008
by @gureenjoh
SAFARA A TAƁO
FATIMA MUHAMMAD GURIN
*GUREENJOH*
*ADABI WRITERS ASSOCIATION*
*PAID BOOK*
*008*
"Yaya wai ga chan Amal ta zo da kuka gida wiwi wai an kama maigidanta"
"Mene??"
Daga Daddy Rabi'u har Momma suka faɗa a tare cike da mamaki da kaɗuwa.
"To wai a dalilin mene?"
"Kamilar bata yi min bayanin komai ba wai Amal ɗin ta kasa natsuwa"
Mommah ta saki salati
"innalillahi wainna ilaihi rajiun"
Shawara suka yi za su je gidan su ji me kuma ya faru kwata kwata auren wata biyu kenan an fara zuwa gida kuka da tashin hankali? Tafiya suka yi suka bar Momma na kula da Hibbah.
Ko da isar su gida sun samu har lokacin Amal na a haukace fuskar nan suntum saboda kuka, Hajiya kamila ma ta yi mai isar ta yaranta na gidan aure har sun iso, sun tasa Amal ɗin a gaba ta ƙi magana kiran Daddyn ne ya saka Hajiya kamilar ta saka Amal a gaba suka nufi parlorn na Daddy da har ya ƙira Daddy Z sun iso tare.
Amal na ganin daddy ta fara sabon kuka ya ce ta zo ta zauna gefenshi, nan ta iso ta zauna
"Daddy sun zo sun kama shi sun kuma yi seizing takardun gidanmu"
Ta ƙarasa cikin kuka
"su waye su?"
"Ya ce wai hukumar custom ne don dama ya ce sun riƙe musu kaya, kuma ya tattara kuɗi ya saka ciki har da bashin banki yanzu kayan na chan wurinsu bankin kuma lokacin biya ya yi ba'a biya ba shine suka karɓi takardun gidan. Don Allah Daddy do something"
Daddy Z ya ce
"Would you shut up! Kaman ya yayi wani abu? Me kike tunanin zai yi?"
"Calm down Zubair, ai ba zamu zuba ido komai yayi ta faruwa ba tunda aure ya haɗa. Yanzu a ina suka kaishi?"
"Nima ban sani ba Daddy" ta sake faɗa tana kuka.
Hajiya kamila da ita kam haushin Daddy Rabi'u da Zubair take ji na yadda take ganin kaman su suke hanata rawan gaban hantsi a gidan kuma duk suna goyon bayan Momma a komai a cewar ta don ko suna ganin tana da yara maza ne ta yadda ko Daddy ya mutu za su taya su cin gado ta yi tsulum ta ce
"Ni sai nake ga duka waennan tambayoyi ba ita ya kamata a yiwa ba, ka ga ita amarya ce ko fara zagayen gidajen 'yan uwanshi bata yi ba bare sanin abokanshi ko wani a wurin aikinshi, Daddyn yara a ƙira ko waliyyanshi ne a samu wani abokinshi sai a ji duk bayanan da ya kamata"
Daddy Z yayi kwafa ba tare da ya ce komai ba don shi dama ba son yaron yake ba, kuma tunda Hajiya kamilar ta mishi rashin mutunci akan wai yana bakin ciki Amal zata auri mai kuɗi ne yake so ya hana ya cire kanshi a shirgin auren Daddy ne yayi assigning aka yi binciken, yanzu ma halin ko in kulan ya nuna bai tofa ba har suka gama magana daddy ya ce taje ta bar kukan nan komai zai daidaita in shaa Allah, nan suka fice suka bar su su uku.
"Zubair me kake gani ne? Don wannan dai ɓangarenku ne hukuma"
Murmushi yayi
"Yaya ai kuma kuna iya damawa duk ɓangarorin, duk kuma abin da kuka yanke sai a yi"
Ya zame kanshi, Daddy yayi murmushi don ya fahimta.
