haura zuwa inda ta san za ta samu Hibbah don ko jiya sai da suka sake tattaunawa da Aunty Kubra akan hankalinta bai kwanta da barin Hibbahn a gidan ba saboda ta san har yanzu suna chusguna mata, ita Momma ta kawo uzuri da cewa sai a hankali zata manta Dukda tabo ne da babu ranar warkewarshi don har meeting ta je cikin last week an yi mata zancen da ya sosa ranta akan hakan. Ta dai yi wa Aunty kubrahn Alkawarin sake sassauta wa don haka da kanta ta tura kofar.
Hibbah dake jingine da gado hannunta riƙe da counter ganinta ya sa ta ɗan zabura ta miƙe zaune da kyau.
"Kin manta yau Asabar ne?"
Sanyi ta ji a ranta don bayan gaisuwa da ya jiki wannan ne karon farko da magana mai tsawon words biyar ya shiga tsakaninsu da momman tun bayan tarwatsa aurenta da Sagir yayi.
"A'a zan sauƙo yanzu"
Kai momman ta gyaɗa tana juyawa ta ce
"Make sure kin yi looking presentable"
Tana kai nan ta fice.
Miƙewa Hibbah ta yi dama ta yi wanka sai ta nemi doguwar rigarta wani simple egyptian Abaya peach ta saka ta saka gyalen ta duba fuskarta a madubi duk ta susuce don haka ta ɗan murza powder tare da saka lip balm ta fito a hankali take tafiya iska na ɗaukarta har ta isa ga sashen na mahaifinsu, da sallama ta shiga kusan kowa ya hallara hakan ya sa ido duk suka dawo kanta musamman su Hajiya Zakiya da Hajiya Kamila da tunda abin nan ya faru basu sanyata a ido ba kuma basu nemeta ba.
"Ina kwana Hajiya?"
"Aw ashe fa kina gidan, ni wlh na ma manta da baki yi aure ba baiwar Allah sannu!"
Momma ta ɗan runtse ido ta buɗe, Daddy zai yi magana Hajiya Zakiya tace
"Ina za ki tuna da ita tunda ta zama matar kulle, ni na zaci ma mahaifiyarta ce ta hanata zuwa gaishemu don bamu kai zama iyaye a gareta ba"
Momma bata ce komai ba kuma dama yaranta da ma mijinta sun san ba lallai ne ta ce ɗin ba idan ba makura suka kaita ba.
Daddy ya ce
"Mamana Meyasa bakya zuwa gaishe su?"
Kanta ƙasa tace
"Kayi haƙuri Daddy, dama ban samu ƙarfin jikin bane amma zan gyara"
Duk sai da suka sake kallonta hatta Daddyn da yayi magana lallai rayuwa mai chanza mutum, ya san da a da ne zata iya tuburewa akan bata yi laifin komai ba ai itace bata da lafiya basu je sun gaisheta ba amma ji yadda take bada haƙuri basu so hakan ba amma dai suka danne, ta zauna kusa da Mumtaz shi ya miƙe yayi serving nata tace thanks a hankali ta shiga wasa da cokalin.
Sun jima sossai a sashen don ko da aka gama cin abinci parlor suka dawo kowa na laying bukatunshi da burin shi na gaba ga Daddyn Dukda ita Momma ta karanci akwai dan abinda ke damunshi har dai duk suka gama suka watse Hibbah bata ce komai ba, sai da ta ji shiru ma ta san an watse ɗin don ta yi zurfi cikin tunani, ta miƙe don fita kenan ta ji Daddy ya kira sunanta..