"Shikenan zan ƙira shi mahaifin nashi yanzu sai in ji duk yadda komai ya kasance. Allah ya sa muna da abin da zamu iya yi"
Suka amsa da Ameen, sun tattauna kadan kan suka watse.
****
"Hudah!"
Mu'azzam ya shigo sashen yana kiran sunanta.
Tana daga kitchen tana haɗa abincin rana ya sameta
"Me ya faru ne? Hajiya ke cewa kin gaya mata magana ko mene? Sannan nayi ta kiran layinki bakya picking Allah ma ya sa na ƙira hajiyar ta ce min kin dawo tuni"
Numfashi ta sauƙe tace
"Eh na dawo, ina school ɗin Hibbah ta shigo to sai kuma ta samu attack na ciwonta muka tafi asibiti a ruɗe duk na sha'afa ban kira ka ba don har Daddy ya sa aka dawo da ni ma bata farka ba."
Fuskarshi ba yabo ba fallasa yace
"Hibbah Againn! Toh Allah ya bata lafiya"
Ta amsa da Ameen.
"Ka duba abu a wardrobe ɗina ne?"
Tayi tambayar tana cigaba da soya kayan miyan dake kan wuta.
"A'a me ya faru?"
"Shikenan"
Ta faɗa ba tare da ta kalleshi ba, har ya juya zai fita ya dawo.
"Hudah na sanki da biyayya da kuma sanin ya kamata don Allah bana son kawo karar nan da Hajiya take yawan yi akan ki, kinga ita uwa ce kuma shekaru ya ja sai ana yi ana haƙuri da su"
Karo na farko kenan da ta ji wani irin haushi na taso mata akan lamarin hajiyar, dannewa tayi tace
"In shaa Allah"
Ya fice, aikin ta cigaba da yi tana tunanin rayuwarta a gidan tare da suruka da kuma ƙanwar miji har ta gama girkin ta saka a kula ta kai musu nasu ta jera nata a parlor ta nufi ɗakinta don ƙiran Momma ta ji jikin 'yar uwarta.
****
Alhamdulillah ko da Hibbah ta farka bata farka da kukan ko damuwa ba, Momma ta taimaka mata ta wanke baki tare da alwala ta zo tayi sallah kan Momma ta zuba mata abinci har lokacin Mumtaz na nan sai sannu yake mata kuma ta ji daaɗin kulawar tasu, ta ci abincin ba laifi kan Mumtaz ya je ya sanar akan ta farka bai jima da dawowa ba sai ga Dr. Najeeb da wasu nurses biyu.
Fita suka yi don a duba ta, ya dubeta
"Kin karya min alƙawari"
Ta ɗan yi murmushin yake
"Alkawarin da ban san na ɗauka ba?"
"Eh ke baki sani ba amma ni na daukarwa kaina cewar ba za ki sake kwana da damuwar komai ba kuma da yardar Allah sai gashi kin karya min shi."
Ta ce
"Hmmm"
"Da kamar wuya ko? Yanzu ina ne ke miki ciwo?"
Ta girgiza kai
"Babu kawai zuciyata ce bata yi mini daaɗi"
"Za ma tayi in shaa Allah, kin san babu abin da ya fi ƙarfin Allah ko?"
Ta gyaɗa kai yace
"Toh oya ga wayana buɗe qur'ani ki karanta shine abincin ruhi kuma kina gamawa tabbas zuciyarki zata yi daaɗi"
Nurses ɗin sai mamaki suke ganin yadda suke hirarsu su biyu shi kam ma ya manta dasu, shi da bashi da yawan magana sai wasa idan yayi ra'ayi ga addini da ya samu daidai gwargwado kuma shine kan gaba a komai nashi.
Babu musu ta karɓi wayan, ya kalli nurses ɗin yace
"Patient ɗin mu bata bukatar wata allura ko ruwa a yanzu mu dan bata lokaci"
Fita suka yi, shi kuma ya ja kujera ya zauna yana kallonta tayi bismillah tana karatun ba da ƙarfi chan ba a hankali take yi sautin na fita kaɗan kaɗan ya ɗan lumshe ido ya buɗe a kanta har tayi ayoyi goma na farkon suratul yunus da ta chanka, sai ta sauƙe numfashi ta ɗago suka haɗa idanu a hankali ta mayar da kanta ta ƙara biyar kan tayi sadakallahu azeem ta miƙa mishi ya ce
"Masha Allah! Ƙanwata ashe Malama ce"
Ta ɗan yi murmushi
"Ɗaliba dai"
"A haka ɗin? Ko dai kin san gwanaye basa faɗa"
"Ai ban isa zama gwana ba sai dai Gwangwani"
Dariya yayi jin abin da tace.
"Alhamdulillah na ji daaɗi da baki bari kuncin rai yayi overtaking yanayinki ba, Dukda na san akwai shi a chan ƙasan rai"
"kaman yadda ka faɗa abincin ruhin nan da ka bani yayi aiki ƙwarai nima kuma bana son ganin iyayena da 'yan uwana a damuwa ta dalilina. Wannan attack da na samu ma akasi ne don na san kaman yadda ya tuna min da abin da ya faru suma kuma ya tuna musu wanda ko a fuska suka nuna hakan ba zai min daaɗi ba"
Kai ya gyaɗa
"Haka ne, Allah ya yaye ya baki lafiya amma please ki koyi shanye maganganun mutane, don dole za su yi kar kuma ki ce za ki dinga rufe kanki a ɗaki kina tunani be the Energetic and strong Hibbah"
Murmushi tayi Tana godiya ya juya ya fice, Momma da Mumtaz suka dawo.
Anan Mumtaz ya kira Nasir ya bata yayi mata ya jiki, Momma ma Aunty Kubra ta kira don sun dameta da kira ta ba Hibbar itama ta yi mata ya jiki da wani nasihar haka su Aunty Asiya duk sun yiyyi waya kan Hudah a karshe.
"Twiny kiyi haƙuri Daddy ya kora ni baki farka ba"
Ta Yi murmushi
"Ai ya yi daidai ina Amarya ina zaman asibiti, na dai ji ba daaɗi bamu ko yi magana ba"
"Zan roƙi Mu'azzam ya kawo ni mu yini churr muna hirar da muka kwana biyu bamu yi ba"
"Toh Allah ya sa ya bari da kuwa na ji daaɗi, musamman zan girka miki favorite ɗinki"
Hudah ta kwashe da dariya Momma da Mumtaz na taya ta sai Hibbah ta Shagwaɓe fuska
"A ke ɗin? Wacce ta tsani girki?? Lallai da kuwa an yi ruwa da ƙanƙara"
"Zan kuwa baki mamaki Allah"
"Ki ba wanda bai sanki ba dai"
Haka suka yi ta hira karshe Momma ta kwace wayarta.
Da yammacin aka sallameta don ta sake fiye ma da yadda suka zata, ya dai tabbatar mata bayan kwana bakwai ta dawo nan suka tarkata suka yi gida.
*****
Abinci ne a gabanshi sai dai ba ci yake ba bayan wasa da spoon ɗin da yake ta yi a ciki, hankalinshi tuni ya yi nisa har bai ji Shigowar Ummanshi madaidaicin parlorn mai ɗauke da kaya masu kyau da tsari daidai ba sai da ta ɗan taɓa kafadanshi tana zama.
"Najeeb lafiya kake kuwa? Me ya faru?"
Ya girgiza kai
"Babu Umma, gidan naki shiru ina 'yan matanki?"
"Sun tafi makaranta. Ka dai san ba zan amince cewa komai lafiya ba ko? Ka ga nisan da kayi a tunani? Har fa na shigo parlorn nan baka sani ba Najeebu menene?"
Shiru ya yi ta gyara zamanta a hankali ta cigaba da cewa
"A iya sanina baka da wacce ta fi ni kaman yadda nima ba ni da wanda ya fi ka Najeeb, idan kana cikin matsala kaman dukkanmu muna ciki ne don kai ne komai namu a gidan nan duk abin da zai same ka kaman mu ne zai sama don haka ka faɗa min matsalar sai mu shawara a tsakaninmu mu kuma roki Allah mafita"
Idanunshi da suke yanayi da nata ya ɗago ya ɗan kalleta yana tankwashe kafa ya ce
"Umma aure ne nake so in yi amma ina tsoron amincewarki"
Ta ɗan zaro ido
"Me zai hana ni amincewa Najeeb? Ko kana tunanin zan hanaka ne saboda ɗawainiyarmu da na Ƙannenka dake kanka? Wallahi ko daya zan so ka yi, shawarar dai da zan baka shine ka samo 'yar gidan mutunci kuma masu rufin asiri da zata iya haƙuri da kai a kowani yanayi, na san hidima na yi maka yawa ƙwarai da gaske amma don ƙarin mace ɗaya cikin rayuwarmu ba komai ba ne."
Kanshi ya shafa yana sauƙe ajiyar zuciya.
"Umma ai na samu matar"
"Toh fa! Abin ashe na wuri ne ka ce mu fara shiri. Wacece?"
Tayi maganan da wasa fuskarta ɗauke da murmushi
"Umma Hibbah ce nake So! Wannan yarinyar da kika duba a asibiti, wacce aka fasa aurenta watanni biyu baya"
Ɗan shiru ta yi kan ta ce
"Ka tabbatar kana sonta Najeeb? Ko dai tausayinta kake? Ba zan taɓa baka shawarar ka aureta saboda kana tausayinta ba don idan saboda hakan ne babu inda alaƙar taku zai tafi Dukda na san ana gina so daga tausayi, idan don ibtila'in da ya sameta ne zai wuce don abu sai dai idan bai faru ba yau da gobe sai Allah duk kowa zai manta, zata cigaba da rayuwarta kuma ta nema wa kanta farin ciki."
"Umma wallahi ina sonta har cikin raina, sam tausayi ba shine ya gina min soyayyarta ba na ji ina sonta tun kan in san me ya sameta, sanin me ya sametan kuma bai sa na ji zuciyata ta sauya ba sai ma gaba da take yi, zan iya cewa a 'yar zaman da take yi asibiti na fahimci kyawawan hallayarta, natsuwarta da ma mutuncin gidansu Dukda miliyoyi a yanzu na kallonsu marasa mutuncin amma a idona daban nake kallo saboda ba zan taɓa hukunta ta ko iyayenta bisa kuskuren da ya faru a rayuwarta ba"
Numfashi Umman ta sauƙe a hankali tace
"Shikenan, in shaa Allahu Idan Abban naku ya shigo sai in sanar mishi amma baka ganin ta fi karfinka Najeeb?"
Dariya ya ɗan yi marar sauti
"Dariya ma na baka? Wannan yarinyar fa mahaifinta mai kuɗi ne, ita ɗin 'yar gata ce gaba da baya zaka iya da bukatunta? Ko zata amince ta aureka alhali ta san sun fi mu ta kowani ɓangare?"
"Umma babu abin da suka fi mu, yadda suke ci su sha mu ma nan muna ci kuma mu sha haka bukatu babu wanda bama saukewa daidai gwargwado bare ma na gamu da mahaifinta mutumin kirki ne da duniya bata dameshi ba"
Ta dai yi shiru ba kuma don wai tana ƙin Hibbah ba sai don tunanin tazarar matsayin su, Dukda Alhamdulillah sun kasance cikin masu rufin asiri don ci sha da sutura bai gagare su ba, Abban su Najeeb tsohon ma'aikacin gomnati ne da yayi retire sai pansho da yake karɓa, a lokacin da yake aikin ne ya tsayawa Najeeb ya yi karatu kasancewar shi mai hazaƙa da son yin Allah ya taimaka yana jamb a SS3 ya zama hightest scorer a gabaɗaya Kano inda ya samu scholarship ta dalilin wannan ya tafi china ya karanci fannin likitanci, shima bai zauna ba don yana karatun ne yana duk sana'ar da ya samu su kan taimaki juna idan yana takure bashi dashi Abban ne zai kurkurda ya tura masa haka shima idan ya samu bai taɓa mantawa da su ba zai turo.
Tunda ya tafi bai waiwayi gida ba saboda scholarship ɗin babu batun zuwa gida idan zaka je sai dai idan kaine zaka yi kudin jirgi ka je ka dawo don haka ya zauna shekara shidda churr sai da ya zama cikakke kuma kwararren likita a fannoni da dama kan ya dawo, ko da ya dawo bai sha wahala sossai wurin samun aiki ba saboda kwazonshi nan ya karɓi ragamar kula da su, kannenshi duk suna makaranta a yanzu haka ga ɗawainiyar gidan.
Miƙewa yayi da tray ɗin abincin ya fita zuwa kitchen ɗinsu dake tsakar gidan ya ajiye kan ya dawo parlorn ya ɗauki wayanshi ya fita zuwa ɗakinshi dake ta mashigar gidan jikin madaidaicin gate ɗin nasu wanda haɗe yake ciki falle ɗaya mai girma da toilet ciki, komai na ɗakin neat and clean saboda tsaftarshi sannan yadda aka tsara ɗakin ma yayi kyau sossai Dukda ba kayan alatu aka zuba masa ba a kan katuwar katifarshi mai tudu sossai da ya sha shimfida ya kai kwance yana kallon saman ɗakin cike da tunanin y ta yadda zai fuskanci Hibbah, yana da tarin abubuwa da yake son ji daga gareta amma yana ga gwara ya bi komai sannu a hankali har ya cimma nasarar saninta sossai.
Najeeb bai yi ƙasa a gwiwa ba ya cigaba da bi da ita ta dabara yana nuna mata kulawa yana janta da hira da wasa, tun bata wani sakewa har ta zo ta fara sakewa dashi sossai kasancewar bata da wani abokin hira, babu wayanta kuma bata zuwa ko ina sai ya zamana tana tattauna wasu abubuwan da shi matsayin friend ɗinta.
Hajiya kamila fitina sossai ta tayar wa Daddy saboda damuwan Amal, har gani suke wai bakin ciki ake yi mata da samun miji irin Alqaseem shine aka je aka yi masa asiri don ya rasa dukiyar shi gabaɗaya, shi kuma Daddy yana goyon bayan hakan tunda yana da yadda zai yi ya gagara Amal har da ciwo, dole Daddy ya nemo mahaifin Alqaseem ɗin don jin abin da ke faruwa.
Ko da suka zauna dattijon ya ce mishi ai Alqaseem ɗin na legos har yanzu amma komai ya kamalla na chuku-chukun sakeshi suna tsammanin ma a sabuwar wata zai dawo.
Daddy yayi adu'a da Fatan kiyaye gaba kan suka rabu da dattijon, Hajiya kamila da fitan mutumin ya sa tayi zuruf ta fito daddy ya kalla
"Hankalinki ya kwanta ai ko? Toh sai ki kyaleni na sha iska"
Fuuuu ta wuce kaman iska ya bita da kallo yana girgiza kai.
A tsakar gidan ta gamu da Hibbah da dawowarta asibiti kenan, sanye da hijab har ƙasa da yanzu da su take fita ta ƙura mata idanu har Hibbahn ta zo zata wuce tace
"Aniyar moɗa dai sai dai ta bi randa ki kaiwa tsohuwarki saƙon cewa duk malaman buzayen da ake bi sai an sake shiri. Ta ji da rufa rufan cikin da kuke ta yi ta kyalemin yarinya ta sha iska a gidan mijinta..."
Hibbah bata yi magana ba ta raɓata don wucewa Mujiba ta fusgo hijabinta har wuyanta na shaƙe wa, tana waigowa ganin Mujiba ce bata yi wata wata ba ta zabga mata mari idanunta na rinewa a take ihuuu mai ƙarfi da Mujiba ta kwala shi ya janyo hankalin jama'ar gidan tuni aka fara fitowa.